Ticker

6/recent/ticker-posts

Gaskiya Ina Laifinki?


Wannan waƙar ‘yar tagwai ce. Babban amsa amonta “ya”. Yawna baitocinta arba’in da biyar (45). An kamala ta Talata, 3/7/2013, a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina. A irin hasashenta, babu abin da ya fi gaskiya daɗi a duniya. Tsohuwa ce da gidan kowa ana sha’awar ta, kuma duk wurin da aka rasa ta ko aka hana ta zama ko aka ba ta tsoro wurin ya ɓaci. Farfaɗo mata da martabarta ta samu sakewa a zamaninmu shi kaɗai ne zaman lafiyarmu da kwanciyar hankalinmu. Rashin ba ta masaukin ƙwarai shi ya lalata zamaninmu.
---------------------------------
--------------------------------

1.                 Shukuran ga Allah wahidun mai agaji,
Da salati gun Manzo aminin shiriya.

2.                 Na yo yabo matuqa dukan asahabihi,
Manyan gwaraje masu nakkasa qarya.

3.                 Saqo garan ya xan’uwa ka tsaya ka ji,
Komi mukai mu bi gaskiya shiryayya.

4.                 Ita ce amintatta a kowane zamani,
A sahu tana gaba ba a kai ta a baya.

5.                 Launinta ba surki fari ne ko’ina,
Riga da taggo ba qananan kaya.

6.                 Ta girmi kowa shekaru wane mutum!
In kai musun haka je ka tambayi qarya.

7.                 Qarfinta ya fi na xan Adam da mutantani,
Doki da zaki ta aje musu kuyya.

8.                 In ta tsaya gantsarwa doro babu shi,
Ziqau take tankar a soke tavarya.

9.                 Muryarta daxi ke gare ta a ko’ina,
Ga shiga jiki ta zarce sautin kurya.

10.             Zance na kowa bai fice ba nata ba,
Ita qunshiyar zancenta bai da musanya.

11.             Zancen waninta ya bar xaga maka hankali,
Bari dai ta furta yanzu ka ji kumurya.

12.             Ba ta Karen miski da shadda don qawa,
Mai su idan ya rasa ta zai yi quyaya.

13.             Ba ‘yar sarauta ce ba, ba ‘yar fada ba,
Fadar da babu ta an baro ta a baya.

14.             Carbi, tulin rawani, gafakka, kandili,
In an rasa ta su zan tumullin kaya.

15.             Faxi gare ta qure ta wane xan Adam!
Wane gaban qato taya ta amarya?

16.             Ce babu shakka shi tsawo ko rijiya,
Qarya ka xan rame da babu mavoya.

17.             Iccenta shi ka fure da ‘ya’ya mai yawa,
Wane kaxanya xorawa da magarya.

18.             Ita ce nagartar jarumai a fagen faxa,
Ta tsere sanda wargajewar kwanya.

19.             Manyan mazanta a ko’ina su ke zara,
Maqiyansu dole su vuya tun day hanya.

20.             Dokinta dole fagen suka shi ke zagi,
Sauran a bayan nata sui ta tavarya.

21.             Mai son ta in ya guje ta kunyanai take,
Zangonsu bai nisa ta bar shi a hanya.

22. Mai son ta, mai aurenta, ba ya da fargaba,
Shi ke zagin taro a kowace hanya.

23. Komai ya lalace idan aka bincika,
Ita anka ba tsoro saboda hamayya.

24. Ita xai ta kai maqiyinta ke kewan ta zo,
In an ka gurmatsai cikin gogaggya.

25. Ita ce watan Salla saboda farin jinni,
Ciyo ga reta ga masu wasan vuya.

26. Akushin tuwo ce babba ta ishi unguwa,
Don ba ta varewa ya kumbun qwarya.

27. Ita sanfara ce babba gagari muciya,
Tuqin tuwo in ga ta ba a tukunya.

28. Allonta ba ya faso ku tambayi Gangaram,
Alaramma ba ya musanta iccen danya.

29. Zaqinta ya zarce zuma saqa fari,
Balle maxi da ake da ‘ya’yan xinya.

30. Ita tat tsayar da samai qasai ba ginshiqi,
Da wata da taurari irin su Surayya.

31. Mai gaskiya bai waiwaya in ya wuce,
Bai dube-dube irin na xaukar kaya.

32. Bai soke kai qasa juddadun ya qi tassuwa,
Fuskarsa ba ta baqi irin na tukunya.

33. ‘Yar tsohuwa ke samun sa’ar zamani,
Tsufanki duk bai sa jikinki mijirya.

34. Surukinki yai sa’ar xiyar babban gida,
Ko ba a so sunansa dai Rabakaya.

35. Ba ta kira a qiya a tsira da arziki,
Magujinta sai ya gama da wasan vuya.

36. Tsoron mijinki a dole ne don xaukaka,
Tun bai tsaya ba ake riqe masa kaya.

37. Ki yi dariyarki da gaske ba mai ja da ke,
Hauru farare ba baqi da wushirya.

38. An ce da ni ke yada zango Yawuri,
A cikin garin Ngaski in ji Baraya.

39. Na gai da rini masu kere itatuwa,
Xan goriba tilas ya gai da giginya.

40. Kushe ki yas sa duniya tay yamutse,
UN tana ta rabon faxa da tavarya.

41. Nijeriya an bar Arewa cikin duhu,
Ta yi cefane amma tuwo ta ci gaya.

42. Duk wanda yaq qi batunki zai da na sani,
Domin gudun ki ka sa a faxa haxaya.

43. Muddin kina tsaye wa mutum ya yi kangara!
Wasan kixi da rawa a qaga mashaya.

44. Fafau ba za ki faxa ba sai ke tabbata,
Zancen da duk ba ke ba shi ne qarya.

45. Roqon da nay yi Aliyu Bunza ga Qadirun,
Koyaushe tare da ke muke baja kaya.


Aliyu Muhammadu Bunza,
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua
Talata, 3/7/2013

Post a Comment

0 Comments