Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Salon Hira A Cikin Waƙoƙin Kabiru Classic




Bahaushe yana da hanyoyin da yake bayyana sha'awarsa ko damuwarsa ga duk wani abu da ya shafe shi. Saboda haka, kiɗa da waƙa na daga cikin hanyoyin da Hauwasa ke amfani da su domin bayyana ra'ayinsu ko sha'awarsu ko kuma damuwarsu. Rubutattun waƙoƙi, waƙoƙi ne da aka tsara su a rubuce, aka kuma aiwatar da su a rubuce,ta hanyar rerawa cikin daɗaɗɗan sauti. Wannan bincike ,ya ginu a kan adabin Hausa, musamman rubutacciyar waƙa. Binciken ya karkata akala ne wajen zaƙulo waƙoƙi masu salon hira na Kabiru Yahya Classic...

__________________________
NA
ABUBAKAR MACCIƊO
______________________ 

SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan kundin digirin nawa ga mahaifiya ta Hajiya Hauwa’u da mahaifi na Alhaji Macciɗo da kuma dukkan iyalan gidanmu ga baki ɗaya. Sannan da dukkan waɗanda suka tallafa min a lokacin da nike wannan karatu, tun daga farkonsa har zuwa wannan mataki. Ina rokon Allah ya tallafi rayuwarsu kamar yadda suka tallafamin, ya kuma sa albarka a cikin rayuwarsu duniya da lahira.

GODIYA
Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da godiya a gare shi, dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikkai wanda ya halicce mu, ba don komai ba, sai don mu bauta mishi. Ya Allah! Ka yi salati ga Muhammadu, da alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi salati ga Ibrahim da alayen Ibrahimu, lallai kai abin godewa ne, mai girma. Ya Allah! Ka yi albarka ga Muhammadu, da Alayen Muhammadu, kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu, da alayen Ibrahimu lallai, kai abin godewa ne, Mai girma.
            Bayan godiya ga Allah, wanda ya ba ni ikon kammala wannan bincike nawa. Ina matukar godiya ta musamman maras adadi ga malami na, Mal. Dano Balarabe Bunza wanda ya sadaukar da lokacinsa a kai na, tare da haƙuri da ya yi da ni domin ganin wannan aiki ya kammala. Haƙiƙa Mal. Dano Balarabe Bunza ya taimakamin matuƙa da kayayyakin aiki da nuni da kuma shawarwari, wanda hakan ne ya sa wannan bincike ya kammala cikin nasara. Domin haka ban da abin d azan iya saka mashi da shi, sai addu’a. Da wannan nike roƙon Allah ya sa albarka  a cikin rayuwarsa da zuri’arsa baki ɗaya.
       Ina godiya ta musamman ga Mal. Naziru Ibrahim Abbas da ya taimaka min da shawarwari a wajen gudanar da wannan aiki da dukkan malamai na Sashen Nazarin Harsunan Nijeria, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, bisa irin yadda suka jajirce, wajen ƙoƙarin koyar da ni da sukai tun daga shekarar karatu na ta farko har zuwa ƙarshe.
Ina godiya ga iyaye na Alhaji Macciɗo da Hajiya Hauwa’u, waɗanda suka tarbiyantar da ni, kuma suka ɗora ni a kan hanya madaidaiciya, musamman ta neman ilmin addini da na zamani (boko). Ina rokon Allah ya tsare su da talauci da kuma azabar ƙabari, sannan ya kyautata rayuwarsu duniya da lahira, ya sa Aljanna fiddausi ce makomarsu, Amin.
            Haka kuma ina miƙa godiya ta ga ‘yan’uwa da abokan arziki maza da mata waɗanda suka taimaka min da ƙarfinsu da dukiyarsu da kuma addu’o’i domin ganin wannan karatu nawa ya kammala.
            Haƙiƙa ba zan manta da abokai na ba waɗanda suka taimakamin sosai a lokacin da na gudanar da wannan karatu na wato, Nafi’u Abubakar Binji da Salim Muhammad Sani da Ahmad Abdullahi da Aminu Sanusi Sani da Ibrahim A Ibrahim da Gaddafi Labaran da Nasiru Abdullahi da sauran abokai na ga baki ɗaya. Ina roƙon Allah ya saka musu da alhairi.
            Ba zan manta da abokan karatu na ba wato, Mubarak Murtala da Zubairu Lawal Ibrahim da Husaini Abubakar da Bello Aleru da Imrana Sulaiman da Lukman Abubakar da Murtala Guiwa da sauran abokan karatu na, su ma ina godiya a gare su da, irin taimakon da suka ba ni don ganin wannan bincike ya kammala.    
Daga ƙarshe ina miƙa godiya ta musamman ga dukkan dangi na, da kuma duk wanda ya taimakamin wajen karatu na, da kuma wajen gudanar da wannan bincike nawa. Allah ya sakawa kowa da mafificin alkhairi, Amin. 

BABI NA ƊAYA:  SHIMFIƊA
1.0     GABATARWA 

Bahaushe yana da hanyoyin da yake bayyana sha'awarsa ko damuwarsa ga duk wani abu da ya shafe shi. Saboda haka, kiɗa da waƙa na daga cikin hanyoyin da Hauwasa ke amfani da su domin bayyana ra'ayinsu ko sha'awarsu ko kuma damuwarsu. Rubutattun waƙoƙi, waƙoƙi ne da aka tsara su a rubuce, aka kuma aiwatar da su a rubuce,ta hanyar rerawa cikin daɗaɗɗan sauti. Wannan bincike ,ya ginu a kan adabin Hausa, musamman rubutacciyar waƙa. Binciken ya karkata akala ne wajen zaƙulo waƙoƙi masu salon hira na Kabiru Yahya Classic.
       Wannan babin namu zai ƙunshi abubuwa kamar haka: Gabatarwa, Manufar bincike, Muhimmancin bincike, Bitar ayyukan da suka gabata, Hujjar ci gaba da bincike, Farfajiyar bincike, Hanyoyin gudanar da bincike, Dalilan bincike da kuma Kammalawa.

1.1  Manufar Bincike
Manufar wannan bincike ita ce samar da kundi wanda zai fito da salon hira a cikin waƙoƙin Kabiru Yahya Clasicc domin zai taimaka ga masu nazari su sami wani abu da zai taimaka musu,su fahimci salon hira da ke cikin waƙoƙinsa.

1.2 Muhimmancin Bincike
         Salon hira abu ne mai muhimmanci a cikin waƙoƙin Kabiru Yahya Classic, musamman da yake mawaƙin siyasa ne. Saboda haka, binciken ya dangana ne a kan salon hira a waƙoƙin Kabiru Yahya Classic.
        Idan wannan bincike ya kammala zai taimaka ga wasu manazarta da ke da sha'awa ga irin wannan bincike su sami makamar gina nasu.

1.3 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata
A nan an duba ayyukan da suka gabata ne waɗanda suka haɗa da littafai da kuma kundaye.
Abdullahi (1993) Sun yi bayani a kan ma'anar waƙa da nauo'in waƙoƙin baka da tarihin mawaƙin da jigo da salon waƙar da kayan ƙidansa. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa sai dai akwai bambance-bambance. Zan amfana da wannan aikin ƙwarai da gaske.
Aliyu da wasu (1995) aiki ne mai taken "Kwazo Bagage da waƙoƙinsa" marubucin ya yi bayani a kan tarihin mawaƙin da kayan kiɗansa da jigogin waƙarsa, kamar zambo da yabo da habaici da zuga,sai kuma salailan waƙar. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa haka yana da bambanci da nawa. Haƙiƙa zan amfana da wannan aikin.
Ɗanƙal G.L (2000) "Gero Zartu da waƙoƙinsa"  marubucin ya yi bayani ne a kan tarihin mawaƙin da kayan kiɗansa da ma'anar waƙa da asalin waƙa da jigogin waƙoƙinsa kamar yabo, zuga da habaici da zambo. Amman  bai yi bayanin muhimman salailan mawaƙin ba. Wannan aiki yana da alaƙa da nawa sai dai akwai bambance-bambance da nawa aikin. Zan amfana da wannan aikin.
Akwai kuma littafin "Salo  Asirin Waƙa (2001)"  wanda Abdullahi Bayaro Yahya ya rubuta. Wannan littafin an shirya shi cikin manyan babuka uku waɗanda suka haɗa da ma'anar salo da ire-irensa da muhimman abubuwa da suka shafi tubalan salo a waƙa. Sai kuma fito da wasu hanyoyi da suke tabbatar da muhimmancin salo a waƙa. Har wa yau marubucin ya yi tsokaci a kan wasu salailai da yadda suke ƙulluwa a waƙoƙin Hausa.
Kasancewar wannan aiki babban fanni na waƙa zai taimaka ainun wajen gudanar da wannan aikin da yake wannan littafi ya yi bayani a kan salailai da yawa.
Abubakar (2004) "Muhammadu Ango Rabo Yabo da Waƙoƙinsa". Aikinsa ya ƙunshi tarihin mawaƙin da kayan kiɗansa da yawace-yawacensa da dangantakarsa da sauran mawaƙa da turakun da ma'anar turke da salo da ma'anarsa. Wannan aikin na da alaƙa da nawa aiki haka kuma akwai bambanci a tsakaninsu. Zan amfana da wannan aikin matuƙa.
Takware(2005) ya gudanar da aikin bincike mai taken "Nazarin Waƙoƙin Abdullahi Fircin Koko". A cikin aikin bincikensa na neman kundin digirinsa na farko da ya yi a Sashen Harshen Nijeriya da ke Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato, a inda ya yi bayanin zubi da tsari da jigogin waƙar da salailai da ke cikin waƙoƙin Abdullahi Fircin Koko.Idan aka lura wannan aiki yana da alaƙa da nawa aikin bincike, duk da yana magana a kan "Rayuwa da Waƙoƙin Abdullahi Fircin Koko”. Amma nawa aikin binciken  yana magana ne a kan " Nazarin Salon Hira a cikin waƙoƙin Kabiru Classic". Wannan aikin  na da alaƙa da nawa kuma akwai bambance-bambance da nawa aiki.
Bafarawa(2006) ya gabatar da aikin bincike a kan "Nazarin Rayuwa da Waƙoƙin Dr. Waziri Junaidu". A cikin aikinsa na neman kundin digiri na farko a Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato. Wannan aikin yana magana ne a kan "Nazarin Rayuwa da waƙoƙin Dr. Waziri Junaidu". Amma nawa aikin binciken yana magana ne a kan "Nazarin Salon Hira A Cikin Waƙoƙin Kabiru Classic". Akwai alaƙa da kuma bambanci a tsakanin wannan aiki da nawa.
Bunza(2009) “Narambaɗa”, dangantakar wannan littafin da bincike na ita ce ya yi bayanin waɗansu salailai masu muhimmanci a nazarin waƙa,kamar yadda za a yi la'akari wajen bambanta habaici da zambo.
    Mustapha Umar (2009) ya rubuta wata maƙala a kan ‘Waƙoƙin Muhammadu Gambo Fagada’  da ya gabatar a taron ƙara wa juna ilmi na Sashen koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Wannan maƙalar ta ƙunshi ma’anar kalmomi da Bayanau da Amsa-kama. Wato ta ƙunshi kalmomi ne masu Amsa-kama a cikin wasu waƙoƙin Gambo Fagada. Wannan maƙala za ta taimaka min matuƙa a wajen gudanar da nawa aiki.
Shehu M. (2009) ya rubuta wata maƙala da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato. Mai suna ‘Gambo mawaƙin Maza ne ba mai cin gashin kansa ba’. Wannan maƙalar ta ƙunshi mawaƙan maza ,dangantakar waƙoƙin maza da waƙoƙin Gambo da kuma Jigon ta’addanci. Wannan maƙala za ta taimaka min matuƙa a wajen gudanar da nawa aiki.
Shafa'atu I.B (2010) mai taken "Nazarin Rayuwa da waƙoƙin Isya Mafara". Wannan aikin yana da dangantaka da nawa saboda an kawo taƙaitaccen tarihin mawaƙin. Haka an kawo ma'anar salo da ire-irensa. Zan amfana da wannan aikin matuƙa.
Shehu (2010) ya gudanar da aikin bincike mai taken "Waƙoƙin Abdu Kurna" a inda ya yi ƙoƙarin bayyana zubi da tsari da kuma fito da salailan da  ke cikin waƙoƙin na Abdu Kurna. Wannan aikin zai taimaka min a wajen gudanar da nawa aikin. Saboda dama a aiki na zan yi nazarin salon hira ne a waƙoƙin Kabiru Classic.            
Sai Bunza (2011) da ya rubuta wata maƙala a kan ‘Sakkwato ce tushen ‘Hausa’ in ji Narambaɗa‘. Wannan maƙalar ta ƙunshi taƙaitaccen tarihin Narambaɗa da farfajiyar ƙasar Hausa da Ɗaurayar zantukan Narambaɗa da kuma wasu waƙoƙin Narambaɗa da aka yi nazari a kansu. Wannan maƙala za ta taimaka min matuƙa a wajen gudanar da aiki na.

Umar.M (2011) mai taken "Rayuwa da Waƙoƙin Ɗanbaba Birnin Tudu" a wannan aikin an kawo taƙaitaccen tarihin mawaƙin haka kuma an kawo ire-iren salo,don haka akwai dangantaka a tsakanin aiki na da wannan aiki.
Yahya H (2012) mai taken "Nazarin waƙar Ta'aziyyar Malam Jafar Mahmud Adam". A cikin aikinsa na neman kundin digiri na farko a Jami'ar Usman Ɗanfodiyo Sakkwato,a inda ya kawo taƙaitaccen tarihin marubucin waƙar Aliyu Muhammad Bunza. Haka kuma an yi nazarin zubi da tsari na waƙar da kuma ma'anar salo da ire-irensa. Wannan aiki yana da dangantaka da nawa aiki. Zan amfana da wannan aiki matuƙa.

1.4 Hujjar Ci Gaba Da Bincike
Duk da bitar wasu daga cikin ayyukan da suka gabata tare da yin tsokaci a kansu, amma har yanzu ba a ga wani aiki da ya leƙo gurbin da ake ƙoƙarin lalubowa ba, saboda haka ganin irin muhimmancin Salon hira a cikin waƙoƙin Kabiru Classic, aka ga ya dace a fitar da wannan hikima a fili domin amfanin masu nazari

1.5 Farfajiyar Bincike
          Wannan aiki ya keɓanta ne a kan Nazarin salon hira a waƙoƙin Kabiru Yahya Classic saboda haka ba za a wuce amfani da waƙoƙinsa ba.
         Wannan bincike ya rabu ne a ƙarƙashin inuwar rubutaccen adabin Hausa da ya shafi rubutacciyar waƙa.

1.6  Hanyoyin Gudanar Da Bincike
 Domin gudanar da wannan bincike an bi hanyoyi da dama domin cimma abin da ake buƙata dangane da wannan bincike da aka yi.
Da farko na sadu da shi kansa Kabiru Yahya Classic domin samun taƙaitaccen tarihinsa.
Hanya ta biyu ita ce an nemi kayan aikin kamar littafai a cikin ɗakunan karatu da kundaye da maƙalu domin karantawa tare da zaƙulo wasu muhimman abubuwan da ke taimakawa a wannan fagen nazari.
Hanya ta uku ita ce sauraren waƙoƙin Kabiru Yahya Classic domin a fito da wannan salo a fili gwargwado.

1.7 Dalilan Bincike
 Babu shakka wannan aiki kamar sauran ayyukan bincike ne, dukkan wanda ya karanta zai ƙaru da wasu abubuwa masu amfani. Haka kuma domin cike giɓin da ake da shi a wannan fanni na salon hira a waƙoƙin Kabiru Yahya Classic. Sannan kuma yana iya zama wani abin amfani, musamman ga manazarta masu sha'awar adabin Hausa, tare da taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa adabin da kuma ƙara wa mutane fahimta.
Haka kuma masu iya magana na cewa ' banza ba ta kai zomo kasuwa ' don haka, duk abin da za a yi yana da wata manufa ta musamman, don haka wannan bincike na ɗauke da fasali biyu. Na farko cike giɓi domin samun takardar kammala karatun digiri na farko a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya (Hausa Studies). Na biyu kuma domin ɗaliban da ke tafe su samu ƙarin haske kan nazarin waƙa da ya shafi salon hira da abin karantawa ko nazari ga masu neman ilmi.

1.8  Kammalawa
         Sanin kowa ne cewa, gabatar da kundin bincike ga kowane ɗalibi wajibi ne. Kasancewar waƙa wata muhimmiyar aba ce a al'adun Hausawa, haka ya sanya aka samu masana da kuma ɗalibai suka duƙufa kanta domin gano sirrin da ke ciki.
         A cikin wannan babi an yi bayanin gabatarwa, kuma an kawo manufar bincike. Haka kuma an kawo muhimmancin bincike tare da kawo bitar ayyukan da suka gabata da kuma hujjar ci gaba da bincike da kawo farfajiyar bincike. Haka an kawo hanyoyin da aka gudanar da bincike da dalilan da suka sa aka gudanar da binciken.

BABI NA BIYU
 TAƘAITACCEN TARIHIN KABIRU YAHAYA CLASSIC.
2.0     GABATARWA
            Wannan babi na ɗauke da taƙaitaccen tarihin Alhaji Kabiru Yahaya Classic. Haka kuma yana ɗauke da lokacin da ya fara waƙa da kuma ficensa. Sai kuma waƙoƙin da yake yi da kuma yanayin rera su.
2.1     HAIHUWARSA
            An haifi Alhaji Kabiru Yahaya Classic a shekarar 1978 a Unguwar Tashar Kali  da ke ƙaramar hukumar Talatan Mafara da ke cikin Jahar Zamfara. Sunan mahaifinsa shi ne Malam Yahaya Ibrahim.
2.2     ILMINSA
            Ta ɓangaren ilimi Alhaji Kabiru Yahaya Classic ya yi karatunsa na firamari a makarantar Abubakar Model Primary School da ke cikin ƙaramar hukumar Mafara da ke  jahar Zamfara.
            Bayan ƙare karatunsa na firamari sai ya shiga makarantar sakandare a makarantar Sheik Abubakar Gummi da ke Sakkwato.
            Bayan Alhaji Kabiru Yahaya Classic ya kammala karatunsa na Sakandare a 1996, sai ya shiga makaranta ta gaba da sakandare mai suna Ahmadu Gusau inda ya yi Satifiket daga 2000 zuwa 2002.
2.3     IYALINSA
Ta ɓangaren iyali Alhaji Kabiru Yahaya Classic yana da mata uku,
akwai:
  1. Hajiya Lubabatu.
  2. Hajiya Shafa’atu.
  3. Hajiya Hauwa’u.
Ta ɓangearen 'ya’yansa, Alhaji Kabiru Classic yana da 'ya’ya tara ga sunayensu kamar haka:
  1. Yahaya.
  2. Khadija.
  3. Ibrahim.
  4. Zainab.
  5. Muhammad.
  6. Fatima.
  7. Hauwa’u.
  8. Safiya.
  9. Mahmud.
2. 4    LAƘABINSA DA DALILINSA
             Laƙabin Alhaji Kabiru Yahaya kuwa ya samo asali ne dalilin wani shago da suka yi bayar da aron kaset-kaset, da wannan shagon ke da taken Classic a matsayin sunansa. Daga wannan shagon ne Alhaji Kabiru Yahaya ya samo laƙabinsa na Classic, a sakamakon haka ne aka fara kiransa da sunan Classic.
2.5     FARA WAƘARSA DA FICENSA
            Alhaji Kabiru Yahaya Classic ya fara waƙa a shekarar 1996. Dalilin fara waƙarsa kuwa shi ne a dalilin waƙokin Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai da yake sauraro. Sauraron waɗannan waƙoƙin Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai ya sa Kabiru Classic fara waƙa.
            Maganar ficensa kuwa, Kabiru Classic ya daɗe yana waƙoƙin amma bai samu yin fice ba sai a 2007-2008 wato lokacin da Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi ke matsayin gwamnan jahar Zamfara a dalilin waƙoƙin da ya rera masa a wannan lokacin.
2.6     WAƘOƘIN DA YAKE YI DA KUMA YANAYIN  RERA
SU.
            Kabiru Classic mafi yawancin waƙokinsa na siyasa ne, saboda da ma da su ne ya yi fice.
Ta ɓangaren yanayin waƙoƙin Kabiru Classic kuwa, a cikin waƙoƙinsa ana samun ɗan jagora fiye da ɗaya wato su biyu suke jagorancin, wato wani lokacin sukan yi jagorancin a waƙarsa wato shi da Zuwaira ko kuma tare da Naja’atu. Haka kuma akwai amshi a cikin waƙoƙinsa.

2.7     KAMMALAWA
          A cikin wannan babin an kawo taƙaitaccen tarihin Kabiru Yahaya Classic sannan kuma wannan babin ya taɓo irin waƙoƙin da Kabiru Classic yake yi da kuma yanayin rera su.

BABI NA UKU
SALON HIRA A CIKIN WAƘOƘIN KABIRU CLASSIC
3.0     GABATARWA
A cikin wannan babin, an kawo ma’anar salo da yadda masana suka yi bayani tare kuma da kawo salon hira a cikin waƙoƙin Kabiru Classic. An yi haka ta hanyar kawo hirar da suka yi, wato Kabiru da abokan hirarsa Zuwaira da Naja’atu. An yi haka ta hanyar tsamo salon hirar, daga waƙoƙinsa da ke ɗauke da shi.

3.1     MA’ANAR SALO
Masana da dama sun bayyana ma’anar salo acikin rubutunsu. Misali:
Sa’id (1981:35) ya bayyana salo da cewa ‘’Salo shi ne yadda mawaƙi ya zana tunaninsa a takarda".
Ɗangambo (19812.3) yana ganin cewa ‘’Salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da Saƙo”. Ya daɗa faɗaɗa tunaninsa da cewa lallai ne Salo ya danganta ga yadda kowane mutum ya zaɓi abubuwan da ya yi amfani da su cikin rubutunsa ko furucinsa don isar da saƙonsa kuma salo yakan ta’allaƙa ne dangane da yadda mutum yake tunani cikin dacewa.
            Guban (1993:54) ya bayyana salo a waƙoƙin Hausa da cewa ‘’Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi yake kyautata zaren tunaninsa ya sarrafa shi cikin azanci don ya cimma burinsa na isar da saƙo ko waƙa”. Salo a waƙoƙin baka abu ne wanda yake daɗa fito da ainihin kyansu ko muninsu ta haka za a iya gane waƙoƙi masu karsashi, masu hikima da balaga da kuma waƙoƙi marasa ma’ana marasa inganci.
            Yahya (2001) a cikin littafinsa mai suna ‘Salo Asirin Waƙa’’ yana cewa “Salo yana nufin duk wata dabara ko hanyar yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar”.
            Gusau (2002:54) cewa ya yi “Salo wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani ta bin yanayin harshensa da zaɓar abubuwan da suka dace da abin da yake son bayyanawa’’.
            La’akari da waɗannan ma’anoni da masana adabin Hausa suka bayar ina iya cewa ba wani abu ba ne Salo illa hikima ce ko kuma gwaninta da ake sauyawa cikin magana ko rubutun da ake yi na yau da kullum.
            Haka kuma Salo wasu dabaru ne da mai harshe ke amfani da su domin ƙara wa furucin da aka bayyana ta fatar baki, ko ta hanyar ƙara ma rubutu armashi kuma ya inganta shi ya zama yana ɗauke da wasu kalmomi zaɓaɓɓu. Salo ya danganta ne ga irin kalmomi da jimloli da aka yi amfani dasu, ta la’akari da saƙon da yake ɗauke da shi.

3.2          HIRA DA YADDA AKE GANE TA A CIKIN WAƘOƘINSA
            Yahya (2001:108-112) Salon hira ko labari, Salo ne mai ban sha’awa mai kuma sa ƙarsashi ga masu sauraren waƙa. Ana iya gane Salon a cikin waƙa a yayin da mawaƙi ke sarrafa harshe cikin muryoyi mabanbanta ya ƙaddarta tamkar yana magana da wani ko kuwa wasu ne daban suke maganar ba shi ba. Idan kuwa Salon labari ne, mawaƙi na ƙoƙarin bayyana abin da ya gudana ne a tsakanin mutane biyu ko fiye.
            Yahya (2016) a cikin littafansa na ‘Salo Asirin Waƙa’ ya bayyana Salon hira da cewa "Idan baitocin  waƙa suka ƙunshi muryar mai magana fiye da ɗaya, wato mawaƙi ya ƙaddarta da shi da wani ne ke magana ko kuwa wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna magana to a fagen nazarin waƙa sai a ce mawaƙi ya yi amfani da Salon hira a cikin waƙarsa”. Mai karatu ko sauraren waƙa zai ji muryoyi na masu magana a cikin waƙar.
Salon hira yakan taimaka wa mawaƙi a ƙoƙarinsa na isar da saƙonsa ta hanyar sa mai saurare ko karatu ya zamo ya ƙara kusantar mawaƙin. Wato sai mai saurare ya ji daga bakin waɗannan mutane ne mawaƙin ke magana, ba wai daga bakinsa shi mawaƙin ba
Akwai hanyoyi da dama da ake gane Salon hira a cikin waƙoƙin Kabiru Classic za ka ji ana musanyar magana a tsakanin Kabiru Classic da kuma abokan waƙarsa waton su ne abokan hirarsa, wato ko dai ya yi hirarsa da Zuwaira ko kuma Naja’atu. Wannan dai ya danganta da wadda ya yi waƙarsa da ita.
Ana gane Salon hirar a waƙoƙinsa, misali ta hanyar tambaya ko kuma musu a tsakaninsa da abokiyar hirarsa ko kuma su kama wa juna don a yi wa wani kirari ko habaici, ko zambo ko kuma bayar da labarin abin da ya faru da dai sauransu.
Ga kaɗan daga cikin waɗannan hanyoyin da suke yin hirar a cikin baitocin wasu waƙoƙi.

3.2.1      TA HANYAR TAMBAYA
An samu hira ta hanyar tambaya a tsakanin Kabiru da Naja'atu a cikin wani baiti na waƙar ‘Sarkin Gobir’ Misali:


Kabiru: Wane ba ya da haure guda cikin baki nai dasashi ne
                 na yi tambaya ko kuma hira?
Naja’atu: Ko ni na so in leƙa kwabacciyar bakina ina gadara
         Wallahi da sai na dara,
Kabiru: Margamar gandutse halor ne gaggado a bar ka ko tilas
       kun jiyo ko kun tura,
Naja’atu : Yanzu ‘yan sarki sun hanƙura kowa ya bi kad da ka 
           yarda da su na sani sun dai lwaye.

3.2.2 TA HABYAR MUSU
            An samu hira ta hanyar musu a tsakanin Kabiru da Zuwaira a cikin wasu baituka  waƙar ta’ Ciroman Wamakko’. Misali:


Kabiru: Ciroma ya ce kar na yi zambo don haka na ƙyale,
Zuwaira: Ko ka ƙyale ni kam sai na kwance buhun lalle,
Kabiru: Ko ke kwance tun da an hana dole ki ma ƙulle,
Zuwaira: Abun ne  yai  mini zafi Kabiru angulu wai ni za ya
          ƙyama.

Kabiru: Kabir  Classic cizon bobo yai mani baibaici,
Zuwaira: Kabiru ai kyawon hutsu a gwada ma shi hutsanci,
Kabiru: Da ni da zambo mun raba hanya gara ki bar naci,
Zuwaira:To in ba ka taɓi ka faɗa mini ko ni ɗai in taɓa ma.

Kabiru: Ki bar ni  in na tashi da kai na in yi zubar kurna,
Zuwaira: Ai ni har na katse adalcin ga da kan nuna,
Kabiru: Ni kuma ke ban haushi batun ga nawa da kir raina,
Zuwaira:To  ka faɗa mini jigon Aliyu ba ni shirarra in taɓa ma.

3.2.3 TA HANYAR ROƘO
An samu hira ta hanyar roƙo a cikin wani baitin waƙar ‘Sarkin Ɓurmin Jabo’ a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:

Kabiru: Kabiru rai na ya ɓaci har gobe abin yanai man ciwo,
Naja’atu: Ina da hauya ta mai ƙwari in na riƙa ta nai man kyawo,
Kabiru: Sai dai ba ni da gonar noma na rasa ko laɓi sai yawo,
Naja’atu: Sarkin ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.

3.2.4   TA HANYAR KIRARI
An samu hira a tsakanin Kabiru da Naja'atu ta hanyar kirari
a cikin waƙar ‘Sarkin Gobir ’. Misali:

Kabiru: Wanda Amadu yah haihi ubanai a duniya Kabir Classic ai
       ba shi yin kalan dangi,
Naja’atu: Sannu ɗan Sarki kuma jikan Sarki kuna gani mai gina
         shi na ɓallar shingi,
Kabiru: Tun da tsuntsu kukan gidansu yas so ya riƙe ga mai buhu
      yar rai na ka mai lelen bagi,
Naja’atu: Yanzu Allah yai Nasiru a gidan Ibrahim Kabiru Wallahi
                   baƙin ciki na ya yaye.

3.2.5   TA HANYAR HABAICI
            An samu hira ta hanyar habaici a tsakanin Kabiru da Zuwaira a cikin waƙar ‘Ciroman Wamakko’. Misali:

Kabiru: Ƙarya ba baƙuwar Classic ce ba ku dai duba,
Zuwaira: Wanda ka hulɗa da ‘yan siyasa bai wuce ƙarya ba,
Kabiru: Kullun sai an man ƙarya sai in ba mu ɓullo ba,
Zuwaira: Allah waddanka mai baƙar ƙarya makashi ɗan tashi
          rama.

3.2.6   TA HANYAR ZAMBO
An samu hira ta hanyar zambo  a cikin waƙar ‘Gaskiya Takobin Yaro’ a tsakanin Kabiru da Naja'atu a cikin wani baitin wannan waƙar. Misali:

Kabiru: Ni Mafara ni ke iccen mangwaro Kabiru ya watsa mani shadda,
Naja’atu: Allah mai hana bawa kuka sai wani yam miƙa mini kaɗa,
Kabiru: Nar rufe kunne nar rufe hanci sannan yam miƙa mini adda,
Naja’atu: Yac ce anshi Kabiru Classic faskari saƙon mai maka zamba.

3.2.7   TA HANYAR LABARI
An samu hira/labari daga cikin wani baiti a cikin waƙar ‘Rayuwa Dukiyar  Ɓoye’ tsakanin Kabiru da Zuwaira. Misali:         
                           
Kabiru: Wani Kwamishina da nig gani har ya ban tausai,
Zuwaira: Ya ɗau fasinja Naija nib bi in fansai,
Kabiru: Nig gane ya ji kunya na kwana jin tausai,
Zuwaira: Lallai kwamishina kan mulkinku na da wuya.

3.3     ABOKAN HIRAR KABIRU CLASSIC
          Abokan hirar Kabiru Classic ba su wuce Zuwaira Isma’il da kuma Naja’atu Musa ba, wato ko dai ya yi waƙa tare da Zuwaira ko kuma tare da Naja’atu.Amma mafi yawancin waƙoƙinsa ya fi yin su ne tare da Naja’atu Musa.
3.4     SALON  HIRA A CIKIN WAƘOƘIN KABIRU CLASSIC
Yahya (2016) a cikin littafansa na ‘Salo Asirin Waƙa’ ya bayyana Salon hira da cewa ‘’Idan baitocin waƙa suka ƙunshi muryar mai  magana fiye da ɗaya, wato mawaƙi ya ƙaddarta da shi da wani ne ke magana ko kuwa wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna magana, to a fagen nazarin waƙa sai a ce mawaƙi ya yi amfani da Salon hira a cikin waƙarsa".
3.4.1   WAƘAR CIROMAN WAMAKKO
          A cikin wannan waƙar ta Ciroman Wamakko an samu hira da dama daga cikin wasu baitocin waƙar a tsakanin Kabiru da Zuwaira. Misali:

Kabiru: Kabiru Allah ya yi mani sa’a Aliyu ya koma,
Zuwaira: Ashe bikin balbela kaza gobe da didima,
Kabiru: Kabiru ai ka san mai gona shi ka batun damma,
Zuwaira: Kai ko marar gona ko ka yi batun damma ba a riƙa ma.

Kabiru: Ai sabo da maza jari ne tuntuni na gane,
Zuwaira: Kaza matuniya nike sirrin Kabiru na tone,
Kabiru: Kowa dai ya tsaya matsayi nai yin haka dai dai ne,
Zuwaira: Ni ta ruwan sanyi zan biyarka ƙarshenta ƙasa zan tuna ma.

Kabiru: Ciroma ya ce kar na yi zambo don haka na ƙyale,
Zuwaira: Ko ka ƙyale ni kan sai na kwanci buhun lalle,
Kabiru: Ko ke kwance tun da an hana dole ki ma ƙulle,
Zuwaira: Abun ne yai mini zafi Kabiru angulu wai ni za ya ƙyama.

Kabiru: Ba ka hayo ƙarfi kai ƙarfi dole kunun dawa,
Zuwaira: In kuma an ƙi biyar magana ta dole a sha yunwa,
Kabiru: Ashe da sauran hankalinki don Allah ki bar tsiwa,
Zuwaira: In ka tashi ɓaramɓaramarka Classic kowa bai hana ma.

Kabiru: Kabiru Classic cizon bobo yai mani habaici,
Zuwaira: Kabiru ai kyawon hustu a gwada mashi hutsanci,
Kabiru: Da ni da zambo mun raba hanya gara ki bar naci,
Zuwaira: To in ba ka taɓi ka faɗa mini ko ni ɗai in taɓa ma.

Kabiru: Ki barni in na tashi da kai na in yi zuba kurna
Zuwaira: Ai ni har na katse adalcin ga da kan nuna,
Kabiru: Ni kuma kin ban haushi batun ga nawa da kir raina,
Zuwaira: To ka faɗa mini jigon Aliyu ba ni shirarra in taya ma.

Kabiru: Tunku ya san jibar da zai ba kashi yarinya,
Zuwaira: Tafiyar kura gefe-gefe ita ba ta biyar hanya,
Kabiru: In ta ce za ta bi hanya ina haɗa ta da zakanya,
Zuwaira: Na san faɗa kana ba da gari har dai in ba mai tare ma.



Kabiru: Rubin garden Biba ya yi nauyi ta bani ta ƙara,
Zuwaira: Ka san Biba da son duniya biɗa da kwaɗan biɗan nera,
Kabiru:Akuya guda da kura tara tag gangama tatatura,
Zuwaira: Wayyo ita am bat ta da turke da gudu ta shaida ma gwamma.

Kabiru: Jikan Jeɗo mai hana ƙarya mai tsoron Allah,
Zuwaira: Kowaj  ja ma bar ni da shi na buge shi da bulala,
Kabiru: Ina ya Allah Kabiru Classic babu kamar Allah,
Zuwaira: Kowa nas san labarin Jeɗo ya kwatanta ga ciroma.

Kabiru: Zamani ya kai mu ga hairi Arɗo ga shi ya haifi Ali,
Zuwaira: Kwalliya ta yi kubebewa Kabiru babu ga ɗan ƙoli,
Kabiru: Arɗo du’a’inka ya yi rana tamu kamar leli,
Zuwara: Da rarrafe aka tashi Aliyu ja mu gani zaki Ciroma.


Kabiru: Aliyu hazo kashe kaifin rana dole na gaishe ka,
Zuwaira: Gwani gare ni cikin Wamakko Kabiru ina naka,
Kabiru: Agola an sa ka gida daɗa sai yag gwada ya hi ka,
Zuwaira: Ba ka raba mu da Aliyu Jeɗo ido maƙiyi kowa nat tsaya ma.

Kabiru: Rana kani kuɗi na na ɓoye in yi bukin dangi,
Zuwaira: Da ka ga mai nama ya gitta dole ka sai tsagi,
Kabiru: Dama ka san shi mai waƙa dole ya yo gogi,
Zuwaira: Makamakale ko ka koma ko ƙauyenci zai gwada ma.

Kabiru: Ga wani makama ya gayyato ni ya ga ni ya ɓoye,
Zuwaira: Mai rayuwa ta birni wane jikinka  jikin ƙauye,
Kabiru: Na yini na kwan ina jira nai jikin saye,
Zuwaira: Kowaɗ ɗauko tuwo nai shi ɗai za ya ci nai ba ya taya  ma.
Kabiru: Yunwa tai yunwa ga Kabiru zaune kamar shege,
Zuwaira: Mutan gari sun sa ka kaɗaici su kuma sun gunge,
Kabiru: Kala ina hammata ga ni na gagara Kabiru na tsige,
Zuwaira: Ga rogo kuma ba ka da kuɗɗi sannan kowa bai kira ma.

Kabiru: Bakin kura buɗe Kabir in tana biɗar nama,
Zuwaira: Ka sha baƙar wuya kai Kabiru am maka ka rama,
Kabiru: Azabar yunwa ta fi ta zambo ba wani na rama,
Zuwaira: Yunwar ta hurce yanzu ga waƙar na kaiwa da koma.

Kabiru: Ga wani ya zo yai mani ƙarya ya aza na ɗauka,
Zuwaira: Ashe sara ka ka kallo nai ka ɓoye asirinka,
Kabiru: Muna ta wayon-wayon da wane ka ga ni na ganka,
Zuwaira: In ba don ba don ba Classic kai ka san ba ya raga ma.
Kabiru: Ƙarya ba baƙuwar Classci ce ba ku dai duba,
Zuwaira: Wanda ka hulɗa da 'yan siyasa bai wuce ƙarya ba,
Kabiru: Kullun sai am man ƙarya sai im ba mu ɓullo ba,
Zuwaira: Allah waddanka mai baƙar ƙarya makashi ɗan tashi rama.

Kabiru: Wani in yallema ma ƙarya dole ka ma ruga,
Zuwaira: Dole ka ruga ka rufe ɗaki kad da ka bar taga,
Kabiru: Tagar ma in tana da hanya ka sanya 'yan raga,
Zuwaira: Don ƙarya in ta shigo ɗakin mine ne ribar gudum ma.

Kabiru: Aliyu ɗan Sarkin Musulmi Macciɗo gwarzo ne,
Zuwaira: Ciroma ka yi tsayayye wane kunun wake ne,
Kabioru: In dai ga Aliyu Orojo Kabiru Sarki ne,
Zuwaira: Na san ba ni rashin komai ma Kabiru in dai ga Ciroma.

3.4.2   WAƘAR SARKIN GOBIR
A cikin wannan waƙar ta Sarkin Gobir an samu hira daga cikin wasu baitocin wannan waƙar a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:

Naja’atu: Ubangiji na ni ban gaza da roƙo nai ba saboda Allah
        kullum ya nai man gatanci,
: Na riƙe Allah shi ya ke tsaya man kullun baƙin     
   mutum   ya yi kaɗan ya ga rai na ya ɓaci,
            : Wanda yaɗ ɗauki mutum yanai mai illoli Kabiru ya ya ma
              za ya jin daɗin kwanci?
: Ni ga Allah nad dogara ban sanyo wani ba da ka yi 
   wannan Allah yanai ma rinjaye.

Kabiru: Wanda Ahmadu yah haihi ubanai a duniya Kabir Classic
                 ai ba shi yin kalan dangi,
Naja’atu: Sannu ɗan Sarki kuma jikan Sarki kuna gani mai gina
         shi na ɓallar shingi,
Kabiru: Tun da tsuntsu kukan gidansu yas so ya rike ga mai buhu
                 yar raina ka mai lelen bagi,
Naja’atu: Yanzu Allah yai Nasiru a gidan Ibrahim Kabiru Wallahi
         baƙin ciki na ya yaye.

Kabiru: Zuga ka tada maƙera bari in tada ubana Sarkin Gobir mai
       martaba Sarkin Isa,
Naja’atu: Sannu-sannu na ke tafiya ta babu garaje cikin iyawar
                    Allah ina kwana nesa,
Kabiru: In ga Sarkin Gobir Nasiru mai ƙauna ta mu yo ido huɗu                    
                 lallai Kabir har na ƙosa,
Naja’atu: Mu muna ƙaunar Sarki Sarki yanai da mu Kabiru amma
        sirrin zukata mun ɓoye.

Kabiru: Wane ɗan Sarki don ba ya da kuɗɗin rogo na ga shi bakin
                 titi yana lasar yaji,
Naja’atu: Ka ga 'yan Sarki sun haɗa kai sun bi gaskiya shi kuma
                  mahaukaci ya koma yana kwasar daji,
Kabiru: Na yi hira da shi sai yana faɗa man ƙarya yana bari amma
                so yake sai yai turji,
Naja’atu: Da ɗan Sarkin yaz zo yana yi min ɓaɓatu saboda
                    mamaki sai da kai na yab banye.

Kabiru: Kai ci zabo Malam ka gane ka sha daɗi ko da ganin burgu
                ba shi yin daɗin nama,
Naja’atu: Lallai mai waƙa ko wana ne ya san daɗi ga mai gidan
         Hajiya Rabi yau can nak koma,
Kabiru: Uwar gida Hajiya Rabi Sarauniya da kin amince man mai
                bugu na nar rama,
Naja’atu: Idan Hajiya Rabi’atu ta yi min gata to ashe Naja’atu wa
                  zai kira na‘yar ƙauye.

Kabiru: Duk ɗiyan Sarki ne mutane in kun gane uba na kirki ne ga
      shi ga’ya’yan kirki,
Naja’atu: Ja mu je baƙon dole jinin Ummaru Sanda mahassada
                    sun gane a yau ta zan taki,
Kabiru: Tela bai san da cikin gari akwai kuɗɗi ba Kabiru sai dai
                 har in yana kwana ɗunki,
Naja’atu: Za ya nemo kaji a kai gida mata nai saboda murna am
         fige kaji an soye.

Kabiru: Nemi Kwano Malam rufawa kanka asiri karankaɓau ba
        rango yake tun farko ba,
Naja’atu: Ina ‘yan Sarki sai ku ɗauki horo na ka ga wanda bai
           zama Sarki ba bai sha daɗi ba,
Kabiru: Ka ga kowa bai san shi cikin duniyar ga ba Kabri Classic
      na yarda bai san kowa ba,
Naja’atu: Ban da Sarki na taimakonsu da sai rugga duk da hakan
         amma wane kai ya jaye.

Kabiru: Mai saran kaba idonka kar ya kauce ga rina gadar zare ta
                katse da mai man labako,
Naja’atu: Ga sanyi ɗan sarki ana kwanan sanyi saboda ba sisi
          gane ba sauran iko,
Kabiru: Ashe ɗan Sarki sai dai ya yi rantsar idi rashin wadata ta sa
      yana haushin maiƙo,
Naja’atu: Na ga ɗan Sarki sai yana ta ɓoyon hannu ashe wajen ga
        tuyar maƙwabta yat toye.

Kabiru: Wane ya ban tausai ƙarfi bai fi jiki ba wani ɗan Sarki
        shaddar rama tai yaɗ ɗunka,
Naja’atu: Ga shi ya bi rariya shaddarsa miyan goro ku ji ƙwarin
                 wake sun hana mai shan iska,
Kabiru: Tunkiya ta cizo nan akuya ta jawo shige gida don shanu
                suna nan bayanka,
Naja’atu: Na ga ‘yan yara suna kuwa sun bi kwarkwaɗa suna
faɗin mai waƙa muna neman maye.

Kabiru: Wance kura mis sa ki ke shiga harka ta Kabiru ni ko can
      ba ni son wargin cizo,
Naja’atu: Ga ruhewa ta nan ina kurin gero da nit hato nab buɗa a
       yau ya zam ɓarzo,
Kabiru: Tun da wargin haka ne a yau ni na yi hushi mu je ga
       Sarkin Gobir ina samo zozo,
Naja’atu: Mun taho da hushi za mu na wajjen noma da mun ka
          duƙa sai ga shi hauya ta karye.

Kabiru: Ranan fa Classic ni na kwana dariya da nig ga mai
       gilɓoshi yana tamnar goro,
Naja’atu: Rinƙa alheri sai muna ta kallon kallo ashe dai mawaƙi
        ba ya son kallon mauro,
Kabiru: Duk abin da na ce wanda ba na alheri ba gare ka ko ni ma
      na sani sai nai ɓauro,
Naja’atu: Mai halin banza wani mai ɗabi’un banza da zuciya ta
         ƙarya mutum ai ya karye.

Kabiru: Wane ba ya da haure guda cikin baki nai dasashi ne na yi
                tambaya ko kuma hira,
Naja’atu: Ko ni na so in leƙa kwacciyar baki na ina gadara wallahi
                  da sai na dara,
Kabiru: Marganar gandutse halo ne gaggado a bar ka ko tilas kun
                jiyo ko kun tura,
Naja’atu: Yanzu ‘yan Sarki sun hanƙura kowa ya bi kad da ka 
                    yarda da su na sani sun dai lwaye.

Kabiru: Wanda yan nemi tuwo yag gaji bai samo ba Kabiru
                 yunwa na sa shi yin kwanan dole,
Naja’atu: Ka ga ‘yan Sarki an ga ba wuri an ɓoye suna ta fatar su
                   ga ko ƙawa nan ta sulle,
Kabiru: Tun da ɗan Sarki bai da amana na gano sun kau da kai in
                ka lura tamkar sun ƙyale,
Naja’atu: Ce yana nan na san da bai barin jayayya ɗan Sarki ko da
                  ya gwada mai ya jaye.

Kabiru: Yau ko al’ummata daɗa ga kallon-kallo da nig ga mai
       tarƙonshi yana kallon gwame,
Naja’atu: Mai dahwahen Sarki yana ganin ya tisra a zuciya tai sai
                  ya yi mummunan hwame,
Kabiru: Ku dakata ba fankan-fankan ne kilishi ba Kabiru sai in ya
      samu kyakkyawan tsome,
Naja’atu: Ni da mai laifi babu shiri ba shiryawa abun da ke damu
                  na dukan sai na juye.

3.4.3   WAƘAR SARKIN ƁURMIN JABO
An samu hira daga cikin baitocin wannan waƙar ta Sarkin Burmin Jabo a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:

Kabiru: Kabiru rai na ya ɓaci har gobe abin yanai man ciwo,
Naja’atu: Ina da hauyata mai ƙwari in na riƙa ta nai man kyawo,
Kabiru: Sai dai ba ni da gonar noma na rasa ko laɓi sai yawo,
Naja'atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki,

Kabiru: Don Allah Jama’a ku riƙa mani za ni fari mutanen Jabo,
Naja’atu: In kuma kun ka bari nif faɗi kun ga jikinmu zan yo
                    tambo,
Kabiru: In kuma kun ka riƙa min za ku ga na wuce sai ƙwambo,
Naja’atu: Sarkin ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.

Kabiru: Im ma har wani bai gane ba shi wani na sani ya gane,
Naja’atu: Ashe mawaƙi ɗan wayo ne duk wada yaf faɗi daidai ne,
Kabiru Da nig ga leda sai naɗ dauka ka ga ashe tulin kashi ne,
Naja'atu: Ka aza ko bantamin zuma ne don ka wuce ka sha zaƙi.

Kabiru: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu farin cikin duk Jabo,
Naja’atu: Ko ‘yan yara suna ƙauna tai tun da jikinsu kan ɗau
                   bobo,
Kabiru: Kabiru na tanya ku da murna sannu da ku mutanen Jabo,
Naja’atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.

Kabiru: Ka je ya Allah yana bayanka Aliyu kaɗa ni in sha dada,
Naja’atu: Ka riƙe dangi ka riƙe sabga tufansa babu mai ko dauɗa,
Kabiru: Kai masu aure kai masu suna ko ni nan Kabir na shaida,
Naja’atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.

Kabiru: Kabir Classic ga ni a Jabo inda farin watan Sarkinsu,
Naja’atu: Mai albarka ɗan albarka Jabo farin cikin an ba su.
Kabiru: Don samun Sarki Aliyu zai wahala hakan an san su,
Naja’atu: Sarkin Ɓurmin Jabo Aliyu rai ya daɗe kana Sarki.

3.4.4   WAKAR GANIN IDO
An samu hira daga cikin wasu baitoci na wannan waƙar ta Ganin Ido a tsakanin  Kabiru da Zuwaira. Misali:

Kabiru: Aliyu ai ko gobe da shi don Shehi hali nai yaka yi,
Zuwaira: Zan yi yaƙe-yaƙen takobuna shi gwamna da jan biro
         yaka yi,
Kabiru Ka sanya hannu yanzu a basu Kabiru ni na yarda a yi,
Zuwaira: Ɓakin ciki na yanzu Kabiru ga dokunan nan ba mahaya.


Kabiru Saboda Baba ba ni aminta ana ta cin haƙƙin marini,
Zuwaira: Ina masaƙi yay yi Classic Kabiru bai zauna ba tuni,
Kabiru: Da sunɗe-sunɗe akan daɗa miƙi mu raina mai mugun
       katani,
Zuwaira: Idan da dama dawo a dama a sha da dama ai ta riya.

Kabiru: Gwamna yi man kashedi inda Jarma ya dai sani gaba,
Zuwaira: Masha Allahu mun yi dace Oranti bai kasa muna ba,
Kabiru: Ke ba ki san komi ba gaba ɗai ki dakata man in ci gaba,
Zuwaira: Kabiru ga ni ina sauraro ina biyar hujjar ka biya.

Kabiru: Oranti hauka za na yi nan gaba in ba ka sassauta mani ba,
Zuwaira: Gwamna yi mai magana ya bari don  ba a san wada za ta
        tsaya mana ba,
Kabiru: Ubangiji gatan marar shi ko ba a so yannab ba’a ba,
Zauwaira: Oranti sannu da ƙirgi daloli ka bai wa ɗanɗa gun
           Safiya.

Kabiru: Da Sallama ni za ni shiga garinmu nai waƙa na fita,
Zuwaira: A gaida jikan Abdullahi ɗan Yari in zo in rabata,
Kabiru: Da safe niz zo ba ni barin Mafara sai rana ta yi fita,
Zuwaira: Ni sai naje gun Asma’u Zuwairatu in gaido Hajiya.

Kabirou: Na sai man shanu da kuɗina wajen rabo an bani tsaki,
Zuwaira: Kar ka ji komai Kabir Classic an yi wa mai rama ma
         buki,
Kabiru: Lallai turmi ba ya riƙa ta Kabiru in dai ga madaki,
Zuwaira: Mutum ya lura da Allah yay yi ni ba wani mai sa in ci
                   wuya.

Kabiru: Tumbin yaƙi mai gudun Hisabi ba ya shakkar sababi,
Zuwaira: Kabiru rabin jin daɗin duniya mura ma ta mai ladabi,
Kabiru: In dai ba ka da mugun aiki ba ka jin shakkar laƙabi,
Zuwaira: Idan miya ta riga abinci a nan ake gane maciya.

Kabiru: Idan duma gero taka ci ku ƙyale goge gun kabuwa,
Zuwaira: Da an ka maran na ƙi na rama saboda albarkar taƙawa,
Kabiru: Kabiru ko ni na koyi tuma kar da a ce na koyi nawa,
Zuwaira: Ba na jin haushin dillali na tutu in dai ga masaya.

Kabiru: Wasu da sun ga na yi wa Shehi waƙa za su ga APP ni ka
                   yi,
Zuwaira: Bara na Ƙara faɗa wa mutane Kabiru PDP ya ka yi,
Kabiru: Mai ganewa ya ƙi ya gane kasan komai na yanayi,
Zuwaira: Ba kai ɗai ba Kabiru PDP ko ni ma na yi biya.

Kabiru: Da tunkiya ta kamu da ciwo na lura domin ba ta tuƙe,
Zuwaira: Shi ko manomi cikon gadara na gan shi kunkurin shi
         rike,
Kabiru: Na saki kowa na riƙe Jarma Oranti albashinmu da ke,
Zuwaira: Da ka riƙe Allah ka ci gaba za ka watsa alkaryar maƙiya.

Kabiru: Bugun ku bai kai gare ni ba Kabiru balle in ji jiki,
Zuwaira: Kabiru ka more rijiya matsalar ka guda na rashin wasaki,
Kabiru: Ai ina da guga aru-aru igiyar ɗaurawa naj ji jiki,
Zuwaira: Ka sai da guda ka sawo tsawo don Allah rage sauga ta
        tsiya.

Kabiru: Shigo-Shigo ba zurfi banza Kabiru ban yarda fa da shi,
Zuwaira: Ya wuce reza baki na Kabiru ya wuce almakashi,
Kabiru: Bakina jari na Kabiru shi nika kwana tare da shi,
Zuwaira: Saboda Allah shi yay yo mani kowa bai sa in ci wuya.

3.4.5   WAƘAR HANA KISHIYA WAƘAR MIJI
An samu hira a cikin wasu baitocin wannan waƙa ta Hana Kishiya Waƙar Miji a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:

Kabiru: Maciji mai sarar gayya sai mun bugi mai mugun nuhi,
Naja’atu: Idan tsafi ne kai wa jaha sai mun tuɓuke wannan kahi,
Kabiru: Azabar da kay yi wa jama’a za ka ɗanɗano wannan dahi,
Naja’atu: Domin Sallar bana na shaida jama’a da yawa ba sa
          kawa.

Kabiru: Mu yi ma wankan babban bargo mu gwada maka ƙarfin
       addu’a,
Naja’atu: Don yanzu matasa sun shirya fatansu mu dai zarce sa’a,
Kabiru: Har Ƙuru har bokan ƙuru banke su muke yi ba ba’a,
Naja’atu: Akuri da magarya duk ɗai ne bambanci ba wani mai
          yawa.

Kabiru: Wani ya hau kuka ya faɗo kuma ga shi a cikin shingi
       ƙaya,
Naja’atu: Da ya tambaye ni tun farko da na gwada mashi ɗan
          ɗibar miya,
Kabiru: Ku ji yarinya mai gandarƙi kuma ta iya babbar zolaya,
Naja’atu: Ni da wane ba sauran ƙauna sannan kuma ba wata
           jituwa.

Kabiru: Yau mai ƙarfi ga talakkawa Zamfara duk mun koma awo.
Naja’atu: Sai an yi takarda a rubuce sannan ka ka cin bashin
          dawo,
Kabiru: Babu tallafi mun lalace daɗa yau ba noma ba kiwo,
Naja’atu: Ya mai da mutane shanu nai fuskarsa kamar naman
          dawa.

Kabiru: Ni Kabiru na dai kai ƙarshe ɗunkin afatati  ba ni yi,
Naja’atu: Masu yi muna kallon ‘yan wahala ku ci ku ɗai babu
          taɓin tayi,
Kabiru: Wasu sun kashe  al’umma da Jaha ko jin shakka ma ba su
        yi,
Naja’atu: In Allah ya kai ƙarshensu za mu kai su ko a rabin awa.

3.4.6   WAƘAR RAYUWA DUKIYAR ƁOYE
A cikin wannan waƙar ta Rayuwa Dukiyar Ɓoye an samu hira daga cikin wasu baitocin waƙar a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:

Kabiru: Bello Matawalle waƙa ce zan yi saurara,
Naja’atu: Daɗa yau da mu da guntaye za a yin tsera,
Kabiru: In an tsere ma a bubbuge ka ba kara,
Naja’atu: Duk inda kag ga guntu wajjen faɗa za ya.

Kabiru: Ni da ‘yan siyasa na ɗau anniyar daru,
Naja’atu: Kabiru faɗa mani ni ma in ji in ƙaru,
Kabiru: To mun yi wa junanmu sani damu sau wauru,
Naja’atu: Sai ka je ka koyo ni gunka in koya.

Kabiru: Komai za a man PDP nake ƙauna,
Naja’atu: Babbar Jam’iyya ta ita ma tana so na,
Kabiru: Kai ko tana guda na ita za ni sa kai na,
Naja’atu: Balle da amana ɓota ba ta ƙin hauya.

Kabiru: Kashin baƙi sai taron garke na gardawa,
Naja’atu: Don waƙar da nay yi fashin baƙi sai an nemi Hausawa,
Kabiru: Da ma ɗaurin giwa wa za ya sa tsauwa,
Naja’atu: Kar ku ɗauki giwa tamkar barkata karya.
Kabiru: Na ƙyale rijiya tun da ruwa su na rafi,
Naja’atu: Kafin na tuba sai na san wa na wa laifi,
Kabiru: Sai babbar murna ke shi gini tafi,
Naja’atu: Kuma sai ya yi shi ɗai don kaucewa ingwayya.

Kabiru: Kabiru Classic wai mi nir rasa yanzu,
Naja’atu: Balle ka canja Jam’iyya na faɗi ɗanzu,
Kabiru: Zafin biɗa ka samu kuma na faɗi yanzu,
Naja’atu: Komai akwai gida na kuma ba ka taɓin hauya.

Kabiru: Ɗaukar rigima ta sai fati marinjayi,
Najaatu: Ko kare ya kai gwarzo ai ba ya cin tayi,
Kabiru: Lema nika so don ita kowa yake yayi,
Naja’atu: Bam barin ɗiya in tahi don tambaɗa goya.

Kabiru: Ai gaskiya guda sure shi yake zautu,
Naja’atu: Mu mata har abada ba ma gudun shantu,
Kabiru: Na daina jin a Zamfara an zagi Dallatu,
Naja’atu: Sukar mashi ta gagari masu ingwayya,

Kabiru: Za ni jaddad maku ni Allah nake bauta,
Naja’atu: Shi ka ƙara kwana na to kun jiya ƙatta,
Kabiru: Ga duniya tana so na ni ina ƙinta,
Naja’atu: Don na ga ta kashe Jama’a duniya manya.


Kabiru: Ga ma'aikatan Zamfara nan za su yin bore,
Naja’atu: Mai shan nonon ‘yan soke bai gudun saye,
Kabiru: Mai ƙaramin albashi bai shan miyar sure,
Naja’atu: Kai wanga bala’i  don Allah Kabir saya.

Kabiru: Wani ya ja ni faɗa kolo mai ƙujen baki,
Naja’atu : Wai istigifari mai kwana yana tsaki,
Kabiru: Sai ya ga fasiƙanci sannan yake ɗauki,
Naja’atu: Ɗan tsurku moriyarka butulci ka kan koya.

Kabiru: Duniya katifa ce kullun ina lura,
Naja’atu: Mai dakonki bai hau ki ba don ba a yin kara,
Kabiru: Dama ɗan dako gun kwana ba shi yin tara,
Naja’atu: Fatansa ya farka da lafiya aji za ya.

Kabiru: Wani kwamishina da nig ga har ya ban tausai,
Naja’atu: Ya ɗau fasinja Naija nib bi in fansai,
Kabiru: Nig gane ya ji kunya na kwana jin tausai,
Naja’atu: Lallai Kwamishina kan mulkinku na da wuya.


3.4.7   WAƘAR GASKIYA TAKOBIN YARO
An samu hira a cikin wasu baitocin wannan waƙar ta Gaskiya Takobin Yaro a tsakanin Kabiru da Naja'atu. Misali:

Kabiru: Yau na yo guɗaɗɗar waƙa kowa ya gane a misali,
Najaatu: Kafin in shiga tsabar waƙar zan kafa tau hujja da dalilai,
Kabiru: Yau magidanta Zamfara Kabiru an haɗa al’umma da iyali,
Naja’atu: Asusu yau ya zan tarihi ba maganar ajiya aka yi ba.

Kabiru: Ko wane za ya sauka in hau ɗan Ali ɗin nan dai nika
       ƙauna.
Naja’atu: Idan lalurata ta taso ku bar ni kullun in yi da kai na,
Kabiru: Ba ni buƙatar komi gare ku ƙadangare tuni ya aje zana,
Naja’atu: Bai dawo wa inda ya bar ta to ko can mi zai yi da saɓa.

Kabiru: Ni Mafara nike iccen mangwaro Kabiru ya watsa mani
       shadda,
Naja’atu: Allah mai hana bawa kuka sai wani yam miƙa mini
          kaɗa,
Kabiru: Nar rufe kunne nar rufe hanci sannan yam miƙa mani
        adda,
Naja’atu: Yac ce anshi Kabiru Classic faskari saƙon mai maka
           zamba.

Kabiru : Ni da nar rayu Sabon Birni har wani zai nuna mani tsage,
Naja’atu: Karyarka wane ta sha ƙarya fara ta grime maka sunge,
Kabiru: Ƙuru in gaskiya gare ka wajen tafiya mis sa ka ka waige,
Naja’atu: Ya karkace wurin sata don ba yanke hannu aka yi ba.

Kabiru: Ku zo ku je kallon ta tuba wai jiya an jefe muna wada,
Naja'atu: Inda ina wajen aka jifar da sai na kwaɗa masa sanda,
Kabiru: Talakka ka iya ɗaukar fansa don fansa tai ba ta da tsada,
Naja’atu: Mai mulki kowa ab bai so noma nai shine yaka girba.

Kabiru: Indai ana zuwa ruwa Kabiru ai wata ran sai an kasha tulu,
Naja’atu: Mai gaugawa ga dama koko can wata ran sai ya kwaɓa
         ƙullu,
Kabiru: Sara ni kai ina dubawa cikin duhu na lura da ƙyallu,
Naja’atu: Ko an rufe tukunyar kashi ba tausan hanci taka ji ba.

Kabiru: Ba saukar ƙuru ba ga mulki ni EFCC nika hange,
Naja’atu: Ko shi yag gina EFCC ni  na san sai tai masa dabge,
Kabiru: Sata har ta rashin lissafi ya yi ta wai don ba ya da shinge,
Naja’atu: Lalli zamu ga wasar kura gardawa sun ƙoshi da gumba.

Kabiru: Ni Mafara nike kowa nau ne a bincika min ba ni da bare,
Naja’atu: Matizkabura Kabiru Classic mu garzaya har in wuce
          ware,
Kabiru: Baƙin ɓarawo ɗai ab ban so sala ya bar muna yar riƙe
       sare,
Naja’atu: Bai ƙaunar jajjayen kaya shin ba ‘yan banga ya ka so ba.

Kabiru: Ba ni cikin tawagar masoyanka hannu riga mun yi da
        tsaido,
Naja’atu: Na san ka sadda da ba ka da sisi na fi ƙarfin kai mani
          dodo,
Kabiru: Za ni faɗi ƙaramin taƙadiri tun Mafara har in wuce
      Mando,
Naja’atu : Babu mutum ɗaya mai kwaraka tai ka aza na mance
           haba duba.

Kabiru: Ina uowan biri da gada kuma babu rowan riga da farari,
Naja’atu: Ban bin wane a kowace hulɗa buri nai lalata samari,
Kabiru: Ai gara in wuce da talauci ko kuma kullun in jiƙa gari,
Naja’atu: In sha in riƙe nawa mutunci ko da kullun ba ni kwabba.

Kabiru: Yau ga ƙurungu mugun kifi hulla ya soke ta ga goshi,
Naja’atu: 2019 zan maku kyauta ga ƙato nan ba mu da mai shi,
Kabiru: Nan gaba bai iya ɗaukar kainai tun da haramce zai ci ya
      ƙoshi,
Naja’atu: Tun da haramun ba ta narewa ba wai sai waƙa muka yi
        ba.

Kabiru: Babban gida yana ban sha’awa za ka ga ɗa na gidan
       maganarci,
Naja’atu: Yai tausayi da tsoron Allah ya ɗauka ya ba mabuƙaci,
Kabiru: Dangi sui fahari da shi Kabiru domin ya fidda su takaici,
Naja’atu: Yai musu aure yai musu suna ba ya gajiya da hakan ya
        ka yi ba.

Kabiru: Kwamishina zai aurar da ‘yar shi ba ya da kuɗɗi yas saɗa
      ganga,
Naja’atu: Yat tafi ƙauyen Birnin Gwari yac ce shi a’a na gadanga,
Kabiru: An kawo masa fura da nono har da tuwo nai shaƙe da
        langa,
Naja’atu: Muna ido huɗu sai yas sarƙe idanuwa nai sun daɗa
          taiɓa.

Kabiru: Ni Mamuda ina ƙaunarka kai nika hange safe da yamma,
Naja’atu: Ni biyarka ta yi min rana don ba ni da yunwa ba ni da
          tsuma,
Kabiru: Ko da ban da ƙiba ki faɗa musu kowa ya san ba ni da
        rama,
Naja’atu: Allah ya kau da ɓacin rana mu roƙon Allah mu ka zaɓa.

Kabiru: Ni can dori ina ɗan yaro duk sata ba ta wuce jakkai,
Naja’atu: Zuwa-zuwa loto na canji har sata ta kai ga dawakai,
Kabiru: Sata ta wuce doki Zamfara yau ta kai an saci Sarakai,
Naja’atu: Shi ke nan kuma sai tarihi kamar ruwa in sun wuce
        gyabba.

Kabiru: Ba don ƙaunnar wane ba Kabiru jemu na sai ya kashe
                  gora,
Naja’atu: Baƙar wuya da azabar yunwa ta saka al’umma tuna
          bara,
Kabiru: Isa ka kawo tsanda Classic mai nema ai ba ya da tara,
Naja'atu: Lallai mai nema bai tara sai in ba yunwa ya ka ji ba.

Kabiru: Zamfara ba ta mutum ɗaya ce ba gida na gado ne na
        marayi,
Naja’atu: Allah ya jaraba mu Classic ta faɗa hannu na ɓarayi,
Kabiru: Za ta fito da hukuncin Allah ka taimaka Allah mabuwayi,
Naja’atu: Zamfara mu Mamuda muke so Allah ba kwana ya ka yi
        ba.

Kabiru: Kabiru hawan kuka wuya gare shi ba a hawa sai an yi
       dabaru,
Naja’atu: Amma wanda sana’a tai ce hawan miya mi zai yi wa
          daru,
Kabiru: Wutar ga an daɗe da kasha ta ni kuma na so yanzu ta
       huru,
Naja’atu: Idan akwai tafki kusa na san kashe wutar ba za ya daɗe
                   ba.

Kabiru: Tun lokacin da yay yi jawabi tun nan nis san ba ya da
                 wayo,
Naja’atu: Kai bari mamakin shi Classic ɗan duƙushi sharri yaka
                    koyo,
Kabiru: Ruwa idan da rabonka cikinsu zuba ga kwando bai maka
                 yoyo,
Naja’atu: Don haka ɗan Ali ja mu ka kai mu mu kori burgun nan
                   yai laba.

Kabiru: Ku jama’a ga mai ƙaton kai ya zaka ya sace mani hulla,
Naja’atu: Ai ita zai sa wa ran salla mu kuma sai mun sa masa
          ƙwalla,
Kabiru: In taƙamarsa ɓoyon kurya mu sai mun watsa shi ga talla,
Naja’atu: Dama waƙa ce aiki na ban da hasumi ban iya gaba.

Kabiru: Mai iya noman Najeriyag ga duk mun ce mun bar mas
       hauya,
Naja’atu: Mun so mu taimaka a yi noman yac ce shi ya ƙoshi da
         gayya,
Kabiru: Tun jiya ga shi a kuyyar fari don Allah dai Alhaji sauya,
Naja’atu: Komai da shawara yaka kyawo to akasin nan za a ga
           kwaɓa.


Kabiru: Mai kallo na hunta Kabiru to Ali Bagudu yai mani riga,
Naja’atu: Yai maka taggo yai maka wando ba ka da sauran mai
           maka burga,
Kabiru: Jarman Bargu ya riƙe ni amana a rijiya ta kai mani guga,
Naja'atu: In  sha in shayar da Musulmi mun gode ɗan Amadu
          Baba.

Kabiru: Hauka tana ga dogo Kabiru salo da kuri na ga gajeru,
Naja’atu: Kabiru ai kai ma dogo ne sanar da ni don gobe na ƙaru,
Kabiru: Ko ni ina ciki yarinya hauka ta suka ga tsageru,
Naja’atu : Ni ko salon da kac ce gare ni na kama sai nai masa
           ƙwamba.

3.4.8   WAƘAR IBRAHIM GWAGGO
An samu hira a tsakanin Kabiru da Naja'atu a cikin wasu baitoci na wannan waƙar ta Ibrahim Gwaggo. Misali:

Kabiru: Iliminka ya kai ga komai mai daɗin jingina sannu bango,
Naja’atu: Ni dai Classic ina son na tambai ka wurin Maji daɗin mi
        ka hango,
Kabiru: Shi bai halin 'yan siyasa su shanye madara su ce yaro an
      shi gwango,
Naja’atu: Ya tsarkake zuciya tai Maji ɗadi mu ba mu fatan a ce
           bai zamo ba.
Kabiru : Kashin kare ya fi taki a gonarsu sai ɗan sheri kawai zai yi
       noma,
Naja’atu; Ka jawo faɗa Classic da bakinka sai ranar tammaha in
        shigar ma.
Kabiru: Na bar faɗan ba ni yi je ki fanshe ni na koma innuwa in ci
      girma,
Naja’atu: Girman dutse kawai za ya ruɗe ni lallai na yarda ba
          allaƙa ba.

Kabiru: Ni dai Classic komai ya same mu na san Allah ka yi ba
       wani ba,
Naja’atu: Mai garwayen tanadi ɗan maƙwabcin mu ya yo sata tsayi bai
        ga nai ba,
Kabiru: Ya raina kowa gida ko iyayensa sun san sheri yake bai
        baro ba,
Naja’atu: Da in haihi ɗa mai irin ɗabi’unsa har gara na ƙaura ban
         samu ɗa ba.

Kabiru: Kaiwa a hau ai raha in ji kakanmu sai dai ya ce ƙaya na
       magarya,
Naja’atu: Mai son nama farauta ake ba shi shi dai talgin taɓi na
          tukunya,
Kabiru: Ni dai waƙar ga ban yo garaje ba gona ta ruhe gaya
       banya.
Naja’atu:  Mai gaskiya kai riƙe gaskiyarka ba za a gwadama
     kunya gida ba.

Kabiru: Ibrahim Gwaggo ka gadi kakanka gun san Jama’a da son
       tallakawa,
Naja’atu: Ko ni ma nan ina son zurri’arku Naja’atu ce tsasto gun
         Kanawa,
Kabiru: Mu dai Allah muke kai wa kayanmu na san ko dole in
       girmi wawa,
Naja’atu: Lallai da kuɗɗin ƙwarai nas sayo ƙyalla kowa ya lura
          ban sa na yi ba.

Kabiru: Ashe tsaka mai wuya ba a ƙaunarta na sai nonon dala mai
       ƙudahi,
Naja’atu: Duk wanda yah haihu ƙarfi a ‘yayansa ba na sa tammahar zai
        yi ƙarhi,
Kabiru: Nonon da nis so in sha an umurce ni lallai an ce dawon
        dunyi hyahi,
Naja’atu: In ka sai wanda ba don ni ba Kabiru ai dambu za ka sha
         ba fura ba.

Kabiru: Mutane Jama’a ku kalle su in kura ta wuce ga ƙasa nan,
Najaatu: Can da iyaye ake wa da matansu to yanzu ni na faɗi ga
        ɗiya nan,
Kabiru: Ibrahim Gwaggo mai so ya cuce ka mu dai mun ce bari
                  nan gani nan,
Naja’atu: In Allah ya yi gwarzo mutanen mu ƙaryar wancan ya ce
         bai zamo ba.

Kabiru: Fagen siyasa a Shinkafi zan tare don aiki na wa mai
        gida na,
Naja’atu: Ko ni Classic ina so na rakke ka amma in ya bari mai
           gidana,
Kabiru: Zan je wajen nasa in Jalla ya yarda ko da Maji daɗi zan
        sanya rana,
Naja’atu: Allah yake fidda shuka mutanenmu ba wai ruwa ko
                     yawan ƙoƙari ba.

3.5     KAMMALAWA
A wannan babin an kawo ma’anar Salo da kuma ma’anar Salon hira, tare da yadda ake gane hirar a cikin waƙoƙin. An kuma kawo sunayen abokan hirar Kabiru Classic tare da kawo wasu waƙoƙin da suka yi hirar a cikinsu.

Babai na Huɗu: Kammalawa
4.0       Gabatarwa
A wannan babin za a yi bayanin kammalawa ne da yadda tsarin aikin ya kasance tun daga babi na farko har zuwa na ƙarshe. Wannan babi ya ƙunshi waiwaye da sakamakon bincike da waɗanda aka yi hira su da kuma Rataye.
4.1      Waiwaye
Hausawa na cewa ‘waiwaye adon tafiya’. Don haka za a dubi ayyukan da suka gabata na masana, domin ganin irin koƙarin da suka yi wajen fito da ma’anar salo da ireirensa, musamman masana irinsu Yahya, Sa’idu Gusau, Ɗangambo, Sa’id, Guban da makamatansu. Ga irin yadda kowannen su ya kalli ma’anar salo  kamar haka:
Ɗangambo (1981) Ya bayyana salo da cewa “Salo shi ne yadda mawaƙi ya zana tunaninsa a takarda".
Sa’id (1981) yana ganin cewa “Salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo”,
Guban (1993) ya bayyana salo a wakokin Hausawa da cewa “Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi yake kyautata zaren tunaninsa ya sarrafa shi cikin azanci don ya cimma burinsa na isar da sako ko waƙa".
Yahya (2001) ya bayyana salo da cewa “Salo yana nufin duk wata dabara ko hanyar yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa”.
Gusau (2002) cewa ya yi “Salo wata hanya ce da ake bi a nuna gwaninta a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta yanayin harshensa da zaɓar abubuwan da suka dace da abin da yake son bayyanawa”.
Ta la’akari da waɗannan ma’anoni daga bakin masana kuma magabata ya sa aka karkata akalar wannan aikin akan salon hira a cikin wakokin Kabiru Classic inda aka dubi wasu waƙoƙinsa kamar waƙar Sarkin Gobir da waƙar Sarkin Ɓurmin Jabo da waƙar Hana Kishiya Waƙar Miji da waƙar Gaskiya Takobin Yaro da waƙar Rayuwa Dukiyar Ɓoye da waƙar Ciroman Wamakko da waƙar Ganin Ido da kuma waƙar Ibrahim Gwaggo.
4.2      Sakamakon Bincike
Wannan aiki ya gano cewa ana samun salon hira ta hanyoyi da dama a cikin waƙoƙin Kabiru Classic, wanda yake yin hirar tare da abokan waƙarsa. Kaɗan daga cikin hanyoyin da aka samu salon hirar a cikin waƙoƙinsa akwai:
1. Ta hanyar tambaya.
2. Ta hanyar musu .
3. Ta hanyar roƙo .
4. Ta hanyar kirari.
5. Ta hanyar zambo.
6. Ta hanyar habaici.
7. Ta hanyar ba da labari.
Waɗannan su ne manyan hanyoyin da aka fi samun hira a cikin waƙoƙin Alhaji Kabiru Yahaya Classic.
4.3      Shawarwari
Shawara abu ce mai muhimmanci ƙwarai, da wannan ne ya sa aka ga ya dace a keɓe wani sashe a cikin wannan kundi domin ba da shawarwari a matsayin gudummuwa wajen fito da salon hira a cikin Waƙoƙin Kabiru Classic. Ga wasu daga cikin shawarwari, musamman ga ɗalibai da malamai da manazarta masu nazarin Adabin Hausa musamman abun da ya shafi waƙa.

1.           Wannan bincike na bayar da shawara kan yin nazarin salo a cikin waƙoƙin Hausawa, domin ƙara haɓɓaka harshen Hausa.

2.           Nazarin salo na ƙara bunƙasa tunanin mai yinsa, don haka wannan bincike na bayar da shawara kan mayar da hankali wajen nazarin salo musamman a cikin waƙoƙi.

3.           Nazarin salo abu ne da ke fito da wasu keɓaɓɓun kalmomin harshe, ke nan nazarin salon na bunƙusa harshe. Don haka wannan bincike na bayar da shawara kan mayar da hankali a kan nazarin salo domin ƙara bunƙasa harshen Hausa.

4.           Haka kuma wannan bincike na bayar da shawara musamman ga ɗalibai da su duƙufa wajen nazarin waƙa domin fito da irin hikimomin da ke ciki.

5.        Salo abu ne mai faɗin gaske, don haka wannan kundi na bayar da shawara kan cewa, mai nazarin salo ya zurfafa wajen nazarin salailai  gwargwadon  iyawarsa.

Manazarta


















Post a Comment

0 Comments