Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Ba Ka Da Dole




An tsara waƙar a tsarin ‘yar tagwai. Babban amsa amonta “wa”. An tsara ta cikin baitoci saba’in da tara (79). An kammala ta ranar Jmu’a 25/1/2013 a Sakkwato. Addu’a ce da godiya ga Allah ga irin taimakonSa ga bayinSa ga tsallake tarkon miyagun abokan zaman zamani. Godiya ga Allah wajibi ne ga kowane bawa, bale wanda Allah Ya kuɓutar da shi ga tarkon makircin abokan ƙarshen zamani “kifi ku ci ‘yan’uwanku”. Allah Ya yi muna tsari da tsarinSa. Amin!
-----------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
------------------------------
1. Ya Ahadun ya Samadun ya Kaafi babba,
          Ya Witirun Wahidun tilo ga misaltarwa.

2. Ya Alqahhaaru ka buwaya ga mulkinKa,
          Masu ganin sun buwaya su Kaka karyawa.

3. Ya Kaafi Ka wadaci duk wani bawanKa,
          In Ka ce: “Kun” Yakuunu xai za shi zamowa.

4. Ya masani al’amar na fai had da na voye,
Ya masani ko’ina da babu musuntawa.

5. Ya mai ilmin sanin qiraza da zukata,
          Ka san kominsu tun gabanin furtawa.

6. Ya mai ilmin da masu ilmi ka bixowa,
          Kai ne nassi gare ka sharhi ka fitowa

7. Ya mai xaga arzuka na bayi darajarsu,
          Kai ka buwayar da mai buwaya ga karawa.

8. Ya mai xaga martabar quje kan giwaye,
          Ko so, ko qi, da ya faxa, ba a musawa.

9. Ya mai raba arzukan da ba mai qwacewa,
          Kowa ka hana, aradu ya gama tavewa.

10. Ya mai xaga xa cikin xiya ya zamo babba,
          Yai rinjaye a kan xiyan da ka xasawa.

11. Ya ma’ishi gun waxanda an ka ci haqqinsu,
          Ka iya qwato shi ko ina aka voyewa.

12. Ya mai sakayya kan butulcin makusanta,
          Na shaidi hakan ga, na gani, sai godewa.

13. Ya mai sa qaiqayi ya koma ga masheqi,
          Duk qwazon kakkavansa bai hana sosawa.

14. Ya mai rikitar da makiri ga muradinsa,
          Qarshen tarkonsa shi haqon zai kamawa.
15. Ya matsarin wanda ba a so ba a qauna,
          An sha sara da sassaqa ya qi macewa.

16. Ya matsarin wanda an ka so ya yi ma savo,
          Kak qaddartai da bin umurni na hanawa,

17. Ya matsarin wanda ba a son a ji muryarsa,
          Kai masa gangar maqogoro mai burgewa.

18. Ya mai son wanda ba a son a ga ya rayu,
          Masu buqatar su kau da shi na ta macewa.

19. Ya mai qaddarta masu giba ruxewa,
          Geronsu yana batun tumu suka girbewa.

20. Ya mai dabirta tsegumin mai qyashewa,
          Yau ta hau kansa shi ake labartawa.

21. Ya mai saka wa kowane da xabi’arsa,
          Ni na shaida haqiqatan ga amincewa.

22. Ya mai bin kowane mutum da xabi’arsa,
          Kul-ba-daxe masu hanquri na ganewa.

23. Ya mahani yaudara da cin fuskar sabo,
          Kowa yac ce ya yi su bai ko morewa.

24. Ya mai saka wa masu sakayyar cuta,
          Ran da macuci ya cutu an gama cutarwa.

25. Ya masanin masu sunsuno abu munana,
          Mugun shaqensu duk hana musu fesawa.

26. Ya mai saka wa masu yi bisa niyyarsu,
          Shi ko mai tsegumi ka bar shi ga tavewa.

27. Ya masanin yanzu, xazu ka san shi dukansa,
          Ka san jiya gobe ban da ku wa ka gayawa.

28. Ya masanin cutukan jiki har na qiraza,
          Ba wani ciwon da zai buwai Ka ga warkarwa.

29. Ya wanda ya fid da Musa tarko matsananci,
          Ga ‘yan-sai-mun-gani ruwa na nocewa.

30. Ya wanda ya qaddaro Yunusa shiga kogi,
          Kifi ya haxe shi yaf fito ba cutarwa.

31. Ya hasken nan da ba duhun da ka kutsawa,
          Wa tafin xan Adam ya ce zai karewa.

32. Ya farkon nan da bai da farkon farawa,
          Ya qarshen nan da bai da qarshen qarewa.

33. Ya wanda ya yo sama’u kana ya yo qassai,
          Yay yo rana wata fitillun haskawa.

34. Ya wanda ya qaddaro duhu yai taurari,
          Don jefe shaixannun da ke linqayowa.

35. Ya kai makashin mazan da ke karya mazaje,
          Ka dai sha maqure maza sai shurewa.

36. Ya Sarkin alqawal da ba ya tadawa,
          Muddin ka yarda an gama ba fasawa.

37. Ya masanin yaudarar ido balle baki,
          Qwazon ‘yan jita-jita bai kai ga cikawa.

38. Ya kai mai zamani da sassauya lamurra,
          Duk mai ilmin saninka shi zai ganewa.

39. Ya kai mai mai da xan sarauta xan wasa,
          Ai ta kashe mai kixi yana tattakawa.

40. Ya Faradun ya Ahadun ya kai mabuwayi,
          Ya kai Samadun Aliyu na son furtawa.

41. Nai ladabi nai zaman biyayya ga abin ga
Amma koyaushe ni kaxai aka kushewa.

42. Tun abu na can duqunce har yaz zama buxe,
          Duk sharrukan da an yo ban ramawa.

43. Lallai kan an shigo ni an ci ni da zamba,
          Hulxa duka kissa ce kaman ban ganewa.

44. Nay yi shiruna ana bugu ban rama ba,
          Har dai an xebe xammahan ban miqewa.

45. Ai qazafi, ai tsince, an yi ashar sosai,
          An yi ta giba da arashi babu ragawa.

46. An nuna, ai tsaki an sha yin zunxe,
          An sa ni cikin sahu ana muzantawa.

47. An tara dubu gaban abokai an zagan,
          Har a gaba na a takaran ban ramawa.

48. An leqa qauye an ci sunana sosai,
          Duk alqaryarmu ban da inuwar hutawa.

49. An dai gama cin ido da yin yankan qauna,
          Ga cin zarafin da mumini bai yafewa.

50. Wallahi irin tu’annutin na qiyayya ne,
          Cin zuququn muqarrabi babu ragawa.

51. Makirci ne da zamba cutar kushewa,
          Babbar fatar su in kalamin riddewa.

52. Tilas ne godiya gare Ka ma ji roqo,
          Kan nasarar nan da nag gani mai xorewa.

53. Tun ba mu mace ba gaskiya tai aikinta,
          Qarya ko sai idanuwa taka zarewa.

54. Wayyo! Kaina Alu Ilaahu ka saka min,
          Can ranar nan da Alqiyama ka tsayawa.

55. Nai maka shukura haqiqatan ka ceta min,
          Ka sa na xauki hanquri bisa cutarwa.

56. Wai ko anya akwai basira ga macuci?
          Bayan ceto shi, shi ya ce zai cutarwa.

57. In har ga hankali idanu mudu ne,
          In ba shuka ina tumu za ya fitowa?

58. Na yarda da Walga Bunza mai waqar Tashe,
          Ya ce: “Qarshen ruwa Kware suka komawa”.

59. Zaki ya ce: “Mutum abin mamaki ne”,
          Mai mamakin halinsa ya gaza ganewa.

60. Shi zai zarge ka ko’ina zai vata ka,
          In kun haxu hanya sallama zai farawa.

61. Bayan ya nakkasa ka ya ci mutuncinka,
          Zai bixi gyaran zama na baya ga wallewa.

62. Wai wanda ka ba wurin zama don shi yi kauje,
          Shi zai jifa da shimfixarka ta kwantawa.

63. Assha! Ustazu wanga aikin bidi’a ne,
          Qin girmama wanda ya’ aza ka ga ganewa.

64. Don ka hau gwangwala shaqiyyai na tavi,
          Sai ka yi doro ka mance ranar saukewa?

65. Ko mun so, ko a yarda, ko an kafirce,
          Xan gaba na can gaban na baya ga qyargawa.

66. Tambayi ragon gidanku shaida wa Naturke,
          Kunnensa yana gani qaho ke tserewa.

67. Don haka ban rama cin mutunci da qazuffa,
          Na bar su wajen Ilaahu can mai sakawa.

68. Sharri yaron da babu qiuya ba naki,
          In an aikai zama guda yaka dawowa.

69. Malam kai kak kira shi, kab ba shi takarda,
          Ya dawo ma da ambulon ka qi karvawa.

70. Kura na san baqin jininki halitta ne,
          Had dai ga mahasada macuta na qurewa.

71. Zomo wayonsa fil azal na halitta ne,
          Hatta barci yake idon ba su rufewa.

72. Shata yai gargaxi ga taron mamugunta,
          Ya ce: “Su yi hattara abin na juyowa”.

73. Ranar da ya birkito ka san ba ka da kaico!
          Domin shukar da kay yi ce kaka girbewa.

74. Wauta ce zahirinta illanta mutane,
          Ita ce illarka in kana mai ganewa.

75. Babu musibar da taf fi cutar da mutane,
          Bayyana laifinsu ko’ina kaka zannawa.

76. Yadda ka hango halin waxansu ka kushe su,
          Kai ma haka naka wansu ke daxa kushewa.

77. Ya Allah ya Wahaabu ceto nika roqo,    
          Ga ni cikin bunguli ruwa na marawa.

78. Masu jirage abara me kuka dubu na?
          Kowammu da ya ga dorina sai zuqewa.

79. Sunana Ali xan Muhammadu xan Bunza,
          Birninmu na Shehu Jami’a nika koyarwa. 

Aliyu Muhammadu Bunza
Jumu’a 25 ga Junairu 2013
Sakkwato

Post a Comment

0 Comments