Ticker

6/recent/ticker-posts

Nason Gargajiyar Bahaushe A Cikin Magungunan Musulunci



Allah maɗaukakin Sarki ya halicci mutum, ya kuma hore masa lafiyar da yake amfani da ita wajen fantamawa a harkokinsa na yau da kullum, shi kuma ke ƙaddara cuta bayan ya tanadi maganinta. Akwai nau’o’in magunguna daban – daban waɗanda Hausawa suke amfani da su...

                                                           
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
Ƙibɗau:harunaumarbungudu@gmail.com
Lambar waya: 08065429369

Da
Bashir Aliyu Tsafe
Lambar waya: 08066785802
                                                                       
Tsakure.
Allah maɗaukakin Sarki ya halicci mutum, ya kuma hore masa lafiyar da yake amfani da ita wajen fantamawa a harkokinsa na yau da kullum, shi kuma ke ƙaddara cuta bayan ya tanadi maganinta. Akwai nau’o’in magunguna daban – daban waɗanda Hausawa suke amfani da su, waɗanda ko suka tanada da kansu, ko kuma suka nema daga wani. Akwai wasu nau’o’in magunguna da Hausawan suke amfani da su tun asali kafin shigowar addinin Musulunci a ƙasar Hausa waɗanda ga jama’a suke samunsu, kuma ana aiwatar da su a gargajiyance. Su kuma wasu magungunan sai bayan shigowar addinin ce aka same su, ko kuma a ce addinin ne ya samar da su, tare da bayanan yadda ake amfani da su. Wannan takarda ta lura cewa akwai nason gargajiyar Hausawa a cikin magungun addinin Musuluncin ta hanyoyi da dama, don haka za ta fito da ire – iren nason gargajiyar a cikinsu. Yaya magungunan gargajiyar suke? Yaya magungunan addinin Musulunci suke? Yaya hanyar jirgi ta haɗu da ta mota a waɗannan nau’o’in magunguna? Idan an karanta wannan muƙala za a sami bayanai masu inganci da kwarjini.  
1.0     GABATARWA
Allah (S.W.T) Ya yi halittu daban-daban kuma Shi ke sarrafa komai da kowa da dukkanin abubuwan halitta masu rai da waɗanda ba su da rai, kamar Mala’iku da Aljannu da Mutane da sauran dabbobi. Kuma Allah mahalicci  a bisa hikimarsa Ya yi halitta mabambanta ta fuskar launi da kuma ƙabila (Suratul Hujrat:12).
Kamar yadda Allah (S.W) Ya yi halittu haka kuma ya ƙagi cututtuka masu tarin yawa ya watsa su tare da su, kuma ya sanya kowace cuta tana da magani sai dai mutuwa da tsufa ne kaɗai ba su da magani, kamar yadda manzon Allah ya faɗa (Bukari littafi na farko shafi: 602). A dalilin cututtukan da ke addabar mutane tun a lokacin da aka fara halitta ya sanya su kuma mutane suka duƙufa wajen neman magani ko magungunan cututtukan da suka dame su, kuma haka ya wanzar da samun waɗansu daga cikin mutanen sun ɗauki hidimar ta kasance abin da suka sa a gaba a zamansu na duniya har ma suka ɗauke ta hanyar neman abincinsu tun a farkon lokaci har zuwa yau.
1.0.1   Ma’anar Gargajiyar Bahaushe
            Kalmar gargajiya kalma ce da ta samo asali daga gado ne aka samu gadajje da gargajiya. Kalmar gargajiya ta yi ƙauri musamman idan aka ce gargajiyar Bahaushe da ke takin saƙa da kyawawan aƙidun musulunci. (Bunza, 2006)
1.0.2   Ma’anar Magungunan Gargajiya
          Magani wata hanya ce wadda ake amfani da ita don kuɓutar da rai daga wata cuta ko damuwa da ya kamu da ita wadda ta dami zuciya ko sassan jikinsa. Duk da cewa ba mai iya warkar da mutum daga kowace irin cuta sai Allah amma kuma Ya ba da iznin a nemi magani, don bai halicci cuta ba sai da ya saukar da maganinta. (Bunza, 2006)
            Domin haka ne ya sa ake fafitikar neman magani don ko  a sami yin gamon katar da maganin da ya da ce wajen warkar da cutar da take damun mutum. Haka kuma kwantar da hankali bisa amfani da maganin da mayar da komai ga Allah yana taimakawa matuƙa wajen waraka daga cutar jiki ko neman biyan buƙata.
2.0     Asalin Magani
          Abin da kamar wuya “wai gurguwa da aure nesa” a iya cewa ga yadda magani ya fara samuwa, domin babu wanda zai bugi ƙirji ya ce lokaci kaza aka fara samunsa. Wannan ya yi daidai da ra’ayin wani masani Adamu M.T (1998) inda yake cewa: 
            “Idan muka juya wajen binciken ta yadda magani ya samu a duniya, sai mu ga abu ne mai matuƙar wuyar gaske, domin kuwa tun farkon samuwar mutane a nan bayan ƙasa, suke ta ƙoƙarin kare kansu daga cututtuka, ko kuma yin maganinsu gaba ɗaya, malamin ya cigaba da cewa suna yin hakan ne kuwa ta yin amfani da wasu tsire-tsire ko sihiri ko ƙage-ƙage da dai makamantansu. Ba a nan ya tsaya ba, ya bayyana muna cewa: ko da masana magunguna na duniya sun yi matuƙar saɓani wajen bayanin asalin shi magani da kuma tabbatar da haƙiƙar samuwarsa, wasu daga cikinsu suna ganin asalin magani shi ne ilhama, wasu suna ganin mafarki shi ne asalin magani, wasu sun ce haatifi wasu na ganin dabbobi ne asalin maganin  wasu ƙiyasi, wasu jarrabawa wasu ƙwayoyi wasu kuma addini.     (Adamu, M.T. 1998).
          Magani ya samo asali ne tun lokacin da Allah (S.W.T) ya halicci cuta. Manzon Allah Annnabi Muhammad (S.A.W) ya faɗa cewa kowace cuta tana da magani. Don haka magani ya samo asali tun lokacin da Allah ya halicci cuta. (Bukhari: 602)
2.1     Addinin Musulunci
          Addinin musulunci shi ne miƙa wuya ga Allah (SWT) baki ɗaya tare da kaɗaita shi da kuma dogaro gare shi da yi masa ɗa’a da kuma tsarkake shi daga shirka. Addinin Muslunci shi ne addinin da Allah maɗaukakin sarki ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da shi zuwa ga bayinsa a duniya baki-ɗaya. (Bunza, A. M. 2005)
2.2     Mene ne Cuta
          A harshen Hausa idan aka ce cuta ana nufin zalunci, domin idan an ce wane ya fara cuta ko ya iya cuta ko kuma macuci to duk dai ana nufin azzalumi kenan.
A maganance kuwa, cuta tana nufin rauni da raɗaɗi tare da wahalar da mutum kan gamu da su a sanadiyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma damuwa a zuci. (Adamu, M. T 1998).
2.3     Nason Gargajiyar Bahaushe A Cikin Magungunan Muslunci
          A nan za a dubi wasu wurare ne don a ga irin yadda magungunan gargajiya ko hanyoyin amfani da su suka yi naso a cikin magungunan zamani na addinin Musllunci ne.
2.3.1   Magunguna A Addinin Musulunci
          Addinin Musulunci ya zo da hanyoyi daban-daban na yin maganin cututtuka don waraka daga cuta, (Bunza, A. M. 2006). Daga cikinsu akwai wanda za a karanta a tofa a jiki akwai wanda za a sha a shafa akwai kuma wanda za a yi wanka da ruwan maganin. Daga cikin ire-iren cututtuka da kuma maganinsu akwai:
2.3.1.1          Sihiri
          Sihiri shi ne a kawar da mutum daga wani tunani na abin da yake so ko kuma a sanya masa ƙyama daga wani abu da yake amfana da shi (Al’ilaju Birruka Shafi 2-3). Wato  dai yin amfani da wata hanya da za a sa wani abu ya faru ga wani mutum ba tare da ya gani ko an gane shi ba, ba tare da ya taɓa ko an taɓa masa ba. Wannan hanya ce ake yin amfani da iskoki don samun biyan buƙata; ta hanyar binne wani abu ko jefawa a rijiya ko kogi da sauran irin waɗannan dabarun.
            Ana yin sihiri tun kafin shigowar addinin Musulunci a ƙasar Hausa, kuma akwai hanyoyin da ake bi domin a warware sihirin a al’adance. Amma da addinin Musuluncin ya shigo sai aka samar da wasu hanyoyi waɗanda akwai nason tsofaffin hanyoyin warwarewar na gargajiya a cikinsu. Bari mu dubi yadda abin ya kasance.
Daga cikin hanyoyin maganin sihiri da aka samu bayan shigowar addinin Muslunci kamar yadda ya zo a cikin littafin Al’ilaju Birruka akwai:
i.          Karanta Ayoyin ƙarshe na Suratul Baƙara Da Suratul Ikhlas Da     Mu’awwazatain sau  uku koma fiye da haka har tswon kwana uku ko kwana        bakwai ko wata ko ma fiye da haka sai a sami kofin ruwa a tofa a ciki,     sa’annan a riƙa ɗebowa da hannun dama ana shafawa a jiki. Wannan          maganin akwai nason gargajiyar Bahaushe a cikinsa saboda ko da ana yin ƙulumbuttai ko shingidi-bagidi a tofa ko a shafa ga jiki domin a karya sihiri.
ii.         Haka kuma ana yin ƙaho a wurin da aka ga wata cuta ko ciwo ya bayyana sai a jaye jinin da ke a wannan ciwon, sa’annan sai a karanta Suratul Ikhlas            sau uku a tofa a wurin. Shi ƙaho ana yinsa tun kafin zuwan addinin muslunci         a ƙasarmu inda akan janye jinin da ya mutu da shi sai mutum kuma ya sami             lafiya, don haka ya zama wani naso ne da gargajiya ta yi a kan wannan       hanyar da addinin Muslunci ya zo da ita.  
iii.        Idan ana tunanin an yi wa mutum wani sihiri ne ko kuma shi ya faɗa cewa            an yi masa sihiri, sai a samu ganyen magarya ɗanye kamar kunne bakwai a          daddaƙa shi sai a samu ruwa a wani ƙaramin bokiti a zuba tare da ganyen magaryar da aka dagdaga a cikin bokiti sai a karanta waɗannan       ayoyin kamar haka:
1. Ayatul Kursiyu ƙafa ɗaya
2. Suratul A’araf  Aya ta 117-122
3. Suratul Yunus  Aya ta 79-82
4. Suratul Ɗaha    Aya ta 65-70
5. Suratul Kafirun Ƙafa ɗaya
6. Suratul Ikhlas   Ƙafa ɗaya
7. Suratul Falaƙ    Ƙafa ɗaya
8. Suratul Nas      Ƙafa ɗaya
A lokacin da ake karanta waɗannan ayoyin za a yi karatun ne numfashin mai karatun na shiga a cikin ruwan, idan an kammala sai a ba maras lafiya ya sha kamar sau uku, sai kuma a wanke jikin maras lafiyar da sauran ruwan. Za a ci gaba da yi wa maras lafiya haka har tsawon kwana uku ko kwana bakwai ko wata ɗaya (Imam Sa’id Aliyu bn Rahman:Addu’a Al’ilaju Birruka).
A gargajiyar Bahaushe za a yi ƙoƙari a gano inda ake tunanin an bizne wani abu sai a je a tono shi a warware abin da aka biznen, sai mai ciwo zai warke. Haka kuma wata hanyar ita ce wadda za a yi hayaƙi domin kiranye ga wanda ya yi sihirin don ya warware shi, ko kuma a yi turare wanda mai ciwon zai yi tari a ƙalla sau uku sai ya faɗi sunan wanda ya yi masa sihirin da kansa. Haka kuma akan yi wa marar lafiya mai wannan sifar wanka da ruwan magani ko a fesa masa ko ma a shafa masa don a warware sihirin da aka yi masa. A wannan zamani kuwa an samu nason gargajiyar Bahaushe a cikin maganin addinin musulunci domin Bahaushe na da wannan hanya ta maganin ko waraware sihiri tun kafin addinin musulunci, sai kuma addinin ya tanadi a gudanar da irin wannan maganin ta irin wannan hanyar. (…..)
2.3.1.2 Maganin Zazzaɓi Mai Zafi
Zazzaɓi ciwo ne da ke shigar mutum ta wasu dalilai da dama waɗanda suka zama sanadiyar samuwar zazzaɓin. Manzon Allah (S A W) ya ce zafin zazzaɓi yana daga cikin numfashin jahannama  don haka ku sanyaya shi da ruwa (Sa’id Aliyu bn Rahman:138). Don haka idan mutum yana fama da rashin lafiya ta zazzaɓi mai zafi sai a yi masa wanka da ruwa ko kuma a jiƙa wani ƙyalle da ruwa a riƙa goggogawa a jiki, mai zazzaɓin zai samu sauƙin ciwon in Allah ya so. A gargajiyar Bahaushe idan zazzaɓin ya yi zafi ana samun sayyun sanga-sanga a dafa watau a tafasa su sai a yi wa mai fama da ciwon zazzaɓi suraci idan aka yi haka a ƙalla sau biyu ga yini har kwana bakwai za a samu sauƙin ciwon cikin lokaci. Da wannan an samu nason gargajiyar Bahaushe a cikin maganin addinin musulunci.
2.3.1.3 Maganin Basir
            Basir ciwo ne da ke faruwa a dalilin bushewar ciki wanda hakan kan haddasa kashin jini ko na majina ko fitowar dubura daga jikin mai fama da ciwon basir. Idan haka ta faru ga wani, Manzon Allah (SAW) ya ce a samu zira’in Akuya a dafa a yi romonsa a ci, a kuma shanye romon za a samu sauƙin ciwon basir/ɗankanoma. (Za’adul Ma’ad shafi 521). Haka ma a gargajiyar Bahaushe akwai hanyoyi da ake bi don samun waraka ga ciwon basir, ana amfani da saƙe-saƙin iccen maɗaci a jiƙa a sha ko kuma a daka bedi a sha, haka kuma akwai ɓawon Hano da shi ma za a jiƙa a sha, waɗannan duk hanyoyi ne da ake amfani da su a gargajiyar Bahaushe tun kafin zuwan musulunci, don haka wannan ya yi naso ga magungunan da addinin musulunci ya zo da su a wannan cuta.
2.3.1.4 Ciwon Ido
            Manzon Allah (SAW) ya ce a shafa kwallin ismit yana maganin ciwon ido. (Musnad Ahmad hadisi na 7934) Kuma  yana ƙara kariya daga ciwon ido ko dundunin ido (wato gani garaye-garaye). Haka kuma ana amfani da ruwan zuma a yi kwalli da ita a ƙalla sau uku ga yini yana maganin ciwon ido. A gargajiyar Bahaushe ana shafa kwalli domin a yi kwalliya tun kafin zuwan addinin musulunci, haka kuma ana amfani da shafin kwalli wajen maganin tsuna ko ma ciwon idon. Wannan ya yi naso matuƙa ga yanayin maganin ciwon ido da addinin Muslunci ya zo da shi wanda aka yi bayaninsa a sama. 
2.3.1.5 Ciwon Naƙuda
            Ciwon naƙuda ciwo ne da ke zo ma mace musamman a lokacin da ta zo haihuwa. A lokacin da Maryam ta zo haihuwar Annabi Isah (A.S) sai Allah Ya albarkaceta ta hanyar yi mata ishara ta bakin ɗanta cewa ta ci dabino domin rage raɗaɗin haihuwa. Don haka idan mace na da ciki musamman ta kusa haihuwa ana so ta riƙa cin dabino za ta samu sauƙin raɗaɗi a lokacin da ta zo haihuwa, ke nan dabino magani ne mai rage zafi da raɗaɗi a lokacin haihuwa. (Haƙƙul mubin: hadisi na 831) A gargajiyar Bahaushe a kan yi amfani da sayyu da saƙe-saƙi a jiƙa a ba mai naƙuda ta sha don samun sauƙin naƙuda tun kafin zuwan addinin musulunci. Ke nan wannan hanya ta jiƙe-jiƙe ta yi tasiri matuƙa a wajen ciwon naƙuda da addinin musulunci ya zo da ita.
2.3.1.6 Ciwon Da Ya Shafi Ƙoda Da Anta Ko Wata Cuta Da Ta Shafi Ciwon Ciki
            Ciwon ƙoda da Hanta ciwo ne da ke addabar al’umma musamman a wannan lokaci don haka addinin musulunci ya zo da hanyoyi na waraka daga irin wannan cuta, daga cikin irin wannan hanya akwai. Za a samu dabino a ƙalla bakwai mai kyau a wanke shi da ruwa mai tsafta a ci da safe da kuma yamma. Za a yi haka sau da yawa har lokacin da ake ganin an samu waraka. (Du’a Ilaju bir ruƙa hadisi na 107). A gargajiyar Bahaushe akwai hanyoyi da ake bi musamman waɗanda za a jiƙa sayyun ɗoruwa da na Bagaruwa   a jiƙa su tsawon kwana uku, idan an tabbatar da cewa sun jiƙa sai a ba maras lafiya ya sha, wannan hanya ce da ake amfani da ita a gargajiya tun kafin bayyanar addinin musulunci kuma ko da ya zo bai sa aka bar amfani da ita ba sai dai kawai hanyar da ya zo da ita, (Bunza, A. M. 2005).
Kammalawa
          A wannan takarda, an bayyana magungunan addinin Muslunci ne da yadda gargajiyar Hausawa ta yi naso wajen aiwatar da shi. Akwai wasu magungunan da addinin musluncin ƙara tabbatar da su kawai ya yi, kamar irin na basir da sauran irinsa. Wasu magungunan kuwa hanyoyin aiwatar da su ne suka ɗauki samfurin na gargajiyar Hausa, kenan dai gargajiyar ta yi naso cikin magungunan addinin Muslunci. 

MANAZARTA

Contact Us…

Post a Comment

0 Comments