Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Waƙoƙin Bara Na Ƙarni Na Ashrin Da Ɗaya A zamfara



Wannan aikin bincike mai take “Nazarin Waƙoƙin Bara na Ƙarni na Ashrin da Ɗaya a Zamfara” ya fuskanci nazari ne a kan waƙoƙin da mabarata ke bara da su don su sami sadaka daga jama’a. Wannan aikin bincike ya nazarci sigogi da falsafar waɗannan waƙoƙi domin bambance tsakaninsu da wasu waƙoƙin da ba su ba. Waƙa wata muhimmiyar hikima ce wadda ɗan adam ya ba ƙima ta...

A Thesis Submitted to the Postgraduate School
USMANU ƊANFODIYO UNIVERSITY, SOKOTO, NIGERIA.
In partial fulfilment of the Requirements for The Award of The Degree of
Ph. D. Hausa.

 By
HARUNA UMAR BUNGUƊU

DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES

TSAKURE
Wannan aikin bincike mai take “Nazarin Waƙoƙin Bara na Ƙarni na Ashrin da Ɗaya a Zamfara” ya fuskanci nazari ne a kan waƙoƙin da mabarata ke bara da su don su sami sadaka daga jama’a. Wannan aikin bincike ya nazarci sigogi da falsafar waɗannan waƙoƙi domin bambance tsakaninsu da wasu waƙoƙin da ba su ba. Waƙa wata muhimmiyar hikima ce wadda ɗan adam ya ba ƙima ta musamman fiye da sauran wasu maganganu, duk abin da aka waƙe Hausawa kan saurari waƙar don su ji abubuwan da ta ƙunsa don su yi aiki da su, ko kuma ma su ji daɗi su sami nishaɗi. Wannan aikin ya dubi jigogin waƙoƙin bara kasancewar sun sha bamban da sauran waƙoƙi kamar yadda aikin ya nuna. Wani shehun malami na faɗin “Salo asirin waƙa”, domin salon ne ke mayar da waƙa yadda ya dace ta zama idan ba shi to ba waƙar. A wannan aiki/ kundi na duba irin salailan waƙoƙin bara waɗanda almajirai suke amfani da su wajen bara a yankin nazarin wato Zamfara. Haka ma aikin ya dubi tasirin waƙoƙin a kan masu saurarensu ta fuskar zaburar da su wajen  bayar da sadaka.
ABSTRACT
This thesis titled “Nazarin Waƙoƙin Bara na Ƙarni na Ashirin da Ɗaya a Zamfara” focusses on the types of songs that beggars employ in their begging for alms from people. This thesis studied the stucture and philosophy of these songs for the purpose of differentiating ‘waƙoƙin bara’ from other types of waƙoƙi. Song is an important aspect of art which is regarded much more as important than other aspects of human discourse. Whatever is in a song the Hausa people listen to it for the message it contains or for entertainment. This is so with the act of begging. Beggars in Zamfara use different types of songs (oral and written) when begging for alms from people. This thesis mainly focussed on the themes of ‘waƙoƙin bara’ for they stand different from other types of ‘waƙoƙi’ as presented in the work. A scholar has once said ‘Salo asirin waƙa’ meaning style is a secret behind all songs. This shows that it is style that makes a song what it is; without style, there is no song. This work also examined the different types of style, such as Theme style, Philosophy, etc that beggars employ in their art in Zamfara. Also, the effect of these songs on their listeners (which motivates them to give alms) were presented.  



Post a Comment

0 Comments