Ticker

6/recent/ticker-posts

Samun Gafarar Zunubai na Kwana Goma a Ranar Juma'a



Kankare zunubai daga Juma'a zuwa wata Juma'ar ba ya samuwa sai ya ciki Sharuɗɗan da aka ambata a cikin hadisi. Sharuɗɗan su ne kamar haka:

Samun Gafarar Zunubai na Kwana Goma a Ranar Juma'a

Abu Aysha

Daga Salmanal Farisy رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ, yace;Manzon Allah SAW yace;
(Babu wani mutum da zaiyi wanka ranar juma'a kuma ya tsarkaka gwargwadon iko na tsarkinsa, kuma ya shafa mai daga mansa, kuma ya sanya turare, sannan ya fita zuwa masallaci, bai ƙetara tsakanin mutum biyu ba, sannan ya sallaci abinda aka wajabta masa, sannan yayi shiru a lokacin da Liman yake Huɗuba, face an gafarta masa tsakanin wannan juma'ar zuwa wata juma'ar)
@صحيح البخاري-رقم:(883).
A wata riwar acikin Saheehu Musulim;
(. . . . . Da karin kwana ukku. . . . )
@صحيح مسلم
ابن حجر رَحِمَهُ اللهُ تَعَالَى:-
Yana cewa;
Kankare zunubai daga Juma'a zuwa wata Juma'ar ba ya samuwa sai ya ciki Sharuɗɗan da aka ambata a cikin hadisi. Sharuɗɗan su ne kamar haka:

Yin wankan Juma'a
Yin tsafta da gyaran jiki da tufafi
Sanya turare mai dadin ƙamshi da shafa mai
Sanya tufafi mai kyau
Tafiya masallaci cikin nutsuwa
Kada ka ƙetara tsakanin mutum biyu
Kamewa daga chutar da wani
Kuma kayi nafilar gaisuwar masallaci
Kuma ka yi shiru ka saurari huɗuba
Kuma ka baryin Lagwu lokacin huɗuba
Ka fuskanci Liman lokacin da yake Huɗuba
@فتح الباري:(372/2)
  Allah ne mafi sani

Post a Comment

0 Comments