Ticker

6/recent/ticker-posts

Rawar Da Waka Take Takawa Wajen Samar Da Hadin Kan ‘Yan Nijeriya: Tsokaci A Kan Wakar Alhaji Musa ‘Dan Ba’u (‘Yan Nijeriya)

Daga.

 Haruna Umar Bungudu

Da

Haruna Umar Maikwari.

 Na Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi Da Kere-Kere Ta Gwamnatin Tarayya, Guasu,  Jihar Zamfara.

Mak’alar da aka gabatar a taron tattaunawa don k’arawa juna sani wanda Tsangayar Harsuna na Kwalejin Ilimi Ta Minna, Jahar Neja, ya Shirya A Ranar 18- 21/11/2013.

www.amsoshi.com

        Tsakure:


        Wak’a wata ‘bangare ce daga cikin Adabi, wadda ke cin gashin kanta, masana da manazarta da dama sun gudanar da bincike da nazarce-nazarce a kan wak’a, inda dukansu suka taka muhimmiyar rawa. Saboda wannan gudummuwar tasu ne a yau in dai d’alibi ya ce zai yi nazari a kan wak’a, to sai dai hannunsa ya gaji domin neman tudun dafawa, ba dai don ya k’ure nazarce-nazarcen ba. Ba burin wannan muk’ala ba ne ta yi nazarin wak’a ba, sai dai tana da k’udirin bayyana yadda wak’a a matsayin wani ‘bangare na adabi ta ke taka muhimmiyar rawa wajen isar da sak’o na samar da had’in kan ‘yan k’asarmu (Nijeriya).



Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan wak’a, sun kuma bayyana cewa wak’a tana d’aya daga cikin hanyoyi mafi sauk’i da ake bi wajen isar da sak’o. Wannan ko shakka babu haka abin yake, don kuwa idan muka yi la’akari da aikin da magabata suka yi irinsu Mujaddadi Shehu Usmanu ‘Danfodiyo, da Abdullahin Gwandu, da Muhammadu Bello, da Nana Asma’u, da Isan Kware, da Abdullahi Mai Bod’inga da dai sauran almajiran Shehu. Za a ga cewa sun yi wak’ok’i na jihadi domin isar da sak’on da suke son isarwa na addinin musulumci. Haka kuma idan aka dubi irin wak’ok’in da ake koyar da yara da su a k’ananan makarantun furamare da ma islamiyoyi za a ga cewa, yara sun fi gane duk wani darasi da aka koyar da su a cikin sigar wak’a. Idan muka d’auki makarantar furamare za mu ga cewa, indan aka koyar da yaro haruffan turanci ko na Hausa a cikin wannan sigar zai fi saurin rik’ewa bisa ga a koyar da shi ba tare da wak’a ba. Haka kuma idan muka koma a kan makarantar islamiyya kuma za mu ga cewa, duk darasin da aka koya wa yara da wak’a kamar su haruffan larabci, da hadisai, da addu’o’i, da tauhidi wad’anda suke da alak’a da wannan za a ga cewa yaran sun fi saurin rik’e su.

A tak’aice dai a nan ana nuna cewa, wak’a tana jan hankali, kuma ta fi saurin shiga kai wajen isar da sak’o. Wannan ya sa ‘yan siyasa suke amfani da mawak’a domin su bayyana wa jama’a manufarsu.

Ba burin wannan muk’ala ta yi nazarin wak’a ba, sai dai tana da k’udurin ta bayyana yadda wak’a take a matsayin wani ‘bangare na adabi ta ke taka muhimmiyar rawa wajen isar da sak’o na samar da had’in kan ‘yan k’asarmu, Nijeriya.

1.1 K’ASAR NIJERIYA.


Nijeriya dai k’asa ce mai tarin arziki, kuma tana a cikin Jamhuriyar Afrika. Nijeriya ta yi iyaka da k’asar Chadi daga Gabas, daga Yamma kuwa ta yi iyaka da Dahomey, daga Kudu ta yi iyaka da Jamhuriyar Benin, daga Arewa ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijer.

Babu shakka haka abin yake domin kuwa Alhaji Shehu Aliyu Shagari (1973) ya fad’a muna a cikin wak’arsa ta Nijeriya cewa:

  1. “Ko gabascin Borno akwai k’asa,


                   Ta Faransi kusan Nijeriya.”

  1. “Yanzu ko ta zan Jamhuriya,


                   Chadi a gabas da Nijeriya.”

                             ----------------

  1. “Dahomey k’asa ce mai yawa,


                   Daga wajjen Yamma mu zagaya.”

                   ------------------------

  1. “To tsakankaninsu akwai k’asa,


                   Babba mai suna Nijeriya.”

  1. “Ingilishi ke mulkin ta da,


                   Kamin ta zamo ‘yantacciya.”

  1. “Ita wagga k’asa makekiya,


                   Babba ce a cikin Afrikiya.”

(Shehu Shagari: Wak’ar Nijeriya )

Baya ga sanin da muka yi cewa ga inda k’asar Nijeriya take, sai gashi tsohon shugaban k’asa Alhaji Shehu Aliyu Shagari (1973) ya fad’a muna da kansa. Dubi baitocin a sama.

Sunan Nijeriya an samo shi daga kogin Neja, (wato River Niger), wata Baturiya ce matar Gwamnan Arewa a zamanin mulkin mallaka wanda ake kira Lord Lugard, mai suna Florer ita ce ta rad’awa k’asar suna, kuma wannan ya samo asali ne daga kalmar nan ta Niger Area, (wato yanki kogin Neja).

Alhaji Shehu Shagari (1973) a wasu baitoci da ya kawo yana cewa:

  1. “Turawa sun ka rad’a mata,


                   Wanga suna wai Nijeriya,”

  1. “Sun kira wani kogi Niger,


                   Mu Kwara muke cewa, jiya.”

  1. “Daga sunan kogin nan d’aya,


                   Suka sa na k’asa suka rataya.”

  1. “Don kogin ya bi cikinta ne,


                   Ya ratsa k’asa ya zagaya.”

(Shehu Shagari: Wak’ar Nijeriya)

Anan idan mun fahimci Alhaji Shehu Shagari za mu ga cewa da kansa ya bayyana muna cewa, turawa ne suka rad’awa Najeriya suna, kuma turawannan su ne turawan mulkin mallaka wato Florer da mijinta Lord Lugard. Don haka shakka babu a nan aka samu wannan sunan na Nijeriya.

1.2  HARSUNA/K’ABILUN DA KE CIKIN K’ASAR NIJERIYA.


Masana da yawa sun gudanar da bincike dangane da sani shin ko harshe nawa ke akwai a cikin Nijeriya? Wasu masanan suna ganin cewa akwai ak’alla harshe d’ari biyu da hamsi (250), a Nijeriya. Wasu kuma suna ganin cewa ai harsunan da ake amfani da su a Nijeriya sun kai kimani d’ari uku da tisi’in da hud’u 394 (Ikara 1987:18). Ko ma ya abin yake Allah masani. Amma dukkansu sun yi amanna cewa, harsuna uku su ne suka fi yawa da fice a k’asar. Wad’annan harsunan su ne: Hausa, Yoruba,da Igbo/ Inyamurai.

1.3 RARRABUWAR KAN ‘YAN NIJERIYA.


Had’d’ad’iyar k’asa Najeriya wadda ta samu ‘yanci tun a shekarar (1960), kimani shekara hamsin da uku (53) kenan a yau. Ita dai Najeriya tana da yawan harsun kamar yadda muka fad’a a can baya. Dukkan wani d’an k’asar ya san cewa, k’asar tana da harsuna daban-daban, haka kuma ba lallai ba ne ya kasance ana zaman lafiya ba, kuma bai zama lallai a yi tashin hankali ba.

A zamanin da can an yi yak’in basasa, wanda su Yakubu Gawon suka yi. Wannan yak’in dai an fi sanin sa da suna yak’in Biyafara, (Biafara), a wannan yak’in dai an rasa rayuka da dukiya da dama, kuma wannan yak’in ya shafi wata k’abila da take a Kudu maso Gabascin k’asar. Ba wannan kad’ai ba akwai wasu dalilai da suka sa aka sumu rarrabuwar kai sun had’a da: addini da siyasa da k’abilanci da ‘bangaranci.

Idan muka dubi addini za mu ga cewa, tsarin addinan ba iri d’aya ba ne wanda kowa yake ganin kamar nasa ne kawai na k’warai. Kuma inda ya kamata a nuna addini ba a nan ake nuna shi ba sai dai a yi amfani da addinin a cuci al’umma da shi. Rashin sani yadda za a yi addinin shi ya hardasa rarrabuwar al’umma. Da kowa zai bi addininsa gwargwado bisa gaskiya to da an samu daidaici a kan matsalar addini.

K’abilanci, nuna k’abilanci ba abu ne mai kyau ba, amma ‘yan Najeriya sun dage kowa in ba d’an k’abilarsa ba, ba ya son wani sai dai wanda ya fito daga k’abilarsa wannan gaskiya ne mutum zai gane haka a lokacin da ya nemi wani abu ga wani wanda ba d’an k’abilarsa ba, ko ya nemi ya zauna a cikin wata k’abila da ba tashi ba.

Siyasa, siyasa ita ma ta taka rawar gani wajen rarrabuwar kan ‘yan Najeriya, kowa ya je kamfe sai ka ji yana cewa ‘yan k’abilarsa su za’be shi kuma su tabbata shi ya kai labari don su kare mutuncin harshensa da addininsa. Za ka ga an zuga jama’a a ce masu wane ba d’an k’abilarmu ne ba kuma ba addini d’aya muke ba, don haka kar wanda ya za’be shi.

‘Bangaranci kuwa ya k’unshi nuna inda mutun ya fito. Kamar dai yadda kowa ya sani cewa Najeriya tana da manyan yankuna guda shida (6), wato (Six Giopolitical Zone), Arewa maso gabas, Arewa maso yamma, da Arewa maso tsakiya. Kuma a Kudu akwai Kudu maso Gabas, kudu maso yamma da Kudu maso tsakiya. A tsarin mulkin k’asar nan ana ba da mulki ga duk ‘bangaren da ya cancanci a ba shi in har ya cika sharud’d’an da doka ta tanadar, amma za ka ga wasu ba su gamsu da wannan tsari ba, su dai a dole sai an ba d’an uwansu. Haka kuma za ka ga wasu ba ma ‘yan siyasa ba suna k’in juna saboda ba yankinsu d’aya ba.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

2.0 RAWAR DA WAK’A KE TAKAWA WAJEN HA’DA KAN ‘YANNIJERI YA.


Wak’a dai kamar yadda muka fad’a baya tana isar da sak’o ga al’umma, kuma hasali ma duk wanda ka ga ya yi wak’a to yana da wani sak’o da yake son ya isar. In kuma a’a to ya yi aikin banza kamar yadda marigayi Kaftin Suru Ummaru ‘Da (RTD), ya fad’a a wata wak’arsa. Ya ce:

Kway yi wak’a ba jigo,

                   Ya yi riga ba taggo,

                   Yai awaki ba Faggo,

                   Ga amarya ba ango,

                             Banga amfani nai ba.”

(U. D. Suru)

Wannan ko shakka babu duk wanda ya yi wak’a to akwai abin da yake son ya isar ga al’umma.

Kafin mu kai ga yin wannan aikin ya kamata mu san shin mene ne wak’a?

Masana da yawa sun ba da gudunmuwa wajen samar da ma’anar wak’a,. Ga wasu daga cikinsu:

Yahya ya ba da tasa ma’anar wak’a da cewa:

“Magana ce da ake shisshirya kalmominta cikin azanci, ta yadda wajen furta su ana iya amfani da kayan kid’a”. Yahya (1997).

Shi kuma ‘Dangambo (2007:) cewa ya yi:

“Muna iya cewa, wak’a wani sak’o ne da aka gina shi kan tsararriyar k’a’ida ta baiti, d’ango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (k’afiya), da sauran k’a’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, za’bensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”.

A wani aikin kuma Gusau cewa ya yi:

“Wak’ar baka fage ce wadda ake shirya maganganu na hikima, da ake aiwatarwa a rere cikin rauji tsararre, wad’anda za su zaburar da al’umma tare da kuma hankaltar da su dangane da dabarun tafiyar da rayuwa da za su ba da damar a cim ma ganga mai inganci. Wak’a bisa jimla, takan zama fitila wadda take haskaka rayuwar jama’a kuma take kare rayuwar al’umma daga sallacewa”  Gusau (2011).

 

Bungud’u kuma ya bayar da ma’anar wak’a kamar haka:

“Wak’a ta k’unshi wasu jerin hikimomi ne da a kan tsara domin su dad’ad’a zukatan masu saurare, inda a kan yi amfani da wata za’ba’b’biyar murya don rerawa, ana kuma yin amfani da za’ba’b’bun kalmomi domin fizgar hankalin jama’a ya dawo gare su da zimmar bin diddigin ma’anoni da manufofinsu.

 

Domin ganin yadda wak’a take taka rawa wajen samar da had’in kai za mu duba wata wak’a da Alhaji Musa ‘Dan Ba’u ya yi a lokaci bukin cikar shekara hamsin da Najeriya ta yi. Ga yadda abin yake.

Mawak’in ya bud’e wak’arsa da d’an wak’a kamar haka:

Jagora: “ ‘Yan Najeriya ‘yan uwa mu yi k’ok’ari,

                             Mu zan had’a kanmu mun kama hanyar gaskiya.”

          Y/Amshi: “ ‘Yan Najeruya ‘yan uwa mu yi k’ok’ari,

                             Mu zan had’a kanmu mun kama hanyar gaskiya.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

 

Wannan ko ba a fad’a ba ya fito da jigo wak’arsa a cikin wannan amshi na wak’ar. A gaba kuma yana cewa:

Jagora: “ Gyara man Mai sama Allah kai ke da mu,

Y/Amshi: “ Ka taimaki Najeriya kandami babbar k’asa,

          ‘yan Najeriya ‘yan uwa mu yi k’ok’ari,

          mu zan had’a kanmu mun kama hanyar gaskiya.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

 

Idan muka lura a nan mawak’in ya yi addu’a ya rok’i Allah da ya taimaki k’asar Najeriya. Wannan duk don dai a samu zaman lafiya.

A gaba yana cewa:

Jagora: “ Kifi da kada, tsari, kwad’o, dorina,

                   Halittarsu daban-daban amma in mun tuna.”

         Y/Amshi: “ Duk gidansu yana ruwa.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

 

Anan mawak’in yana nufin ai ko kifi da yake dabba ne ya zauna a cikin ruwa da shi da sauran halittu daban-daban kuma ba iri d’aya suke ba, amma ai duk Allah ne ya halicce su, kuma Ya saka su a ruwa gashi sun zauna tare. Na me, mu da ke mutane muke ta famar mu raba k’asarmu alhali tun a farko ba a rabe take ba.

Wani abin sha’awa anan shi ne da mawak’in ya ba da misali da dabbobin cikin ruwa, sai ya kuma yi kira ga wasu daga cikn k’abilun cewa su zauna lafiya. Ga abin da yake cewa:

Jagora:      “Ina Yarbawa,Nufawa, Jama’ar Igbo,

        had da ku Jama’ar Tivi.”

Y/Amshi: “ Duk mu taru mu je gaba d’aya

                                      Can ga hanyar gaskiya.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

 

Anan mawak’in ya kira wasu daga cikin k’abilun Najeriya, kuma ya nemi duk su zo a komawa gaskiya waton a aje duk wani k’abilanci, a yi tafiya d’aya babu cuta ko nuna k’abilanci.

Baya ga kira ya bayyana irin yadda jama’ar da ke cikin k’asar da cewa ai Allah shi ya k’addaro mun ka zauna a wuri d’aya do haka ai sai mu yi hank’uri mu yi zaman amina. Ga abin da ya ce.

Jagora: “ Kun gani Najeriya mai yawan fad’in k’asa,

                                Al’adunmu daban-daban addinanmu daban-

                             Daban, Allah mai k’addarawa a kowane al’amar.”

               Y/Amshi: “ Shi Ya k’addaro mun ka zaunu wuri d’aya,

                                Kuma k’asarmu tana d’aya.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

Alhaji Musa ‘Dan Ba’u ya bamu shawara cewa,  kada mu yadda wasu su zo su raba mu. Ga dai abin da ya ce a cikin wak’a.

Jagora: “ Kar mu yadda da ‘yan baranda da ‘yan zambar ciki,

                                Masu son su raba mu.”

                    Y/Amshi: “ ‘Yan Najeriya ‘yan uwa mu yi k’ok’ari,

                             Mu zan had’a kanmu mun kama hanyar gaskiya.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

 

Babu shakka wannan mawak’i ya san duk inda muka munana, don kuwa tambaya ya yi cewa duk wannan tashin hankali da k’one-k’one da kashe-kashe wai wa an ka yiwa? Mun gode wa Allah da yassa ‘Yan Amshinsa ‘yan Najeriya ne don kuwa sun amsa masa. Ga dai tambayar da amsar a cikin wak’ar kamar yadda ya yi ta:

Jagora: “k’one-k’one cikin k’asa, tada tarzomar k’asa,

                                 Duk wannan bai da kyau, an yi hasarar dukiya,

                                Wani gu har rayuwa. Jama’a na yi maku tambaya,

                               ‘Barnar nan da an ka yi du wa an ka yi wa ita.?”

                   Y/Amshi: “ Mu ‘yan Najeriyag ga mu an ka yiwa ita,

 wata k’asa ta yi dariya.”

                                                  (Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

Gashi ko ‘yan Najeriyar da suka san ciyo kansu sun amsa wannan tambaya da mawak’in ya yi ga ‘yan Najeriya, domin kuwa tuni sun fad’a cewa mu an ka yi wa wannan ‘barnar don da kud’inmu za a yi gyaran duk abin da muka ‘bata in kuma an salwantar da rayuwa ne to bayan had’uwar mu da Ubangiji Allah to kuma mu dai muka rage. Kuma wata kasa ta yi dariyarmu tunda mu muka yi wa kanmu hasara.

Alhaji Musa ya k’ara da cewa:

Jagora: “ Ni d’an Najeriya, kai d’an Najeriya, ita ‘yar Najeriya,

                                Ke ‘yar Najeriya, to mu zauna lafiya.

               Y/Amshi: “ Da juna mu yi hank’uri.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

 

Anan mawak’in ya yi kira ga shi kansa da saura ‘yan Najeriya cewa duk mu zauna lafiya da juna, kuma mu yi hank’uri. Bahaushe ko ya ce zaman lafiya ya fi zama d’an sarki. Kuma ya fad’a da kansa cewa, mai hank’uri yana dafa dutse har ya sha romonsa.

Daga k’arshe dai mawak’in ya rufe wak’arsa da bayyana muna ko shekara nawa Najeriya ta yi da samun ‘yanci. Ga dai abin da ya ke cewa.

Jagora: “ Yau Najeriya shekara hamsin ga rak,”

                 Y/Amshi: “ Da samun ‘yancinta mun gode Allah ‘yan uwa.”

(Alhaji Musa ‘Dan Ba’u)

 

Wato dai anan mawak’in ya bayyana lokacin da ya yi wak’ar, kuma ya rufe wak’ar da godiya ga Allah.

Anan muka kawo k’arshen wannan muk’alar kamar dai yadda suma masu wak’ar suka rufe da gode wa Allah mu ma dai sai mu go yi bayansu da wannan godiyar zuwa ga Allah mai garma da d’aukakan da ya kawo mu a nan inda muka kawo k’arshe wannan aikin.

KAMMALAWA.


Komai nisan dare gari zai waye, wannan karin magana na Hausawa ya yi daidai don kuwa gamu a ganga za mu taka tudu. Wannan muk’alar bayan Gabatarwa ta duba K’asar Najeriya da kuma Yare/K’abilun da ke cikin Najeriya da Rarrabuwar kanun ‘yan Najeriya, da Rawar da wak’a ke Takawa Wajen Had’a Kan ‘Yan Najeriya. Inda aka biyo da wasu baitoci domin kafa hujja. Wannan muk’ala na iya zama wata babbar hanya da za ta ja hankalin mai sauraren wak’a da mai nazarin duk da ya sadu da wannan muk’ala da ya aje duk wata husuma da yake tare da ita ya nemi zaman lafiya da had’in kai na k’asa. Akwai mawak’an Hausa da dama manya da k’anana wad’anda lokaci bai bar mu mu ambata ba irin su Alhaji Mamman Shata da Alhaji Musa ‘Dank’wairo da Alhaji Shehu Ajilo da sauransu wad’anda suka yi wak’ok’i don neman had’in kan ‘yan k’asar nan (Nijeriya) kuma kuma sun amfanar matuk’a muna k’ara gode masu da fatar Allah ya k’ara had’a kanmu amin.

  Manazarta 


 

https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments