Ticker

6/recent/ticker-posts

Rahma Abdulmajid: Jarumar Jarumai Mata Marubuta

Daga

Dr. Umar Aliyu Bunza

Sashen koyar Da Harsunan Nijeriya,
Tsangayar Fasaha Da Nazarin Musulunci,
Jami’ar Usmanu D’anfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya:   07063532532
Kibdau: aliyubunzaumar@yahoo.com

www.amsoshi.com

Tsakure


Ciwon mace na mace ne! Mata jinsi ne da ke fama da matsaloli a zamantakewar al’umma. Wannan ya sa wasu marubuta mata suke fad’i-tashi da fitar da rubuce-rubuce domin yayata matsalolin da ke tarnak’i ga rayuwar mata. Rahma Abdulmajid wata jaruma ce da ta yi fice ga wallafa k’agaggun labarai da ke k’unso matsalolin mata iri-iri. Ta rubuta littattafai masu yawa wad’anda wasu cikinsu suke nuna matsaloli iri-iri na jinsin mata. Manufar wannan mak’ala ita ce shiga cikin wasu littattafan Rahma domin sharhin wasu matsalolin mata da ta yi wa fid’a.

 

1.0       Gabatarwa


Mace mutum ce da Allah ya halitta domin namiji ya had’u da ita ga ci gaban rayuwarsu. Allah ya yi ta mai rauni don haka ya sa namiji ya zan jagora gare ta, ya kuma taimaka mata zuwa ga kowane irin nasara. Wannan ya sa mace ta kasance amanar Allah babba ga hannun namiji[1]ta hanyar kawo mata abinci, samar da muhalli da bayar da kariya da sauransu.

Duk da kasancewar mace k’ark’ashin kulawar namiji, mata da yawa sukan tsinci kansu cikin matsaloli da ke hana su sauke nauyin bautar da take k’ashin bayan da Allah ya halitta su dominta. Matsalolin mata, wani lokaci, sukan ginu daga yadda maza suka yi rik’on sakainar-kashi da hak’k’in da Allah ya d’ora musu, wani lokaci kuma matsalolin sukan taso daga gefen mata ta yadda suke jan k’afa ga kiyaye iyakokin da Allah ya gindaya musu. Ta dalilin matsaloli daban-daban, mata da yawa sun rasa rayukansu, wasu suka haukace, wasu kuma suka fad’a fitintinun rayuwa masu yawa.

Adabi kafa ce da ake iya hangen kowane abu na al’umma ta kowane gefe. Matsalolin mata wani abu ne da ake ganinsa a cikin rassan adabin Hausa masu yawa kamar tatsuniya da karin magana da wak’a da sauransu. A shekarar 1933 aka fara samun rubutaccen k’agaggen labarin Hausa wanda shi ma ya kasance wata taska da ake hangen kowane abu da ya shafi rayuwar al’umma. A shekarar 1978 mata suka fara shiga k’aga rubutaccen labarin Hausa lokacin da Hafsat Abdulwahid ta yi nasarar gasar Kamfanin Buga Littafai Na Nijeriya Ta Arewa (NNPC) Zariya, da littafinta mai suna So Aljannar Duniya. Tun daga wannan lokaci sai mata suka sami wata kafa ta bayyana matsalolinsu domin a ji muryoyinsu cikin wad’annan mata har da Rahma Abdulmajid.

An haifi Rahma Abdulmajid a shekarar 1980. A shekarar 1996 Rahma ta fara rubuta k’agaggen labari da wani littafi mai suna ‘Wa Ya Fi Kishi.’ Ciwon mace na mace ne! Rubuce-rubucen Rahma wata kafa ce muhimmiya ta haska matsalolin mata da kuma hanyoyin warware su. Idan aka yi nazarin adabin Rahma, sai a ga cewa, ta fi damuwa da mace da matsalolinta kama daga soyayya har zuwa aure. A gefe d’aya, sai kuma takan damu da kawo hanyoyin da mace za ta ceci kanta, ta inganta rayuwarta ta kowane hali. Manufar wannan mak’ala ita ce  nazarin adabin Rahma da zimmar nuna ta a matsayin jarumar jarumai mata marubuta. Za a yi haka ne ta duba yadda ta kalli matsalolin mata cikin adabin nata, abin da ya sa adabinta ya yi fice, musamman ga mata. An fara da duba tarihinta a tak’aice, sannan aka juya akala zuwa duba matsalolin mata cikin adabin nata.

2.1       Tak’aitaccen Tarihin Rahma Abdulmajid


          An haifi Rahma Abdulmajid a ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 1980. Sunan mahaifinta Abdulmajid d’an asalin k’asar Sudan. Ya shigo Nijeriya, ya zauna a Unguwar Agege cikin birnin Lagos a gida mai lamba 21 Isa S.T.F. Abdulmajid ya rasu a shekarar 1986, lokacin Rahma na k’aramar yariya mai shekaru 6 a duniya. Kafin rasuwarsa ya haifi ‘ya’ya 22. A cikinsu akwai maza guda 11 da mata 11. Rahma ce auta a cikin ‘ya’yan nasa duka.

          Rahma ta fara karatun Alk’ur’ani mai tsarki a makarantar mahaifinta (gidansu) har zuwa shekarar 1989 lokacin da mahaifinta ya rasu. Wannan ya sa ta ci gaba da karatu a wata makaranta da ake kira Nibrasil Huda. A wannan makaranta ce Rahma ta fad’ad’a karatunta a fannonin ilmin Musulunci kamar Hadisi da Nahawu da Fik’ihu da sauransu.

          Ta fannin ilmin boko, Rahma ta fara karatun boko tana ‘yar shekara goma sha d’aya, wato shekarar 1991 a makarantar  Keke Primary  da ke unguwarsu. Haka kuma ta sami wata malama mai suna Latifa wadda suka yi shekara biyu tana k’ara koya mata karatu. Da ta kammala sai ta sami takardar shiga makarantar gaba da firamare mai suna Diary Farm.  Daga baya aka yi mata sauyin karatu zuwa wata makarantar Arabiyya da boko mai suna Rahmatu Islamic School da ke Ikeja inda nan Rahma ta kar’bi shaidar karatu na matakin farko. Daga nan ne ta zarce da karatun Larabci zalla a makarantar Ulmil Islamiyya.

A shekarar 2000 Rahma ta sami wani sauyi karatu zuwa Zariya inda a can ta kammala karatunta na shekara d’aya a Kwalejin Jama’atu Nasrul Islam. Da ta kammala sai ta yi difiloma a ‘bangaren shari’ar Musulunci har zuwa 2002 lokacin da ta kammala difiloma.

A wannan shekara (2002), Rahma ta sami gurbin k’ara karatu a Jami’ar Al’azhar da ke birnin Alk’ahira na k’asar Masar inda ta had’a digirinta a fannin tarihi da al’adun duniya a shekarar 2007.

            Aure yak’in matai Rahma AbdulMajid ta yi aure a ranar Asabar sha d’aya ga watan Nuwamba shekara ta dubu biyu da shida (11-11- 2006) da masoyinta mai suna Auwal Sa’ad. A daidai wannan lokaci, (2016), Rahma na da ‘ya’ya biyu mata: Maryam da Fatima. Malam Auwal Sa’ad mijin Rahma sojan Nijeriya ya rasu a ranar 10-11-2015 a can yankin Sambisa a k’ok’arin sojojin Nijeriya da aka tara a jihar Borno domin yak’ar k’ungiyar Boko Haram wadda ta hana yankin zaman lafiya. Ya rasu a daidai lokacin da washegari zai cika shekara tara (9) da aurensa da Rahma AbdulMajid. Allah ya jik’an sa, ya yi masa rahama, amin.

Rahma ta fara rubuta adabinta na Hausa a shekarar 1996 wato tana daf da cika shekara goma sha shidda (16). Littafin da ta fara rubutawa shi ne mai suna Wa Ya Fi Kishi wanda yake cikin juzu’i uku (1-3), aka kuma buga shi a shekarar 1996 daga mad’aba’ar Sauk’i Bookshop, Kano.  Daga wannan lokaci zuwa yau, Rahma ta rubuta littattafan k’agaggun labaran Hausa da ba su kasa 30 ba kan jigogin soyayya, fad’akarwa, tarihi, fafutukar ‘yancin mata da sauransu. Fitacce daga cikinsu wanda kuma aka fi jin sunan Rahma da shi, shi ne mai suna ‘Mace Mutum’ wanda ta wallafa a shekarar 2012, aka kuma buga shi a mad’aba’ar Iya Ruwa Publishers Kano.

Idan aka yi la’akari da littattafan Rahma, za a ga cewa, yawancinsu sun k’unshi matsalolin rayuwar da mata suke fad’awa cikinsu. A lokaci d’aya Rahma kan shirya wa wata mace gagarumar matsala wadda za ta jima cikin tarnak’inta, sannan bayan wani lokaci sai ta ‘bullo mata da mafita. Wannan na nuna, Rahma jaruma ce da ke yi wa mata hannunka-mai-sanda domin koda sun sami kansu cikin wata matsalar rayuwa, ya zan suna iya fitar da kansu cikin ruwan sanyi ba sai sun dogara ga namiji ba. Wani abu kuma shi ne, Rahma ta cika sanya namiji ya zan sila na matsala ga mace cikin adabinta. Haka kuma, wajen samar da mafita ga matsala, ta fi amfani da hikimar mata, a maimakon amfani da namiji a matsayin tsanin mafita ga mace.

 

3.1       Matsalolin Mata A Adabin Rahma


Matsala wani yanayi ne maras dad’i da mutum ke shiga a dalilin wani abu da ya aikata, ko aka aikata masa. Sau da yawa mata kan shiga matsaloli saboda wani dalili. Matsalolin mata da ke k’unshe cikin adabin Rahma sun had’a da kishi, soyayya, da aure da maraici, da jahilci da sauransu. Dukkan matsalolin kan haifar wa mata tarnak’i da shiga halin k’ak’a-ni-ka-yi da wani lokaci har yake sa wata mace rasa ranta.

3.1.1    Kishi

Kishi kumallon mata! Kishi wata sifa ce da mutum kan nuna ta hanyar harzuk’a da bayyana ‘bacin ransa, saboda wani da yake so ko soyayya da shi, ya nuna sha’awarsa ga wani ko kuma wani ya nuna sha’awa gare shi. Tsananin son da mace ke yi wa mijinta ko neman ke’bancewa zuwa ga mijinta ko wanda take son ta aura, da take nuna k’auna, da kyakkyawar fata gare shi, tare kuma da nuna k’iyayyarta ga duk wata da take son sa da aure ko kuma shi yake son ta da aure Bakura  (2014: 5-6).

Kishi ga mace, shi ne jin haushi da k’in jinin kusanci na so, ko mallaka ko tarayyar wata mace ga wani abu da take so, ko take tarayya da shi. Kishi sau da yawa ya kasance matsala ga wata mace har ya kai ta ga rasa sukuninta da ‘yancin walwalarta.

Rahma ta d’auki kishi a matsayin wata babbar matsala, kuma barazana da ke dagula lamurran mata na yau da kullum. Wannan ya sa a wasu littattafanta ta kawo wasu mata da suka rungumi kishi, ya dabaibaye su da matsaloli masu yawa. Ga misali, littafin Wa Ya Fi Kishi wanda a ciki ta kawo labarin wata mata Binta da kishi ya yi sanadiyyar ciwon hanta gare ta. A cikin littafi na 2, Rahma ta kawo yadda Bintar ta bayyana kishi a matsayin silar shigarta matsalolin rayuwa inda take cewa:

Binta ta juyo suka fuskanci juna, haba D’ahir baka da godiyar Allah so kake na had’iye ka? Wace irin k’auna ce ban nuna maka ba? Duk abin da nake yi maka ina yi ne abu biyu, k’auna da kishi gudun kada ka hango wata bayan, kada kai min munafinci kana tare da Nafisa tun ina tarairayarka, me ye dalilin juya maka baya da nai? Haba dai D’ahir ka cuce ni, ta k’ara fashewa da kuka, D’ahir ina cikin shagwa’baka ka kawo min zancan k’arin aure wanda har yanzu ban daina jin haushi ba amma na daure don maganar da kai min na cewa in ba na kyauta maka sona zai yi maka rauni ina cikin lalla’bawa, ashe kai cuta ta kake kada ka d’auki alhakin wani ka ce shi ne ya gaya min, na je makaranta a nai mana gargad’i amma hankalina na wurinka, na je wurin aikinka aka ce ka tafi gida, raina bai so na sauya shawaran zuwa J. S, in siyo abinci dan kada ya kasance kana gida kana jin yunwa, kuma zai d’au lokaci ban k’are abinci ba, duk da gajiya ta na tafi dan hidimarka, amma D’ahir dan cin amana na same ka a can da ido na ganka kuna rik’e da hannun juna kai da Nafisa, wannan shi ne abin da ya jawo min bak’in ciki, k’unar hanta, ta’buwar hankali da kuma zuwan ‘yata ba rai wacce na d’ora rayuwata akanta, haba wace irin cuta ce ba ka yi min ba?’ Ta dad’a fashewa da kuka da gyad’a kai. Wa Ya Fi Kishi 2? (shafi na 35-36).

Ashe kafin shigar kishi cikin zuciyar Binta, tana zaune lafiya, cikin k’oshin lafiya da mijinta. Tana kowace irin kyautatawa gare shi. Daga lokacin da Binta ta sa kishi a zuciyarta, sai lamurranta suka sauya. Yau lafiya, gobe ciwo, musamman daga ranar da ta ga mijin nata da wata mai suna Nafisa wanda shi ne babban abin da ya hura wutar kishin zuciyarta. Nafisa wata ce da ke son D’ahir, amma shi ba ya kula ta. A wannan ranar da Binta ke maganar ganin su, ba rik’on hannun juna ne suka yi ba, ita Nafisar ce ta rik’o shi bayan ya gaya mata ba dad’i, ya juya zai tafi. Ba ta tsaye binciken komai ba, sai ta sa ciwon kishin cikin ranta. A hankali rashin lafiya ya ci k’arfinta, aka kwantar da ita asibiti. Abu ya tsananta, amma ba a san mene ne dalili ba. Ranar da D’adir ya gaya mata tsakaninsa da Nafisa, sai ta yi da-na-sani, ta ba shi hak’uri bisa zargin da ta yi masa masa cikin rashin sani, sannan zamansu ya koma daidai. Irin haka wasu mata da yawa suke fad’awa fitina saboda kishi maras dalili.

Shi ma littafin Ni Ma ‘Yata Ce 2, akwai matsalar kishi a cikinsa wanda wasu mata biyu suka nuna. Rahina mata ce ga Ma’amun, kuma ita ce mahaifiyar Rashida. Bayan mutuwar aurenta sai Ma’amun ya auri wata mai suna Amina. Ya d’auki Rashida ya ba ta domin kula da karatunta da sauransu. Ita kuma Rahina ta auri wani mijin. Wata rana Rahina ta zo ganin Rashida, ta ji ‘yar ta kira Amina da kalmar momi. Wannan ya sa kishi ya motsa a zuciyarta. Ga yadda Rahma ta kawo bayanin:

Rahina ta amshi bak’uncin wasu yanayi da ba ta san da zuwansu ba, wanda a yayin da k’wak’walwarta ta kasa kunne wajen jin ‘yarta na kiran wata mata Momi ba ita ba, sai ta fahimci bak’in cikin na so ya nuna gazawarta, da sauri ta shirya yak’ar yanayin ta hanyar dawo da ilahirin walwalarta ga Ma’amun da ke ba ta kujera (shafi na 27).

A wannan wuri, kishin Rahina shi ne damuwarta ga ‘yarta ta kira wata mata momi. Ba shakka, mace na kishin wata ta auri mijinta koda bayan rabuwar aurensu, haka kuma tana k’in jinin zaman ‘yarta a hannun wata da tsohon mijinta ya aura. Irin haka ne ya sa kishin Rahina ya motsa jin yadda ‘yarta ta kira wata momi ba ita ba.

Ita kuma Amina matsalar kishi ya motsa mata ne lokacin da ta fito ta sami mijinta Ma’amun da tsohuwar matarsa cikin fara’a. Ga yadda marubuciyar ta kawo batun:

Amina wadda ta sanya dogon hijabi mai ruwan toka ta yi hakan ne da zaton Rahina ta zo da mijinta, amma da ta gan ta ita kad’ai da kuma kwalliyar da ta sha ita da kyawunta, sai ta ji dama ita ba hijabi ta sanya ba kwalliyarta ta ca’bo, ba ta tsaya a nan ba, sai ta ji wutar kishi ta lullu’be ta a yayin da ta ga mijinta da tsohuwar matarsa na rayuwa cikin fara’a (Shafi na 28).

Amina mace ce kyakkyawa, mai natsuwa, da ladabi ga mijinta Ma’amun. Ba ta zarginsa da komai a zamanzu, amma kishi ya motsa mata a lokaci guda da ta gan shi da tsohuwar matarsa Rahina. Yadda Ma’amun ya tarbi Rahina ba abin zargi ba ne, domin shi ta sama a falo, kuma ta shigo cikin yanayi na lumana bayan da ta yi sallama.

Idan aka dubi halin kishi da kowace mace ta nuna, ana fahimtar cewa, shi kishi wata matsala ce babba a rayuwar matan Hausawa wadda a lokuta da dama takan sanya su shiga damuwa da ba wani dalili k’wak’k’wara.

3.1.2    Aure

Aure yak’in mata! Aure halartacciyar zamantakewa ce tsakanin namiji da mace. Aure shi ne wata yarjejeniya c eta zama tare tsakanin namiji da mace bisa wani tsari na addini ko al’ada (Adamu, 1998: 4). A al’ummar Hausawa, aure ya kasance wani muhimmin mataki na cikar kamala ga kowane mutum, namiji ko mace. Idan mutum ya yi aure, akan dube shi a matsayin wanda ya dace da mutuntawa, wani lokaci har ma abokin shawara. Wannan kan sa kowa, namiji da mace na son yin aure idan suka kai balaga, kuma suka sami abokin aure da hankali ya natsu da shi.

A lokuta da dama akan sami gittawar matsaloli cikin auren wasu mutane. Matsalolin aure na kasancewa na rashin samun haihuwa, ko haihuwar ‘ya’ya mata, ko zargi ko kuma rashin jituwa da ke tasowa tsakanin ma’aurata.

Idan aka sami matsala cikin aure, yawanci mata ne suka fi shan wuyarta. Mata kan tsinci kansu a halin k’ak’a-ni-ka-yi tsakanin gidan miji zuwa gidan iyayensu. Miji kan tilasta mace barin gidansa. Idan ta k’i, sai ya ci gaba da azabtar da ita ba yadda za ta yi. A irin wannan hali ne ake samun mace na fama da rama da rashin lafiya nau’i-nau’i ba tare da an san mafari ba. Yawanci a irin wannan hali, mata ba su bud’a baki su fad’i, shi kuma miji sai ya dage ba wani abu mai illa da ya sani.

A gidan iyaye, mace da ta sami matsalar aure kan fuskanci tsarguwa da tsana daga mutanen gidan har ya kai ba ta sha’awar zama gidan. Wani lokaci wasu iyaye kan sanya mata dokar lek’a koda k’ofar gida, musamman idan ya zan an yi zama da mijin, kuma rashin gaskiyar ya k’are kanta.

Rahma ta dubi matsalar aure a matsayin wani muhimmin abu da ta kawo shi cikin wasu littattafanta. Ga misali, littafin Baya Na Suka 1-2.

Baya Na Suka labari ne da wata yarinya mai suna Zainab ta fito a cikinsa. Ta yi ilmin addini har ta hardace Alk’ur’ani. Ta auri wani saurayi Al’amin. Kafin aure, Zainab mace ce da ba ta da kowace irin gur’batar tarbiyya. Kowa yana yaba kirki da halayenta. Bayan aurenta da Al’amin sai ta shiga shan giya a dalilin magani da mahaifiyar wata yarinya da ta so shi ta yi mata. Lokacin da Al’amin ya fahimci shan giyar Zainab sai ya nemi ya ji ta yaya ta fara shan giya, sai ta amsa masa da cewa:

Komai bai ishe ni rago tunaninka ba hatta karatuna, a yayin da ina buk’atar hakan domin samar da cikar burin abin da ya nisanta ni da kai, kwatsam sai barasa ta d’auke mini wannan nauyi. Ana gobe zan zana jarrabawata ta k’arshe a shekara ta biyu da daddare ka bugo mini waya da misalin k’arfe d’aya ka bayyana mini irin halin kad’aici, takurawa da azabtuwar da kake ciki a domin rashina. A wannan rana ban yi barci ba, kuka nake da tunani, da zan samu duk wata hanya da za ta isar da ni gare ka a wannan lokaci da na yi ko da zan bar jarrabawata. Ko da haka ba ta samu ba, ya yi tasiri a jarrabawata inda sai da na maimaita wannan takarda a shekarar gaba da ita. Ba na son hakan ya sake faruwa don haka na shiga neman duk abin da zai sassauta mini. Baya Na Suka 2, Shafi na  9-10.

Idan aka yi nazarin wannan bayani sosai, sai a fahimci cewa, matsalar rayuwar aure ce ta sa Zainab ta fad’a a halin shan barasa. Halin tunanin mijinta shi ne abu na farko da ya bud’a kafar fara shan giya gare ta. Tunani kan miji, musamman a lokacin da aka yi nisa da shi, wani abu ne da ke jefa mata cikin k’uncin rayuwa. Mace da ta auri namijin da take so, kuma ya zan yana ba ta kowace irin kyakkyawar kulawa[2] na sa ta sami sukuni a rayuwarta, ta manta da komai. Wannan zai ba ta damar samun kowace irin walwala da ‘yancin rayuwa da fita daga kowane irin bak’in ciki. A irin wannan hali, idan mace ta yi nisa da miji, takan kasance cikin damuwa da tunaninsa, musamman idan ya zan wasu al’amurra da ya d’auke mata sun koma kanta. Haka idan irin wannan miji ya sanar da matarsa halin kad’aici da kewarta da yake ciki, abin zai dame ta. A irin wannan yanayi, mace na iya aukawa a kowace irin hanya ido rufe domin sassauci ga halin  da take ciki. Irin haka ne Zainab take ciki, kwatsam sai wata mai suna Salamatu ta gabatar mata da giya a matsayin wani abu da zai sassauta damuwarta. A hankali ta mai da giya wani sashe na wartsake damuwar rayuwarta.

A cikin littafin Za Ta Iya 1-3, nan ma wata mata ce mai suna Hajiya Rabi ta fad’a matsalar zaman aure. Tana zaune da mijinta tsawon lokaci ba su haihu ba. Ana nan matar da ya aura ta biyu mai suna Zuwaira ta haihu. Bayan wannan lokaci ne sai Hajiya Rabi ta sami ciki, ta haifi tagwaye. Haihuwar Hajiya Rabi ya sa Hajiya Zuwaira ta shirya yadda Alhaji Zakanya zai tsani uwar gidarsa da ‘ya’yanta. Hajiya Zuwaira ta fara da shirya k’aryar cewa, direban Alhajin mai suna Lauwali ne ya yi wa Hajiya Rabi ciki. Ga yadda batun ya gudana:

Jiya Allah ne ya kiyaye da k’yar na k’waci kaina wajan direban ka Lawali….

Jiya ne da ya kai ni makaranta wajen taron iyayen yara, muna dawowa, sai ya biyo ni d’aki, na ce akan me? Wai zai gaya mini cewa, nan gaba in ban tayar ba yaya za ta k’wace gida, domin wai ba ka haihuwa, ga shi wai na kawo Sadik ka kar’ba, dan haka ita ma yanzu za ta shiga kawo maka ‘ya’ya, wai shi ne take nemansa, yanzu wai har ya yi mata ciki, kuma a haka za ta yi ta haihuwa, to wai ni ma in zo mu k’ara wai ba mai sani. Za Ta Iya 1, Shafi na 34.

 

Shi kuma Alhaji Zakanya bai tsaya bincike ba, sai ya wuce asibiti. Koda ya isa d’akin nata, sai ya sami wata wasik’a da aka bari a k’ark’ashin filon Hajiya Rabi, kuma wasik’ar na da sunan Lauwali. Bayan da ya karanta, sai ya tayar da ita cikin fushi, ya tambaya te game da wasik’ar. Ta nuna ba ta san komai ba. Da bai amince ba ne, sai ta ce:

Na fahimci inda batun ya dosa Alhaji, babu kuma abin da ake nufi da ni, ban da a yi mini sharri, a raba ka da ni da ‘ya’yan da muka samu, amma ni ba ni da wata kariya, ban da shaidar Allah da taka, dan haka ka shaide ni Alhaji, ban da wata alak’a da wani namiji kafin –da-bayan na aure….Ya had’e hannayenta zuwa wuyanta da shak’a. Za Ta Iya 1, Shafi na 36-37

Matsalar da Hajiya Rabi ta shiga, matsala ce babba. K’iren k’arya a jingina ga mace, musamman game da wani namiji, matsala ce da take shafuwar matan aure da yawa.  Matsala ce da take kawo rashin zaman lafiya, wani lokaci har da mutuwar aure. Ita kan ta Hajiya Rabi, wannan k’iren k’arya ya haifar mata matsala da mijinta, ya yi watsi da ita da ‘ya’yanta duka. Mahaifinta shi ma ya hana ta zuwa gidansa. Don haka sai kakarta ce ta zauna da ita a wani k’auye. Wannan ya sa yaranta; Ahmad da Nafisa suka taso da rayuwarsu a k’auye. A zamantakewar rayuwa, irin wannan hali da Hajiya Rabi ta shiga ana samun sa ga wasu matan aure masu yawa.

Ita ma Hassana da ke cikin littafin Tuwon K’aya matsalar aure ta kai ta ga rasa gata, da shiga halin k’unci da rasa rayuwarta. Ita d’iya ce ga wani attajiri mai suna Alhaji Idris. Ta wayi gari cikin mutuwar son wani saurayi Musa. Babbar matsalarta ita ce iyayenta sun k’i amincewa da Musa saboda sun san d’an bangar siyasa ne da ba shi da kykkyawar madafa. A haka dai Hassana ta dage ita shi take so, kuma za ta aure shi. Alhaji Idris ya yi yarjejeniya da ita kan aurenta, ta ce duka ta d’auka. Aka d’aura auren. Bayan lokaci da auren sai iyayenta suka rasu a had’arin jirgin sama. Aka bar ta da yayanta mai suna Mujitaba.

Ana nan siyasa ta tashi, jam’iyyar adawa ta tsayar da Mujitaba takara. Ita kuma jam’iyya mai mulki ta su Musa ta tsayar da maigidan Musa. Musa ya sa Hassana ta rik’a sukan yayanta har aka yi za’be ya fad’i. Cin za’ben ya ba Musa damar ya je hajji ya sayi gida da mota. Ita kuma Hassana a maimakon ta sami sassauci, sai k’ara lalacewar lamurra. Ta kwanta rashin lafiya, Musa ya fita batunta, ya koma yana neman mata abinsa. Sabon gidansa ya gyara shi, ya ce na amarya ne. Rashin lafiya ya ci k’arfin Hassana, a maimakon ya kai ta asibiti sai ya tura ta wajen wani boka da ya gallaza mata azaba. Ta tsero, Musa ya sake tura ta Kamaru inda a can ta rasu cikin k’ask’anci. Kafin rasuwarta, wata rana ta ta’ba bayyana masa damuwar da take ciki na aurensa. Ta ce:

Musa dubi rayuwata a sunan wai ka samu aiki. Ban buk’aci k’aryar arzik’i ba, amma a k’alla don ka canja mini d’aki ko ka sai mini rasho dan in samu sauk’in ciwo na Musa ba ka fad’i ba. Kud’in rashona fa bai kai kud’in ko turaren da kake fesawa ba, amma kake k’yashi, kullum kai ne canja kaya, canja abinci yawon kashe kud’i wa har matan waje. Amma ni da ‘ya’yana ne ba mu kai mu huta ba don da kud’in makarantarsu da na abincinmu da shi za ka sai gidan da har yau ko labarin tubali ban ta’ba ji ka ajiye ba. Shafi na 45.

Kalaman Hassana na bayyana irin matsala da k’uncin rayuwa da take ciki. Dukkan buk’atocinta masu sauk’in aiwatarwa ne ga irin Musa, amma sai ya yi watsi da su. Kafin aurensa kuwa, Hassana tana cikin kowane irin jin dad’i. Ba ta cikin kowace irin matsalar rayuwa. Irin wannan matsala da Hassana ta shiga musamman rashin abinci da kula da neman matan waje ga mijinta na cikin manyan matsalolin aure da wasu mata suke fad’awa a hannun maza har su rasa rayukansu. Ita kuma Indo matsalar aure nesa ya sa ta shiga wasu matsaloli. Ga yadda nata matsalolin suka kasance:

Ku bari ya sake ni ko a mai da ni inda ya d’auko ni, na gaji. Bak’in ciki da wuya za su kashe ni a gidan nan. Ban ta’ba ganin iyayena ba tun da na aure shi, ai ko bauya sai haka! Jikina da zuciyata ba su ta’ba hutawa daga bauta da bak’in cikin da ake cusa mini ba. Na haihu, ‘ya’ya sun mutu, babu tausayi. Wad’anda suka saura an raba ni da su. In na had’a gumina na tara dukiya don ‘ya’yana ko don na gan su sai a kwashe a yi aure. Wayyo ni Allah na! Mace Mutum shafi na 49

Aure a wani gari mai nisa matsala ce ga mata wadda ke sa wasu su d’auki lokaci mai tsawo ba su je garin iyayensu ba. Indo wannan matsalar ce ta dad’e cikin zuciyarta har lokacin da ta sami damar fad’arta. Tun da ta auri Malam babba ta baro garinsu ba ta sake ganin iyayenta ba har ta haifi ‘ya’ya da ba su kasa hud’u ba. Matsala ta biyu ita ce, yadda mijin nata ke amsar kud’ad’enta da sunan kai wa d’iyanta da ke raye a wasu garuruwa da ya tura su karatu, amma sai ya je ya yi aure abinsa. Wannan matsala ce da ke sa mace ba za ta mallaki komai nata ba. Irin wannan na cikin matsalolin aure da wasu mata suke fuskanta a k’ark’ashin mazajensu.

3.1.3    Soyayya

Soyayya gamon jini! Soyayya na nufin nuna k’auna daga ‘bangarori biyu na masu k’aunar juna, musamman mace da namiji (CNHN, 2006). Shi kuma D’akingari (…., 22-23), cewa ya yi, soyayya ita ce k’awa-zuci ko tsananin k’auna da buk’atar kusantuwa ga wani mutum, ko wani abu daban. A tak’aice  Soyayya ita ce wata irin shak’uwa da amincewa da ke shiga tsakanin wasu mutane kan wani dalili na musamman. Yawanci, an fi lura da soyayya tsakanin namiji da mace wadda a hankali wani lokaci take kai ga aure.

A sha’anin soyayya, yawanci mata sun fi fuskantar matsala. Mace kan fad’a matsalar soyayya ne saboda takan yi saurin mik’a wuya da rungumar wanda take so ba tare da la’akari, ko bincike game da tarbiyyarsa ba. Da yawa mata kan fad’a tarnak’in soyayya saboda yadda suke rud’uwa da abin duniya ko kwalliya da matsayin da namiji ya jingina wa kansa, ya kuma gabatar gare su. Wannan yakan sa wata mace ta zurfafa ga son wani namiji, ta k’ak’aba shi a cikin zuciyarta ta yadda lokaci guda sai ta fad’a had’arinsa.

Yawancin matsalolin soyayya da mata suke fad’awa sun fi alak’a da gur’bata rayuwarsu da tozarta matsayinsu. Matsalolin sun had’a da cikin shege, guje wa iyaye, haukacewa, barin gari, shiga karuwanci da sauransu.

Rahma Abdulmajid ta saka matsalolin soyayya a matsayin wani abin dubawa da kuma yin tsokaci cikin wasu littattafanta. Ga misali, a cikin littafin  Za Ta Iya, Rahma ta kawo yadda tarnak’in soyayya ya sa wani saurayi ya ci zarafin wata mai suna Nafisa. Nafisa tana soyayya ne da wani saurayi mai suna Sadik’. Mahaifiyar Sadik’ ba ta son alak’ar d’anta da Nafisa. Wannan ya sa ta shiga hanyoyi masu yawa don yadda za ta tozarta k’imar Nafisa a zuciyar Sadik’. Irin wannan sharri ne saurayin ya zo wa Nafisa da shi lokacin da take tafiya tare da Sadik’. Ga yadda Rahma ta kawo bayanin:

Nafisa a gefensa ita ma da doguwar riga ta rungume litattafai a k’irjinta, suna takawa a hankali a harabar makarantar dan fitowa daga ciki. Kwatsam sai ga wani saurayi mai shigar rashin natsuwa ya shawo gabanta yana k’ok’arin jawo hannunta. ….wai kina nufin ki ce ba ki san ni ba ne dan kin gan ki da sabon saurayi?....Au ai da kin gaya mini cewa kin nunawa wani cewa ke ‘yar mutunci ce, sai na tufa miki asiri tun da na san ba ni kad’ai ne namijin da ke tare da ke ba, amma tun da abin na wulak’anci ne, zan tona miki asiri yau… Oga ka d’auki ragowarmu sai maneji, ba ta da kowa ba ta da komai, mu ne ke d’auke da nauyinta, mu kuwa ba dan Allah muka d’auki nauyinta ba, sai dan mu ma ba mu da kamarta wajan biya mana buk’ata. Ka gane mana, dan haka in kana so in gaya maka siffanta ne sai in gaya maka kai ma yau ka je ka gwada ta ka gani ko.’ Za Ta Iya 2, Shafi na 3

Sharrin da wannan saurayin ya yi wa Nafisa abu ne da ake samunsa a tsakanin masoya, musamman idan ya zan ba a son dangantakar tasu. D’aya daga cikin manyan abubuwan da ke zubar da mutuncin mace shi ne danganta ta da fasik’anci da wani namiji. Yawanci, masu neman aure ba su amincewa da alak’ar budurwarsu da wani daban. Don haka, abin da saurayin ya yi, ya yi ne domin ya sa Sadik’ ya tsani Nafisa, soyayyarsu ta lalace. Bayan wannan sharri bai ci ba, sai aka sake k’ulla mata wani na daban. A wannan karo an yi amfani da wani saurayi ne aka tura shi domin ya yi zance da ita. Shi kuma saurayin mai suna Ahmad, yana ganin ta sai ya gane ita ce k’anwarsa da ta ‘bata tana yarinya. Bayan d’an tattaunawarsu, sai suka rungume junansu. A wannan lokaci an riga an zo da Sadik’ yana la’be domin a k’ara tabbatar masa yarinyar da yake so fasik’a ce. Ganin abin da ya faru ya sa Sadik’ ya suk’e, ya kuma yarda da labaran da aka yi ba shi game da Nafisa. Nan take ya shirya halaka ta wanda dole ta bar gari tare da mamarta. Da suka shirya barin gari sai ta rubuta masa cewa;

Na bar garin nan, amma a domin ka Abubakar. Ban san lokacin had’uwa ba, amma ina fatan ya zamo ka huce a lokacin don mu iya samun hafimtar juna….Ina ci gaba da sonka Sadik a kowane hali muke kuma a ko’ina. Domin ka dace da zuciyata…Nafisarka. Za Ta Iya 2, shafi na 73.

Shi ma littafin Hadari Sa Gabanka 1, yarinyar da take cikinsa mai suna Nadiya ta fad’a matsalar soyayya. Nadiyya yarinya ce mai natsuwa, amma sai ta fad’a soyayya da wani saurayi mai suna Faruk’. Ga yadda Rahma ta kawo wani ‘bangare na soyayyar Nadiya da Faruk’:

….Tun da take ba ta ta’ba had’uwa da zanen zuciyarta a samarin da ke zabarin son ta ba sai da ta ci karo da soyayyar Faruk’ a shekarar bara, kamar wasa yake cewa ita dama gidansa ke jira a dalilin ta ce masa ‘Gidanka na da kyau’ A wata ziyara da ta ta’ba raka Mudi gidan Faruk’. Mudi da Faruk’ ba su ‘bata lokaci ba suka sami shawo Nadiya har ta fad’a matsanancin son Faruk’ kamar za ta had’iye shi. Shafi na 13.

Faruk’ wani d’an ta’adda ne da sana’arsa ita ce satar dukiyar mutane ta hanyar yanar gizo. Koda Nadiya ta fara soyayya da Faruk’ yana tunanin hanyar da zai washe dukiyar mahaifinta. Wannan ya sa da ya sami kar’buwa ga Nadiya sai ya ga cewa ya sami hanya mafi sauk’i da zai kai ga manufarsa. Rahma ta kawo bayanin Faruk’ a cikin littafin nan na Hadari Sa Gabanka 1 kamar haka:

A idon jama’a dai sana’arsa ita ce had’a tashar yana gizo da tauraron d’an Adam amma a kan aikinsa da ya sani shi da yaransa shi ne raba me kud’i ko wani babban asusu da hak’k’insa. Ya yi kud’i yadda ba a zato, yana da gidan da ba kowane irin wane ne zai iya zama ya dace da shi, kamar yadda yake hawa kowace mota sabuwar yayi matar da zai sa gidan nasa ne bai ga wadda ta dace ba sai da ya had’u da kyakkyawar Nadiya ‘yar hamshak’in me kud’in asali wato Alh. Sagir sai dai kash! Tun kafin had’uwa da ita ubanta ya shigo layin wad’anda yake mafarkin yi wa yasa don cika aninin da ya rage masa a fadar kud’i. Sai dai bak’untar zuciyarsa da ta yi bai sauya komai ba, sai ma ganin da yake aurenta a matsayin babbar d’iyar Alhaji kuma wadda take wakiltarsa a komai bayan Mudi zai iya kai shi ga mallake ilahirin dukiyar wannan bawan Allah….. Shafi na 11-12.

Ga ‘ya mace mai mutunci irin Nadiya, soyayya da irin Faruk’ matsala ce babba gare ta. Shi Faruk’ ba Nadiyar ce a zuciyarsa ba, amma ya rik’e soyayyarta a zahiri domin cimma burinsa na sace dukiyar mahaifinta cikin sauk’i. Daga k’arshe, a k’ark’ashin soyayyarsa ta yaudara ya tarwatsa iyayenta. Ya kashe k’anin mahaifinta Mudi, ya kashe mahaifinta Alhaji Sagir, da k’aninsa kanal….. ya kuma k’ona ofishinta. Ita ma ranta ya tsira ne daga sharrinsa dalilin wani saurayi mai suna fatihu. Wannan ya nuna matsalar son Faruk ga Nadiya wani tarnak’i ne babba wanda da yawa wasu mata sukan tsinci kansu cikin makamancinsa, su rasa gaba ko baya, wasu ma har su halaka.

Shi ma littafin Ba Ita Ba Ce 1-2 wasu mata tagwaye ne suka fad’a tarnak’in soyayya. Salma da Salima sun fad’a son wani saurayi guda mai suna Mus’ab. Mus’ab ya fara gabatar da soyayyarsa ce ga Salma. A wannan ranar da suka rabu ne Salma ta sami had’arin mota abin da ya kai sai da aka kai ta asibiti a k’asar Afrika ta Kudu. A yanayin jinyarta son Mus’ab ya ci gaba da bunk’asa cikin zuciyarta alhali ba ta da wata hanya ta had’uwa da shi.

Ita kuma Salima ta had’u da Mus’ab a gidan wata k’awarta da ta auri abokinsa mai suna Yusha’u. A nan gidan ne Mus’ab na ganin Salima sai ya zaci ita ce Salma saboda kama da suka yi. A nan ya nuna mata sani, ita kuma ta nuna ba ta san shi. Ya gabatar da buk’atarsa ta soyayya, ta kuma yarda. Salima ta ci gaba da soyayya da Mus’ab har lokacin da ta koma wajen jinyar Salma. A can ne ta gabatar wa Salma labarin tsananin son da take yi wa saurayinta da ta yi wa suna Bawan Allah. Ga yadda ta ce mata:

Haba ke dai bari Sal Sulaiman, ban ta’ba zaton a rayuwata zan fad’a soyayyar wani namiji kamar yadda na fad’a son Bawan Allah. Kin san wani abu ne, masoyin ya had’e ne, yana da karatu, kyau, aji, da hankali. Kuma dai…. Kai gaskiya Salma ba abin da zance miki, sai ina matuk’ar son Bawan Allah na oh! Irin son mutuwa tare rayuwa tare d’in nan. Sal dan ina jin rayuwa ba shi za ta yi mini wuya. Ba Ita Ba Ce 1, shafi na 28.

Ita kuma Salma, a nan a karo na farko ta fad’a wa Salima abin da ya dad’e a zuciyarta kamar haka:

Sali na fad’a soyayyar wani saurayi da ya gan ni ya yi tayin soyayya tsakanina da shi. Bai wuce awoyi da shigarsa kacokan cikin tunanina ba, na sami wannan matsala. A halin yanzu ya yi kowane irin siye tunanina, ya kutsa kowane loko na zuciyata da raina. Ina jin duk inda kike ji a soyayyarki da Bawan Allah, ko in ce fiye da haka, amma fatana yanzu shi ne in cire shi daga zuciyata sai dai ya gagare ni.  Shafi na 29.

Matsala mafi girma da ke cikin soyayyar wad’annan tagwaye ita ce, sanya tsananin son wani da hak’ik’ance ba a iya rayuwa idan aka rasa shi. Wannan abu ne kuma ya ci gaba da bunk’asa cikin zuciyar kowacensu, ba tare da sun san saurayi guda ne suke tarayyar so su biyu ba. Bayan da aka sallamo Salma daga asibiti ne sai Salima ta gayyaci Mus’ab gidansu. Zuwansa Salma ta had’a ido da shi. Wannan ya haifar mata ciwon zuciya. Ita ma Salima a nan ta fara rashin lafiya mai tsanani. Su biyu suka kwanta ciwo asibiti dalilin Mus’ab. Kowace na tsananin son sa. Irin wannan makauniyar soyayya, matsala ce da ake samu ga wasu mata da ke sa son wani abu cikin ransu, idan suka rasa shi sai ya zama sanadiyyar shigarsu wani mawuyacin hali.

Shi ma littafin Da Hannun Maza 1, wata yarinya ce ta shiga matsalar soyayya da wani saurayi mai suna Ibrahim. Salamatu ta fara had’uwa da Ibrahim ne  a lokacin da ya taimake ta, ya k’wato mata jakar hannu da wani ya fizge a hannunta. Tun a wannan ranar Salamatu ta shiga tarkon son Ibrahim.

Wata rana tana k’ofar gida sai Ibrahim ya biyo. Suka gaisa inda a nan ta nuna buk’atar ya rik’a biyowa gida su gaisa. Sannu-sannu son Ibrahim ya nuna cikin zuciyarta. Salamatu ta kasance mai yi wa Ibrahim hidima; ta ba shi kud’i da abinci, ta kuma yi masa wankin tufafi. Takan je d’akinsa taya shi hira. A haka ya yi mata ciki. Da ciki ya bayyana, sai Ibrahim ya gudu, ya bar ta. Wannan hali ya sa Salamatu sambatu da furta kalaman da-na-sani da ke  nuna ta fad’a tarnak’in soyayya. Ga kalaman da ta furta:

Ibrahim me na yi maka ka yi mini wannan sakayyar? Ibrahim ban ta’ba tunanin guje maka ba, duk rintsi duk tsanani. Na ci da kai, na sha da kai, na siturta ka. Ni ce har wankinka Ibrahim, na ba ka ruhina da jikina, ashe sakayya ta ita ce ka yi mini ciki ka sanya ni a uk’uba ka gudu ka bar ni! Allah Sarki! Wayyo Ibrahim. Shafi na 53.

La’akari da wannan kalami na Salamatu na nuna matsala ce ta fad’a cikinta. Kafin shiga soyayyarta da Ibrahim, Salamatu yarinya ce natsattsiya da ba ta kula maza balle shiga d’akin kowane saurayi. Son da take yi wa Ibrahim ya sa ta manta matsayinta, ta ba shi amana, shi kuma ya yaudare ta, ya yi mata ciki. A al’ummar Hausawa, bayyanar ciki ga mace ba tare da aure ba na cikin mafi munin abin kunya da k’yama da ke nuna gur’batar tarbiyyarta. Sanin haka ne ya sa Salamatu kuka da shiga mawuyacin hali.

Ita ma wata mai suna A’isha da ke cikin littafin Mace Mutum sakamakon soyayyarta da wani saurayi da ya fito da sunan aurenta, ta yi ciki, ya kuma yi watsi da ita.

….. Baba na ji ya sauko daga benensa, cikin fushi ya dinga taka ni, yana rafka mini duk abin da ya samu, ana rik’e shi wai sai ya kashe ni. Daga baya bayan na yi laga-laga sai ya sanya cewa sai na fad’i wanda ya yi mini. Ban san abin da zai kai ni ga yin ciki ba, amma da na yi na san wanda ya yi, kuma na fad’a. Baba ya d’auki hularsa ya tafi gidan. Nan aka bar ni tsakanin masu la’anata, tir, da tofin Allah tsine. Wasu na alhaki ne ya cika da ni, wasu na gadon uwata na yi. A haka muke har baba ya dawo yana ture-turen ashar ya sake rufe ni da duka da k’yar aka k’wace ni, ‘shegiya, ‘yar shegiya…. Ba ni kika yi wa ba, kanki kika yi wa, gashi can shi da ubansa sun kafe kai da fata cewa ba shi ya yi ba, sai ki kama hanya ki bar gidan nan, ki je ki nemi wanda ya yi miki ciki…. Shafi na 369.

Idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa, A’isha ta yi ciki ne a daidai lokacin da ba ta san ciki ba. Ta yi ciki ne tana da shekaru goma sha biyar. Ke nan tana sabuwar balaga idan har ma ta balagan. Wanda ya yi cikin zumunta ne da ya fito da sunan son ya aure ta. Mahaifinta ya amince da shi, ya kuma yarje masa zuwa zance. A wurin zancen, yana ke’bewa da ita wuri mai d’an nisa ga idanun mutane. Ba a ankara da abin da saurayin ke yi ba, sai da ciki ya bayyana. Bayyanar cikin ya kawo wa A’isha matsaloli da suka jefa ta cikin rikicin rayuwa. Bayan duka na fitar arziki da mahaifinta ya yi mata, ya yi ik’irarin ta bar masa gidansa. Da aka lalla’be shi, sai ya bar ta, amma ba ta huta da tsarguwa da tsangwama ba. Da ta haihu sai kuma aka kashe yaron alhali tana son abinta. Wad’annan matsaloli ne da mata ke fad’awa ciki da sunan soyayya da wani, sai a yaudare su, a bar su a igiyar ruwa.

3.1.4    Maraici

Maraici shi ne mutuwar iyaye, musamman ga k’aramin yaro. Maraici hali ne na rasuwar mahaifi, da ke kula da lamurran ‘ya’yansa. Maraici abu ne da ke kawo talauci ga yara da yawa. Maraici na cikin manyan matsalolin da ke jefa ‘ya’ya mata halin k’uncin rayuwa a koyaushe.

Babban abu na farko da maraici yake haddasa wa ga mace shi ne talauci. A cewar CNHN (2006), Talauci shi ne rashin wadata. Talauci yanayi ne na rashin abin masarufi da zai ishi mutum tafiyar da al’amurran rayuwarsa na yau da kullum. Talauci abu ne da kowane mutum ba ya son sa. Manzon Allah (S A W) ya rok’i Allah kariya daga abubuwa uku ciki har da talauci inda ya ce:

‘Ya Allah ina neman tsarinka daga talauci da k’aranci da k’ask’anci, ina kuma neman tsarinka daga in yi zalunci ko a zalunce ni. Tirmizi da Abi Zarri suka ruwaito hadisin.[3]

Talauci kan sa wasu mutane su rasa ‘yancinsu, su yi watsi da damarsu, su fad’a cikin halin k’unci da matsuwa. Mutane da dama sun shiga kunya da aikata miyagun ayyukan ta’addanci domin k’ok’arin fita daga cikin talauci.

A halin zamantakewar jama’a, jinsin mata ne talauci ya fi yi wa illa babba. Mace ta kasance mai raunin k’arfin jiki da za ta iya fafutuka da k’arfinta da kai-kawo domin kawar da talauci gare ta. Rashin k’arfi na sa duk lokacin da talauci ya shafi mata, sai wasu su shiga sayar da mutuncinsu, daga k’arshe sai rayuwarsu ta gur’bata, kuma k’arshe a yi watsi da su.

Wani abu da halin talauci ke shigar da mata shi ne sayar da ‘yancinsu. Kowace mace na son ta huta gwargwado, ta sami walwala, ilmi da shiga cikin tsara a dama da ita. Mata da ke cikin talauci kan bar damarsu da ‘yancinsu, su kama ayyukan cikin gidajen masu hali. Yawancin ayyukan cikin gida da matan suke yi sun had’a da shara, wanki, wanke-wanken kayan abinci, dafuwar abinci, gyaran d’aki da sauransu. Dukkan wad’annan ayyuka ne na yau da kullum da ba za su bar mace ta sami damar neman ilmi da sauransu ba. Irin wannan na sa har mace ta k’are rayuwarta ba ta sami ‘yancin sanin Ubangiji ba, bale ta bauta masa.

Wata illar kuma ita ce talla. Talla wata babbar hanya ce da ke kai mace ga gur’batar rayuwa. Hanya ce ta d’aukar wani abin masarufi, ana zagayawa da shi domin masu buk’ata su gani, su saya. A rayuwar mace talla aibi ce babba da ke kai ta ga kowace irin hasara.

Idan mace musamman budurwa ta fara talla, wannan zai kasance wata kafa ga ashararun maza na fara neman hanyar huld’a da ita. Shaid’anun maza kan fara shiga huld’a kai tsaye da yarinyar da ke talla ta hanyar sayen abin da take tallatawa. Daga saye yau da gobe, sai su shiga neman zance da ita, a hankali sai kyauta da sauransu. Wannan sai ya ba su damar gabatar da buk’atarsu gare ta[4]. Idan ta bijire, sai su shiga ci mata mutunci da neman ta biya su har abin da ba su ba ta ba. Idan magabatanta suka yi yunk’urin ba ta kariya, sai cin mutunci ya had’a da su domin su suka saya mata.

Abu na biyu mai aibi da talla ke haifarwa ga mace shi ne zubar da mutunci. Mace mutum ce mai mutuncin gaske ga kowane namiji nagari. Maza kan mutunta mace, su ba ta kariya a yanayi mai yawa, matuk’ar ba ta yi wani abu na zubar da mutuncinta ba a addini ko al’ada. Talla hanya ce da ke yada mutuncin mace kai tsaye ga kowane namiji. Idan mace ta shiga hanyar talla, ana kallon ta a matsayin yasasshiya, wadda ta rasa kulawa tagari. Ana dubanta a matsayin ‘yar iska koda ba haka take ba. Wannan na sanya a yawancin lokuta ko da an gan ta a halin buk’ata ba a ba ta gudunmmuwar da ta dace. Wannan kan haifar da matsaloli masu yawa ga mata.

Rahma Abdulmajid ta sanya maraici matsayin d’aya daga cikin manyan matsalolin mata cikin adabinta. A littafinta na Za Ta Iya, ta nuna yadda halin maraici ya sa wata yarinya mai suna Nafisa ayyukan cikin gida ga wasu gidajen masu hali guda biyu. Gida na farko shi ne gidan mahaifinta wanda ya kore su tare da mahaifiyarsu tun suna jarirai[5] A gidan ta yi ayyukan wanke-wanke da gyaran d’akin wani saurayi mai suna Sadik’. Sadik’ ya fad’a tarkon son Nafisa, amma ita ta yi k’ok’arin nisantar da kanta domin tsoron matsayinsa. Ga yadda Rahma ta kawo yadda Nafisa ta bayyana k’orafinta cikin littafin Za Ta Iya 1:

Da ni ‘yar iska ce, to sai in ce za ka iya nemana, domin kowane lokaci d’an iska kan kai kansa inda Allah bai kai shi ba, amma ta’adata ba ita ce iskanci ba, dan haka a aure kam ka fi k’arfina, dan ba zan kai kaina inda Allah bai kai ni ba. Shafi na 49.

A wani wuri cikin wannan littafi ta ci gaba da nuna fargabarta take cewa,

Na lura in har zanci gaba da zama a k’ark’ashinka ma’ana ina yi maka aiki, to ba za ka hak’ure mini ‘yancina ba dan haka ka yi hak’uri, zan bar aikin a yau ba a gobe ba. Shafi na 49.

Bayanan Nafisa na nuna fargaba da k’in jinin da take yi ga soyayyar Sadik’. Ta lura ci gaba da aikinta a k’ark’ashin Sadik’ zai haifar mata rashin ‘yancin da take ji tana da shi a gidan. ‘Yancinta a wannan hali shi ne rashin sa mata ido da mahaifiyar Sadik’ Hajiya Zuwaira da duk masu aikin gidan ke tsoro ba ta yi ba wadda tana iya yi mata komai idan ta ji irinta marashiya gata tana soyayya da d’anta. Tsoron abin da zai iya faruwa ya sa Nafisa ta yanke barin aikinta kai tsaye, babu ‘bata lokaci.

Gida na biyu da Nafisa ta koma aiki shi ne gidan wata mata mai suna Ester inda a can yayanta Ahmad ya taras da ita. Ga yadda Rahma ta kawo batun a cikin lttafin Za Ta Iya 2:

A k’ofar gidan suka had’u. ‘Ahmad wana’ Nafisata’ suka rungume juna. Tuni mutanen ginin suka soma taruwa. ‘Waye wannan? Wata mata ce ta tambayi Nafisa, …..Nafisa ta juyo, ‘Madam yayana ne.’ Matar ta juyo Ahmad gare ta tana murmushi, ‘Ko shi ne Ahmad da kike fad’i?’ ya juyo gare ta, ‘Wace  ce wannan Nafisa?’ ‘Ita nake yi wa aiki Ahmad. Shafi na 7.

Idan aka dubi rayuwar Nafisa kacokam, sai a ga cewa halin maraici ne ya saka ta cikin talaucin da ya sa ta shiga ayyuka a gidajen wad’annan mutane. Irin wannan yanayi matsala ce babba a rayuwar mata masu yawa cikin al’umma. Wasu mata ta irin wannan hali suke rasa ‘yancinsu da damar da suke da ita, wasu ma a irin haka har su rasa rayukansu.

A cikin littafi Mace Mutum akwai wata yarinya mai suna Amina wadda matsalar maraici ya jefa ta cikin yanayin rayuwa mai wuya. D’aya daga cikin yanayin shi ne na tallar ruwan sanyi ba da son rayuwarta. Ga yadda Rahma ta kawo batun tallar Amina:

…Amina dai ba ta son wannan sana’a, amma ta tuna ba ta da za’bi. Ba za ta ma iya cewa ba za ta yi ba. Sai dai ta kasa rabuwa da tunanin makaranta. Yanzu an kusa jarrabawar k’arshe. An kusa yin jarrabawar gasar shiga sakandire wato. An wuce ta a komai, d’alibai sun yi nisa sun bar ta. Da abin ya dame ta sai ta yi wa Mama Bilki magana, wadda ta yi mata alk’awarin yi mata sauyin makaranta da za ta shigar da ita sahun wannan jarrabawa. Amma da sharad’in sai ta sayar da ruwa na wata ta tara kud’i. Haka za ka ga Amina tsakanin cunkoson motoci da ruwan k’wandaloli tana ratsawa tana tallar ruwa mai sanyi…. shafi 289-28

Amina d’iya ce ga wani mai suna Alhaji Garba Ciroma wanda ya k’i kar’barta a matsayin d’iya lokacin da aka haife ta. Ciroma ya zargi mahaifiyar Amina mai suna Fatima God’iya da samu ciki da wani, amma ba shi ba. Dalilin Ciroma shi ne malaminsa ya gaya masa namiji zai haifa matuk’ar dai shi ya yi ciki. Matakin da Ciroma ya d’auka ya tilasta Fatima God’iya barin Sakkwato ta koma Lagos. A can Lagos ne Fatima ta rasu, ita kuma Amina ta ci gaba da rayuwa a hannun mutane daban-daban. A hannun wata Bayarba mai suna Mama Balki wadda ta ku’butar da ita daga rikicin k’abilar Yarbawa ta fara talla kan dole. A ra’ayin Amina karatu take so ta yi, amma dole ta kar’bi tallar ruwan sanyi domin shi ne sharad’i na k’arshe na ba ta damar karatunta. Wannan ya nuna ba don maraicin uba da ya k’i kar’bar ta a matsayin d’iya, da mutuwar mahaifiya ba da Amina ba ta tsinci kanta da tallar ruwan da ya kusa kawar da matancinta ga wani ba[6]. Irin wannan matsala ce ke sa a yau ake samun yara na yawon gararamba, ba karatun addini, ba na boko. Wasu cikin yaran da za su sami damar ilimi, da sun zama masu d’imbin amfani ga al’umma kamar yadda Amina ta kasance bayan da ta sami ilmi.

 

4.1       Kammalawa


Adabin Rahma Abdulmajid taska ce da ta tattara al’amurran da suka shafi rayuwar mata. A zamantakewar al’umma, mata na fuskantar matsaloli masu yawa wad’anda su ne suke dagula ci gabansu. Wannan ya sa ake ta yekuwar taimaka musu ta hanyoyi masu yawa. Matsalolin mata da Rahma ta kawo cikin littattafanta wad’anda a wannan mak’alar aka yi nazarin wasu kad’an cikinsu, na nuna Rahma ta nuna damuwa da jarunta sosai wajen yin fashin bak’in matsalolin a cikin fasalin k’aga labarin hira.

Wani abu kuma shi ne, la’akari da aka yi da zamanin fara rubuta adabinta zuwa yau, ta rubuta littattafai da suka kai 30.[7] Rubuta irin wannan adadi cikin shekaru 20, abu ne wanda sai namijin tsaye, mai yalwar lokaci zai iya. Rahma tare da kasancewarta matar aure, mai hidimomin miji da ‘ya’ya ba su hana ta amfani da d’an lokacin da take da shi ba ta yi wannan gagarumar gudummuwa ga adabin Hausa ba.

Wani abu da mak’alar ta gano na jaruntar Rahma shi ne, kasancewarta ta farko da ta rubuta littafin k’agaggen labarin Hausa mafi yawan shafuka da yawan kalmomi. Littafinta mai suna Mace Mutum ya k’unshi shafuka …. da yawan kalmomi miliyan sha d’aya da dubu sittin da bakwai da d’ari bakwai da saba’in da biyar (11, 67775).

Daga k’arshe, akwai buk’atar ci gaba da nazarin littattafan Rahma saboda akwai amfani mai yawa da za a samu cikinsu. Ba lamarin rayuwar mata kawai ba, akwai darussan da suka shafi kyautata tarbiyya, da dabarun sasanta husuma, da fad’akar da al’umma da sauransu. Ta hanyar nazari kad’ai za a iya fito da wad’annan muhimman abubuwan ci gaba a sarari ga d’alibai da alumma baki d’aya.

                                                            Manazarta


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

[1] . Aliyu Rila, M. R. (1990), shafi na 299, ya kawo hadisin Annabi (S A W), inda yake cewa, Kashedinku, kashedinku ga mata, haqiqa su tsararru ne cikin hannunku kun riqe su da amanar Allah.

[2] . Al’amin ya kasance miji mai ba da kyakkyawar kulawa ga matarsa Zainab irin kulawar da ake yi wa mai yin irinta da suna ‘Bawan mace.’

[3] . Domin ganin wannan hadisi, a dubi Qahxani, S. A. (2008), Addu’a’u Minal Kitabi was Sunnati wa Yalihi Al-Ilaju bir-Ruqa Min Alkitabi was-Sunnati, shafi na 45.

[4] Littafin wasar kwaikwayo na Zamanin nan Namu wanda Shu’aibu Maqarfi ya rubuta a shekarar 1953, a wasarsa ta biyu ya nuna yadda talla ke lalata tarbiyyar yara mata. A wasar ta biyu ya yi amfani da wata yarinya mai suna ‘Yar Masu Gida wadda mahaifiyarta take aza wa talla. ‘Yar Masu Gida yarinya ce mai kyakkyewar tarbiyya wadda dalilin talla tarbiyyarta ta gurvace har da kwana xakin sarkin samari.

[5] . Alhaji Muhammadu Zakanya ya kori Hajiya Rabi da tagwayenta lokacin da Hajiya Zuwaira Jari ta sa aka liqa wa Hajiya Rabi samun ciki da direban gidan mai suna Lauwali.

[6] . Wata rana ta makara ne wani Bayarbe mai suna baba Bukalo mai taya ya rutsa ta da qarfi cikin wani xaki da ya yi mata wayo, ya kira ta ta kawo masa ruwa. Ya kai ta qasa, tana kururuwa, sai Allah ya kawo wani da ya yi masa magana, sannan ya bar ta ta tafi.

[7] . An kawo wannan adadi ne idan aka dubi kowane littafi da zaman kansa. Idan kuwa aka haxe littafin da ta raba zuwa gida biyu ko uku, za a ga cewa ta wallafa littattafai ne guda 17. Wannan adadin ya tsaya ne ga abin da nake da su a hannuna da kuma waxanda na ga sunayensu cikin wasu littattafanta. A hannuna ina da littattafanta na kan wannan adadi na 17, guda sha huxu.

Post a Comment

0 Comments