NA
HAFSAT ABDULLAHI
SADIYA ABUBAKAR
SHAMSIYA SULAIMAN
SASHEN HAUSA TSANGAYAR HARSUNA, KWALEJIN ILIMI DA ƘERE-ƘERE TA GWAMNATIN TARAYYA DA KE GUSAU, JAHAR ZAMFARA.
SADAUKARWA
Mun sadaukar da wannan kundin bincike na samun takardar shaidar malanta ta ƙasa
(NCE) a Sashen Hausa na kwalejin Ilimi Da Ƙere-Ƙere da ke Gusau a jihar Zamfara
ga mahaimafanmu wato: Sulaiman Muhammad da marigayi Mal. Musa Kotarkoshi da
Abubakar G. Shu’aibu.
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai kowa mai komai da ya ba
mu rai da lafiya da ikon gudanar da wannan bincike.
Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Fiyayyen halitta wato Annabi
Muhammadu (SAW) tare da iyalan gidansa da Sahabbansa da duk magoya bayansa tun
farko har ya zuwa ranar ƙarshe.
Godiya ta musamman ga dukkan bayin Allah da suka taimaka muna domin ganin haƙarmu
ta cimma ruwa, musamman ga iyayenmu kamar: Sulaiman Muhammad da marigayi Mal.
Musa Kotarkoshi da Abubakar G. Shu’aibu sai godiya zuwa ga iyayenmu mata da
suka haɗa da: Malama A’isha Sulaiman da Malama Rabi’atu Ladan da Malama Zainab ɗanmalam.
Sai godiya zuwa ga mazajenmu wato; Mal. Sirajo Umar da Mal. Basiru Ibrahim da
Mal. Nasiru Ibrahim Mainasara. Haka kuma muna miƙa godiyarmu zuwa ga ‘yan’uwa
da abokan arziki daga ciki har da; Aminu Umar da amina Abdullahi da Nana
Firdausi Nasir da dukkan sauran waɗanda ba mu samu damar kawo sunayensu ba
Allah ya saka masu da mafificin alheri amin.
Haka kuma muna miƙa kyakyawar godiyarmu ta musamman ga malamanmu Na
wannan sashe kamarsu; Haruna Umar Maikwari wanda ya ɗauki tsawon lokacinsa yana
kula da aikinmu har Allah ya sa aka kawo ƙarshe. Allah ya saka masa da
mafificin alherinSa amin. sai Shugaban Sashen Hausa (H.O.D) Dr. Haruna Umar
Bunguɗu, Shugaban Tsangayar Harsuna (Dean) Malam Surajo Guluba, , Mal. Aminu
Saleh, Mal. ɗahiru Sankalawa da mal. Bashir Tsafe da Mal. Ibrahim ɗan’amarya da
Mal. Sani Soba da sauran su.
JINJINA
Hausawa kan ce, “yabon gwani ya zama dole” wannan haka ne, don haka dole mu
jinjina ma malaman mu musamman Mal. Haruna Maikwari da ma wasu daga cikin
mutanen da suka taimaka muna da wasu shawarwari da gudummuwa, da goyon baya da
suka bamu, wajen samun bayanai masu gamsarwa domin wayar da kan ɗalibai da ma
duk masu neman ƙarin haske dangane da aikinmu. Muna masu roƙon Allah ya saka
masu da maifificin alheri. Amin.
ƘUNSHIYA
Shaidantarwa -
-
-
-
- -
-
- ii
Sadaukarwa -
-
-
-
- -
-
- iii
Godiya
-
-
-
- -
-
-
- iv
Jinjina
-
-
-
- -
-
- -
vi
Ƙunshiya -
-
-
-
- -
-
- vii
BABI NA ɗAYA
1.0 Gabatarwa
-
-
-
- -
-
- 1
1.0.1 Yanayin Bincike
-
-
- -
-
- 3
1.0.2 Muhallin Bincike -
-
-
-
-
- 3
1.0.3 Hanyoyin Gudanar da Bincike
-
-
-
- 4
1.0.4 Manufar Bincike
-
-
-
-
- -
5
1.0.5 Matsalolin Da Suka Taso -
-
-
-
- 6
1.0.6 Matsalolin Da Aka Fuskanta
-
-
-
- 8
BABI NA
BIYU
2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata
-
- 9
2.0.2 Salon Nazari Da Tsarinsa -
-
-
-
- 14
Babi Na Uku
3.0.1 Ƙagaggun Labarai -
-
-
-
- -
16
3.0.2 Tarihin Ƙagaggun Labarai na (1933)
-
-
- 18
3.0.3 Jigo -
-
-
-
- -
-
- 21
3.0.4 Kashe-Kashen Jigo -
-
-
-
- -
22
3.0.4.1 Babban Jigo
-
-
-
- -
- 23
3.0.4.2 Ƙaramin Jigo
-
-
-
-
-
- 23
3.0.5 Ma’anar Salo -
-
-
-
- -
- 24
3.0.6 Ma’anar Wayo
-
-
-
- -
- 28
Babi Na
Huɗu
4.0.1 Tsokaci A Kan Littafin Ruwan Bagaja
-
-
- 30
4.0.2 Ma’anar Taurari/Tauraro -
-
-
-
- 32
4.0.2.1 Babban Tauraro -
-
-
-
-
- 32
4.0.2.2 Ƙananan Taurari/ Ƙaramin Tauraro
-
-
- 32
4.0.3 Tsohon Salo A Cikin Ƙagaggun Labarai
-
- 33
4.0.4 Haɗuwar Imam Da Zurƙe
-
-
-
- -
36
4.0.5 Neman Ruwan Bagaja
- -
-
-
- 37
4.0.6 Muhimmancin Rayuwa Littafin Ruwan
Bagaja
- 38
4.0.7 Nazarin wayo A Littafin Ruwan
Bagaja
-
- 39
4.0.7.1 Wayo Don Samun Abin Duniya
-
-
- 39
4.0.7.2 Wayo Don Samun Karɓuwa ga
Wasu
-
- 41
4.0.7.3 Wayo Don Samun Aron Kuɗi -
-
-
- 41
4.0.7.4 Wayo Don Tsira Da Mutunci
-
-
-
- 42
Babi Na
Biyar
5.0 Jawabin Kammalawa - -
-
-
-
- 45
5.0.1 Shawarwari -
-
-
-
- -
-
47 Manazarta
-
-
-
- -
-
-
- 48
Babi Na ɗaya
Gabatarwa
Wannan bincike mun yi shi ne domin mu bayar da tamu gudunmuwa wajen bunƙasa
sashen Hausa, don haka mun rututa wannan bincike ne mai taken “Nazarin Jigon
Wayo A Cikin A Cikin Littafin Ruwan Bagaja” don amfani ga masu nazarin harshen
Hausa.
Maƙasudin yin wannan binciken shi ne, saboda kwaɗaitar da masu sha’awar harshen
Hausa, musamman saboda masu sha’awar gudanar da bincike a irin wannan fage na
nazarin Adabi wanda ya danganci zube.
Domin samu sauƙin gudanarwa mun kasa wannan aikin namu a kan tsarin babi-babi
har babi biyar.
Babi na farko za mu kawo bayani ne a kan Gabatarwa, Yanayin Bincike da Manufar
Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin Da
Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta.
A babi na biyu kuwa nan ne za mu yi tsokaci dangane da Waiwaye A Kan Ayyukan Da
Suka Gabata da kuma Salon Nazari Da Tsarinsa.
A babi na uku za mu yi bayani a kan Tarihin Ƙagaggun labarai ta Tsokaci a Kan
kagaggun Labarai da Ma’anar Jigo da Kashe-Kashensa da Ma’anar Salo da Ma’anar
Wayo duk a wannan babin.
A babi na huɗu kuwa nan ne muka yi tsokaci a kan littafin Ruwan Bagaja da
Ma’anar Tauraro da kashe-kashensa da ma’anar Salo da Tsohon Salo da ke cikin
littafin da Haɗuwar Imam Da Zurƙe a littafin da Neman Ruwan Bagaja da
Muhimmancin Rayuwar Mutum a littafin Ruwan Bagaja da Nazarin Wayo
littafin Ruwan Bagaja inda muka fito da Wayo Domin Samun Karɓuwa ga jama’a da
Wayo domin Tsira da Mutunci da Wayo Don Samun Aro da Wayo Don Samun Muhalli duk
a wannan babi.
A babi na biyar kuwa nan ne za mu yi bayani a kan Jawabin Kammalawa da
Shawarwari sai Ta’arifin Wasu Kalmomi.
Yanayin Bincike
Kamar yadda aka sani mun gano cewar akwai buƙatar mu yi nazari a kan wasu
bayyanai da marubuta suka yi a kan wannan binciken kuma mun gano cewa, mu
yi Nazarin wannan Littafi na “Ruwan Bagaja” , don haka muka ga ya kamata mu
gudanar da wannan binciken domin zuwa gaba ko kuma mu ce domin masu
tasowa yanzu da su san cewa wannan littafi yana rawar da yake takawa a cikin
adabin Hausa.
Haka kuma a yunƙurinmu na gudanar da wannan aikin Binciken mun sha wahala sosai
saboda rashin samun wasu litattafai da suka yi Magana a kan wannan aiki namu.
Haka kuma yawace-yawacen da muka yi wajen samun wasu bayanai ya sa mun wahala
matuƙa.
Muhallin
Bincike
Wannan bincike mun gudanar da shi ne a ɓangaren adabin Hausawa, sai dai domin
samun sauƙin gudannarwa mun keɓance aikin namu a kan littafin “Turmin Danya”
wanda Sulaiman Ibrahim Katsina ya rubuta, kuma Jigon wayo ne kawai za mu mayar
da hankali a kai.
Hanyoyin
Gudanar da Bincike
Wannan ya rataya ne a kan wasu hanyoyin tattara bayanai daban –daban na
marubucin littafin ko mai aikin bincike na wasu ayyuka waɗanda suka gabata
domin yin nazari a kan binciken da ake gudanarwa domin samun ra’ayoyi daban-daban.
Bayan wannan akwai wata hanya wadda mai bincike ke bi domin samun ra’ayoyi
daban-daban don ƙarin haske ga aikinsa na bincike da yake gudanarwa, wato ta
hanyar tambayoyi ga ma’abuta wannan ilimi.
Kamar yadda bayani ya gabata mun lura da cewa, dukkan mai aikin bincike
dole ne ya yi amfani da littafai daban-daban domin samun ingantu da kuma
cikakkun bayanai masu gamsarwa. Haka kuma mun mayar da hankali a wurin gudanar
da wannan bincike namu domin kuwa har ɗakunan karatun wasu manyan
makarantu mun leƙa. Mun kuma ziyarci ɗukunan karatu, don yin bincike ga kaɗan
daga cikinsu: Jami’ar Usman Danfodio inda muka shiga ɗakunan karatunsu wato
(library).
Haka ma binciken namu bai tsaya a Jami’ar Usman Danfodio kawai ba a’a har
Jami’ar Bayero da ke Kano mun leƙa a ɗakin karatun ɗalibai duk a wannan
Jami’ar.
Binciken namu bai tsaya a waɗannan Jami’o’in ba kurum. Domin kuwa ziyarar
binciken ta kai mu ga daɗadɗ’iyar Jami’ar Ahmadu Bello mai tarihi ita ma mun
shiga lunguna- lunguna domin gudanar da wannan bincike namu. Daga nan sai muka
cirata zuwa Jami’ar Katsina, inda a can muka samu ziyarar sauran makarantu kuma
yanayin binciken ɗaya ne.
Manufar
Bincike
Binciken yana da muhimmamcin gaske domin ta fuskar bincike ne a kan gano
cikakkiyar ƙwarewar ɗalibai da fahimtarsu da hazaƙarsu. Ta wannan hanyar
karance-karace za a ci karo da wani sabon al’amari domin ya ƙara tabbatar da
abin da aka riga aka sani a fagen ilimi.
Binciken yana fitar da bayanai domin amfani al’umma, wani babban muhimancin
bincike shi ne a duk lokacin da mai bincike ya tsunduma a fagen aikinsa yakan
yi karo da wasu ra’ayoyi daban-daban wanda yana iya zama sabon darasi gareshi.
Manufar wannan binciken shi ne mu fito da wasu abubuwa da wannan littafi na
Turmin Danya ya ƙunsa musamman Jogonsa da Salon da aka yi amfani da shi. Muna
kuma fatar wannan nazari namu ya zama abin dogaro ga masu nazarin harshen
Hausa.
Matsalolin
Da Suka Taso
Wannan bincike namu mun gudanar da shi ne a kan hanyoyin da suka dace, na irin
hanyoyin da ake bi wajen samun bayanan da suka dace ta hanyoyi da dama. Mun ci
karo da matsaloli da dama wajen binciken mu kamar haka.
Rashin isassun kuɗin mota, da matsalar iska waɗansu masana da muke tuntuɓa
wajen gudanar da wannan bincike namu, haka ma wani lokaci za mu kashe kuɗin
mota domin zuwa wajen waɗansu mutane da abin ya shafa, sai mu iske ba su
nan. Haka ma kowa ya san irin halin da ake ciki a ƙasar nan na rashin tsaro, a
inda ba ko ina za mu iya shiga ba dole sai da taka tsantsan.
Aikin bincike aiki ne mai wahalar gaske, musamman ma ga irin mu ɗalibai mata
masu rauni da kuma karancin ilimi. Saboda haka lokacin da muke gudanar da
wannan aiki na bincike wasu matsaloli da dama sun sha kanmu. Daga cikinsu
akwai
Matsalar karɓar lacca da aikin aji da na jinga da kuma karatun jarabawar gwaji
da ta ƙarshen zangon karatu.
Akwai kuma matsalolin gida kasancewar mu mata da suka haɗa da girke-girken
abinci kula da tarbiyar yara, akwai rashin lafiyarmu da ta ‘ya’yanmu. Duk waɗannan
matsaloli ne da mu ka yi ta cin karo da su .
Akwai matsalar tuntuɓar magabata da masana, saboda wasu daga cikinsu suna ganin
kamar za mu ɗauki sirrinsu ne mu watsa wa duniya.
Haka ma akwai matsalar yawan ɗaukewar wutar lantarki, domin sai mun tattaro
bayanan mu na cikin aikin kwatsam sai wuta ta ɗauke. Kaɗan kenan daga
irin matsalolin da muka ci karo da su.
Matsalolin
da aka Fuskanta
Kamar yadda aka sani a dukkan bincike za a iya samun nasarori da akasin haka,
wato matsaloli a wajen gabatar da aikin. To don haka wajen bincike nan mun
fuskanci matsaloli da dama kamar rashin kuɗi da za mu buga wannan aiki namu.
Haka kuma akwai matsalar haɗuwarmu idan mun yi alƙawali, kuma idan za mu tafi
wajen ganawa da waɗanda za mu yi hira da su, saboda lokacin ba lallai ne
a same su ba.
Haka akwai sha’anin rashin lafiya yakan kama magidanci , ko kuma halin tafiya
wajen ƙaro ilimi wato a bangaren su masana.
Ba nan kaɗai muka samu matsala ba kuma mun fuskanci matsalar karamcin lokaci.
Domin wannan aiki na bincike aiki ne da ya kamata a ce an gudanar da shi a
cikin shekara ɗaya.
Babi Na Biyu
2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata.
Ayyuka da suka gabata fage na adabin Hausawa suna da yawa, saboda haka wannan
aiki namu ba shi ne na farko ba a wannan fage. Don haka ya zama wajibi a garemu
da mu waiwayi wasu ayyuka da suka gabata masu alaƙa da wannan aiki domin mu ga
inda suka zo daidai da kuma inda suka sha bambam, ko kuma suke da dangantaka da
namu.
Daga cikin ayyukan da suka gabata a wannan fage akwai; bugaggun littafai
daban-daban, da suka gabata a kan fannoni daban-daban na adabin Hausawa ga wasu
daga cikinsu;
ɗangambo A (1984) a cikin littafinsa mai suna “Rabe-Raben Adabin Hausa Da
Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa” marubucin ya bayyana ma’anar adabi ya kuma
karkasa adabin Hausa, inda ya kawo zube da waƙa da wasan kwaikwayo. A ƙarƙashin
zube nan ne ya bayyana cewa akwai littafai waɗanda aka yi rubutun zube a
cikinsu.
Wannan aikin na shaihin Malami ɗanganbo yana da alaƙa da namu aikin, saboda ya
taɓo zube, yayin da mu ma a namu aikin zube ne wanda ya danganci nazarin
littafi. Inda muka samu bambanci da shi kuwa shi ne, shi marubucin littafin
yana magana ne a a kan zube gaba ɗayansa mu kuma mun taƙaice aikinmu ga littafi
ɗaya mai suna “Turmin Danya.”
Yahaya I.Y. (1988), ya rubuta littafi mai suna “Hausa A Rubuce” a cikin wannan
littafi masanin ya yi bayanin rubutu, tarihin samuwar rubutu yadda aka samu
rubutun zube, wasu daga cikin littafan da aka samu na zube, gasar da aka shirya
don samun littattafan zube tarihin wasu hukumomi na gudanar da ayyukan rubutu
musamman na boko da na Arabiyya.
Wannan aikin na shaihin malami Yahaya I. Y. Yana da alaƙa da aikinmu saboda ya
yi tsokaci a kan zube da littattafan zube da tarihin Rubutu da dai sauransu.
Aikin yana kuma da bambanci da namu saboda shi yana magana ne a kan adabi
dukkansa, mu kuma muna magana ne a kan wani sashe daga cikin adabi ko shi kuma
mun taƙaita akin manu a kan littafin “Turmin Danya”.
Sagiru A.G (1991) a nasa kundin bincike mai taken “Nazari Da Sharhi A Kan
Littafin Uwar Gulma” wannan manazarci ya gudanar da aikinsa ne a kan tsari na
babi- babi har zuwa babi baiyar. Bayan ya yi gbatarwa a babi na ɗaya ya kuma yi
waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, sai a babi na uku da na huɗu inda ya taɓo,
jigo, warwararsa, taurari, manya da ƙanana da kuma salo duk a cikin littafin
“Uwar Gulma”.
Wannan aiki na wannan manazarci yana da alaƙa da namu aikin, musamman da ya yi
bayani a kan jigo da warwararsa, haka namu aikin zai yi tsokaci a kan
jigo da warwararsa da salo da taurari. Amma duk da haka mun sha bamban da shi
saboda shi ya gudanar da aikinsa ne a kan littafin “Uwar Gulma” mu kuma namu
aikin muna yin sa ne a kan littafin “Turmin Danya”.
Gobir, (1993), ya rubuta wani kundi mai suna “Malam Muhammadu Umar Kwaren Gamba
Da Waƙoƙinsa” manazarcin ya taɓo jigo da salo da tarihin Mawaƙin. Mun bi sahun
wannan manazarci wajen nemo salo da jigo da tarihin marubuci, wannan ya sa
aikinmu yake da alaƙa da nasa. Inda kuma suka bambanta shi ne, shi Gobir yana
nazarinsa ne a kan waƙa mu kuma muna namu a kan zube.
Hadiza A. Da Wasu (1999), a kundin Bincikensu da suka gudanar mai taken “Nazari
A Kan Littafin Jatau Na Ƙyallu”. Marubutan sun fara ne da mayar da taƙaitaccen
tarihin marubucin wannan littafi, sun kuma yi tsokaci a kan ma’anar jigo,
babban jigo da ƙaramin jigo. Sun ci gaba da yin sharhi a kan littafi tare da
bayani a kan salo da zubi da tsarin wannan littafi tare da tsokaci a kan
taurari.
Wannan aiki na su Hadiza yana da alaƙa da namu aikin saboda dukan mu muna
nazarin Littafi ne, sai dai inda muka sha bamban shi ne su suna nazarin
Littafin “Jatau Na Ƙyallu” ne mu kuma muna nazarin jigon wayo a littafin
“Turmin Danya”.
Shafa’atu A. I. (2005), sun rubuta kundi mai taken “Nazari A Kan Littafin Iliya
ɗan MaiƘarfi” a wannan kundin sun yi bayanin jigo, warwararsa da salo da
tarihin marubuci da sharhin littafin.
Wannan kundin nasu yana da alaƙa da namu saboda dukanmu muna nazari ne a kan
littattafan zube, sai da inda muka bambanta shi ne su suna nazarin littafin
“Jatau Na Ƙyallu” ne yayin da mu kuma muna nazarin jigon wayo a littafin
“Turmin Danya”
Hannatu A da Wasu (2008), a nasu kundi mai taken “Nazari A Kan Littafin Ai Ga
Irinta Nan” a wannan kundin sun yi bayanin jigo, salo tarihin marubuci da
sharhin littafin.
Wannan kundi nasu yana da alaƙa da namu kundin saboda dukkanmu muna nazarin
littattafan zube ne. Amma fa mun samu bambanci a yayin da su suke nazarin
littafin “Ai Ga Irinta Nan” mu kuma muna nazarin littafin “Turmin Danya”
Firdausi A. Da wasu (2010), sun rubuta wani kundi mai taken “Nazari Da Sharhi A
Kan Littafin Jiki Magayi” manazartan sun karkasa kundinsu a kan babi-babi
sannan suka gudanar da aikinsu a cikin babi na uku da na huɗu. Sun kuma yi
bayani a kan salo, jigo, da sharhin littafin, sun kuma yi bayanin taƙaitaccen
tarihin marubucin wannan littafin.
Wannan kundin yana da alaƙa da namu aikin saboda su sun gudanar da aikinsu a
kan littafin zube haka mu ma mun gudanar da namu aikin a kan zube. Amma inda
muka samu bambanci shi ne, su sun yi nazarin littafin Jiki Magayi ne mu kuma
muna nazarin littafin Turmin Danya.
2.0.2
Salon Nazari Da Tsarinsa
Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin
mutum.
Salon nazari wata hanya ce ta isar da saƙo da bayyana tunanin mutum. Haka kuma
salo ya na nufin hanyoyin da marubuci ko mawallafi kan bi domin yi wa harshe
kwalliya ko kuma yi wa rubutun sa ado, haka kuma wata dabara ce da marubuci kan
yi amfani da ita domin samun sauƙin isar da saƙonsa a cikin rubutunsa. A
dalilin haka ne mu ka yi amfani da hanyoyin guda uku na nazarin salo.
Na farko dai irin kalmomin da muka yi amfani da su, kalmomi masu sauƙi ne. Sai
kuma muka saka su a inda ya dace.
To anan za mu yi amfani da salo mai jan hankali, domin mu ja hankalin mai
karatu ya karanci wannan kundi, ba tare da wata wahala ba ko ya ƙagara da
karatun wannan bincike ba.
Idan mai karatun wannan aiki ya kwantar da hankalinsa ya biyo mu cikin natsuwa
to zai ga irin matakan salon da muka yi amfani da shi wajen rubata wannan kundi
saboda mun yi amfani da littatafai masu saukin fahimta.
An kuma yi amfani da nuna ƙwarewar harshe sosai a cikin wannan kundi saboda
anyi amfani da kalmomi masu burgewa da kuma armashi waɗanda ke sa mai karatu ya
ji daɗi a zuciyarsa, wannan shi zai sa binciken namu ya yi kwarjini da farin
jinni ga makaranta.
Babi Na Uku
3.0.1 Ƙagaggun Labarai
Sanin jama’a ne cewa wasu masana sun yi tsokaci a kan ƙagaggun labarai na zube
daga cikinsu akwai:
Ahmada Magaji (1982) cewa, ya yi “Zube labari ne da mutum ya shirya da ka,
sannan ya rattaba a zube”
Shi kuma Isah Mukhtar (2002), yana cewa, “Zube wani irin zance ne wanda aka faɗarsa
da baka ko kuma a rubuce, wanda yake bayyana yiwuwar wani al’amari, wanda zai
iya yiwuwa a zahiri, amma bai faru ba ko kuma ba zai taɓa faruwa ba.
Irin waɗannan abubuwa ba dole ne a ce sun faru ba, amma duk da haka sukan sa ɗan
Adam ya yi tunanin ya ƙirƙiro waɗansu halaye masu kyau ko akasin haka.
Wani dalili da ke sa ɗan Adam ya ƙirƙiro wa kansa labarai su ne, ƙoƙarin fitar
da wasu abubuwa musamman waɗanda suka shige masa duhu. Misali makeken ruwa
kamar kogi, ko rana da wata da taurari, ko waɗansu bishiyoyi masu ban al’ajabi
da ban mamaki. Akwai waɗannan abubuwan daban-daban da suke fitowa a cikin
labarai wani lokaci su ne ke zama tuballan gina labarin.
Ire-iren rubutattun labarai na Hausa kan ginu ne ta hanyoyi daban-daban misali.
- Ana iya samun labaran baka a tattara su a rubuta su.
- Ana kuma samun wasu labarai na wata ƙabila a fassara su a rubuta su.
- Ana iya yin tsokaci dangane da halin da wata al’umma ta shiga na
rayuwa ta zahiri sai a rubuta shi a matsayin labari.
A ɓangaren jigoginsu kuwa ya ce, ƙagaggun rubutattun labaran Hausa, yawanci
adabin Larabci da na Turanci ya yi tasiri ƙwarai gare su.
Hausawa musamman marubuta na farko sun kwaikwayi rubuce-rubucen adabin Larabawa
da na Turawa suka haɗa su da nasu. Don haka jigon ƙagaggun rubutattun labaran
Hausa, bisa jimla za mu iya cewa sun ƙunshi muhimman abubuwa guda uku.
- Adabin gargajiya na Hausa
- Adabin Larabawa da tasirin addinin musulunci
- Adabin Turawa
Bisa ga waɗannan bayanai za mu iya cewa, lallai ne waɗannan littattafan cike
suke da tasirin maƙwabtan Hausawa a cikinsu kuma waɗancan dalilai su ne suke ba
ɗan Adam damar ya fito da dabarar ƙirƙirar labari, kuma ko ya saka wani abu na
nuna wayo da Bahaushe yake da shi ko da tsakaninsa da baƙo ko ma ɗan gida,
wannan daidai ne.
3.0.2
Tarihin Ƙagaggun Labaran Hausa Na (1933)
Tarihi ya nuna cewa, ƙagaggun labaran Hausa ba su daɗe da samuwa ba, musamman
idan aka kwatanta shi da rubutacciyar waƙa wadda ta soma wanzuwa tun farkon
shigowar addinin musulunci a cikin ƙasar Hausa, duk da ire-iren rubuce-rubucen
da Turawa ‘yan mishan da na mulkin mallaka suka yi a cikin harshen Hausa, kuma
babu wanda aka kira ƙagaggen labari saboda babu wanda ya ƙunshi ƙaguwa kai
tsaye. Dukkan rubuce-rubuce nasu (Turawa) a cikin Hausa sun tsara su ne don
koyarwa a can ƙasashensu.
An fara tunanin samar da litattafai a cikin Hausa ne kuma waɗanda za a yi
amfani da su domin koyar da Hausa, bayan da aka kafa makarantun ilimin zamani a
garuruwa daban- daban na Arewacin Nijeriya.
Makaranta ta farko da aka fara buɗewa ta gwamnati ita ce, makarantar Hans
Vischer (ɗan Hausa) a Shekarar (1909) a garin Kano. Tun daga lokacin da aka
kafa wannan makarata sai aka lura akwai ƙaranci litattafan koyarwa, wannan
matsala ta ƙarancin litattafan koyarwa a makaranta ita ta jawo aka kafa hukumar
fasara wato (Translation Bureau) a ƙarƙashin shugabancin Mr. C.E.J Withing a
cikin shekar 1929.
An fara zaunar da hukumar ne a garin Kano a unguwar Nasarawa gidan ɗan Hausa
(Hans Vischer) a cikin shekarar 1931 aka mayar da ita a mazauninta na dindindin
a Birnin Zariya. Kuma a shekarar 1932 aka mayar da shugabancin ta ga hannun
wani Bature mai sauna R.M East.
Kamar yadda suna hukumar ya nuna, aikin da ya rataya a wuyan hukumar shi ne,
fassara labarai daga wasu harsuna zuwa harshen Hausa, haka kuma ita ke da
alhaki wallafa litattafai a cikin harshen Hausa da kuma shirya litattafai manya
da ƙanana don karantarwa a makarantu da kuma taimakawa ‘yan ƙasa su riƙa
wallafa litattafai da kansu. Hukumar ta fassara littattafai da yawa kamar:
- Dare Dubu Da ɗaya
- Labarun Hausawa Da MaƘwabtansu
- Labaru Na Da Da Na Yanzu
- Saiful Muluki
- AbdulƘadir Tanimud Dari
- Al’amurran Duniya Da na Mutane da sauransu
Wani yunƙuri wanda kuma shi ne ya haifar da samuwar tsintsar ƙagaggun labaran
Hausa shi ne, na canza sunan hukumar fassara zuwa hukumar Talifi da aka yi a
shekarar 1932. saboda haka sai nauyin da ke kan hukumar bai tsaya a kan fassara
kawai ba, har ma da wallafe-wallafen litattafai na fannoni daban-daban a cikin
harshen Hausa.
A daidai wannan shekara ne ta 1933 Daraktan ilimi na Arewacin Nijeriya Hans
Vicher ya ƙaddamar da shirin gasar rubuta ƙagaggun labarai, don samar da ƙarin
litattafan karatu a cikin rubutun zube. Saboda haka aka miƙa ragamar gudanar da
gasar ga wannan hukuma ta talifi kai tsaye, sai shugabanta Dr. R. M East ya
zagaya manyan garuruwan Arewacin Nijeriya ya sanar da malamai masu ilimin
zamani da na arbiyya bayani gasar da kuma irin labarin da ake so ga duk mai
sha’awa. Malamai da yawa sun rubuta labarai sun aika sai dai guda biyar ne
kawai suka yi nasarar cin gasar. Waɗannan su ne:
LITTAFAI
MAWALLAFI
Ruwan Bagaja
Mal. Abubakar Imam
Ganɗoki
Mal. Bello Kagara
Shehu
Umar
Alhaji Abubakar Tafawa ɓalewa
Jiki
Gagayi
John Tafida Umar da Dr. R.M East
Idon
Matambayi
Mal. Muhammadu Gwarzo
Waɗannan littattafan su ne littattafan ƙagaggun Labaran Hausa da aka fara
samarwa bisa shawarar Turawan mulkin mallaka.
3.0.3
Jigo.
ɗangambo (2007:12) Abin da ake nufi da jigo shi ne saƙo, manufa ko abinda waƙa
ta ƙunsa, wato abinda take magana a kai.
Jigo a fagen adabi yana nufin manufar marubuci, wadda dukkan bayanai suka
dogara da ita. Saboda haka ana iya cewa Jigo shi ne irin saƙon da marubuci ke
son sadarwa ga jama’a kuma duk wani salo da tsari ko wata dabara da marubuci zai
yi amfani da su, zai yi hakan ne da nufin isar da saƙonsa ga jama’a. Sarɓi,
(2007:71).
Dangane da abin da muka gani game da jigo za mu iya cewa, jigo shi ne dukkan
wani saƙo da ko manufa ko ginshiƙin abin da ya sa aka rubuta labari, ko dalilan
da suka sa marubuci ya rubuta littafinsa. Don haka duk wani abu da za a faɗa a
cikin labari, ya kan danganci jigo wannan labari.
Da wannan muke gani Jigo a matsayin igiya maɗaura kayan kowane rubutu da aka yi
a fagen adabi ta kowane ɓangare wato Zube da Waƙa da Wasan Kwaikwayo in ba da
shi ba to kayan za su kwance. A nan jigo na nufin burin zuciyar mawaƙi ko
marubuci wanda yake son jama’a su fahimta.
3.0.4
Kashe-Kashen Jigo
Kamar yadda aka riga aka sani cewa, da yawan masana da manazarta sun tofa albarkacin
bakinsu a fannin adabi kuma sun yi aiki da ya danganci wannan fage da muke
bayani a kai. Wato jigo. Mafi yawansu duk sun tafi a kan cewa, Jigo ya kasu
kashi biyu. Wato, Babban Jigo da Ƙaramin Jigo.
Masana sun bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, kamar dai yadda Bunza (2009)
da sarɓi (2007) suka bayyana cewa jigo ya kasu kashi biyu, wato ɓabban jigo’ da
‘ƙaramin jigo’. Yanzu bari mu zo da su ɗaya bayan ɗaya don ganin yadda abin
yake.
3.0.4.1
Babban Jigo
Babban jigo shi ne abin da mawaƙi ko marubuci ya sa gaba gadan- gadan domin ya
feɗe shi a gane shi sosai. Bunza (2009: 63).
Galibi shi babban jigo mawaƙi ko marubuci ya kan faɗa a cikin waƙarsa ko kuma
tun a sunan waƙar ya zan yana tafiya da saƙon wannan waƙar, idan kuma mawaƙi ko
marubuci bai faɗa a waƙarsa ba kuma ba a gane a sunan waƙar ba, to sai mai
nazari ya yi ƙoƙarin yin anfani da kalmomin fannu da aka gina waƙar da su waɗanda
za ka samu ƙananan jigogin.
3.0.4.2 Ƙaramin
Jigo.
Ƙaramin jigo ya saɓa wa babban jigo ta kowace fuska. Na farko dai abin da ya
kyautu a kula shi ne, ƙarmin jigo ɗa ne ga babban jigo, domin babban jigo ke
haifar da shi. Haka kuma ba don ƙananan jigogi ba da babban jigo bai fito fili
sosai aka ganshi ba. Duk wata waƙa da aka gina wani babban jigo ɗaya, za a samu
wasu ƙananan da yawa da za su mara wa babban jigon baya, domin Ƙawata shi da ƙara
fayyace shi sosai. Bunza (2009:64)
Idan aka ce ƙananan jigogi dai, to ana nufin tuballan da suka gina babban jigo,
su waɗannan tuballan sun danganta daga waƙa zuwa waƙa, ma’ana dai kowace waƙa
da irin nata tuballai da suka samar da jigonta. Haka abin yake ga rubutun zube.
3.0.5 Ma’anar
Salo.
Malamai da masana sun bayar da ma’anar salo ta hanyoyi daban – daban duk da
yake abu ɗaya suka fuskanta.
Sa’idu Muhɗ Gusau a tashi fahimtar ya ce:
“Salo shi ne hanyar da aka bi aka nuna gwaninta da dabaru a cikin furuci ko
rubutu. Kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa
da zaɓar abubuwa da suka dace game da abin da yake son bayyanawa. Daga nan ne
za a fahimci salon mai sauƙi ne ko tsauri, mai tsauri ko mai daɗi ne da armashi
ko mai kashe jiki maras karsashi da sauransu” Gusau (1993).
Yahya kuwa ya ce:
“Salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya
bayyana” Yahya (1999)
Shi kuma ɗangambo cewa ya yi:
“Masana da manazarta suna ganin cewa Salo yana da wuyar a gane shi a bisa kansa
sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa” dangane da ma’anarsa.To amma muna iya
cewa salo shi ne hanyoyin isar da saƙo, ɗangambo, (2007).
A bisa ra’ayin Abdulƙadir ɗangambo yana cewa za a iya karkasa salo kamar
haka;
1.
Salo wani ƙari ne da ya ƙunshi zaɓi cikin rubutu ko furuci.
2.
Salo wani ƙari ne na daraja a cikin karatu ko furuci wanda
ba lalle ne a same shi cikin kowane rubutu ba.
3.
Salo ya shafi kauce wa wata daidaitacciyar ƙa’ida
4.
Salo harshen wani mutum ne, wato yadda salon wane ya
bambanta da na wane.
Haka kuma ya ci gaba da bayyana mana cewa salo yana da nau’oi har guda biyar,
1.
Miƙaƙƙen salo: Wato salo na kai tsaye mai sauƙin ganewa,
wannan salo yana iya zama kamili mai iya isar da saƙo ba tare da “ado” ko ƙaƙale
ba .
2.
Salo mai armashi ko mai karsashi: Shi ne salon da ya gamsar
ta hanyar karsashi ƙaƙale da burgewa
3.
Raggon salo: Shi ne salo mai kashe jiki kuma marar
gamsarwa.
4.
Tsohon salo/Sabon salo: Salon da ke yin amfani da tsofaffin
hanyoyi ko sababbi don isar da saƙo, yana iya zama mai gamsarwa ko akasin haka.
5.
Salo mai sarƙaƙiya ko mai tsauri. Shi ne salo mai wahalar
ganewa saboda tsaurin saƙar manufofi ko tsauraran kalmomi.
Wani manazarcin na ganin cewa: .
“Salo shi ne yadda mawaƙi ya zana tunaninsa a takarada, za a dube shi a gani
shin yana da manufa, kuma bayaninsa yana da ƙarfi ko raunanna ne ana fahimtarsa
cikin sauƙi ko kuma sai an yi lalabe kafin a gane manufarsa. (Bashir 2007).
Shi kuma Sarɓi cewa ya yi:
“Salo na nufin zaɓi cikin gudanar da wani abu/aiki. Amma fagen nazarin waƙa
salo hanya ce da marubuta waƙoƙi ke bi wajen isar da saƙonsu ga jama’a” (Sarɓi,
2007).
A tamu fahimtar, mun lura da dukan bayanan da waɗannan masana da manazarta suka
kawo suna nufin salo ya ƙunshi hanya ko hanyoyin da mawaƙi ko ke bi domin isar
da saƙonsa ga jama’a.
3.0.6
Ma’anar Wayo
Wayo dai yana nufin dubara ko tsara wani abu da zai taimaka wa mutum. Wayo na
nufin wata hanya da mutum ya bi ya kare mutumcinsa, tare da tsara wasu bayanai
ko halaye ko ayyuka da za su zame wa mutum garkuwa ga zubewar mutuncinsa.
Mutane sukan yi amfani da dabarar da Allah ya ba su su shirya wani abu da zai
sa su cimma nasara a kan wani abu da suka saka a gabansu. Wannan ko shakka babu
haka abin yake saboda idan aka ce mutum yana da wayo to galibi ana nufin yana
iya tsara wani abu da zai kare masa mutuncinsa kuma ko da aikinsa za a yi ko sa
shi gaba za a yi ga wata haraka ko wani abu ake buƙata ya aikata to kowa zai ji
natsuwa cewa ba za a ji kunya ba. Idan kuma shi ne za a tunkara da wata lalura
ko wata matsala don a ribace shi to kuma za a shiga shakku don za a yi tunani
mai zurfi kafin a shimfiɗa masa wata gada da za ta karye da shi a samu sa’arsa.
Da wannan za mu iya gane cewa, masu wayo suna ribantar zaman duniya. Sai dai
idan wayon ya yi yawa, wani lokaci yanakan ɓaci ya kuma zama illa. Saboda
wannan ana buƙatar idan mutum zai shirya wayo a kan wata harƙalla ko wani
sha’ani, to akwai buƙatar ya tsara shi daidai da abin da hankalin waɗanda aka
tsara don su zai iya ɗauka. Idan wayon ya saɓa haka to yana zama illa ga wanda
ya tsara wayon.
Babbi Na
Huɗu
4.0.1
Tsokaci A Kan Littafin Ruwan Bagaja.
Littafin Ruwan Bagaja littafi ne da Abubakar Imam ya rubuta, kuma shi ne wanda
ya zama zakara wato na farko a cikin gasar da aka yi dangane da ƙagaggun
rubutattun littattafan da muka kawo a sama kamar yadda aka gani, kuma har da
littafin da aikinmu yake keɓanta a cikinsa.
An shirya littafin a kan tsarin babi-babi har zuwa babi takwas, inda kowane
babi yake ɗauke da kan labari da aka ware a wannan babi, da manufar ware jigon
yadda ‘ya’ya suke sharewa iyayensu hawaye kanwata matsala da ta dame su. Haka
kuma littafin yana da shafuka arba’in da huɗu (44).
Haka kuma idan muka leƙa littafin kai tsaye za mu ga cewa, duk da yake yana da
fasali irin na tatsuniya, to an juya tsari da falsafar labarin littafin
Alfu-laila-wa-laila wanda yake na Laranci ne. Kamar yadda malam Abdullahi
Bayero Yahya ya nuna a cikin littafinsa mai suna “Adabin Abubakar Imam” .
Bayan da marubucin ya yi amfani da salon tatsuniya ya gina labarinsa sai ya
samu wani tauraro da ya yi amfani da shi don ya samu damar isar da saƙonsa
cikin sauƙi. Wannan tauraro dai ya sha alwashin sai ya samo Ruwan Bagaja waɗanda
aka ce idan an ba Yarima ya sha zai warke. Yayin neman wannan ruwan tauraron ya
sha wahala sosai saboda an nuna muhimmancin wannan ruwa da kuma muhimmancin
nema don biyan buƙata. A nan an samu wani tsari na dabarar sarrafa labarin wasu
da suke ba na ƙasar Hausa ba ne.
Idan muka kalli jigon wayo a cikin wannan littafi za mu ga cewa, irin nau’in
zamantakewar Hausawa da aka yi amfani da ita da kuma yadda shi kansa Tauraron
wannan littafi ya ke shirya wayonsa a duk inda ya samu kansa, to wannan ma ya
isa mu gane cewa, kowace rayuwa da yadda ake tsara ta kuma a saka dabara a ciki
domin kauce wa wahala ko muzanta. Duk da cewa Turawan mulkin mallaka a wancan
lokaci bisa ga tasu manufa suka gina labari, wato suma nasu wayo kenan.
4.0.2
Ma’anar Taurari/Tauraro
Tauraro ko taurari dai a cikin rubutun zube yana nufin wani mutum da aka yi
amfani da sunansa wajen gina wannan labari da aka yi a rubuce, haka abin yake
ko a cikin wasan kwaikwayo wadda aka rubuta ko wadda aka gabatar a cikin faifan
bidiyo. Tauraro ya kasu kashi biyu. Wato babban tauraro da Ƙaramin/ Ƙananan
Taurari/tauraro.
4.0.2.1
Babban Tauraro.
Babban tauraro dai a cikin rubutun zube ko a faifan bidiyo shi ne mutumen da aka
fi yin amfani da shi wajen gudanar da wannan rubutu ko wasan da ake nunawa a
bidiyo domin isar da saƙon da ake son a isar ga jama’ar da ake son a sanar.
4.0.2.2 Ƙananan
Taurari/Ƙaramin Tauraro.
Ƙaramin Tauraro/Ƙananan Taurari dai su ne mutanen da aka yi amfani da su a
cikin rubutun zube ko a faifan bidiyo a yayin da ake gudanar da wata wasa ko
ake rubuta wani Ƙagaggen Labari don isar da wani saƙo.
4.0.3
Tsohon Salo A Cikin Ƙagaggen Labari
Haƙiƙa dabarar ƙagawa ta taimaka wa marubuta ƙagaggen labarin Hausa wajen
shirya littafan zube. Wannan damar ce Abubakar Imam ya samu har ya shirya
littafinsa na Ruwan Bagaja da ma sauran littafai. Amma a wannan kundi ba za mu
yi bayanin kowane littafi ba sai dai za mu fi mayar da hankali a kan littafin
da muka keɓance muhallin da za mu yi wannan aikin, wato littafin “Ruwan
Bagaja”.
Sau da yawa wasu al’adu da wasu lamurra na wani sha’ani sukan auku musamman a
cikin littattafan zube, waɗannan abubuwa ba wai sun taɓa faruwa ne da gaske ba,
kuma takan ɗauro wani wuri daban ya zamana abin ya taɓa aukuwa. Lamurran yau da
kullum sukan faru a yayin da ake ƙulla zarin bayani a cikin littafi. Wasu
abubuwa da ake zanowa a cikin ƙagaggen labari sukan kasance wasu abubuwa da ake
cuɗanya da su a wannan lokaci. Waɗannan abubuwa sukan iya zama sana’a ce, ko
zamantakewa ko wani sha’ani na daban.
Idan aka yi la’akari da abin da yake faruwa a yau za a iya cewa, mafi yawan
wasu zauna gari banza ne ba su da wani takamaiman aiki kuma ba su da wata
sana’a. Idan marubuci ya ɗaga alƙalaminsa zai iya yin aiki sosai da ya jiɓinci
wannan lamari.
Irin wannan damar ce Abubakar Imam ya yi amfani da ita ya isar da wani saƙo a
cikin littattafansa na zube.
Yanzu dai kafin zuwa ko’ina ya dace mu kalli wayo a cikin ƙagaggen labari.
A cikin ƙagaggen labari dai wayo kan taka muhimmiyar rawa saboda zamansa wani
abin gudanar da rayuwa. Kowane mutum ko al’umma yana ko suna da tsari da suka
yi na gudanar da rayuwarsu. Wannan tsari kuma yana buƙatar dabara da za ta
taimaka masa ya kauce wa shiga wani haɗari ko kunya. A cikin ƙagaggun labarai
ana amfani da wannan domin a isar da saƙo ga mai karatu cewa, yin wayo don
gudun kar mutum ya muzanta ko ya rasa rayuwarsa yana da matuƙar muhimmanci.
Haka kuma wannan yana daga cikin nau’o’in salon gina ƙagaggen labari, duk da
cewa wannan salo tsohon salo ne amma kuma an gina shi daidai da wayon jama’ar
da suka yi zamani a wannan lokaci.
A littafin Ruwan Bagaja dai an yi amfani da irin wannan salo domin a samu wata
hanya ta isar da saƙo. Marubucin littafin ya nuna cewa, daga cikin taurarin da
ya yi amfani da su akwai Sarki kuma akwai Yarima da Liman da kuma shi kansa
Imam da Zuƙe da dai sauransu. Sai ya nuna cewa Yarima wato wani daga cikin waɗanda
za su gaji Sarki ya kamu da rashin lafiya sai aka nemo Liman ya yi masa addu’a
don ya samu sauƙi sai Liman ya ce zai samu sauƙi amma fa sai an samo masa Ruwan
Bagaja. To a wannan yanayi neman ruwan da za a yi sai ya saka masa wasu
wahalhalu da za a haɗu da su kafin a samu ruwan. Wannan ya nuna cewa,
muhimmancin rayuwar wannan Yariman ba ƙarama ba ce. Haka kuma ana son mutum ya
sani cewa, cikar buri ba ƙaramin lamari ba ne. Saboda haka Imam ya daure duk
wata wahala da zai haɗu da ita zai jure sai ya kawo wannan ruwan. Inda ya dace
ya yi amfani da ƙarfi sai ya yi, kuma inda ya dace ya yi amfani da dabara ta
wayo domin kauce wa salwatar rayuwarsa ko faɗuwar girmansa ko dai wani abu da
zai kawo cikas ga rayuwarsa.
4.0.4 Haɗuwar
Imam Da Zurƙe
A wannan littafi dai an nuna wani mai suna Yarima baya da lafiya sai aka nemo
liman sai liman ya ce ba zai warke ba sai an ba shi ruwan bagaja, su kuma ruwan
na bagaja samunsu wuya ke gare shi. Sai wani mai suna Imam ya ce shi kuma sai
ya samo su. Anan fa sai ya shiga neman ruwan a hanyarsa ta neman ruwan ya haɗu
da mutane daban-daban daga ciki har da Zurƙe ɗan Mamman wannan mutum dai mai
suna Zurƙe mutunen ƙauye ne kuma shi ma kansa wannan mutum wato malam Zurƙe sun
sha gwagwarmaya da Imam. Saboda a cikin wannan littafin an nuna sun haɗu kuma
har wata dangantaka ta shiga tsakaninsu, duk da cewa dangantakar ba wai ta
zaman kirki ba ce.
Imam ya haɗu da Malam Zurƙe a wani kogi mai suna kogin ƙaruna kuma shi Zurƙe ya
jefa Alhaji Imam a cikin kogin ya nutse har ya haɗu da ‘yan ruwa, Allah ya taimake
shi suka warkar da shi daga makautar da ta same shi yayin neman wata yarinya a ɗan
dago inda aka yi masa magani ya makauce.
4.0.5
Neman Ruwan Bagaja
A cikin wannan littafin na ruwan bagaja za mu ga cewa, tun da sarki ya muzanta
liman Abubakar Imam ya ga cewa ran liman ya ɓaci sai ya yi ƙoƙarin gwada
gaskiyar liman. Tun da wannan ta shiga tsakanin sarki da liman sai ya yi ƙoƙarin
ya nuna gaskiyar liman ya nuna cewa, liman fa ba barkwanci yake yi wa sarki ba.
Shi kuwa Imam bai san inda ruwan Bagaja suke ba sa ya je ƙofar gabas don neman
sa’a ba don gabas ɗin ruwan bagaja yake ba. Ga dai abin da yake faɗa a cikin
littafin: “da komawa ta gida sai na ɗan .......ba don a san inda za ni ba”
(Shafi na 6) daga nan sai Imam ya shiga neman ruwan bagaja ya nema a nan ya
nema a can har sai da ya sha wahala sosai, daga ƙarshe dai sai da ya samu
taimakon Aljannu sannan ya samu cikar burinsa.
Bayan da Imam ya samu Ruwan Bagaja sai ya zo da su jama’a dak suka tabbatar da
gaskiyar liman ta cewa, idan an ba Yarima ruwa zai warke. Da Imam ya dawo sai
Liman ya karɓi kwalbar da ruwan bagaja suke ciki sai ya ɗauki wani tsinke ya
tsoma shi a ciki ya fitar ya tsoma shi a cikin wani kwano sai aka ba
Yarima ya sha.
4.0.6
Muhimmancin Rayuwa A Littafin Ruwan Bagaja
A littafin “Ruwan Bagaja” dai marubucin ya nuna muhimmancin nema a cikin shafi
na takwas (sh:8) saboda a fitar da Liman a kunya, tun da Liman ya nuna cewa,
idan aka ba Yarima Ruwan Bagaja zai samu lafiya shi kuma sarki ya ce duk inda
za a samu ruwan sai ya samo su don ya ceci rayuwar Yarima. Ga dai abin da
marubucin ya faɗa a cikin littafin a shafi na takwas. “....idan aka ba Yarima
Ruwan Bagaja to zai ji sauƙi” sai Alhaji ya ce, “indai akwai shi duniya sai dai
na mutu gun nemansa” wannan jawabi da Alhaji ya yi ya nuna cewa, cikar buri
yana da amfani matuƙa. idan aka yi la’akari da irin wahalar da mai neman ruwan
ya sha wajen nemansu. Alhaji ya share kimanin shekara goma sha biyar wajen
neman ruwan bagaja. Bayan da aka dawo da wajen neman ruwan sai aka kawo ma
liman ya ɗauki wani tsinke ya tsoma shi a cikin kwalbar ruwan sai ya cire ya
tsoma shi a cikin kwano sai aka ba maras lafiya ya sha sai ya miƙe ya tashi ya
warke da rashin lafiyar da take damunsa.
4.0.7
Nazarin Wayo A Littafin Ruwan Bagaja
Wannan shi ne ainihin aikin da za mu yi a wajen gudanar da wannan bincike.
Sanin jama’a ne cewa, shi wannan littafi kamar yadda muka faɗa a baya cewa,
aikinmu zai mayar da hankali ne wajen yin Nazarin wannan littafi na “Ruwan
Bagaja” kuma a ciki ne za mu fito da yadda malam Zurƙe da Imam suka gudanar da
zamantakewarsu da wasu Taurari da suke a cikin wannan littafi.
4.0.7.1
Wayo Don Samun Abin Duniya
A wannan zamani mutane ba kasafai suke taimako ba, wannan ya sa tunda Tauraron
ya samu kansa inda bai san koya sai ya yi tunanin ya yi wa wani Attajiri wayo
ya karɓi kuɗi a hannunsa don ya samu abin gudanar da tasa rayuwar. Ga dai yadda
ya yi har ya karɓi kuɗi a hannun wani Attajiri don ya samu yadda zai riƙe kansa
a garin da kuma na guzuri ko da ya tashi wucewa gaba.
A shafi na 7 a wannan Littafi na Ruwan Bagaja, sakin layi na 3 marubucin ya
kawo yadda Tauraron wannan littafi ya yi wayo don ya karɓi kuɗi ga wani
Attajiri ga dai yadda abin yake:
“Bayan na yi kwana saba’in ina tafiya, sai na isa Tumbutu.
Na yi shiri irin na fatake, na isa gun Sarki na ce ni falke ne,
kayana suna baya, za su zo bayan kwana uku. Abin da ya
sa na ce haka, don na baro wasu shanu ne a baya na wani falke”.
Idan muka lura da abin
da Tauraron ya yi a nan za mu ga cewa, wayo ne ya yi tunda har yana da
masanniyar wani falke da ya wuce a baya, kuma ya san cewa, guzurinsa ya ƙare
sai ya zo ya gaya wa sarki cewa shi falke ne kuma shanunsa suna nan tafe wannan
wayo da ya yi ya yi shi ne don ya samu masauki. Tunda idan ya ce yana da dukiya
kuma shi sana’a yake yi to ai ba za a yi masa kallon banza ba kuma za
girmama shi duk inda ya je. Haka kuma a al’adar mutane duk mutumen da yake da
dukiya ba a raina shi dole ana yi masa kallon arziki.
4.0.7.2
Wayon Don Samun Karɓuwa Ga Wasu
Wannan wayo da Tauraro ya yi amfani da shi wayo ne wanda a wannan lokaci shi ne
ya fi dacewa ya yi amfani da shi domin ya samu karɓuwa ga wasu da yake son su
aminta da shi. Wannan ya sa ya bayyana a shafi na 7 sakin layi na 4 cewa :
“Kullum da yamma sai in samu taro, in sayo miya,
In bi ƙofar gidan da na saka in warwatsa ko’ina,
Abin da ya sa nake haka , don ina da wani aboki ne Attajiri.”
Wannan wayo da Tauraron ya yi a wannan lokaci shi ne ya fi dacewa da jama’ar
wannan lokaci. Yana yin haka ne saboda a ko da yaushe in mai kuɗin ya zo sai ya
ce masa kar ka zauna a nan awai miya, wai don Attajirin nan ya ɗauka cewa shi
ne yake ciyar da almajiran wannan garin. Kuma idan shi ke ciyar da almajirai to
wannan ya nuna cewa kenan shima Attajiri ne kamar sa.
4.0.7.3
Wayo Don Samun Aron Kuɗi
Wannan wayo ne da ake yi wa masu kuɗin domin su samu kwanciyar hankali ga wanda
suka ba aron. Kuma domin a samu su bayar da kuɗin ba tare da an sha wahala
wajen su bayar ba. Tauraron wannan littafi ya yi amfani da wannan wayo don ya
samu aron kuɗi ga Attajirin ko da yake ba biya zai yi ba. Ga dai yadda abin
yake a shafi na 7 a sakin layi na 4:
“...sai suka fara tsammanin haka, sai na ci bashi gunsa
kamar na rabin jaka, kullum sai in yi masa romon baka,
ina cewa, idan shanuna sun zo ba na sayar wa kowa sai shi
kaɗai”
wannan dai wayo ne da Tauraron ya yi a lokacin da yake neman ya samu kuɗi ga
hannun Attajirin nan da yake abotaka da shi.
4.0.7.4
Wayo Don Tsira Da Mutunci
A wannan wuri Tauraron ya yi amfani da wannan salo na yin wayo don ya tsira da
mutuncinsa. Da zuwan Malam Zurƙe ya sauka a gidan sarki ya kuma gaya wa sarki
cewa shi daga ƙasar Larabawa yake, kuma kullum yana mafarki da wannan ƙasar ta
Sarkin ana gaya masa cewa ya zo ya riƙa yi masu Salla. Da sarki ya ji haka sai
ya yi na’am da shi ya ba shi masauki kuma ya tara jama’ar gari suka aminta da
shi ya zama shi ke koya masu salla duk da cewa bai san komai ba a cikin karatu
sai dai wata aya wadda ya hardace wato “Mudahammatani”
Ana haka sai ga wani malami wato Malam Zurƙe an samu ya zo ya faɗa masu cewa ba
a kan gaskiya wannan Imam yake ba don haka sai aka tara jama’a don a bayyana
masu gaskiya. A nan idan aka ƙaryata Imam to lallai mutuncinsa zai zube, wata
kila ma a kashe shi ko a kore shi da wannan gari ko ya fuskanci wani hukunci
mai tsanani. Ga dai yadda abin ya gudana a shafi na 9 sakin layi na 5,6,7,8:
“Bayan an natsu na yi shiru na share ƙasa, sai ka ce mai shirin hadɗ’i, na zana
wata alama haka( ) na Dubi Malam Zurƙe na ce Masa Mene ne wannan?
Ya ce, “Nu’ara ce”
Na ce, “Haba! Sake dai”
Ya ce, “Ra.”
Na ce, “Haka ake “Ra” a gidanku”
Ya ce, “Lam’ara ce”
Na ce, “Wane maƙaryacin malami ya koya maka haka?”
Duk ya ƙare tsice-tsincen baƙaƙensa na Alƙur’ani masu kama da wannan alama na
ce ƙarya yake yi. Da ya ce ya bani gari na ce ku matso ku gani.
Sa’annan na dubi mutane na ce, “wannan ba ra ba ce ba lam’ara ba ce ba nu’ara
ba ce, tsayuwar wata daren farko ne nan”
Jahilai suka duba suka ce “Haka nan ne Malam! Haka nan ne malamin malamai! Haka
kuwa tsayuwar wata yake”.
Wannan wayo da Imam ya yi ya taimaka masa bai rasa matuncinsa ba ya kare masa
shi.
Babi Na
Biyar
5.0.1
Jawabin Kammalawa.
Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki Mai Kowa Mai komai,
Mahaliccin sammai da ƙassai da ya bamu ikon kammala wannan aikin Bincike. Yabo
da jinjina ga AnnabinSa Muhammadu (SAW) Imamin Manzanni Cika makin Annabawa
Muhammadu ɗan Abdullah, da iyalan gidansa da Sahabbansa da magoya bayansa tun
daga farko har ƙarshe.
Hausawa kan ce, “Komai nisan dare gari zai waye” wannan ko shakka babu haka
yake. Saboda a nan ne za mu naɗe tabarmar wannan bincike mai taken “Nazarin
Jigon Wayo A cikin Littafin Ruwan Bagaja”.
Kamar yadda aka gani a baya mun raba aikin nan namu gida biyar bisa ga tsarin
babi-babi har babi biyar.
Babi na farko ya ƙunshi, Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin Bincike, Hanyoyin
Gudanar Da Bincike, Matsalolin da Suka Taso da Matsalolin da aka fuskanta.
A babi na biyu kuwa kamar yadda doka ta tanadar mun kawo Waiwaye A Kan
Ayyukan da Suka Gabata inda har muka kawo wasu littattafai da kundaye waɗanda
suke da alƙa da namu aiki mun kawo bambancinsu da namu aikin. kana muka yi
byanin Salon Nazari da Tsarinsa.
A babi na uku kuwa mun kawo, bayanai a kan Ƙagaggun labarai da Tarihinsu inda
har muka ce sun samu tun a shekarar 1933 kuma mun kawo wasu ayyuka da aka samu
a wannan shekarar. Mun kawo ma’anar jigo da kashe-kashensa da ma’anar salo da
ina har muka ce dabara ce. Mun kawo ma’anoni daban-daban daga masana, kana muka
yi bayanin ma’anar wayo.
A babi na huɗu kuma nan ne muka yi tsokaci a kan littafin Ruwan Bagaja inda
muka zo ba bayanai game da littafin, haka kuma mun kawo ma’anar taurari inda
har muka ce su ne waɗanda aka shirya labarin da su. Haka ma mun bayani a kan
tsohon salo a cikin ƙagaggun labarai. Sai Haɗuwar Imam da Zurƙe da duk shiritar
da suka aikata. Mun kawo bayani a kan neman ruwan Bagaja da muhimmancin rayuwa
a cikin wannan littafi. Daga nan kuma muka shiga Nazarin wayo a littafin, yayin
da muka kawo wayo don samun abin duniya, sai wayo don samun karɓuwa ga wasu,
sai kuma wayo don samun aron kuɗi da wayo domin tsira da mutum.
Shi kuwa wannan babi na biyar shi ne muka kammala aikinmu a cikinsa kamar yadda
aka gani yana ƙunshe da Jawabin Kammalawa da Shawarwari.
5.0.2
Shawarwari
Muna son mu yi amfani da wannan damar mu ba ‘yan’uwanmu ɗalibai shawara su
mayar da hankali wajen gudanar da sha’anin karatunsu tare da yin ƙoƙari
gwargwadon hali, su kasance masu ƙwazo ga karatunsu. Idan kuwa Allah ya kai su
ga lokacin da za su gudanar da bincike in suka ci karo da wannan aiki namu to
su yi ƙoƙari su ɗora daga inda muka tsaya na wannan bincike.
Muna kira ga wasu waɗanda ba nazarin wannan kundi suke yi ba da su yi ƙoƙari su
koyi darussan da ke cikin wannan kundi kar su yi ƙasa a guiwa su kasance masu
kyautatawa ga al’ummar su ta Hausa. Kuma su saka wayon da yace da hankalin waɗanda
za su yi wa wayon kar su kasance sun tafka kuskure a cikin tsarinsu.
Manazarta
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.