Ticker

6/recent/ticker-posts

Sa’a Wadda Ta Fi Manyan Kaya: Nason Tsafi Ko Waninsa (Albiris) A Al’adar Aure A Garin Bungudu

Daga

Haruna Umar Bungudu
Kibd’au:harunaumarbungudu@gmail.com
Lambar waya: 08065429369

Da

Haruna Umar Maikwari
K’ibd’au: maikwariharuna@gmail.com
Lambar waya: 07031280554

Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi da Kere-Kere Ta Gwamnatin Tarayya,  Gusau. Jihar Zamfara.


Paper Presented To The Department Of Nigerian Languages, Bayaro University Kano, At The 1st International Conferance on Hausa Studies In The 21st Century, On Monday 10th – Thursday 13th November, 2014.

www.amsoshi.com

Tsakure.


        Wannan Muk’alar za ta yi tsokaci ne dangane da wasu al’adun aure wad’anda aka gudanar a garin Bungud’u masu nason maguzanci ko tsafi, wannan al’ada ita ce ake kira “Albiris”. Takardar za ta kalli dalilan da suka sa Hausawan wannan yankin gudanar da ita tare da muhimmancinta. Haka kuma takardar za ta binciko yadda ake gudanar da wannan al’adar mai kama da tsafi har da masu yin ta da kuma dokokinta.

 

GABATARWA


Garin Bungud’u wani gari ne da ke cikin yankin Zamfara wanda yake kimanin kilomita goma sha shida daga babban birnin jihar Zamfara wato Gusau. Kasancewar jama’ar wannan gari Hausawa ne mafi yawansu sai kuma Fulani. Jama’ar garin sun had’a da Katsinawa da Gobirawa wad’anda akasarinsu Hausawan ne ko kuma Fulani. K’asar Bungud’u ta yi iyaka da k’asar Maru da Maradun ta gefen Yamma, ta yi iyaka da Gusau ta Gabas. Sannan ta yi iyaka da k’asar Anka da ‘Dansadau a ‘bangaren Kudu, a sashin Arewa kuwa ta yi iyaka ne da k’asar K’auran Namoda.

K’asar Bungud’u k’asa ce mai fad’in da albarkar noma, kuma akwai gulbin Sakkwato wanda ya ratsa gefen garin, ya fito daga Gusau zuwa nan Bungud’u ya zarce Maru har dai zuwa Sakkwato. (Gusau, Babu shekarar bugawa).

1.1 Ma’anar Al’ada


        Wani masanin cewa ya yi “Al’ada ita ce tarsashin rayuwar mutum tun daga haihuwarsa har zuwa balagarsa da girmansa da mutuwarsa (Ibrahim, Y. Y. 1977).

Al’ada sababbiyar hanyar rayuwa ce wadda akasari jama’a na cikin al’umma suka amince da ita. (Gusau, S.M. 1986).

Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar d’an Adam tun daga haihuwa har zuwa kabarinsa (Bunza, 2006).

Babu tabbacin cewa al’ummar garin asalinsu maguzawa ne amma dai wasu al’adun irin wad’annan da suke gudanar ne ke sa a rik’a ganin wani d’an nason hakan a cikinsu, wato dai abubuwa irnsu albiris kan nuna cewa kamar wata bauta ce mutanen ke yi wa rana. Domin hak’ar wannan binciken ta cim ma ruwa zai fi kyau mu dubi yadda masana suka bayyana ma’anar tsafi don yin k’ok’arin fayyace dangantakar su da albiris kamar haka:

Tsafi na nufin bin wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa iskoki hidima, da yanka, da bauta, domin biyan wata buk’ata, ko samun wani amfani, ko tunkud’e wata cuta. Bunza (2006).

2.0 Al’adar Albiris


Albiris wata al’ada ce da ake gudanarwa a garin Bungud’u a lokacin da ake bukin auren budurwa. A ranar wankan amaryar ne k’awayen amarya tare da amaryar ke zuwa a tsakiyar gulbin Bungud’un a turbud’e tuwo a yi ta dukan wurin da kara ko tsumomi sannan a je dutsin Babakiyawa a shiga wani kogonsa a fito ta hanyar bin wasu k’a’idoji.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

2.1 Yadda Ake Gudanar Da Albiris


          A lokacin auren budurwa bayan an d’aura auren a ranar wankan amarya ne amarya da k’awayenta kan shirya don zuwa wurin albiris. Daga cikin shirye-shiryen sukan tanadi tuwon dawa malmala uku, daga cikinsu za su d’auki d’aya sai su hau kan turmi su d’aga ta sama su fara wasu maganganu kamar haka:

Ranata ranata,

Iyeriye, iyeriye,

Sa uwaye kuka,

Sa kakanni kuka.

Daga nan sai su sako wannan malmalar k’asa a kan faifai, daga nan sai a tattara ta a kwashe a nufi gulbi ana yin wak’ok’in gad’a iri daban-daban har sai sun kai tsakiyar gulbin sai su tona wani d’an rami su jefa tuwon tare da gashin jikinsu na mara da na hammata da kuma na kai, sai su turbud’e su. Da sun gama turbud’ewar sai su fara dukan wajen da sanduna ko karan da suka tanado, sukan d’auki lokaci kamar minti goma ko k’asa da haka suna dukan wurin, daga nan sai su ruga aguje don babu mai son a bar ta a baya.

Da barin wannan wurin sai su nufi falalen dutsin gulbin mai suna Babakiyawa, wannan dutsen yana da wani kogo mai fita daga k’asa zuwa sama, wannan kogon ne kowa zai shiga amma da d’ai-d’ai da d’ai-d’ai, ana yi ana ‘bollowa ta sama har sau bakwai. Daga nan sai a nufi gida ana cigaba da wak’ok’in gad’ar kamar dai yadda aka zo da farko.

Idan an koma gida to albiris ya k’are sai a cigaba da wankan amarya kamar yadda al’adar garin ta tanada. Ana tu’be amaryar ne sai alwanka ta je ta yi mata tsarki (kama mata ruwa) sai a dawo da ita a d’ora ta kan turmin nan da aka hau a lokacin da za a je albiris, k’awayenta da sauran danginta har da wasu ‘yan kallo na wurin sai a saka mata wasu manya-manyan goro farare guda biyu a cikin bakinta (gefen dama da na hagu).

Alwanka wata tsohuwa ce k’ak’k’arfa wadda ke yi wa amaryar wanka idan za a kai ta gidan angonta, akan samu wata tsohuwar ta taimaka mata da zuba ruwa ita kuma tana cud’awa, amaryar tana kuka su kuma k’awayen sai wak’ok’in gad’a suke yi kamar haka:

Jagora:         Daga bana ba ke raya ba,

‘Yan amshi: Daga bana ba ke raya ba,

Jagora:        Ke raya ga bangon d’akinki,

‘Yan amshi: Ke raya ga bangon d’akinki,

Jagora:        Ba ta koma hira ga darni,

‘Yan amshi: Ba ta koma hira ga darni,

Jagora:        Ba ta koma wane sakanni,

‘Yan amshi: Ba ta koma wane sakanni.

Haka kuma akwai wata wak’ar da suke cewa:

Jagora:         Gangara gangara ga mu gangara mu je aljanna,

‘Yan amshi: Gangara gangara ga mu gangara mu je aljanna,

Jagora:         Allah Sarki,

‘Yan amshi: Iye,

Jagora:         In ya ga dama ya maida tsohuwa yarinya,

‘Yan amshi: Gangara gangaraga mu gangara mu je aljanna,

Ko kuma su rera wannan wak’ar da suke cewa:

Jagora:         ‘Yar tsohuwa mai d’an k’ok’o,

‘Yan amshi: ‘Yar tsohuwa mai d’an k’ok’o,

Jagora:         Allak kashe ki watan gobe,

‘Yan amshi: Allak kashe ki watan gobe,

Jagora:         Allak kashe ki mu sha gumba,

‘Yan amshi: Allak kashe ki mu sha gumba,

Suna dai rera wak’ok’i daban-daban har a k’are wankan amaryar. Da zarar abokan sun ga an gama wankan sai su fara ce mata:

Ke ar lik’e, ke ar lik’e.

K’e ar lik’e, ke ara lik’e.

Ita kuma sai ta kame turmin ayi ‘bam’bara ta k’i saki sai an sha wuya sosai a cire ta a d’auke ta a kai ta cikin d’aki inda iyayenta mata kad’ai ne tare da wasu tsofaffi mata ke shiga a cigaba da ba ta nono har lokacin da za a d’auke ta zuwa gidan mijinta. Ban nono shi ne wasu shawarwari da za a rik’a ba amarya na zaman gidan miji kamar na cewa duk abinda mijinta ya ce ta yi ta yi ba tare da gardama ba, da cewa ta yi biyayya ga mijin da sauran mutanen gidan da kuma bin umurnin iyayen mijinta da barin ragwanci da yin k’ok’arin biyan buk’atun mijinta da sauran shawarwari makamantan wad’annan.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

2.2 Muhimmancin Albiris


Albiris yana da muhimmanci k’warai ga jama’ar yankin, amma babban muhimmancinsa shi ne korar miyagun aljanu wad’anda za su iya kawo matsala ga wannan auren. Ana ganin cewa duk auren da aka yi albiris wajen yinsa za a samu zaman lafiya, babu wani abun da zai kawo matsalar zaman saboda an magance shed’anun aljanun. Idan bak’ak’en aljanu suka so mace sukan hana ta d’aukar ciki ko mijinta na haihuwa. A wani lokaci su saka mata zubar jini koyaushe, dole a gaji da ita a sake ta, ko su dinga zubar mata da ciki bayan ta d’auka. (Bunza, 2006).

        Wani muhimmancin albiris shi ne tsarkake ma’auratan, jama’ar suna ganin cewa duk lokacin da aka yi albiris to an tsarkake amaryar daga wasu laifuffuka da ta yi na baya, daga nan sai ta kiyaye wasu laifuffukan a gaba.

Albiris yana rage samuwar kwantai daga cikin k’awayen amaryar domin a cewarsu bayan an turbud’e tuwon a tsakiyar gulbi aka gama dukan wurin, kowace daga cikinsu zata ruga a guje babu wadda zata yi kwantai sai wadda bata ruga ba har aka bar ta a baya, amma duk wadda ta tsere zata yi saurin samun miji.

Yin albiris na kawo sassaucin fad’a a tsakanin mata da miji a lokacin da aka kai amaryar gidan mijinta, saboda wasu k’a’idoji ne ake shimfid’awa don miji ya yi hak’uri da matar kuma ita matar ta yi biyayya ga mijin, idan haka ta samu babu wani fad’a da kan taso sai wanda shed’anun aljanu suke haifarwa, shi ma manya kan shawo kansa.

2.3 Su wa ke Yin Albirs


        Masu yin albiris su ne amarya tare da k’awayenta da sauran ‘yan kallo kuma su duka ne sharud’d’an albiris kan fad’awa. Ba a son wani namiji ya shiga cikin masu yin albiris domin wad’ansu abubuwan da ake yi a lokacin sirri ne mata kawai suke jin su ba tare da maza ba. Ko ma ‘yan matan sai wad’anda suka isa aure ne ke zuwa.

 

2.4 Dokokin Albiris


Albiris yana da dokoki da farko dai ba a yin albiris sai ga sha’anin aure, kuma auren budurwa kawai ba da sauran mata ba, wato ba a yin sa a auren bazawara da na tsofaffi da sauransu.

Sai da yamman ranar wankan amarya ne ake yin albiris ba a yinsa da safe ko da rana ko da a ranar wankan ne.

Ba a tsayawa wani abu da zarar an dawo daga albiris sai wankan amarya kawai.

Bayan an gama dukan wurin da aka turbud’e tuwon albiris dole ne kowace budurwar ta ruga aguje don duk wadda bata ruga ba za ta yi kwantai.

Doka ne a wajen albiris cewa duk wanda ya shiga cikin kogon dutsen nan kar ya yi tusa don in ya yi tusa kogon zai had’e da shi ya matse shi kuma ba zai bud’e ba sai an samo kwandon k’eya (kwarkwata) an zuba a cikinsa.

    2.5 Matsayin Albiris


              A halin yanzu an daina yin wannan al’adar ta albiris. Ana ganin cewa an sami kimanin shekara talatin da daina yin wannan al’adar, amma dai an gudanar da ita tun lokacin da garin ya kafu har wannan lokacin da aka fara daina ta. Ana ganin babban dalilin da ya sa aka daina wannan al’adar shi ne shigowar k’ungiyar Jama’atul Izalatil Bidi’a Wa’ik’amatus Sunnah (IZALA) ne a garin a sakamakon wa’azantarwar da suka rik’a yi wa jama’a da su bar ire-iren wad’annan abubuwan da ba su da tushe bare makama.

KAMMALAWA


Saboda la’akari da k’aramcin lokaci da kuma la’akari da muhimmancin abubuwan da wannan takardar take k’unshe da kuma la’akarin da kasancewar mahalartan wannan taron mafi yawansu Hausawa ne sun san abin nufi, halin da ake ciki an daina gudanar da wannan al’adar a garin an dube su ne a matsayin tunatarwa ga manya-manyan mutane na cikin wannan taron kar zancen ya zama na kunne ya girmi kaka kawai. Sannan wannan takardar ta zama matsayin d’and’ano jiran rabo ga matasanmu da fatar mu k’ara had’uwa wani lokaci idan abokin gabarmu lokaci zai d’aga mana k’afa mu shek’e ayarmu a kan lamarin aure a al’adar Hausawa.

 

 

MANAZARTA


 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Post a Comment

0 Comments