Fahimtar irin farin jini da kwarjinin da ke ga ƙagaggun labaran Hausa, musamman iri su Ruwan Bagaja da Ganɗoki da Shaihu Umar da Jiki Magaya da makamantansu a idon malamai da ɗalibai, tun a makarantun firamare da sakandare da na gaba da sakandare, har zuwa jami’o’in Arewacin ƙasar nan, har ma da waɗanda suka yi yaƙi da jahilci, da kuma ganin irin yadda masana da manazarta fannonin al’ada da adabi da harshen Hausa suka yi rubuce-rubuce da dama a kan abubuwa da dama a fagen ilimi. Misali a dubi yadda manya-manyan Farfesoshi da Doktoci na jami’o’i daban daban na ilimi kamar su hamsin da ɗaya (51) suka yi rubuce rubuce a kan littafin Ruwan Bagaja mai suna...

-----------------------------------
DAGA
GARBA UMAR GUSAU
--------------------------------------
TSAKURE

Fahimtar irin farin jini da kwarjinin da ke ga ƙagaggun labaran Hausa, musamman iri su Ruwan Bagaja da Ganɗoki da Shaihu Umar da Jiki Magaya da makamantansu a idon malamai da ɗalibai, tun a makarantun firamare da sakandare da na gaba da sakandare, har zuwa jami’o’in Arewacin ƙasar nan, har ma da waɗanda suka yi yaƙi da jahilci, da kuma ganin irin yadda masana da manazarta fannonin al’ada da adabi da harshen Hausa suka yi rubuce-rubuce da dama a kan abubuwa da dama a fagen ilimi. Misali a dubi yadda manya-manyan Farfesoshi da Doktoci na jami’o’i daban daban na ilimi kamar su hamsin da ɗaya (51) suka yi rubuce rubuce a kan littafin Ruwan Bagaja mai suna: Ruwan Bagaja In Perspectives: Eight Decades Of Hausa Masterpieces In Prose (1933—2013). Wannan shi ya ba ni sha’awa da in yi wani nazari a kan littafi Shaihu Umar. Don haka, wannan nazari zai yi bayani a kan abubuwan da suka shafi taƙaitaccen tarihin marubucin littafin. Sannan a dubi littafin cikinsa da wajensa, musamman ta la’akari da al’adu da ɗabi’un Hausawa da nazarin ya hango sun yi naso a cikin littafin. Haka kuma, nazarin zai dubi jigon littafin a matsayin ƙashin bayan rubuta littafin. 

1:1     GABATARWA
Littafin Shaihu Umar, wanda Abubakar Tafawa Ɓalewa ya rubuta a shekara ta 1933 aka kuma wallafa shi a shekara ta 1934, shi ne littafi na uku a jerin littattafan da hukumar buga littattafai da sayar wa ta Arewacin Nijeriya da ke Zariya (NNPC) ta buga. Baya ga littafin Ruwan Bagaja na  Abubakar Imam da littafin Ganɗoki na Bello Kagara, idan aka yi la’akari da tsarin gasar da ta samar da littafan ƙagaggun labarai ta shekarar 1933, a ƙarƙashin jagorancin Dokta R.M.East. A cewar, Malunfashi, (2004:5).
A cikin shekarar 1933 ne hukumar Fassara da Talifi
Ta ga ba a sami littattafan adabi da take buƙata ba.
Don haka, ta shirya gasar farko da ta taimaka wajen
Samar da littattafan ƙagaggun labaran Hausa na farko
Ta fuskar zube.”
A nan ana iya cewa, Hukumar Talifi ta samu littattafai da dama a matsayin karɓa kiran wannan gasar. Da yawa daga cikin littattafan da aka rubuto wa Hukumar sun dace da tsarin buƙatun gasar. Lokacin da Hukumar ta zo buga littattafan waɗanda suka lashe gasar, sai da ta tace su sosai, sannan ta fitar da sakamakon gasar kamar haka:
1.     Ruwan Bagaja na Abubaka Imam.
2.     Ganɗoki na Bello Kagara
3.     Shaihu Umar na Abubakar Bauci
4.     Idon matanbayi na Muhammadu Gwarzo
5.     Jiki magayi  na R.M.East da Tafida.
Da ma wasu waɗanda Hukumar ba ta sami damar buga wa ba, saboda wasu dalilai kamar littafin Boka Bowaye na Muhammadu Nagwamatse da littafin Yarima Abba na Muhammadu Jumare Zariya da dai sauransu. Shi dai wannan littafi  na Shaihu Umar ya ƙumshi abubuwa na fagen ilimi waɗanda suka haɗa da al’adun Bahaushe da ɗabi’o’insa da harshensa.

1:2     TAƘAITACCEN TARIN MARUBUCIN LITTAFIN SHAIHU UMAR
Sunan marubucin littafin Shaihu Umar shi ne, Sir. Abubakar Tafawa. An haife shi a wata unguwa da ake kira Ɓalewa da ke cikin garin Bauchi a yau, 23 ga watan huɗu (Afirilu) a shekara ta 1912. Sunan mahaifinsa Bageri (hakimin Lere). Sunan mahaifiyarsa Amina. Ya fara karatunsa na allo a garin Bauchi. Ya fara karatunsa na zamani (makarantar boko) a Elimantare a nan garin Bauchi daga nan ya wuce makarantar Katsina kwaleji. Bayan ya kammala karatunsa a wannan makarantar, sai ya dawo gida Bauchi ya kama aikin malanta a makarantar Midil Sukul ta Bauchi a shekarar 1944. Yana a cikin wannan aikin ne aka zabe shi tare da wasu malamai ‘yan Arewa zuwa Jami’ar London, inda suka yi wani kwas na sanin makamar aikin malanta na shekara ɗaya.
Dawowarsa ke da wuya, sai aka naɗa shi mai kula da malamai a makarantun Elimantare (wato Inspector). Daga nan ne ya shiga siyasar NPC (Northern People Congress)  ta su Sir. Amadu Bello (Sardaunan Sakkwato) Firimiyyan jihar Arewa a shekarar 1946. Marigayi Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa, Firayim Ministan Nijeriya na farko ya rasu a shekarar 1966, yana da shekara 53. Ya rasu ya bar ‘ya’ya maza shida da mata biyar da jikoki da matansa na aure 4. Allah ya jiƙansa da rahamarSA. Allah ya gafar ta mana da mu da uwayenmu da malamanmu da duk kan musulmai.

1.3     AL’ADUN HAUSAWA A CIKIN LITTAFIN SHAIHU UMAR
Abin da ake nufi da al’ada shi ne, hanyoyin gudanar da rayuwar ɗan Adam ta yau da kullun. Al’ada abu ce, da ta shafi rayuwa tun ranar gini, tun ranar zane. A cewar Bunza, M. A. (2006:7) ‘’Al’ada tana nufin duk kanin rayuwar ɗan’Adam ce tun daga haifuwarsa har zuwa kabarinsa.” Shi kuwa Ɗangambo, A. (1987:5) cewa ya yi, “ Al’ada ita ce, sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama’a na cikin al’umma suka amince da ita.” A taƙaice, al’ada wata abu ce wadda ta shafi abin da rai ya riga ya saba da aiwatar da shi har ya zamar masa jiki.
Littafin Shaihu Umar, littafi ne da ya ƙumshi al’adu da ɗabi’un Hausawa tsintsarsu. Kama da zaman iyali na namiji ya auri macce fiye da ɗaya, da zaman fada a masarauta, da sana’ar noma, da sana’ar farauta, da yin hijira, da fita neman arziƙi, da almajiranci da tawakkali ga Allah, da yarda da ƙaddara mai kyau ko mummuna da sauransu. A falsafar dangantakar iyali tsakanin magidanci da iyalinsa, idan aka ce iyali, a iya cewa kawai ma’ana iri biyu a nan. Ma’ana ta fako ita ce, wadda wasu suka ɗauka cewa, iyali sun haɗa mutum da matarsa ko matansa da ‘ya’yansa kurun. Ma’ana ta biyu kuwa, wasu sun ɗaukai cewa, abin da ake cewa iyali shi ne, magidanci da matarsa ko matansa da ‘ya’yansa da duk wanda yake ƙarƙashin kulawar wannan mai gidan. Wannan yana iya haɗa mahaifiyarsa da mahaifinsa da ƙannansa da barori, in dai shi ke kulawa da cin su da tufafinsu da wurin kwanciyarsu.
Ga al’ada a ƙasar Hausa, tsarin zamantakewar iyali a gidan Bahaushe miji ko maigida shi ne shugaba a gidansa. Matarsa ko matansa da ‘ya’yansa, har ma da yaran gida masu yi masu hidima suna a ƙarƙashinsa a matsayin mabiya. Mai gida ne zai ɗauki nauyin ciyar da mazauna a gidan. Shi ne kuma zai yi wa kowa tufafiin saka wa, ya kuma ba su makwanci. Haka kuma shi ne, wanda zai shirya masu irin ayyukan da kowane za yi, ya kuma tabbatar da kowa ya yi aikin da aka ba shi. wannan shi ne,tsarin zama na Bahaushe na asali, inda yake zaune a cikin babban gida tare da magidanta fiye da goma kowane magidanci da nasa yanki a gidan, inda yake tare da nasa iyalin, duk dai a ƙarƙashin “Uban-gandu”.
 Uban gandu shi ne, dattijon gida da ya haifi magidantan wannan gidan nasa da yake da shiya-shiya, inda kowane magidanci yake da tashi shiyar, duk a ƙarƙashi kulawarsa. Ga al’ada, kowane magidanci zai zo shiyar wannan mai gidan nasu (Uban-gandu) da safe, don ya yi masa “ina kwana?” har matansu da jikokinsa, suma zasu zo, domin yi masa ‘ina kwana?’tare da nasa iyalin. Haka irin wannan tsari na iyali ya gada a wajen Bahaushe a ƙasar Hausa.
Abu na farko da wannan nazari ya duba shi ne, tsarin iyali da zamantakewar Bahaushe a cikin iyalinsa. A lokacin da Makau ya ji Sarki ya ce, na koreka daga wannan gari. ‘Ka tafi can wani wuri da ba a hannu na ba.’ Sai Makau ya yi godiya ga Sarki ya taso, ya zo gida, ya tara iyalinsa babba da yaro, maza da mata, ya ce da mu,
“To, kun ga yadda Allah ya ƙaddara wannan al’amari
bisa gare ni.---Duk iyali sai muka fashe da kuka gaba
  ɗaya, muna cewa, wallahi tallahi ba wata ƙasa da zaka
                 tafi ko da lahira ce, in ana rakiya, lalle ba shakka, ma raka ka.”[1]
Wannan bayani ya nuna yadda Bahaushe yake zaune da iyalinsa, da kuma yadda al’amurra suke gudana na shawara tsakaninsa da iyalinsa.
Abu na biyu da wannan nazari zai yi tsokaci a kansa shi ne, al’adar zaman fada ga fadawan sarki a nan ƙasar Hausa. Alal-misali a cikin littafin an nuna cewa:
“mahaifiyar Umar ta so ta yi aure, domin masoya
da yawa sun fito nemanta aure, a cikinsu har da
          wani Bafade na kusa da Sarki ainun wai shi Makau.”[2]
Shi aure wajibi ne ga ɗiya macce, muddin dai ta kai minzalin shekarun aure, ta kuma samu masoyi mai nufin ya aure ta. Don haka, shawarar da uwar Umar ta yanke na ta yi aure ya yi. Duk da cewa, ita Bajawura ce, tana da wata dama irin wadda Budurwa ba ta da ita, ta yin gaban kanta ga sha’anin aurenta, saboda haka ne ta nemi shawarar kakarta bisa al’adar Hausawa.
Abu na uku shi ne, al’adar yaye, wadda ake yi wa yaro ko yarinya, idan kowanensu ya kai shekara ɗaya da wata bakwai bayan haifuwa a al’adance. Al’adar yaye yaro ko yarinya a ƙasar Hausa ita ce, uwaye ba su kan yaye yaransu da kansu ba, musamman ‘ya’yansu na farin. Sai dai su miƙa su ga danginsu na wajen uwa ko uba, can nesa da su. Abin da ake nufi da yaye shi ne, cire yaro ko yarinya daga ba su nonon uwa. Amam kuma ga al’ada ba laifi ba ne a bar yaro ko yarinya su wuce shekara ɗaya da wata bakwai, idan uwaye sun lura da wata matsala da zata iya faruwa ga yaronsu ko ɗiyarsu. matsala kamar ta rashin girma ko ƙiba ko rashin miƙewa tsaye da wuri. Misali a cikin littafin an nuna cewa:
‘’Da aka yaye Umar, sai aka bar shi a wajen kakarsa”[3]
Wannan bayani kuwa haka abin yake dangane da al’adun Hausawa wajen yaye. Wato, kakanni suna da hannu a wajen hora da tarbiyya yaran da suka raina
Abu na huɗu shi ne, al’adar munafunci da aka san wasu fadawan fada da yi wa juna, domin neman shiga ga Sarki. Ga abin da fadawa suka cewa Sarki game da Makau:
‘’Bari dai mu feɗe maka biri har wutsiya. A garin nan ba
ka taɓa samun wanda yake cin amanarka kamarsa ba
(wato, Makau ke nan). Ai Makau ne yake fallasa ka
                     a wajen talakkawanka da kake ganin suna girman kan nan yanzu.”[4]
Kamar dai yadda labarin ya nuna Makau, wanda yake da fada a wajen Sarki ya haɗu da makirci da ƙiyayya daga fadawa ‘yan’uwansa, har suka ɓata shi ga sarki. Wannan makirci ya zama sanadiyar korarsa daga garin baki ɗaya. Wannan shi ne tarihi, wanda ya nuna mana halayyar fada da kuma fadawa ta fuskar Sarauta a da, da kuma yanzu.
Nason wata al’ada ta biyar ta Bahaushe da zamu iya gani a cikin littafin Shaihu Umar ita ce, ta ɗaura laya ko karhu ko guru ko daga, don kariyar kai da kaya (dukiya) daga harin ‘yan fashi (ɓaraayi). Dubi dai yadda ya zo a cikin littafin;
“Sai Maharbin ya kawo wata ‘yar laya
mai sasari ya ba shi, y ace masa, wannan
ita ce abar da na taimake ka da ita.
      Kuma ina tafan ka isa lafiya. Allah ya kausa ɓacin rana.”[5]
A ƙarƙashin wannan labara akwai al’adun Hausawa masu yawa, kyawawa abin koyi ga matasan yanzu. Waɗannan al’adu kowa sune, an taimako da aka san Hausawa da su ta hanyar aikin gayya. Ba shakka, taimaka wa juna da shawara, wannan aikin Hausawa ne ba tun yau ba. Domin Musulunci ma ya ƙarfafa aikata haka. Wato, a taimaka wa mutum baƙo da masauki (gida ko ɗaki) har ma da gona ko mata ya aura duk yana da ga cikin aikin Bahaushe a wancan zamani. A dalilin haka, ga al’adarsa ya samar da gidan baƙi, yanzu kuwa sai jefi-jefi.
Nason wata al’adar ta Hausawa ta shida a cikin littafin Shaihu Umar ita ce, ta sana’ar noma. Ga abin da marubucin littafin yake cewa:
‘’Domin buƙatata yayin da na sami matsugunni sosai,
        sana’ar da zan yi ita ce, noma.’’
          Sana’ar noma ga Bahaushe, al’adarsa ce, gadaddiya tun kakanni da uwaye. A cikin wannan shafi na 12 mai kan labarin ‘Ka Zauna A Maƙarfi’’. Maharbin da suka gamu da Makau a cikin daji yana ba shi shawara cewa, ‘ya tafi Maƙarfi domin mutane garin sanannu ne wajen aikin gonaki, noma a can yana da riba, amfaninsu kuwa kullun mai albarka ne.’’[6]
Ga hoton wata al’adar ta Hausawa ta bakwai, duk a cikin wannan littafi na Shaihu Umar. Wannan al’ada kuwa ita ce, ta neman ilimin addininsa na Musulunci musamman karatun allo. Al’adar Bahaushe ce a nan dai ƙasar Hausa, idan yaro zai fara karatun Allah, to a makarantar allo za a kai shi, kuma da allo zai fara da zarar ya isa ya riƙe allon. Zai kuma fara da ƙidan baƙi ne. Dubi abin da marubucin littafin ya ce:
‘’Na yi ta karatu, har wajen shekara biyu na sauke.
Na sauke Alƙur’ani ranar laraba sha tara ga wata
                                 Muharran’’[7]
Baya ga wannan al’adar ta yin karatu da allo a makarantar allo, akwai al’adar bara, wadda Bahaushe ya tsinta daga baya, kuma ta zama jiki ga wasu daga cikin Hausawa, musamman a nan Arewacin Nijeriya. A inda Bahaushe yake ƙetarewa har ƙasashen waje domin ya yi bara. Kuma wannan ƙirƙirar al’ada tana janyo wa Hausawa faɗuwar daraja ga masu kishin Hausa da Hausawa.
Al’adar bara, ɗabi’a ce wadda ba ga Bahaushe kai ta tsaya ba, har Larabawa da sauran ƙabilu ma wasu daga cikin su suna aiwatar da ita. Amma kowa ya san cewa, bara da mola suna zubar da mutuncin mai yinsu. Addinin Musulunci bai yarda da yin bara ba, in ba ya zama dole ba. In kuma irin wannan lalora ta sami mutum to, sai ya nemi taimakon jama’a dai-dai buƙatarsa ta hanyar yin baran. Haka kuma shari’ar Musulunci ta yi hani da mai bara ya mayar da ita sana’a.  Ga dukkan tsammani na ire-iren waɗannan lalorori suka shigo da wasu gwamnonin wasu jihohi su hana gudanar da bara a nasu jihohin. Al-misali jihohin Kano da Jigawa da Abuja da Legas. Sun yi haka ne kuwa, don kare mutunci addinin Musulunci da Musulmai Hausawa da ma Arewa baki ɗaya.
Illolin yin bara suna da yawa, amma wasu daga cikin su sun haɗa da:
1.     Faɗuwar mutunci, musamman ga masu yin mola.
2.     ‘Yan ɗauke-ɗauke na kayan mutane, musamman a cikin gidajen mutane, wanda ake zargin almajirai da aikatawa.
3.     Yawon talla da yawon banza a gidajen karuwai da wanke-wanke a gidajen abinci da tasha mota.
4.     Da fama da raga (tsumma a jiki), da dauɗa. Ga kirci da ƙaswa da ƙeya.
5.     Ga fama da yunwa, saboda ƙarancin abinci, da sauransu.
Ire-iren waɗannan matsaloli suna da wuyar magancewa ko ga gwamnoni jihohin da suka nemi hana bara. Saboda manyan almajiran ba su son su bari, haka ma malaman nasu. Gwamnonin ma ba da gaske suke yi ba.

1.4     AL’ADAR HAUSAWA TA YAKE-YAKE DA KAI WA JUNA HARI
          Al’adar Hausawa ta kai wa juna yaƙi da kai hari a ƙauyukka da garurwa, har ma da birane a duk lokacin da aka tsara al’ada ce, domin a faɗaɗa ƙasar mulki da mallakar bayi, domin a sayar a sayi makamai. Don haka, akwai irin wannan al’adar da yi tasiri a cikin zuciyar marubucin littafin Shaihu Umar, waɗanda zamu ga hotonsu a cikin littafinsa. Alal-misali a cikin littafin an nuna cewa, Sarki ya sa an tara masa fadawansa a nan fada yana gaya masu cewa:
‘’Ba wani abu ne ya sa na kira ku ba, abin da nake so
     Game da ku shi ne, ku yi shiri, ku tafi, ku yi hari a can
      ƙasar Gwari. Ina da wata babbar buƙata ne.’’[8]
Wannan al’ada ce ta galibin manyan sarakunan ƙasar Hausa, wadda ko a wancan zamani ba kowa ke yin wannan ba, sai da wani babban dalili. Wannan ya nuna yadda Sarakunan ƙasar Hausa ke dogaro a kan bayi wajen biya masu wasu buƙatu na yau da kullun.
Wata al’adar ta Hausawa ta nuni ga daidaituwar tasirin Musulunci a cikin su ita ce, ta yin tawakkali ga Allah a kan duk wani abu mai kyau ko marassa kyau ne ya faro a kansu. Kasancewa galibi Hausawa Musulmai ne, sukan yi tawakkali su bar duk wani abu da ya faro a garesu mai sosa rai ga Allah mahalaccen kowa. To, irin haka ne ya faro ga mahaifiyar Umar da Makau da ma wasu masoya Makau da suka ji labarin cewa, Sarki ya sa a fidda makau daga garinsa. Sai suka yi baƙin ciki, wasu suna kuka saboda baƙin ciki, waɗansu ma suna ba shi ‘yan kuɗi waɗanda zai riƙe a hannu ko ruwa ya sha a hanya. Wannan al’amari ya kai gaya, domin ya tarar da mahaifiyar Umar tana kuka, sai ya ce:
  ‘’Wannan abu ba na kuka ba ne, ya wuce kuka.
Ko ba haka ba, tun da yake musulma ce ke, ya kama ta
Ki tuna cewa, dukan abubuwa daga Ubangiji (Allah)
Suke samun mutum. Saboda haka, abin da ya fi kyau
A gare mu duka, sai mu yi tawakkali ga Allah, wanda
     Ke aikata komai yadda ya so.’’[9]
Baya ga wannan al’ada ta yin tawakkali ga Allah da aka san Bahaushe da ita, duk da cewa, ba kowane musulmi Bahaushe ke da tawakkali ba da yin amanna da ƙaddara mai kyau ko mummuna ba, amma ba a rasa na Allah ko yaushe. Dangane da wannan labari akwai nuni a kan haka a shafi na 9 a cikin wannan littafin kamar haka:
‘’ To, kun ga yadda Allah ya ƙaddara, wannan al’amari
Bisa gare ni. Sarki ya ce, sai in bar masa ƙasarsa”
Jaddada wannan bayani ya fito fili a lokacin da Makau ya haɗu da Maharbi. Makau ya yi masa bayanin halin da yake ciki. Sai Maharbin ya ce, ‘Haƙiƙa, yadda Allah ya ƙaddaro abu haka yake faruwa.”  Mai gaskiya har abada bai taɓa taɓewa. 

1.5 TASIRIN RAYUWAR HAUSAWA A CIKIN LITTAFIN SHAIHU UMAR
 Tasirin rayuwar Hausawa game da imani a kan ƙaddara mai kyau ne ko akasin haka, Hausawa musumai sun yarda abu ne daga Allah yake. Kuma Allah ne ke da cikakken ikon ƙaddara komai a kan ɗanAdam. Wannan tasirin rayuwar Hausawa na yarda da ƙaddara shi ne ya gina wannan littafi na Shaihu Umar. Wannan shi ne jigon littafin Shaihu Umar. Don mu tabbatar da abin da muka faɗa, muna iya kawo misalai biyu ko uku a cikin littafi:
Da farko dai an haifi Umar bayan rasuwar mahaifinsa, wanda hakan ya mayar da shi maraya. A mafiyawan lokuta, idan yaro maraye ne ba kasafai yakan ji daɗin rayuwarsa ba. To, amma a wannan halin kamar yadda Allah ya ƙaddara. Sai ita mahaifiyar Umar ta auri Makau (wani babban bawan Sarki). Wani mutunen kirki da sanin ya kamata, wanda ya nuna wa Umar (agolansa) so da ƙauna ta kowane hali. Babu shakka, Makau ya nuna hali na gari, kamar dai yadda Hauswa suka aminta suka yarda mutunen kirki ya kasance kuma ya yi.
Abu na biyu shi ne, irin baƙin ciki da iyalin Makau suka samu kansu a ciki a wani ɗan ƙanƘanen lokaci aka raba mai gidansu (Makau) da muƙaminsa da gidansa da garin baki ɗaya. A nan mun ga abin da Allah ya ƙaddara a kan Makau. Kamar dai yadda shi ma ya ce, a lokacin da ya isko matarsa tana kuka dangane da abin da ya sami mai gidanta kamar haka:
‘’Tunda yake ke musulma ce, ya kamata ki nuna
  cewa, dai dukkan abubuwa daga Ubangiji suke
                        samun mutum. Haka Allah yake aikata komai yadda ya so’’[10]
Ƙarin bayani a kan irin wannan ɗabi’a ta yarda da ƙaddara muna iya ganin ta a cikin wannan littafin kamar haka;’ a lokacin da Makau ya sauka a Maƙarfi, ya zauna, sai Allah ya yi masa baiwar samun arziki, har ya aika wa Sarkin Kagara da Sarkin Zagi da Shantali wasu kyaututtuka. Wannan ma wani abu ne da Allah ya ƙaddara. Bayan waɗannan misalai ana iya samun wasu misalan da dama. Ga misali, dubi dai ƙaddarar sace Umar bayan da mahaifiyarsa ta tafi Fatika, da kuma kuɓutar da yi lokacin da kura ta cinye wanda ya sace shi.

1.6     NAƊEWA
          Dangane da darussan koyo a cikin wannan littafi, akwai halaye da al’adu masu kyau da kowane Musulmi ya kamata ya koya, ya kuma aiwatar. Na farko dai riƙo da haƙuri. Haƙuri yana kai mutum ga nasara. Domin mun ga yadda Shehu Umar ya yi haƙuri da wahalhalu da ya sha tun haifuwarsa har zuwa ƙas ashen Larabawa, a inda ya yi karatu mai zurfi na muhammadiyya. Sakamako ya zama wani babban malami, masani a fannunin ilimi a idon jama’a. Don haka, wannan ya nuna mana cewa, kafin mutum ya ci nasara, har jama’a su san shi dole sai ya sha wahala matuƙa. Saboda haka, tare da wahala, akwai nasara. Kuma idan dai har muna son mu cimma burinmu na duniya da na lahira, dole ne mu yi aiki tuƙuru. Haƙiɗa idan muka yi haka zamau samu duk irin nasarar da muke su.
          Abu na biyu shi ne, kyautatawa. Idan mutum ya yi maka sharri, to kai kyautata masa. Kamar yadda tarihi ya nuna mana ɗabi’un manzonmu Annabi Muhammadu (SAW). Idan an zalunce shi, yakan mayar da alheri, muddun ba haƙin Allah aka taɓa ba. A cikin wannan littafi na Shaihu Umar, mun ga yadda aka zalunci Makau. Shi kuma ya mayar da alheri.
          Wani abin lura shi ne taimako. Taimako wajibi ne ga wanda ya cancanta a yi masa. Mun ga yadda Maharbi ya taimaki Makau da irin gudummuwa da Makau ya samu a wajen iyalinsa da abokanan zama, waɗanda suka riƙa ba shi kyautar kuɗi da ban- hanƙuri a lokacin da Sarki ya kore shi garinsa.
          Da ƙarshe, ya kamata mu lura da abubuwan assha da yin tir da suka faro a wancan zamani. Waɗanda marubucin wannan littafi ya zo da su a cikin littafinsa. Waɗanda suka jawo tashin hankali, kamar bauta da kuma cinikin bayi. Waɗannan abubuwa sun jawo halakar ɗuruwan mutane a banza, ba gaira-ba-dalili.

MANAZARTA[1] Don }arin bayani duba shafi na 9 na littafin.1
[2] A  duba shafi na 3 na wannan littafin.
[3] A  duba shafi na 2 a cikin littafin.
[4] Don }arin bayani duba shafi na 5 na wannan littafi.
[5] Don }arin bayani duba shafi na 12 na shi wannan littafin.
[6] Duba shafi na 12 na wannan littafin Shaihu Umar.
[7] A nan ma kana iya duba shafi na 37 domin }arin bayani.
[8] A duba shafi na 8 don }arin bayani.
[9] Don }arin bayani duba shafi na 9 da na 11 da na 25.
[10] Sake duba shafi na 9 na wannan littafin don }arin bayani.