Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba A Wane Bakin Banza: Kyaftin Umaru Ɗa Suru a Matsayin Jarumi/gwarzo

Daga

Haruna Umar Maikwari

Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi da Kere-Kere ta GwamnatinTarayya, Gusau Jihar Zamfara

Email: Maikwariharuna@gmail.com

Phone: 07031280554

Da

Dano Balarabe Bunza

Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Email: danobunza@yahoo.com

Phone: 07035141980, 08113544918.

www.amsoshi.com

Tsakure


Jarumi/gwarzo shi ne mutumin da ya aikata wani aikin a-zo-a-gani na jawo wa kansa da jama’arsa wani amfani ga rayuwarsu ko d’aga sunansu da sauransu. Akan sami jarumai /gwaraje iri-iri a ‘bangarori da dama na rayuwar al’umma. A cikin kowane lamari ana samun wanda ya fi saura yin fice a ciki da suka had’a da yak’i da  noma da karatu da kasuwanci da taimako da ma cutarwa irin ta ‘barayin zamani musamman idan aka yi la’akari da k’asar Nijeriya a yau. Zancen gwarzo/jarumi da aka kawo ya sa wannan muk’ala ta k’uduri fad’ar wani abu game da Kyaftin Umaru ‘Da Suru saboda ya ‘bata hankalin dare ya sami sunan jarumi. Abubuwan da suka tabbatar da zaman Kyaftin Suru jarumi sun had’a da ficensa a ‘bangaren rubuta wak’ok’in Hausa da ya shafi jigogin wak’ok’insa da rerawar da yake yi tare da yaransa da kasancewarsa hazik’i wajen hardace wak’ok’insa da rashin aron muryar kowane marubuci da daidaita k’afiyar wak’ok’insa ba tare da gi’bi ba da ilmantarwa da kuma wayar da kan al’umma. Tare da haka Kyaftin Suru jarumi ne a fagen aikin koyarwa da aikin soja da siyasar zamani. Bugu da k’ari, mutum ne mai gaskiya da amana da rik’o da su baki d’aya. A kan wad’annan abubuwa ne muk’alar ta yanke hukuncin cewa Kyaftin Umaru ‘Da Suru jarumi/gwarzo (Hero) ne.

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

Gabatarwa


A zamanin da an zaci jarumi/gwarzo shi ne wanda ya yi d’auki-ba-dad’i a wurin yak’i da sauran wuraren tashe-tashen hankula kuma ya yi fice. Akan sami jarumawa a yak’e-yak’en addini da na k’abilanci da sha’anin siyasa da shugabancin al’umma da sauran ‘bangarorin rayuwa baki d’aya. Ganin haka ya sa wannan muk’ala ta hango wasu abubuwan rayuwa da Kyaftin Umaru ‘Da Suru ya yi fice a cikinsu da ba za a musanta zamansa jarumi ba a wad’annan ‘bangarori. An yi tunanin haka ne domin k’yallaro abubuwan da wad’anda suka kar’bi sunan jarumawa bai zarce na Kyaftin ba. Kamar yadda karin maganar da ke cewa, Allah ke yin amali ko cikin rak’uma, gaskiya ne domin an ce, yaro ‘bata hankalin dare ka yi suna. Idan aka yi la’akari da wad’annan maganganun hikima za a tabbatar da Kyaftin Umaru ‘Da Suru ya yi fice a abubuwan da za a kawo domin ya ‘bata hankalin dare a kansu har ya sami yin wannan fice. Za a aminta da wannan idan aka fayyace irin ficen da Kyaftin ya samu tun daga k’auyensu da k’aramar hukumarsu da jiharsu da kuma k’asa baki d’aya saboda gudummuwar da ya bayar ga cigaban abubuwan da aka ambata a sama. La’akari da wad’annan abubuwan cigaba da ke sa a kira wani jarumi/gwarzo, muka lura da cewa, Kyaftin Umaru ‘Da Suru jarumi/gwarzo ne idan ma ba jarumin jarumawa/gwarzon gwaraje ba. Abubuwan da za a duba da muk’alar za ta kalla sun had’a da wad’annan:

Wane ne Jarumi/gwarzo?


Kalmar jarumi/gwarzo Bahaushiya ce da masana suka daidaita akalar ma’anarta kamar yadda za a gani kamar haka:

Kalmar gwarzo, gwarzuwa da gwaraje an fassara su da protagonist[1] da Turanci. Haka ma an fassara kalmar protagonist[2] da gwarzo da sunan namiji, gwarzuwa da sunan tamace da gwaraje a matsayin jam’i. Haka kuma an k’ara da cewa a dubi kalmar hero mai nufin gwarzo[3].

A wani wuri kuma, an bayar da ma’anar gwarzo da cewa (i) jarumin mutum (ii) sabon tohon baba (iii) Wani irin lalle mai kamun gaske[4].

A wani wuri kuma cewa aka yi, gwarzo na nufin (a) an energetic, capable worker, a man of pluck and grit (b) a man of about 40 years of age[5].

A fahimtarmu, jarumi/gwarzo na nufin mutumin da ya yi fice ga wasu abubuwan rayuwa da ba kowa da kowa ya sami hakan ba. Misali, idan aka yi zancen rashin tsoro sai a ce a bid’o wane. Wanen nan ya zama jarumi /gwarzo a ‘bangaren rashin tsoro. Haka abin yake a sauran ‘bangarorin rayuwa da suka had’a da shugabanci da siyasa da sauran ayyukan da suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum.

Wane ne Kyaftin Umaru ‘Da Suru?


Sanin ko wane ne Kyaftin Umaru ‘Da Suru a cikin wannan muk’ala ba abin da ke yiwuwa ne baki d’aya ba. Dalili kuwa, babu  muk’alar da ke isa a fayyace tarihin jarumi a cikinta sai dai a gutsuri kad’an a fad’a domin a yi susa gurbin k’aik’ayi ga wanda bai san shi ba domin duk yadda mutum ya yi fice, za a sami wani bai ko ta’ba jin labarinsa ba. Saboda haka ga kad’an dangane da Kyaftin Umaru ‘Da Suru:

An haifi Umaru ‘Da Suru a garin Suru ta tsohuwar jihar Sakkwato a da, yanzu kuwa a jihar Kabin Nijeriya a shekarar 1946 a unguwa mai suna Shiyar Buda. Sunan mahaifinsa Abubakar, mahaifiyarsa kuma A’ishatu, ana yi mata lak’abi da Balaraba. Sunan kakanninsa na ‘bangaren mahaifinsa su ne, Abubakar da Rik’a. Su kuma na ‘bangaren mahaifiya su ne, Muhammadu Ango da A’ishatu, ita ma mai lak’abin Balaraba. An sa Kyaftin makarantar allo tun yana d’an shekara biyu da rabi domin ya saba da zuwa idan ya girma. Haka kuma an sanya shi makarantar firamare yana da shekara bakwai a garin Suru a 1952. Daga nan ya hurce zuwa Middle School a garin Bunza. Bayan ya k’are ya sami nasarar zarcewa zuwa makarantar sakandare a garin Birnin Kebbi a 1960-61, inda ya hurce zuwa HTTC Gombe a1962-65 wurin da ya sami nasarar jarabawarsa ta Grade II lokacin k’arewa. Yana k’arewa sai aka ba shi aikin koyarwa zuwa garin Koko. Gari na biyu da ya yi koyarwa bayan baro Koko shi ne, garin Suru. Daga Suru sai makarantar Mak’erar Gandu a Birnin Kebbi inda ya rik’i muk’amin mataimakin shugaban makaranta. Daga nan kuma, sai aka kai shi garin Kamba a matsayin shugaban makaranta.

Daga garin Kamba Kyaftin Suru ya tafi makarantar sojoji da ke Kaduna, domin koyar da sojoji saboda tsananin buk’atar malaman da za su koyar da sojoji a wannan lokaci.. Daga baya ne gammo ya juye da kaya ya shiga aikin soja gadan-gadan. Ya tafi kwas a k’asashen waje sau da dama irin Amerika da Pakistan da Indiya da sauransu. Haka kuma ya yi aiki cikin k’asa wurare daban-daban da suka had’a da Lagos da Kaduna da sauransu. A tak’aice Kyaftin Suru bai yi ritaya a gidan soja ba sai da ya kai ga muk’amin Captain wanda shi ne sanadiyar kiran sa Kyaftin da ake yi. Ba kyaftin ‘yan k’wallon k’afa ba ne ko sunan da ake lak’aba wa mutum domin wani ra’ayi ko sha’awa ba. Duk wanda ya fara aikin soja har ya kai matsayin Kyaftin zancen fice dahir ne.

Bayan Kyaftin ya yi ritaya daga aikin soja sai ya komo gida ya tsunduma cikin siyasar k’aramar hukuma da jiha baki d’aya. Ya yi takarar shugaban k’aramar hukumar mulkin Bunza a shekarar 1987. Ya ci gaba da fafitikar siyasa a k’aramar hukumarsa da kuma jiha. Ana nan sai aka yi jihar Kabi a shekarar 1991 inda da siyasa ta tashi a zamanin shugaban k’asa Ibrahim Badamasi Babangida, Kyaftin Suru ya tsaya takarar muk’amin shugaban k’aramar hukumar mulki ta Suru bayan da aka raba Suru da Bunza. Kyaftin Umaru ‘Da Suru ya jagoranci k’aramar hukumar Suru har sau biyu a muk’amin shugabanta. Ya sami yin fice sosai saaboda k’wazon da ya nuna lokacin da yake kan kujerar mulkin k’aramar hukumarsu. A cikin wad’annan abubuwa ne da Kyaftin ya yi aka sami gano cewa, jarumi ne da ya yi jaruntakar da ba za a manta da shi a tarihi ba. Abubuwan da za a zayyano nan gaba kad’an domin tabbatar wa wanda bai san ko wane ne Kyaftin Suru ba za su taimaka domin samun abin kamawa.

Kyaftin Umaru ‘Da Suru a Matsayin Gwarzo/Jarumi


Ba za a kira wani gwarzo ko jarumi ba face ya aikata abin da aka san aikin gwaraje ko jarumai ne. Ana samun jarumi a ‘bangaren noma da yak’i da dambe da wak’ar baka da rubutattu da sauran abubuwan da suka shafi ‘bangarorin rayuwar al’umma baki d’aya. Ganin haka tare da sanin Kyaftin Umaru ‘Da Suru ya taka matakan da suka kai a kira shi jarumi/gwarzo ya sa aka yi tunanin rubuta wannan muk’ala. Akwai abubuwa da dama da idan aka kalle su, sun isa a tabbatar/yarda da cewa, Kyaftin Suru jarumi/gwarzo domin ba k’age ba ne, filin wuri ne dabon d’an kama. Ga abubuwan da suka tabbatar da kasancewar Kyaftin Umaru ‘Da Suru jarumi ko tauraro ko gwarzo a zamaninsa.

Fice a ‘Bangaren Rubuta Wak’ok’in Hausa


Kyaftin Suru sanannen marubuci wak’ok’in Hausa ne da ba ya yiwuwa a yi zancen marubuta wak’ok’i a jihar Kabin Nijeriya ba tare da an ambace shi ba. Akwai abubuwan da suka sanya Kyaftin Suru ya yi fice a ‘bangaren rubutattun wak’ok’in Hausa da dama. Kyaftin ya nuna jarumi ne da kansa a wani baitin wak’a inda ya ce:

  1. In ana yak’in wak’a,


Yanzu na wuce in shek’a,

Na yi bom da igwar wak’a,

Na yi nukiliyan wak’a,

Ban ga mai ban tsoro ba.

(Wak’ar K’arkon Mashek’iya Shan K’aik’ai).

Da jin wad’annan kalamai na Kyaftin za a fahimci ba kanwan lasa ba ne a fagen rubuta wak’ok’in Hausa. Daga cikin abubuwan da za a duba a k’ark’ashin ficensa/kasancewarsa jarumi a fagen wak’a akwai wad’annan:

Jigogin wak’ok’insa     


Bisa ga tsarin sanannun jigogin da rubutattun wak’ok’in Hausa ke d’auke da su, Kyaftin bai rago ko d’aya daga cikinsu ba face ya rubuta wak’ar da ke d’auke da su gwargwadon hali. Sanannun jigogin rubutattun wak’ok’in Hausa da aka sani aka kuma saba da su su ne, tarihi/labara da yabo da zambo da habaici da gargad’i da wa’azi da ta’aziyya da ilimi da fad’akarwa da sauransu kafin jigogin su zama jakar magori kamar zamanin da ake ciki. Kyaftin ya rubuta d’imbin wak’ok’i da ke d’auke da wad’annan jigogi musamman idan aka ratsi wak’ok’in da ya rubuta daga fara rubuta wak’ok’insa zuwa lokacin da ya bar duniya. Za a tabbatar da haka idan aka nazarci wak’arsa ta Muhammadu Bello Koko, Baturen makarantar Gwandu N.A. a ‘bangaren abin da ya shafi yabo. Dangane da yin ta’aziyyar rasuwa kuwa, za a ga haka cikin wak’ar ta’aziyyar Magajin Maikwari,Alhaji Muhammadu Bello ‘Dangwandu. A kan wa’azi kuwa, a sami wak’ar masu tsafi da ‘yan bori, zambo kuwa a sami K’arkon mashek’iya shan k’aik’aid a ta Dolon ‘Dansiyasa da sauransu. Kyaftin bai ta’ba kwana da shakkun wak’a ba balle gabansa ya fad’i kamar yadda abin yake ga sauran marubuta wak’a. Saboda tabbatar da ana yin wak’a ne domin isar da wani sak’o ya sa Kyaftin ya ce:

  1. Kway yi wak’a ba jigo,


Ya yi riga ba taggo,

Ba bisashe yai faggo,

Ba amarya ba ango,

Ban ga dale ga rani ba.

(K’arkon Mashek’iya Shan K’aik’ai)

Rerawa Tare da Yaransa


A cikin marubuta wak’ok’in Hausa Kyaftin kad’ai aka samu na rera wak’a da yaransa da murya d’aya a lokaci d’aya. Babu marubuci wak’an da aka samu da irin wannan sifa a wajen rerawa. Yana da yara biyu k’wararri kuma sanannu a fagen rera wak’ok’insa da suka had’a da Musa Maidawa (Surus) da Garba Short (Garus). A cikin wak’ar Gurdumu ce kad’ai ya kawo sunan mutum d’aya wanda ahak’ik’ani ba yarona ba ne, abokinsa ne. Duk da haka tunda ya sa bakinsa cikin wak’ar ya zama yar tunda Kyaftin ne maigida.  Dalilin da ya sa aka ce k’wararri ne shi ne, kowannensu na rubuta tasa wak’a yanzu haka saboda renon da aka ba su tare da baiwar da Allah ya yi musu. Har yanzu ba a sami mai rubuta wak’a ya rera tare da yaransa ba kamar Kyaftin Suru. Za a tabbatar da haka idan aka saurari wak’ok’insa. Akwai wurin day a ambaci sunan yaransa uku da ya yi wannan wak’a da su kamar haka:

  1. Yarana guda ukku su duka sun iya,


Ga Musa akwai Garba ga kuma ‘Dan’iya,

Sun had’a baituna goma har daguda d’aya,

Musa da Garba kowa biyar d’aya ‘Dan’iya,

Tasu gudummuwa ce ga wak’ar Gurdumu

Jarumi ne a Wajen Hardace Wak’ok’insa


Ga al’ada ba kowane marubuci ke iya hardace wak’ok’insa ba.Wasu na rubutawa su karanta amma, ba su iya hardacewa amma, Kyaftin gwani na gwanaye ne wajen hardace wak’ok’in day a rubuta. Duk wanda ya san shi, haka ya san shi. Akwai wata shekara da zai je Abuja, daga lokacin da suka tashi har suka sauka rera wak’ok’insa yake yi day a rubuta ba tare da karantawa daga takarda ko littafi ba, sai dai harda kawai. Mafi yawan masu hardacewak’ok’insu makafi ne. Tare da haka sai Allah ya yi wa Kyaftin baiwar hardace wak’ok’insa ba tare da yana makaho ba. Don haka, Kyaftin Suru gwarzo ne a ‘bangaren harder wak’ok’in day a rubuta.

Bai Ari Karin Wak’ar Kowa ba


Marubuta da yawa aron muryoyin wasu marubuta suke yi, ko dai na masu rubutawa ko na baka su samar da nasu kari amma, Kyaftin Suru ya ku’buta daga aron muryar kowa sai dai a ari tasa. A iya binciken da muka gudanar ba wanda ya tabbatar muna cewa ga wak’a d’aya da Kyaftin ya ari muryar wani ya rubuta tasa. Tare da haka, makusantan Kyaftin Suru irin Aliyu Muhammad Bunza da Musa Maidawa da Garba Garus da Malami Ja’b’bi Bunza duk sun ari muryoyinsa sun rubuta nasu wak’ok’i ba tare da gaya min wak’a d’aya da Kyaftin ya ari muryar kowa ya rubuta tasa ba. A nan za mu iya cewa, Kyaftin ya kai jarumi a fannin rashin aron muryar kowa a wajen rubuta wak’a. Ke nan, wannan ya nuna cewa Kyaftin ba ka aro ne sai dai, a ara gare ka.

K’afiyar Wak’ok’insa ba ta da Gi’bi


Da yawa akan sami wasu marubuta na amfani da wasu kalmomi a matsayin amsa amonsu babba ko k’arami dab a bias k’a’ida ba. Wannan na faruwa ne saboda k’ok’arin ganin Karin wak’ok’insu bai katse ba kawai, ba domin kalmomin da suka yi amfani da su na da ma’ana ba. Idan aka dubi k’afiyoyin wak’ok’in Kyaftin za a sami sanannun kalmomin Hausa ne sai dais u kasance tsofaffin kalmomi ko kuma sababbi da aka fi sani a wannan zamani. Dukyadda aka ga kalmar da ba a fahimta ba a cikin wak’ok’insa, sai dai a tarar da tsofaffi ne amma, ba don ba su da ma’ana ba, daga wak’arsa ta farko hart a k’arshe. Wad’anda suka san Kyaftin kuma, suka san wak’ok’insa sheda ne a kan haka. Misali idan aka tambayi Aliyu Muhammad Bunza zai tabbatar wa mai tambaya, haka abin yake babu sa’bani.

Wak’ok’insa Masu Ilmantarwa da Wayar da Kai ne


Wak’ok’in Kyaftin Umaru ‘Da Suru masu ilmantar da al’umma ne ta kowane hali. Babu bare a cikin wak’ok’insa dangane da ilmarntarwa domin, ko wak’ar habaici aka nazarta za a gano akwai ilmantarwa a ciki, balle wad’anda ke d’auke da ilmantarwa a zahiri. Akwai wak’ok’i masu d’imbin yawa da ke ilmantar da al’umma da Kyaftin ya wallafa. Daga cikin wak’ok’insa akwai masu wayar da kai dangane da wasu abubuwa irin siyasa da sauransu. Ga sunayen kad’an daga cikin wak’ok’in Kyaftin da ke ilmantarwa: Masu Tsafi da’Yan Bori da Labarin Suru da Hak’ik’iya Mai ‘Daci da Wak’ar Had’a Kan Surawa da sauran wak’ok’insa duka da ba a kawo ba. Ga misali daga Wak’ar Masu Tsafi da ‘Yan Bori:

  1. Kowa ka tsafi lahira za shi sha horo,


Don ko Nakiri da Munkaranswa yi mai taro.

  1. Ga wanda yay yi samaniya yay yi taurari,


Sannan ku ce ku bi aljanu hayya ‘yan bori.

Jarumi ne a Fagen Aikin Koyarwa/Malanta


Kyaftin ya yi karatu da karantarwa tun an ace wa Bature zaki. Yana d’aya daga cikin d’aliban da suka yi wa jarrabawar Grade II zama d’aya a lokcinsa kuma, yana d’aya daga cikin wad’anda aka ba aikin koyarwa kai tsaye ba tare da aron hannu ba. Ya koyar a sanannun garuruwa hud’u a Kamba. Ba a nan kad’ai Kyaftin ya koyar ba, ya koyar har a makarantar koyar da sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna lokacin da ake neman malamai ruwa a jallo. Wannan ya faru ne saboda hazak’ar da Allah ya ba shi da ficen da ya samu a wannan lokaci. Kyaftin Umaru ‘Da Suru ya yi fice cikin aikin koyarwa a zamanin day a yi shi kuma, za a sami tabbacin haka idan aka sami bayaninsa a Gwandu N.A kamar yadda aka ambata a baya. Wannan ne ya sa Hausawa suka ce, In Allah ya yi mutum zaki, karo das hi ‘barnauk wanda aka d’aukaka babu shakka ya zama jarumi ko a idon mak’iya ne. Mafi yawan ‘yan bokon jihar Kabi d’aliban Kyaftin ne ko d’aliban d’alibansa. Wasu yaransa ne  wasu kuma, abokansa. Mawuyacin abu ne a sami malamin da ya karantar da Kyaftin Suru a raye.

 Jarumi ne a ‘Bangaren Aikin Soja


Kyaftin Umaru ‘Da Suru soja ne kuma, mai kishin k’asa a ‘bangaren samar da cigaba.Kyaftin Suru ya Shiga aikin soja daga muk’amin Kofur har zuwa na Captain. Yana d’aya daga cikin wad’anda suka sanya aka san garin Suru a idon duniya domin ko ba ka san Suru ba, ka ji ana fad’ar sunan Kyaftin Suru.Haka kuma Kyaftin na d’aya daa cikin wad’anda suka sa aka san garin Suru a Nijeriya baki d’aya. Ya je atisaye cikida wajen Nijeriya kuma, yasami lambobin yabo masu yawa domin k’wazon da Allah ya yi masa. Yanan da aboaki a gidan soja da suka had’a da Mamman Vatsa da sauransu. Haka kuma, Ganar Abacha mai gidansa ne kuma yakan zo gidansa tare da yaransa domin kawai Musa Surus ya rera musu wak’ar “Kunkuru” su yi rawa. Garin Suru ya sami fice saboda k’wazon Kyaftin. Ba mu cesoja bay a da daraja ba sai dai, ba a had’a na da da na yanzu. Kyaftin Suru ya shiga aikin soja a shekarar 1972 zuwa 1987 kuma ya yi ritaya da muk’amin Captain. Duk sojan da ya kai Captain a wannan lokaci ba yaro ba ne balle zamanin da Kyaftin ya yi aikin soja. Ficen da Kyaftin ya yi a aikin soja ya sa ba sai an ambaci sunansa ba. A maimakon haka, da an ce Kyaftin Suru an gane ba sai an nemi bayanin wanda ake nufi ba. Saboda wannan fice ne ma lokacin mulkin siyasa na jamhuriya ta biyu karo na biyu, shugaban k’asan wannan lokaci ya za’bi Kyaftin Umaru ‘Da Suru domin ya zama daga cikin masu tsaronsa amma saboda wata siyasa, aka hana Kyaftin d’arewa kan wannan muk’ami. Wanda ya kai ga wannan mataki na aikin soja, ai ba zai ta’ba yiwuwa a ce bai yi fice ba domin k’arya hure take bat a ‘ya’ya.

 

 

Ficensa a ‘Bangaren Siyasa


Jarumi ko gwarzo shi ne wanda ya yi fice a wani ‘bangaren rayuwa fiye da sauran mutanen da ke tare da shi. Idan aka yi zancen siyasa a jihar Kabi a wancan lokaci, Kyaftin Suru ba kanwar lasa ba ne balle idan aka yi zancen Kulwa (K’asar Suru). Kyaftin ya fara siyasa tun a shekarar 1987 har wuce 2000, ana damawa da shi. A lokacin da karensa na tsaye igiya ne mad’aura kaya, wanda bai yi da ku ba ta kwance. Haka kuma, Kyaftin ya yi wani abin day a k’ara samar masa fice da nuna jaruntaka a lokacin da yake shugaban k’aramar hukumar Suru lokacin da Ibrahim Badamasi Babangida na shugabancin Nijeriya, ya rubuta wak’a mai suna “Nijeriya Ina Muka Dosa?” ya je ya ba shi hannu da hannu. Farar gaskiya ce Kyaftin ya fad’a wa shugaban k’asar dangane da matsalolin da aka kad’a k’asar Nijeriya a ciki. A wannan lokaci in ba irin Kyaftin ba, babu wanda zai yi hakan ya kwashe lafiya. Saboda ficen Kyaftin a cikin siyasar Kulwa, ya rik’i muk’amin shugaban k’aramar hukumar mulkin Suru sau biyu kuma, ba wanda ake so da ya kai shi saboda wasu dalilan da suka had’a da nemo wa jama’a hak’k’ensu a duk wurin da yake. Ga abin da aka ce cikin wata wak’ar da Kyaftinya yi dangane da nemo wa jama’arsa hak’k’ensu:

Tsaya wa talakka a k’wato hak’k’ensa,

Ba a barin sa ya muzguna.

A yau ya k’are kulwa,

Domin kama da su Kyaftin k’ila na.

Kyaftin ya yi fice a cikin siyasa tun jihohi uku na had’e, ina ga sun rabu kowace na cin gashin kansa? Haka kuma ya sami yin fice tun k’ananan hukumomi uku na had’e, ina ga kowace na zaman kanta? Saboda haka, al’amarin Kyaftin Suru shi ne da Hausawa ke cewa, “Ko ana muzuru na shaho, zakaran da Allah ya nufa da yin cara sai ya yi”. Bayan wad’annan akwai abubuwan da suka taimaka wa Kyaftin da samun fice a siyasar ‘bangarensa irin kyauta da son jama’a da kyautata ma mutane da yin tsaye a bi musu hak’k’ok’insu sai yadda hali ya yi. Ba ya kwashe abin rabo ya mayar nasa sai dai a kasa kowa ya d’auki rabonsa.Wannan fice da Kyaftin ya samu ba saboda son kai da guni da hasadar mutane ba ne, sai domin son su da kyautata musu da nemo musu hak’k’ok’insu a duk inda suke.Saboda haka, a dad’e ana yi sai gaskiya.

 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

Mutum ne mai Gaskiya da Aiki da Ita


Kyaftin Umaru ‘Da Suru mutum ne mai rik’o da gaskiya da kuma aiki da ita a duk inda ya sami kansa. Wannan na d’aya daga cikin abubuwan da suka taimaka masa gay n fice a sha’anin siyasarsa baki d’aya. Bayan haka, Kyaftin ya sami taimakon Allah da tsare gaskiya gwargwadon hali wanda shi ne sanadiyar samun kar’buwarsa ga jama’a har suka ba shi goyon baya. Ba za a ji k’arya a bakinsa ba kuma, ba a shirya ta da shi. Ga abin daya fad’a a cikin wak’ar tataccen labarin Suru:

  1. Na san aduwa akwai ta Illela ga hanya,


Ga ‘baure ga su tsamiya har da magarya,

Tsada ce ban gani ba ban ko zuba k’arya,

Bil hak’k’i nake tsayi a kan wak’ar Suru.

Haka kuma, Kyaftin Suru ya k’ara tabbatar da maganar da ke cikin baiti na sama a inda ya ce:

  1. Ni duk maganar da na fad’i ban wata sauna,


Don na wuce fyaure in ina shirya batuna,

 

Zai ce haka ne batunka dogo d’an Suru.

Kammalawa


A cikin wannan muk’ala mai taken “Ba a Wane Bakin Banza:Kyaftin Umaru ‘Da Suru a Matsayin Gwarzo/Jarumi” an dubi abubuwa da suka had’a da wane ne gwarzo/jarumi da wane ne Kyaftin Suru da Kyaftin a matsayin gwarzo. Wannan na tare da rakiyar abubuwan da suka had’a da ficensa a ‘bangaren rubuta wak’ok’in Hausa da aka tattauna wasu abubuwa k’ark’ashinsa kamar haka: Jigogin wak’ok’insa da rerawar da yake yi tare da yaransa da hardacewar da yake yi wa wak’ok’insa da rashin aron muryar kowane marub uci wak’a da rashin gi’bI na k’afiyar wak’ok’insa dailmantarwar da wak’ok’insa ke yi da kuma wayar da kan al’umma. Haka kuma ya yi fice a aikin koyarwa da aikin soja da kuma siyasa. Ba wannan kad’ai ba, Kyaftin mutum ne mai amana tare da rik’on gaskiya da aiki da ita. Daga wannan za a iya yanke hukuncin cewa, Kyaftin Umaru ‘Da Suru jarumi ne ko gwarzo ga abin da ya bayyana a cikin wak’ok’insa.

 

 

 

Manazarta


https://www.amsoshi.com/about-us/

[1] A dubi Hausa Metalanguage (Kamus na kebabbun kalmomi) Vol. 1 shafi na 73

[2] Hausa Metalanguage shafi na 41.

[3] Daidai da lamba ta 2 shafi na 24

[4] A dubi Kamusun Hausa na Bayero University shafi na185

[5] A dubi A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary na G.P. Bargery shafi na 426

Post a Comment

0 Comments