Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari A Kan Gudummuwar Wanzamai Wajen Ya’da Cututuka Ga Al’ummar Garin Gusau

NA

A’ISHA MAMMAN

MURJA MATI

NAFISA ADAMU

KUNDIN BINCIKE WANDA AKA GABATAR A SAHEN HAUSA NA TSANGAYAR HARSUNA A KWALEGIN ILMI DA K’ERE-K’ERE TA GARIN GUSAU, JIHAR ZAMFARA

www.amsoshi.com

Shedantarwa


Wannan aiki ya samu dubawa da tabbatarwa tare da kar’buwa gami da amincewar wad’annan malamai.

MAI DUBA AIKI NA CIKI (Project Supervisor)

Mal. Haruna Umar Maikwari

Sa-hannun…………………………………….

Kwanan wata…………………………………

Sadaukarwa


Mun sadaukar da wannan bincike ga iyayenmu bisa ga kyakkyawar tarbiya da suka ba mu tun daga farkon rayuwa zuwa yau. Iyayen namu sun had’a da: Mal. Mamman Dogo da Mal. Adamu Usman  da Mr Mati.

 

Jinjina


Muna masu jinjinawa babban malaminmu kuma jagoran wannan bincike wanda ya kula da mu wato malam Haruna Umar Maikwari na tsangayar harsuna sashen Hausa. Saboda nuna k’wazonsa wajen duba wannan kundi tare da mayar da hankalinsa wajen wannan aiki tun farkon lokacin da aka fara har Allah ya kawo mu a wannan lokaci. Allah ya saka masa da mafificin alheri. Amin.

 

Godiya.


Muna godiya ga tabbataccen Sarkina nan wanda shi ne mahaliccin kowa da komai.

Haka kuma muna mik’a kyakkyawar godiyarmu zuwa ga iyayenmu, mazanmu da sauran ‘yan’uwanmu da suka taimaka a cikin wannan karatu namu, kamar su; Mal. Mamman Dogo da Mal. Adamu Usman  da Mr Mati. Bayansu kuma muna godiya ga wasu da suka taimaka muna kamar su; Nuhu Adamu da Kuma Nuhu Mamman Dogo da mai gidan Murja wato Mr. Joseph

don bamu tarbiyya tun tasowarmu har zuwa yau da kuma ba mu gudunmuwa da suka yi wajen ci gaba da karatunmu.

Haka kuma muna mik’a kyakkyawar godiyarmu zuwa ga malam Haruna Umar Bungud’u( H.O.D) na sashen Hausa a Tsangayar Harsuna Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau Jihar Zamfara, kuma muna mik’a godiyarmu ga dukkan malaman wannan sashe, mun gode ga baki d’aya Allah ya bar zumunci ya sa ma karatun da muka yi albarka ya sa abin da za mu taimaki wannan jiha da k’asa baki d’aya.

 

K’umshiya



  1. Shedantarwa -        -        -        -        -        -        ii

  2. Sadaukarwa -        -        -        -        -        -        iii



  • Jinjina -        -        -        -        -        -        -        iv



  1. Godiya -        -        -        -        -        -        -        v

  2. K’umshiya -        -        -        -        -        -        vi


Babi Na ‘Daya


1.0.1 Gabatarwa    -        -        -        -        -        -        -        -        1

1.0.2 Yanayin Bincike    -        -        -        -        -        -        -        3

1.0.3 Muhallin Bincike   -        -        -        -        -        -        -        3

1.0.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike   -        -        -        -        -        4

1.0.5 Tambayoyin Gudanar Da Bincike        -        -        -        -        5

1.0.6 Matsalolin Da Aka Fuskanta      -        -        -        -        -        6

2.0    Babi Na Biyu


2.0.1 Waiwaye (Ayyukan Da suka Gabata)   -        -        -        -        9

2.0.2 Salo, Zubi Da Tsarin Bincike     -        -        -        -        -        12

3.0    Babi Na Uku


3.0.1 Asalin Sana’ar Wanzanci  -        -        -        -        -        14

3.0.2 Rabe-Raben Wanzaman Hausawa        -        -        -        15

3.0.2.1 Wanzaman Gado -        -        -        -        -        -        15

3.0.2.2 Wanzaman K’ok’o        -        -        -        -        -        -        16

3.0.2.3 Wanzaman Jarfa  -        -        -        -        -        -        17

3.0.3 Gado A Cikin Sana’ar Wanzanci -        -        -        -        18

3.0.4 Matsayin Sana’ar Wanzanci       -        -        -        -        20

3.0.4.1 Sana’ar Wanzanci A Al’adance         -        -        -        21

3.0.4.2 Wanzanci a Addinin Musulunci        -        -        -        24

3.0.4.3 Sana’ar Wanzanci a Zamanance        -        -        -        26

3.0.5 Kayan Aikin Yin Wanzanci        -        -        -        -        28

3.0.5.1 Askar Aski -        -        -        -        -        -        -        29

3.0.5.2 Dutsen Washin Asaken Aski   -        -        -        -        30

3.0.5.3 Fatar Washin Asaken Aski      -        -        -        -        31

3.0.5.4 Almakashi -        -        -        -        -        -        -        32

3.0.5.5 Sabulun Aski       -        -        -        -        -        -        32

3.0.5.6 Kwanon Aski      -        -        -        -        -        -        33

3.0.5.7 Kalaba       -        -        -        -        -        -        -        33

3.0.5.8 Koshiya     -        -        -        -        -        -        -        33

3.0.5.9 ‘Yartsaga   -        -        -        -        -        -        -        34

3.0.5.10 Hantsaki  -        -        --       -        -        -        -        34

3.0.5.11 ‘Yankara -        -        -        -        -        -        -        35

3.0.5.12 Karkiya   -        -        -        -        -        -        -        35

3.0.5.13 K’aho      -        -        -        -        -        -        -        36

3.0.5.14 Jijiya       -        -        -        -        -        -        -        36

3.0.5 15 Kura Ta Cire Hak’ori   -        -        -        -        -        37

3.0.5.16 Tankolo   -        -        -        -        -        -        -        37

3.0.5.17 Zabira      -        -        -        -        -        -        -        37

Babi Na Hud’u


4.0.1 Tsokaci A Kan Wanzamai a Garin Gusau      -        -        38

4.0.2Amfanin Wanzamai A garin Gusau       -        -        -        39

4.0.2.1 Yin Aski    -        -        -        -        -        -        -        40

4.0.2.2 Kaciya       -        -        -        -        -        -        -        41

4.0.2.3 Cire Gurya -        -        -        -        -        -        -        42

4.0.2.4 Cire Hakin-Wuya -        -        -        -        -        -        42

4.0.2.5 Bayar Da Magunguna   -        -        -        -        -        43

4.0.3 Tsokaci A Kan Cututuka  -        -        -        -        -        44

4.0.4 Hanyar Da Ya Dace a Bi Don Kaucewa Yad’a Cututuka   45

Babi Na Biyar


5.0.1 Jawabin Kammalawa       -        -        -        -        -        48

5.0.2 Sawarwari    -        -        -        -        -        -        -        50

5.0.3 Ta’arifin Kalmomi -        -        -        -        -        -        51

Manazarata  -        -        -        -        -        -        -        -        53

 

 

 

 

 

 

Babi Na ‘Daya


Gabatarwa


Wajibi ne ga dukkan mai aikin bincike ya gabatar da abin da zai yi a cikin wannan babi na d’aya. Da wannan ne muka ga ya dace mu yi shimfid’a wadda za ta haska wa mai nazari, ko wanda zai amfanu da wannan kundi namu. Wato dai mu yi shimfid’a ta gaba d’aya a wannan fage.

Wannan bincike danganci nazari a kan Gudummuwar Wanzamai Wajen Yad’a Cututuka Ga Hausawa na Garin Gusau.

Mun kasa wannan kundi gida biyar wato babi na d’aya zuwa babi na biyar, yayin da a kowane babi za mu yi bayani da za su fito da wannan bincike da za mu gudanar a fili.

A babi na d’aya dai kamar yadda aka sani baya ga wannan  Gabatarwa za mu kuma kawo Yanayin Bincike da Muhallin Bincike da Hanyoyin Gudanar Da Bincike da Matsalolin da Suka Taso da kuma Matsalolin da Za a Fuskanta.

A babi na biyu kuwa za mu mayar da hankali ne a kan Ayyukan da magabata suka yi domin mu samu tudun da za mu dafa. Kana daga bisani za mu kawo Salon Nazari da Tsarinsa.

Babi na uku nan ne za mu gudanar da bayanai da suka danganci Ma’anar sana’ar wanzanci da kayan aikin wanzanci da yadda ake wanzanci da ire-iren wanzamai da muhimmancin wanzamai.

A babi na hud’u kuwa nan ne za mu yi tsokaci game da wanzaman garin Gusau, da muhimmancin su ga al’ummar garin Gusau da ayyukan da suke yi a garin Gusau. Za mu kuma yi tsokaci dangane da cututukan da ake iya samu a sanadiyar sana’ar wanzanci, da kuma hanyoyin da za a bi wajen magance su.

A babi na biyar kuwa nan ne za mu nad’e tabarmar wannan aikin bincike da muke gudanarwa, yayin da za mu kawo Jawabin Kammalawa da Shawarwari da Ta’arifin Wasu Kalmomi. Sai mu kawo Manazarta domin mu d’aure akuyarmu a iccen magarya.

 

 

 

Yanayin Bincike


A k’ok’arin bayyana yanayin bincike da muke gudanarwa mun yi amfani da ingantacciyar hanya, wato babi domin samun nasarar gudanar da wannan bincike. Wannan bincike ne a kan rawar da Sana’ar wanzanci ke takawa waje yad’a cututuka ga Hausawa mazauna garin Gusau.

Saboda haka an yi k’ok’arin fito da wasu abubuwa masu muhimmanci domin masu nazari su amfana sosai, don haka yanayin wannan bincike yana da matuk’ar sha’awa da kuma wahala musamman idan muka lura da cewa babu wani aiki da muka ci karo da shi mai irin wannan take da muka za’bo.

Muhallin Bincike


Sana’ar Wanzanci tana da zurfin tarihi a ko’ina cikin nahiyar Afirka kamar yadda za a gani a babi na gaba. Shi wannan ‘bangare, ‘bamgare ne da ya shafi sana’ar wanzanci wadda ta cud’anyi mutane da dama ba kawai mazauna garin Gusau ba hatta da wad’anda suke a wata nahiya daban.

To kamar dai yadda muka fad’a wannan aikin bincike da zamu gudanar, a mu tak’aita shi ne a garin Gusau kawai ba da sauran garuruwan da suke kewaye da garin ba. Kar a manta kuma wannan aikin aiki ne da za mu yi shi a kan rawar da sana’ar wanzanci ke takawa wajen yad’a cututuka a garin na Gusau.

Hanyoyin Gudanar Da Bincike


A lokacin da za mu gudanar da wannan binciken namu mun bi hanyoyi da dama domin samun gamsassun bayanai. Hanyoyin da muka bi wajen gudanar da wannan bincike kuwa sun had’a da:

Hanya ta farko da muka bi domin cimma nasara wajen gudanar da wannan bincike ita ce, ta tattara bayanai daga littatafan da aka wallafa masu dangantaka da wannan aiki, da mujallu da kundaye da muk’alu da dai makamantansu wad’anda suka shafi sana’ar wanzanci.

Sai hanya ta biyu wato ta ganawa ko tattaunawa ido da ido tsakanin mu da wad’ansu masu irin wannan sana’a, da kuma wasu da suke amfani da wannan sana’a duk a nan garin.

Hanya ta uku kuwa ita ce hanyar zantawa da wasu mutane da suke da masanniya a kan abin da yake gudana dangane da wannan sana’a.

Matsalolin Da suka Taso


A wannan bincike mun fahimci cewa akwai wani gi’bi da aka manta ba a cika ba a cikin fannonin da ake bincike a kansu. A al’ada akwai abubuwa da yawa wad’anda suka shafi al’amurran jama’a na wannan zamani amma sai aka yi fatali da su ba wanda ya kula. Tuni wasu mashahuran malamai suka yi iya k’ok’arin su don ganin cewa sun samar wa jama’a abin karatu da kuma abinda za su nazarta. Wannan ya nuna kenan har ko yaushe ba a rasa wasu da suka yi k’ok’ari wajen samar da abin da za a iya dogaro da shi na abin da ake nazari.

Saboda a namu gani wannan fanni da muka d’auka, ba a cika wani abu da ya shafi yadda cututuka suke yad’uwa ba a sakamakon sana’ar wanzanci ba. Wannan na d’aya daga cikin manyan dalilan da suka ja hankalinmu muka fantsama cikin yin nazari a kan wannan fanni.

Wasu da suka taso a wannan lokaci ba su san irin gwagwarmayar da aka sha ba, ba su kuma san illolin da wannan sana’a take da shi ba, wannan ya bamu damar tunanin aikata wannan aiki a matsayin kundi don kammala karatunmu na wannan makaranta.

Matsalolin Da Aka Fuskanta


Kamar yadda ma’anar ke nuni “matsala” wato ita matsala tana nufin irin cikas d’in da aka ci karo da shi a yayin da ake gudan da wannan bincike. A duk lokacin da mutum ya samu kansa a cikin irin wannan aiki na bincike to lallai wajibi ne ya ci karo da wasu matsaloli da za su iya kawo tarnak’i ga aikinsa na bincike kafin ya kai ga cin nasara. A lokacin gudanar da wannan kundi muna samun barazana ta wasu matsaloli da suka had’a da:

Matsalar littafan karatu. Wannan matsala matsala ce babba saboda wannan makaranta ba ta da isassun littafai da za mu duba wannan kuwa ya kawo sai da muka lek’a wasu makarantu don samun wasu bayanai da za su taimaka mu gina namu kundin. Wannan walaha ta ziyarce-ziyarcen wasu makarantu ta kawo muna tafiyar hawainiya ga gudanar da wannan bincike.

Matsalar kud’i: wannan matsala tana d’aya daga cikin manyan matsaloli da suke tauye komai da ake yunk’urin yi har dai in ya zama abu ne mai buk’atar a inganta shi. Matsalar kud’i babbar matsala ce har dai garemu mata da yake d’auke ake da nauyinmu kuma ba kasafai za mu nemi a bamu kud’i a gidajenmu a bamu ba sai an samo kuma sai an gani in babu wani abu da ya fi buk’atarmu muhimmanci sannan a bamu, idan kuwa aka samu wani abu da ya fi tamu buk’atar muhimmanci to, lallai mu ba zamu samu ba sai har an samu wasu gaba sannan wata kila mu samu. Rashin kud’in dai ya kawo muna matsala, amma yanzu mun shawo kan matsalar.

Matsalar wutar lantarki: wannan matsala ta taka rawa sosai wajen yi wa wannan aiki namu tarnak’i wato matsalar ta kawo tafiyar hawainiya wajen gudanar da wannan binciken. Ana kuma iya gane cewa wannan zancen namu na matsalar wutar lantarki gaskiya ne idan aka dubi yanayin garin na Gusau za a ga cewa babu isasshiyar wutar lantarki wadda da ita ne kawai za a iya buga muna rubutunmu a cikin Kwamfuta (Computer). Wannan ya sa muka saka wannan matsala ta rashin wuta a cikin matsalolin da suka taso suka dabaibaye gudanar wannan kundi.

 

 

 

 

Babi Na Biyu


2.0.1 Waiwaye A Kan Ayyukan Da Suka Gabata


Kamar yadda muka riga muka sani cewa waiwaye shi ne adon tafiya, to ko a wannan aiki waiwayen zai taimaka muna, don haka za mu waiwayi baya mu ga irin ayyukan da suka gabata wad’anda suke da dangantaka da namu aikin..

Domin yi wa aikin mu kwalliya za mu binciki littattafai da kundaye da muk’alu da dai sauran wasu ayyuka da suka shafi namu don mu ga inda suka tsaya sai mu d’ora ko mu gina wani.

Alhassan H. Da wasu (1982) a cikin wani littafinsu da suka rubuta mai taken “Zaman Hausawa” wad’annan marubuta sun tsara wannan littafi a cikin tsarin kanun batutuwa kamar haka; a ciki sun yi tsokaci a kan Duniyar Hausawa da Aure da Haihuwa da Tarbiyya. Haka kuma sun yi bayani a kan sana’o’in Hausawa inda suka kawo sana’ar noma, sak’a, k’ira, wanzanci da dai sauransu. A cikin tsokaci da suka yi da wanzanci ya sa muke ganin aikinsu zai taimaka da wani abu ta ‘bangaren wanzanci wanda za mu iya samun haske gare shi.

Nafisa (2003), ta rubuta kundin bincike mai taken “Sana’ar Jima a Garin Gusau”, ” don samun takardar shedar kammala karatun N.C.E a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau, Jihar Zamfara.

Kundin ya yi tsokaci dangane da ma’anar sana’a da yadda ake gudanar da ita kana ta bayyana matsayin masu sana’ar a idon jama’a. Wannan kundin ya yi kama da namu sai inda bambancin yake ita tana nazarin sana’ar Jima ne mu kuma muna nazarin sana’ar wanzanci da irin yadda ake kamuwa da wasu cututuka a sanadinta.

Hassana (2003), wannan d’alibar ta rubuta kundin mai taken “Sana’ar Fawa A Garin Gusau” wannan kundin ya yi muna amfani matuk’a saboda ta hanyarsa ne muka k’ara samun wasu ayyuka da suka gabata. Manazarciyar ta yi bayanin sana’ar fawa da yadda ake yinta da muhimmancin ta ga rayuwar al’umma tare da yadda take gudana a cikin garin Gusau a halin yanzu.         Wannan kundin yana da alak’a da namu sai dai mu namu yana kallon yadda ake kamuwa da wata cuta a sakamakon sana’ar. Ta rubuta wannan kundin ne domin samun takardar shedar kammala karatu a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau, Jihar Zamfara.

        Hauruna Umar Bungud’u(2009), ya rubuta muk’ala mai taken “Kakka’be K’ura da ‘Dauraya  A Cikin Magugungunnan Gargajiya Na Hausawa Da Yadda Ake Amfani Da Su” Bungud’u ya yi bayani a kan magungunnan gargajiya na Hausawa da yadda ake amfani da su, inda ya ce akwai na shafawa da na tofawa. Wannan Muk’ala ta taimaka ga aikinmu, saboda a namu aikin za mu yi tsokaci a kan cuta da kuma yadda ake samunta a sakamakon wani aiki na wanzamai.

Sallau (2010) ya rubuta wani littafi mai taken “Wanzanci Da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa” masanin ya tsara littafin nasa a kan tsarin babi-babi inda ya fito da babi biyar.

A babi na farko ya yi bayani a kan k’asar Hausa da mutanenta. A babi na biyu kuwa a nan ne ya kawo bayani a kan asalin sana’ar wanzanci da ire-irenta da matsayinta da kayan aikinta. A babi na uku kuwa ya yi bayanin sana’ar wanzanci da ta danganci cire gurya, hakin wuya da dai sauransu. A babi na gaba ya yi magana a kan aski da gyaran fuska. A babi na gaba ya yi bayani a kan K’aho da tsaga.

Bisa ga abin da muka gani a cikin aikin Sallau mun d’ibi na d’iba don mu gina namu kundi wannan ya nuna cewa aikinsa yana da alak’a da namu aikin. Sai dai kuma inda bambanci yake shi Sallau ya raja’a ne a kan sana’ar wanzanci mu kuma mun mayar da hankali ga yadda ake kamuwa da cututuka a sakamakon wannan sana”a.

2.0.2. Salo Da Tsarin Bincike


Salo shi ne hanyar da marubuci ke bi domin samun nasarar isar da sak’onsa ga masu karatu ko sauraro.

Idan aka ce salo to, ana nufin duk wata dubara da marubuci ko mai magana ya bi wajen isar da sak’onsa a cikin sauk’i.

Gusau (1993: 5), cewa ya yi. “salo shi ne hanyar da ake bi a nuna gwaninta da dubara a cikin furuci ko rubutu, kuma yana nuna yadda mutum ya shirya wani abu ta bin yanayin harshensa da za’bar abubuwan da suka dace game da abin da yake son bayyanawa.

A duk lokacin da aka yi maganar salo ana magana ne a kan irin k’warewar manazarci, wajen aikin bincike da kuma yadda yake jawo hankalin mai karatu a kan aikin da marubucin ya yi a kowane lokaci.

A wannan kundin dai za mu yi amfani da salo mai burgewa wajen aiwatar da wannan kundin ta yadda duk wani ya d’aga shi sai ya amfana matuk’a. Wannan ba ya rasa nasaba da irin ziyarar da za mu yi a wuraren da ake yin wannan sana’ar wanzanci, saboda tattara bayanai da suka shafi wannan kundin. Don haka muka yarda cewa dukkanmu za mu ziyarci masu wannan sana’a da muke aiki a kai don samun ingantacciyar hujja.

 

 

 

Babi Na Uku


3.0.1 Asalin Sana'ar Wanzanci


Yana da wuya a ce ga lokacin da aka fara yin sana'ar wanzanci, wannan kuwa ya faru ne saboda sana'a ce dadaddiya a k’asar Hausa. Kamar yadda ba a san lokacin da Bahaushe ya fara gashi a kai ba, haka da wuya a ce ga lokacin da dabarar aski ta zo masa (Bunza, 1990: 149-150). Amma a iya cewa, sana'ar wanzanci ta sarno asali ne ta la'akari da bukatun rayuwar d’an Adam. A dalilin tasowar bukatu sai ya k’irk’iro wa kansa hanyoyin da zai warware wannan matsala, saboda samuwar gashi a kai ya sa mutum tunanin neman hanyar da zai rage shi ko rabuwa da shi, domin ya sami sauk’i ya kuma ji dad’in rayuwarsa. Haka yake ga sauran ayyukan da wanzamai suke yi. A takaice a iya cewa ta wannan hanya ce sana'ar wanzanci ta same asali har ta bunkasa ya zuwa matakin da take a yanzu inda har wasu zuri'o'i suka mayar da ita sana'arsu ta gado.

 

 

 

3.0.2 Raben-Raben Wanzaman Hausawa


        Dangane da aiwatar da sana'ar wanzanci a k’asar Hausa a iya cewa, wanzamai sun kasu zuwa kashi uku kamar haka; wanzaman gado da wanzaman k’ok’o da kuma wanzaman jarfa.

3.0.2.1 Wanzaman Gado


Wanzaman gado su ne wad’anda suka gaji yin sana'ar wanzanci daga wajen mahaifansu, kamar yadda su ma mahaifan nasu suka gaje ta a wajen nasu mahaifan bayan sun zauna an koya masu yadda za su yi dukkan ayyukan wanzanci. Ire-iren wadannan wanzamai ne suke gadon gidajen da za su rik’a yin ayyukan wanzanci, kuma daga cikin su ne ake nad’a sarkin aski ko magajin aska. Idan bukatar aikinsu ta tashi, a mafi yawancin lokaci a gidajensu ake tarar da su don a sanar da su wuri da lokacin da ake buk’atar su je domin gudanar da ayyukansu. Kuma mafi yawancin wad’annan wanzamai za a tarar ba su da rainuwa, domin kuwa duk abin da aka ba su a matsayin ladar aikinsu sai su kar’ba suna murma da farin-ciki da godiya. Dalilinsu shi ne, suna yin aikinsu ba don kud’i ba sai don gado da taimakawa wa al'umma.

 

3.0.2.2 Wanzaman K’ok’o


Kashi na biyu na wanzaman Hausawa su ne wanzaman K’ok’o.Wanzaman K’ok’o ba sa yin dukkan ayyukan wanzanci, iyakar ayyukan da suke yi sun had’a da aski da gyaran fuska, akwai wad’anda kuma suke yin K’aho, Irin wad’annan wanzamai ne za a rik’a gani a kasuwanni da cikin garuruwa suna yawo da zabira rataye don neman wanda za su yi wa aski ko gyaran fuska. Haka kuma, suna yin rumfuna a kasuwanni ko shaguna a cikin garuruwa domin masu buk’atar aski ko gyaran fuska su rik’a tarar da su. Su dai wad’annan wanzamai suna yin wannan sana' a ce domin su sami hanyar abinci, kuma za a tarar mafi yawancinsu yaran wanzaman gado ne. A lokacin da suka yi wa mutum aski ko gyaran fuska sukan gaya masa adadin kud’in da zai biya. Akwai kirarin da ake yi wa irin wad’annan wanzamai kamar haka:

 

“Wanzaman k’ok’o a ci tuwo, a yi aski,

                   Cire belun-wuya da belun-mata sai’yan gado”

3.0.2.3 Wanzaman Jarfa


Kashi na uku na wanzaman Hausawa su ne wanzaman jarfa ko ‘yan tsaga. Ire-iren wad’annan wanzamai ne suke yi wa ‘yan mata tsagar kwalliya. Wad’annan wanzamai na yin k’ungiya tattare da matansu da 'ya'yansu su rik’a yawo gari-gari unguwa-unguwa suna sauka gidajen da ‘yan mata suke domin yi masu tsagar kwalliya. A lokacin da suke yin wad’annan tsaga suna yin kid’a da wak’a domin kuranta ‘yan mata maganin nuna kasala ko fargaba a lokacin da ake yi masu tsagar. Haka kuma suna yin zambo da habaici ga ‘yan matan da suka nuna kasala da jin tsoro a lokacin da ake yin tsaga. A wannan lokaci ne kuma wanzamai ‘yan jarfa a cikin kid’a da wak’ar da suke yi, za su rik’a kira ga ‘yan uwa da abokan arziki da samarin ‘yan matan da suka sauka a wurinsu da su rik’a kawo kari na nuna murnar ana yi wa ‘ya‘yansu tsaga wadda za ta k’ara masu kyau. A wannan lokaci ne ‘yan uwa da abokan arziki da samarin wad’annan ‘yan mata za su yi ta bayar da kyautar abubuwa wad’anda suka had’a da kud’i da abinci da sutura da dabbobi.

 

3.0.3 Gado Cikin Sana' ar Wanzanci


Kamar yadda aka fad’a a bayanan da suka gabata, ita sana'ar wanzanci ana gadonta ne wajen iyaye da kakanni na wajen uba.Wato da wuya a sami mutum wanda bai gaji sana' ar wanzanci ba yana yin dukkan ayyukan wanzanci. Haka a wajen yin ayyukan wannan sana'a gado na taka muhimmiyar rawa ta a zo a gani. Abin nufi a nan shi ne a wajen yin ayyukan wanzanci, kowane wanzami yana da gidajen da yake yi wa aiki. Wani wanzami ba ya zuwa gidan da wani yake yin aiki ya yi. Haka su ma masu gidajen da ake yi wa aikin wanzanci ba sa kiran wani wanzami wanda ba shi ne wanzaminsu na gida ba ya yi aiki. Al 'ummar Hausawa sun amince da wannan dole sai wanzamin da aka gada tun asali ko 'ya'yansa ko wanda ya amince ya yi ne kad’ai yake zuwa gidajensu domin yin ayyukan wanzanci a tsakanin iyalansu.

Wani tsari mai ban sha' awa dangane da yadda ake tafiyar da sana' ar wanzanci a k’asar Hausa shi ne, shi wanzami ba shi da iyakar k’asar da zai rik’a gudanar da ayyukansa.Yana iya fita daga garinsu ko k’asar dagacinsu ko hakiminsu ko sarkinsu, kai a wannan zamanin har jiharsu yana iya bari ya tafi wuraren da mutanensa suke domin yi masu aikace-aikacen wanzanci. Misali, idan Bahaushe ya auri Bafulata wadda ita a al'adarsu macen da ba ta ta’ba haihuwa ba idan ta sami ciki ba za ta haihu a gidan mijinta ba, sai dai ta tafi gidan mahaifanta goyon-ciki, to idan ta haihu ba mahaifanta ne za su kira wanzamin gidansu ya yi aikin ba. A nan hakkin mijinta ko mahaifansa ne su kira wanzaminsu na gida ya yi ayyukan, domin kuwa Hausawa na cewa, mace ba ta kiran wanzami sai namiji.

A wani lokaci takan kama a sauya wanzamin da aka gada, dalilin yin haka ya had’a da, idan wanda ake yi wa ayyukan wanzanci ya tashi daga garinsu ya koma wani gari wanda ke nesa da garinsu na asali, a wannan sabon gari da ya sauka idan ya buk’aci a yi masa ayyukan wanzanci, sai ya nemi wani wanzami don ya yi masa. Daga wannan lokaci wannan wanzami ya zama wanda zai rik’a yin ayyukan wanzanci a gidansa, sai kuwa idan ya sake tashi daga wannan gari ko kuma idan wani laluri ya faru a tsakaninsu.

Haka kuma, idan wanzamin gidan ya rasu ko wata lalura ta rashin lafiya ta same shi, kuma ba shi da mai yin gadonsa, to ya zama dole ga wad’anda yake yi wa aikin wanzanci su sami wani wanda zai maye gurbinsa. Daga nan shi ma wanda ya maye gurbin ya zama wanzamin wannan gida, sai kuwa idan wata lalura ta shiga a tsakaninsa da masu wannan gida, misali sa’bani ko rashin fahimtar juna da sauransu.

Idan ba ta wad’annan hanyoyi da aka yi bayaninsu ba, matuk’ar wani wanzami ya yi wa wani wanzami dan uwansa cin iyaka a gidajen da yake yin ayyukansa, to ‘barma na iya faruwa a tsakaninsu. Domin kuwa kowane daga cikinsu zai yi ta k’ok’arin yin ire-iren surk’ulle da tsatsube-tsatsuben da ya iya don ya nakkasa abokin hamayyarsa ko ya ‘bata aikinsa.

3.0.4 Matsayin Sana'ar Wanzanci


Kowane irin al' amari wanda ya danganci yadda d’an’Adam yake tafiyar da rayuwarsa yana da irin nasa matsayi a idanun masu yin sa da wad’anda ake yi wa. Wannan ne ya sa aka ga ya dace a duba matsayin sana’ar wanzanci a al’adance da a addinance da kuma a zamanance.

 

3.0.4.1 Sana' ar Wanzanci a AI' adance


Sana'ar wanzanci tana da babban matsayi a al'adar Hausawa wannan kuwa ya faru ne saboda ire-iren muhimrnan ayyukan da wanzamai suke aiwatarwa. Haka kuma al’ummar Hausawa suna girmama wanzamai, wannan ne ya sa Alhaji Sale Gambara a cikin bakandamiyarsa yake cewa, “a duk gari akwai manya uku wad’anda su ne kamar haka; shugaban da yake jagorancin mutanen garin, sai limamin garin daga nan sai wanzamin garin”. Haka kuma a fannonin adabin Hausawa akwai wurare da dama wad’anda aka bayyana muhimmancin wannan sana'a. Misali, a cikin littafin da Alhaji Nuhu Bamalli ya rubuta mai sunan "Mungo Park Mabudin Kwara", wanda aka yi bayani a kan tafiye-tafiyen Mungo Park a sassan Afrika ta Yamma a shafi na 42-43 an yi .bayyanin inda wannan matafiyi ya bayyana ya zama wanzam.

Haka su ma mak’wabtan k’asar Hausa suna bayyana muhimmancin wanzami a idon Hausawa. A iya ganin haka a wak’ar da ‘Dan'anace ya yi wa Shago inda yake cewa:

"Dan Abdu Gazaguru,

Ai na hwad’a maka goga,

Wanga kashi da kay yi ba dawa ne ba,

Kar ka kashe Na'ila wanzami na,

Ai shi ka yo muna gyara, ... "

Kuma kasancewar wanzaman gargajiya masana tsubbace-tsubbace da sihirce-sihirce ne masu ban mamaki da al’'ajabi da ban tsoro ya sa al 'ummar Hausawa suke d’aukar su kamar wasu dodanni ko wasu mutane da ake tsoro. Wannan ne ma ya sa ba a yi wa wanzamai gardama ko gatse ko shisshigi dangane da yadda suke aiwatar da ayyukansu, don tsoron kar su yi wa mutum wani abu da zai cuce shi. Haka kuma al 'ummar Hausawa sun d’auki wanzamai a matsayin wasu mutane masu bayar da taimako idan wata lalura ta rashin lafiya ko bukatar maganin gargajiya ta taso. A nan ma makad’an Hausawa sun bayyana irin rawar da wanzamai suke takawa wajen yin ire-iren wad’annan tsatsube-tsatsube. Misali, a wak’ar da Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa Ciroman Aski na Jalingo ya bayyana irin yadda wanzamai suke harbin 'yan'uwansu a lokacin da suka zo yin aski sai su rik’a yin kyarmar hannu wadda take yin dalilin a rik’a yankar wanda ake yi wa aski. Ga irin yadda ya bayyana haka cikin wannan waka:

"Ga wani ya zo aski,

Sun harbai hannu nai na karkarwa,

Da ya zo gun aski,

Sai na ga jini na ta zubowa ... "

Haka kuma karin maganar Hausawa ya kara fito da

matsayin wanzami a idon Hausawa kamar haka:

“Kowa ya ci ladar kuturu, dole ya yi masa aski.

Ku shekarar jaki, sai wanzamin kura.

Wanzami ba ya son jarfa”.

Wad’annan dalilai ne suka sa al'ummar Hausawa suke matukar kyautata wa wanzamai da dukkan abin da ya dace na kyautatawa, kuma kowane mutum ya yarda da dukkan ayyukan wanzanci, ana yi masa da dukkan iyalinsa. Idan buk’atar aikin wanzami ta kama matukar bai zo lokacin da ake buk’atar ya zo ba, ana tarar da shi har gidansa don a gani ko lafiya? Wannan dalili ya sa yin ayyukan wanzanci a wurin Hausawa a jiya wani al'amari ne wanda ya zama dole a yi shi.

3.0.4.2 Wanzanci a Addinin Musulunci


Idan muka duba sana’ar wanzanci ta fuskar addinin Musulunci za mu ga cewa, akwai makusanciyar dangantaka a tsakanin wannan sana’a da addinin Musulunci. Wannan kuwa ya faru ne saboda muhimmancin wannan sana’a ga rayuwar mutum tun daga farko rayuwa har ya zuwa wannan zamani don kuwa kowane mutum yana da buk’ata gare ta Domin kuwa yana da wuya kowane mutum ya wadatar da kansa da iyalansa daga yin aski da sauran ayyukan wanzanci. Hukuncin sana’ar wanzanci a shari’ar addinin Musulunci aiki ne da wani ka iya d’auke wa wani. Domin ya wajaba a cikin kowane gari a sami wanzamai masu yin sana’ar aski da sauran ayyuka. Idan kuwa ba a samu ba, to a hak’ik’a mutanen wannan gari sun fad’a a cikin kuskure. Shehun Malami Abdullahi Fodiyo (Allah Ya k’ara yarda da shi), ya ce," rashin wanzami a cikin gari zai tilasta wa kowane mutum ya tafi neman mai aski, haka kan sa mutum cikin tsanani da gajiya da dakatar da yin ayyukansa na yau da kullum" . Ya cigaba da cewa " idan wannan sana’a ta yawaita a gari, to za ta yawaita a sauran garuruwa.Wannan ne zai sa yawancin mutane su daina barin ayyukansu na yau da kullum domin neman wanzami" (‘Danfodiyo, Ba Ranar Bugu: 23). Saboda haka ne addinin Musulunci yake kwad’aitar da mutane su rik’a yin irin wannan sana’a. Wannan malami kuma ya nuna wajibi ne ga dukkan mai yin wannan sana’a ya zama mai neman ladar lahira fiye da abin da zai samu na duniya, domin shi arziki ba a iyakance shi ta hanya d’aya ba. A aikata dukkan ayyuka da kyakkyawar niyya domin a sami lada. Shari’a ta bayyana babu bambanci a tsakanin ibadar mutum da tasarrufinsa (wato mu'amalolin rayuwarsa na yau da kullum), domin komai ga Allah yake komawa.

Wani al'amari da yake kara bayyana muhimmin matsayin da sana’ar wanzanci take da shi a addinin Musulunci shi ne, wannan sana’a tana zama hanya ce ta tsayuwa a kai da yawa daga cikin Sunnonin Annabi, tsira da amincin Allah su k’ara tabbata a gare shi. Ga wasu daga cikin abubuwan da sunnar Annabi ta yi ummurni Musulmi su dinga yi kamar haka:

  • Yin kaciya.

  • Aske gashin mara.

  • Tsige gashin hamata.

  • Yanke farce.

  • Aske gashin baki (Al-Bukhari.Ba Ranar Bugu :38).

  • Yin k’aho (Ba Ranar Bugu: 11).

  • Tsayar da gemu (‘Danfodiyo,1986 :199).

  • Aske gashin kai (Gumi,1979 : 782-783, Bn Arabi,1972:1709).


A takaice a iya cewa, sana’ar wanzanci tana da babban matsayin a addinin Musulunci domin kuwa hanya ce ta kyautata kiwon lafiya da kuma bin wasu sunnoni na Manzon Allah (SAW) wad’anda suka yi horo da a tsabtace jiki.

3.0.4.3 Sana'ar Wanzanci a Zamanance


Sallau dai a cikin kundinsa ya bayyana muna cewa, a fassarar da aka samu a cikin shahararren kundin nan mai suna "Encyclopedis Britannica vol. 1 (1989:887), an fassara wanzami a matsayin mutum wanda yake yi wa mutane aski da gyaran fuska da aske gashin baki. An k’ara da bayyana cewa a k’asashen da a yau ake kira Turai shekaru d’ari shida da suka gabata, wanzamai na yin ayyukan fid’a da tiyata da sauransu kamar ire-iren ayyukan da likitocin zamani suke yi a yau. Don kuwa a wancan zamani an sami wani wanzami mai suna Ambroise Pare wanda yana daga cikin mutanen farko wad’anda suka k’irk’iro hikimar yi wa marar lafiya aikin fid’a don a fitar da cutar da take cikin jikinsa. Haka kuma a Faransa an kafa doka wadda ta bayyana cewa, dukkan wanda yake yi wa shugaban wannan k’asa aski da gyaran fuska, to shi ne shugaban k’ungiyar masu yin aski da tiyata na wannan k’asa. Wannan tsari ya yi kama da irin yadda ake yi a k’asar Hausa, don kuwa dukkan wanzamin da yake yi wa sarki aski shi ne shugaban dukkan wanzaman da suke a wannan k’asa.

A dai cikin wannan kundi an sami k’arin bayanin da ya bayyana cewa, a lokacin da ya gabata a k’asashen Turai, ana yi wa wanzamai lak’abi da sunan “likitoci masu gajerar igiya”, Ana kuma yi wa likitoci wad’anda suka koyi ayyukan fid’a da tiyata a makarantu da jami’o’i lak’abi da sunan “likitoci masu doguwar igiya)”. An k’ara da bayyana cewa, a lngila, sai a cikin shekara ta 1745 ne aka raba ayyukan fid’a tsakanin wanzamai da likitocin zamani, don kuwa kafin wannan shekara ayyukan da suka danganci fid’a da tiyata suna yi ne tare.

Saboda haka, a iya cewa a k’asar Hausa ma sana’ar wanzanci na da babban matsayi a wannan zamani domin kuwa a kowane k’auye ko birni da mutum ya ziyarta zai tarar da wuraren da ake yin aski. A wasu wuraren ma za a tarar da shaguna ne wad’anda aka k’awata domin yin aski da saisaye. A nan za a tarar mafi yawancin masu yin askin ba wad’anda suka gaji yin wannan sana’a ne ba, suna yin ta ne domin samun hanyar abinci. Haka kuma samun hikimar yin kaciyar sa-wandonka da wanzarnai ke yi ya sa al’ummar Hausawa a wannan zamani sun mayar da hankalinsu wajen yi wa ‘ya’yansu irin ta, Wannan ne ya sa a yanzu mafi yawancin mutane ba sa kai ‘ya ‘yansu asibiti domin a yi masu kaciya, sai dai su kira wanzamin gargajiya mai yin irin wannan kaciya domin ya yi wa yaran.

3.0.5 Kayan Aikin Yin Wanzanci


Wanzamai na amfani da kayayyaki iri daban-daban domin yin ayyukan wanzanci. Ire-iren wad’annan kayayyaki sun had’a da askar aski da almakashi da sabulu da kwanon aski da kalaba da koshiya da ‘yar tsaga da hantsaki da tankolo da zabira da karkiya da ‘yankara da jijiya da k’aho da kura ta cire hakori.

3.0.5.1 Askar Aski


Askar da ake amfani ita wajen yin aski karama ce madaidaiciya, tsawonta bai kai kamu d’aya ba. Akwai bambanci tsakanin wadda ake askin jarirai da wadda ake yi wa manya aski. Ta askin jarirai ba ta kai girman wadda ake yi wa manya aski ba. Da kuma askar aski ake amfani wajen yin kaciya, ana amfani ne da irin wadda ake yi wa manya aski wato mai kaifi da nauyi wajen yin kaciya. A halin yanzu ana amfani da askar aski iri uku, akwai ta asali ta bak’in k’arfe. Irin wannan aska ita wanzamai suka gaji amfani da ita, kuma mak’eran Hausawa ne suke samar da ita ga wanzamai. (Sallau, 2010).

Bisa ga wannan bayani da Sallau ya yi za mu cewa ya bayyana muna dukkan yadda wannan askar da ake aski da ita yake kana ya fad’a muna tsawon ta yadda duk inda mutum ya ganta za iya gane wannan aska.

 

3.0.5.2 Dutsin Washin Asaken Aski


Dutsin washin asaken aski dutsi ne karami mai sul’bi da ake amfani da shi domin yin washin asaken aski idan kaifinsu ya dak’ushe, wato kaifinsu ya ragu. Idan kuwa kaifinsu ya dak’ushe duka, to sai a kai ga mak’eri mai kud’ar

asaken aski domin a sake kod’a su. Ana amfani da dutse ta hanyar goga askar samansa sannu a hankali har sai an tabbata askar ta wasu. Hanyar da ake gane aska ta wasu ita ce, sai a dan fera fatar hannu, idan askar ta fere fatar sosai aska ta wasu ke nan. Akwai duwatsu iri uku da ake amfani da su wajen wasa asaken aski. Na farko shi ne na gatarin aradu, wato dutsen da ke fadowa idan an yi tsawa lokacin ruwan damina. Hanyar da ake bi domin samun dutsen gatarin aradu ita ce, da zarar an yi tsawa, aka kuma yi dacen ganin wurin da ta fad’i sai a yi gaggawa a je a zuba madara ko nonon shanu a wurin da tsawar ta fad’i, idan an tona sai a tarar da dutsin domin madarar ko nonon da aka zuba zai hana shi yin k’asa da nisa.

Dutsi iri na biyu da ake amfani da shi dornin washin asaken aski shi ne, na k’ank’ara mai sul’bi wanda ake samu a kogi ko wurin da ke da duwatsu.

Dutsi na uku da ake amfani da shi domin washin asaken aski shi ne wanda Turawa suka yi domin washin alluran asibiti, Saboda yanayinsa ya yi kama da wanda ake washin asaken aski sai wanzamai suka rik’a amfani da shi domin yin washin asaken aski.

3.0.5.3 Fatar Washin Asaken Aski


Fatar wasa asaken aski fatar dabbobi ce ake samu daga wajen dukawa wadda aka jeme. Ana amfani da mai fad’in misali inci d’aya da rabi, tsawonta kuma misalin inci goma sha biyar zuwa ashirin. An fi amfani da mai kauri irin tamanyan dabbobi domin kuwa ta fi inganci da k’ara wa aska kaifi.

Amfani fatar washin asaken aski shi ne, idan aka wasa askar aski da dutsi kaifinta ba zai kai sosai ba sai an wasa da fata. Ana shafa ruwa ga fatar sai a bi da askar ana shafawa bisa fatar sannu a hankali. Wannan ne zai daidaita kaifin askar yadda idan an zo yin aski askar za ta tuje gashin da sauki. Mafi yanwancin wanzamai na d’ora fatar wasa  asaken askin ga zabira daga gefe.

3.0.5.4 Almakashi


Almakashi ana amfani da shi ne wajen gyara tsawon gemu da gashin baki da saje, ko kuma don yin saisaye, Shi ma almakashi akwai iri biyu; na farko shi ne na gargaiiya wanda mak’eran gargajiya suka k’era amma a yanzu ba irin wannan almakashi da yawa.

Almakashi na biyu kuwa wanda wazamai suke amfani da shi Turawa suka kawo shi k’asar Hausa, a halin yanzu mafi yawanci wanzamai da shi suke amfani.

3.0.5.5 Sabulun Aski


Wanzamai na amfani da sabulu wajen yin aski ko gyaran fuska domin a rage wa suma k’arfi, Bayan an shafa wa suma ruwa sai a bi da sabulu a goga ko’ina. Ana yin haka ne domin sumar ta yi taushi yadda za a ji dad’in askinta. Kafin zuwan sabulun Turawa wanzamai na amfani da sabulun toka ko sabulun salo wajen yin aski, amma a yanzu da sabulun Turawa ake amfani.

 

3.0.5.6 Kwanon Aski


Kwanon aski ana amfani da shi ne domin zuba ruwan da za a rik’a amfani da shi wajen yin aski da gyaran fuska da kaciya da tsaga. A da can kafin zuwan Turawa, wanzamai na amfani da k’ok’o ne domin zuba ruwan aski. Wannan ne ma ya sa ake kiran wanzaman da suke yin aski da gyaran fuska da sunan “wanzaman k’ok’o”. A halin yanzu ana amfani da kofin roba ko na k’arfe domin zuba ruwan aski.

3.0.5.7 Kalaba


Kalaba k’arfe ne k’arami wanda tsawonsa misalin inci shida ne zuwa bakwai, kuma ba shi da kauri sosai. Mak’era ne suke k’era kalaba, ba kuma dukkan mak’eri ne yake k’irar kalaba ba, akwai mak’era na daban masu k’era ta. Ana yin ta ne da kaifi a gefe d’aya na kanta sai a lankwasa kan ya zamo kaifi ciki. A kan yi wa gindinta kauri domin a ji dad’in rik’ewa idan za'a yi aiki da ita. Amfanin kalaba wajen ayyukan wanzanci shi ne a rik’a cire belin- wuya da ita.

3.0.5.8 Koshiya


Koshiya wani d’an icce ne k’arami ake sassak’awa da d’an fad’i ga kai da kuma kauri ga k’asansa. Tsawon koshiya misali inci shida ne zuwa bakwai, fad’in kanta kuma bai iyar da kai inci d’aya ba. A takaice tsawon koshiya d’aya yake da na kalaba. Ana amfani da koshiya wajen ayyukan wanzanci domin taushe harshen jariri a lokacin da za a cire belun-wuya. Ita koshiya masassak’a ne suke samar da ita ga wanzamai, akwai kuma wasu wanzamai da suke iya sassak’a koshiya.

3.0.5.9 'Yartsaga


‘Yartsaga aska ce k’arama da mak’era suke k’erawa, tsawonta ya kai misalin inci hud’u zuwa biyar, kanta kuma ana yin sa da fad’i da tsini da kaifi. Wasu mak’era na amfani da k’usa inci hud’u ko inci biyar domin yin ‘yartsaga. Ana amfani da ‘yartsaga wajen ayyukan wanzanci domin yin wasu ayyukan da wanzamai suke yi a farjin mata kamar cire angurya da yanke linzami da cire hak’oran shuwa. Ana kuma amfani da ita domin yin tsagar gado da ta magani da kuma ta kwalliya.

3.0.5.10 Hantsaki


Hantsaki karfe ne da makera suke Rerawa da baki a gindi da kuma tsini a kai. Ba shi da kauri sosai, kuma tsawon sa misalin inci hudu ne. Ana amfani da hantsaki wajen wanzanei domin cire angurya a farj in mata.

3.0.5.11 ‘Yankara


‘Yankara sullen karan dawa ne ake samu a yanka guntu-guntu. Ana samun sulle madaidaici domin yanka ‘yankara. Ana yanka kowane guntu misalin tsawon inci d’aya, Ana amfani da ‘yankara ne a wurin kaciya inda ake rarake uku a saka zare a cikin kowane sai a k’ulla zaren yadda ‘yankaran za su yi kusurwa uku, daga nan sai a rataya wurin kaciya tsakanin azzakarin yaron da ‘ya‘yan golayensa. Amfanin ‘yankara wurin kaciya shi ne su raba azzakarin aron da ‘ya’yan golayensa yadda kaciyar za ta rik’a samun iska, kuma ba za ta rik’a likewa da ‘ya‘yan golayen ba. Wannan na taimakawa wajen saurin warkewar kaciya. Wanzamin da ya yi kaciya ne ko yaransa kan yanka ‘yankara.

3.0.5.12 Karkiya


Karkiya karan dawa ne mai k’wari ake samu a yanka tsawon misalin inci goma sha biyar zuwa inci ashirin. Ana amfani da karkiya ne ga yaron da aka yi wa kaciya lokacin da zai kwanta barci, sai a d’aurata wurin cinyoyinsa domin maganin kar ya manta ya had’e kafafuwansa su matse kaciyar ya yi fami. Ita karkiya wasu wanzamai ne suke yanka ta su ba iyayen yaron da aka yi wa kaciya, wasu iyayen kuma kan yanka karkiya da kansu.

3.0.5.13 K’aho


Wanzamai na amfani da k’ahon sa ne domin yin k’aho. Ana amfani da k’aho madaidaici wanda ba mai girma k’warai ba, kuma ba k’arami ba. Ana yanka misalin tsawon inci biyar ko shida. Ana yi wa wajen tsininsa ‘yar k’aramar k’ofa. Ana amfani da k’aho ne domin yin k’aho da kuma yin k’ahon anhul. Mahauta ne suke samar da k’aho ga wanzamai, su ne suke fitar da shi daga kan san da aka yanka sai su sayar wa wanzaman da suke yin k’aho.

3.0.5.14 Jijiya


Wanzamai na amfani da jijiyar agarar k’afar akuya ko tunkiya domin a rik’a like kofar tsinin k’ahon da a aka kafa wa mutum domin ya like wurin da aka kafa shi a jikin mutum. Wanzamin zai sanya wannan jijiya a cikin bakinsa yana taunawa sai ya lika ta a wurin k’ofar, da an lika shi ke nan sai k’ahon ya like a wurin da aka kafa shi, ba zai fita ba sai an cire wannan jijiya. Ita ma jijiya mahauta ne suke samar da ita ga wanzamai.

3.0.5.15 KuraTa Cire Hak’ori


Ita kura k’arfe ne ake samu domin cire hak’or, yanayinta ya yi kama da abin da kafintoci suke cire k’usa amma ita kura ba ta kai girman abin cire k’usa ba. Wanzamai na amfani da kura ne domin cire hak’ori mai ciwo ko mai girgid’a.

3.0.5.16 Tankolo


Tankolo ‘yar jika ce wadda dukawa suke d’unkawa da fatar akuya ko tunkiya domin wanzamai su rik’a sanya askar aski d’aya ko kuma babba wadda za a sanya asaken aski masu yawa.

3.0.5.17 Zabira


Zabira jikka ce babba mai aljihuna da yawa misali uku ko hud’u. Ana yi mata maratayi dornin a rik’a ratayawa. Ita ma dukawa ne suke d’unka ta da fatar akuya ko tunkiya domin yi wa wanzamai jikar da za su rik’a sanya dukkan kayan aikin wanzanci wad’anda aka yi bayaninsu a baya.

 

Babi Na Hud’u


4.0.1 Tsokaci A Kan Wanzamai A Garin Gusau


Wanzamai a garin Gusau kamar yadda bayanai suka gabata, wanzanci sana’a ce mai asali kuma ana gabatar da wannan sana’a kamar yadda aikin wanzamai ya tanada. A garin Gusau kamar sauran garuruwa akwai wanzamai kuma sukan yi aski da sauran ayyukan da wanzamai ke yi. Kuma ana iya samun wanzamai a ko’ina a garin Gusau duk da cewa a yau an samu ci gaba an bar hanyar gargajiya, amma har wa yau ana samun wanzamai jefi-jefi a garin na Gusau.

Kasancewar garin Gusau gari ne ke da Hausawa masu tarin yawa kuma masu rik’o ga al’adun Hausa ya sa har yau ba su yi watsi da wasu al’adu ba, daga cikin al’adun da ba su yi watsi da su ba sun had’a da wannan sana’a ta wanzanci. Ko da yake ba su yi watsi da sana’ar wanzanci ba, amma sun sauya tafiya sana’a domin kuwa sun saka wasu bak’in abubuwa a ciki. Wannan ba wani abin mamaki ba ne saboda sauyin zamani ya sa suka surka sana’ar da wasu abubuwa.

Wanzamai a garin Gusau suna yi wa sana’ar ta su rik’on sakainiyar kashi, dalili kuwa shi ne za ka iya samun wanzami a kan sana’arsa amma ba ya da wasu abubuwa na aikin sana’ar da za su taimaka wajen samun gamsuwar wanda za a yi wa aikin wanzancin. Abin da muka nufi a nan shi ne. ya dace a iske wanzami yana da dukkan kayan aiki kuma ya nak’alci aikinsa gwargwadon iyawarsa tare da tsabtace kayan aikinsa don gudun kar wata cuta ta yad’u a sakamakon wannan sana’a.

Da wannan ne muke kira ga wanzamai na gargajiya kai har ma da na wannan zamani da su rik’a kula da kayan aikinsu ta hanyar tanadar duk wani abu da sana’ar take buk’ata kuma da yadda ya dace a yi aiki da shi tare da tsabtace kayan aikinsu ta yadda sai wanda za a yiwa aiki ya gamsu cewa ba za saka masa wata cuta ba a yayin da ake gudanar da wani aiki na sana’a a kansa.

4.0.2 Amfanin Wanzamai a Garin Gusau


Sanin jama’a ne cewa a ko’ina aka ga wanzami to yana da rana kuma wannan sana’a ta shi abar so ce ga jama’a. kamar yadda aka sani ne cewa wanzami dai yana taka muhimmiyar rawa a kowace al’umma haka nan a al’ummar garin Gusau wanzami yana da muhimmiyar rawa da yake takawa ga al’ummar garin Gusau. Daga cikin amfani da wanzami yake yi ga al’umma akwai:

4.0.2.1 Yin Aski


A ruwaitowar Bashir Sallau ya bayyana cewa a al’adar Hausawa idan aka yi wa babban mutum aski sau a zubar da sumar da aka aske. Idan kuwa jariri ne ana watsa wannan sumar a saman d’akin jinka. Wasu kuwa na nad’a laya da sumar sai su d’aura wa yaron wai don gudun bakin mutane.

Amma kuma da addinin musulunci ya zo sai aka watsar da wannan hanya aka rik’a aiwatar da abin kamar yadda addini ya tanada ga mabiya. Bayan zuwan musulunci an umurci duk wanda ya yi aski to ya rufe wannan suma da aka cire masa. Idan kuwa jariri ne aka yi wa aski ranar suna akan auna wannan suma tasa a kan sikeli sai a yi sadaka da kud’i kwatankwaci wannan sumar, kana daga baya sai a ba iyayen jaririn su je su rufe.

Wannan nau’in aikin wanzanci yana daga cikin ayyuka masu amfani ga jama’a, don haka al’ummar garin Gusau tana amfana da wannan aikin na wanzamai da suke a garin.

4.0.2.2 Kaciya.


Har yau a garin Gusau kamar sauran k’auyuka ana yin wannan kaciya, kamar yadda muka gani a cikin aikin Suleman Bawa (1984) ya bayyana k’arara cewa, wanzamai suna yin aikin kaciya ga yara. Ya bayyana cewa, kaciya dai ita ce, “yanke ko cire fatar da ta rufe azzakarin mutum”. Kamar dai yadda aka sani a k’asar Hausa wanzamai ne suke yin kaciya kuma sun fi yin ta a lokacin sanyi. A tunanin malam Bahaushe dai wannan lokaci da ya za’ba na sanyi lokaci ne da jikin mutum ya fi sauri tofowa wato saurin warkewa.

A wannan gari na Gusau ana samun wanzamin da zai tara yara a kowace shekara a lokacin sanyi sai a yi masu kaciya. Wannan ya danganci yara da d’an yawa ba wai na gida d’aya kacal ba ana iya tara yaran gidaje da dama sai a yi masu wannan kaciya. Bayan sun warke kuma za a yi wani d’an k’warya-k’waryan buki don yaye wad’annan yara da aka yi wa kaciya. Da wanna muna iya gano cewa wanzamai suna taka rawa mai amfani a garin Gusau.

 

 

4.0.2.3 Cire Gurya


Gurya dai wani tantanin nama ne da ake haihuwar mata da shi, a cikin farjinsu wasu kuma sai sun girma yake fito masu. Idan ba a samu an cire wannan gurya ga mace ba yana iya mace saduwa da namiji idan ta girma. Wanzamai na iya gane mata masu gurya idan suka zo cire masu beli ko hakin-wuya. A nan ne idan budurwa ce sai su binciki farjinta su ga idan tana da gurya sai su cire shi. (Liman 1982)

Irin wannan aiki da wanzamai suke yi yana da tasiri sosai kuma ana yin irinsa a garin Gusau a wancan lokaci kai har ma a wannan lokaci ana cire gurya. Shi ma wannan idan muka duba za mu ga cewa, wannan aiki na wanzamai yana da amfani musammam ga wanda ya ke da wannan ciyo

4.0.2.4 Cire Hakin – Wuya


Wannan shi ma wani nau’in aikin wanzamai ne da suke yi ga wanda yake da wannan ciyo. Hakin wuya wani ciyo ne da yake fitowa ga yara akasari kuma wannan ciyon yana saka su yawan yin amai duk wani abu da suka ci yana k’asa.

Akan gayyato wanzamai su cire wannan hakin-wuyan saboda su samar wa mai wannan ciyon sauk’i. Wanzami shi ne ke zuwa ya duba ya ga in yaro ko yarinya tana da shi sai ya tanadi kayan aikinsa ya fara gudanar da aikin.

Irin wannan aiki mai matuk’ar muhimmanci yana da kyau kuma ana gudanad da shi a wannan gari na Gusau, wannan ya su muke ganin aikin cire hakin-wuya yana da matuk’ar amfani da al’ummar garin Gusau.

4.0.2.5 Bayar Da Magunguna


Wanzamai na bayar da magani a sha a yi wanka ko su gudanar da wani aiki da ake k’aruwa da shi ta fannin lafiya kamar dai tsaga, bayar da garin magani a sha da tanade-tanade da dama.

A garin Gusau su ma ba a bar su a baya ba, saboda suna kar’bar magani ga wanzamai kuma wannan magani yana biyan buk’ata. Don haka muke ganin wannan nau’in amfani a matsayi wani abu na amfani al’ummar garin Gusau

 

 

4.0.3 Tsokaci a Kan Cututuka


Idan aka yi magana a kan cuta za a ga cewa ita cuta tana nufin zalunci idan aka ce wane ya fara cuta ko aka ce ya iya cuta ko kuma macuci to duk dai ana nufin azzalumi kenan.

A magance kuwa, cuta tana nufin rauni da rad’ad’i tare da wahala da mutum kan gamu da su a sanadiyar gazawar wata halitta a jiki ko kuma damuwa a zuci. (M.T. Adamu 1998).

Cututukan da ake iya yad’awa a sanadiyar sana’ar wanzanci sun had’a da; ta hanyar aski da duk wani aiki da za iya yi da aska kamar kaciya da tsaga da k’aho da cire Gurya da dai sauransu. Bincike ya gano cewa ana iya sark’uwa da wasu cututuka ne a sanadiyar wad’annan hanyoyi da aka lisafa. Ana d’aukar wad’annan cututuka ne yayin da aka yi wa wani wanda yake d’auke da wata cuta a saka wa wani ta hanyar yi masa amfani da kayan da aka yi wa mai d’auke da cutar sai ya kamu da irin wannan cutar.

Ana d’aukar ire-iren wad’annan cututuka wato kamar; Kureci, kyasfi, makero, k’urajen aski, soli, k’azuwa, kai har ma da cuyon nan mai karya garkuwan jiki wato (HIV Aids) da dai sauransu.

Ba wad’annan kad’ai ake iya d’auka ba a sana’ar wanzanci ana iya d’aukar duk wata cuta da ake iya kamuwa da ita musamman cutar da ake iya d’auka a sakamakon cud’anya da al’umma.

4.0.4 Hanyoyin Da Suka Dace a Bi Don Kauce Wa Yad’a Cututuka.


Hausawa na cewa, lafiya jari, wannan ya sa ya zama wajibi ga duk wani mutum mai hankali da ya kasance yana mai kula da lafiyarsa da ta iyalinsa in har yana da su. Kula da lafiya yana da matuk’ar muhimmanci. Don haka idan aka ga mutum yana kariyar lafiyarsa ta ya kamata a bashi goyon baya ba wai a tsarge shi ba.

Wasu masu sana’o’i na gargajiya da mu ke da su a k’asar Hausa sukan had’u da tsarguwa ta k’ama daga wasu kad’aitattun mutane, ta hanyar k’yamarsu da kuma sana’arsu. Wannan yana faruwa ne, idan mai wannan sana’a bai gyara jikinsa ba ko ya gyara kayan aikinsa.

Hanyoyin da ya dace mai sana’ar wanzanci ya bi domin gyara sana’ar sa da kuma tsare lafiyarsa da ta wanda yake yi wa aikin da ya danganci sana’arsa sun had’a da:

  1. Tsabtace jikinsa: wato mai sana’ar wanzanci ya kasanace a cikin tsabta ya saka sutura mai kyau ya kuma kasance a cikin natsuwa.

  2. Tsabtace Kayan Aikinsa: a nan ana buk’atar mai sana’ar wanzanci ya san hanyar da zai bi ya tsabtace kayan aikinsa wato ya tanadi wasu sinadarai da za su iya kashe kowace irin cuta da askarsa kan iya d’auka daga jikin wani wanda ya yi wa aiki. Irin wad’annan sina darai akwai na zamani da ake amfani da su kuma akwai na gargajiya.


Akwai hanyoyi guda biyu na tsabtace kayan aiki da suka had’a da: amfani da maganin sipirit. Idan ya samu sipirit d’insa sai ya rik’a amfani da shi yana goge asakensa da ya yi amfani da su bayan ya gama amfani da su.

Hanya ta biyu kuwa ita ce, ta amfani da wuta kamar laita (k’yastu) ya kuna ya k’one duk wata cuta da askarsa ta d’auko daga wani kafin ya yi wa wani amfani da ita.

Idan masu wannan sana’a suka yi amfani da wannan hanya to lallai za su rage yad’uwar cututuka a cikin jama’a kuma wad’annan da suke k’yamar sana’ar su za su samu gamsuwa cewa, wannan sana’a ta su tana da mahimmanci sosai don haka za su martaba wannan sana’a.

 

Babi Na Biyar


5.0.1 Jawabin Kammalawa.


A wannan babi kamar yadda aka riga aka sani nan ne za mu kammala wannan bincike da muke gidanarwa. Kamar dai yadda aka gani mun kasa wannan kundi zuwa gida biyar. Yayin da muka yi amfani da babi – babi har babi biyar. A babi na farko da na biyu mun yi abin kamar yadda dokar makaranta ta tsara muna. A babi na uku da na hud’u kuwa mun yi shi kamar yadda mai dubawa ya tsara muna. Shi kuma bai na biyar nan ne kuma kammala wannan aikin bincike namu.

Baya ga gabatarwa ta gaba d’aya da muka yi a a babi na d’aya inda muka fad’i dukkan abin da za mu gudanar a wannan kundi mu kuma shiga a cikin babi na biyu inda muka yi nazarin wasu ayyuka da magabata suka yi wad’anda suke da alak’a da kuma bambanci da namu aikin. Binciken da wani masani ya yi mai suna malam Bashir Aliyu Sallau shi ne ya taimaka muna wajen samun wasu hujjoji da za mu gwada mu kuma gina namu aikin. Ba na shi kad’ai ba mun d’auki wasu da muke ganin suna da alak’a da namu aikin muka yi amfani da su.

A babi na uku kuma nan ne aikin ya mayar da hankali yayin da muka kawo bayanai da dama da suka danganci sana’ar wanzanci. Bayanan da muka kawo sun danganci, ma’anar sana’ar wanzanci da kayan aikin wanzanci da kuma muhimmanci sana’ar wanzanci. Daga cikin aikin mun kawo asalin sana’ar wanzanci yayin da muka bayyana cewa babu wanda zai ce ga lokacin da ka fara sana’ar kamar yadda farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya fad’a cewa kamar yadda mutum bai san lokacin da suma ta fito a kansa ba haka nan bai iya fad’an lokacin da aka fara sana’ar ta wanzanci. Kayan aikin da muka kawo suna da yawa, daga cikinsu akwai aska da kwanon aski da jijiya da almakashi, dutsen washi da fatar washi da sabulu da koshiya, da kalaba da ‘yartsaga, da hantsaki da karkiya da ‘yankara da dai sauransu.

A babi na hud’u kuwa mun mayar da hankali ne ga wanzamai na garin Gusau da yake nan ne muhallin aikinmu. Haka kuma mun yi bayani a kan cututukan da ake iya samu sakamakon sana’ar ta wanzanci. Mun bayyana aikin da wanzamai ke yi a garin Gusau da muhimmancinsa tare da kuma kawo wasu ayyuka da suke yi a garin Gusau. Yayin da muka ce suna yin aski, kaciya, cire belin wuya, cire gurya k’aho da dai sauransu.

Mun kawo yadda cuta ke yad’uwa a sanadiyar sana’ar inda muka ce tana samuwa ne bayan an yi wa mai cutar amfani da kayan aiki sai a kuma yi wa wani ba tare da an gyara kayan aiki ba. Bincike ya ja kunnen masu sana’ar da su kasance a cikin tsabta a ko da yaushe kuma su tsabtace kayan aikinsu, wannan yana rage yad’uwar cuta.

5.0.2 Shawarwari


A matsayinmu na masu nazarin harshen Hausa muna ba duk wanda zai yi nazari a wannan fanni shawara cewa, in dai ya ci karo da kundin mu kuma in har binciken nasu yana da alak’a da namu da su yi k’ok’arin d’orawa daga inda muka tsaya kar su kwashe d’ai wannan ba ya taimaka wa nazari. Kamar yadda muka za’bo taken da wani bai ta’ba yi ba muka yi shige –shige har muka tattaro bayanan da suka gina muna wannan kundin ya zama abin karatu ga wasu to lallai suma ya zama wajebi su dage don su samar da wani abu mai amfani, ba wai su kwashe abin da wasu suka yi ba.

Baya ga shawara ga d’alibbai muna kuma ba da shawara ga duk wanda yake cikin wannan sana’a da ya bi hanyoyin da muka tsara wajen ganin ya ku’butar da al’umma daga kamuwa da wata cuta.

Samari masu sha’awar shiga wannan sana’ar, su shige ta da gaskiya kar su kasance suna masu yi ma sana’ar rik’on sakainiyar kashi har ta kai su ga yin ‘barna.

Wad’annan da suka rik’a sana’ar wanzanci bisa ga gaskiya muna rok’onsu da su tsare gaskiya a cikin sana’ar wannan zai taimaka masu su samu riba mai albarka, da fatar wanda ya ci karo da wannan kundi ya karanta zai k’aru da abin da ke cikinsa. Allah ya yi jagoranci, Amin.

5.0.3 Ta’arifin Wasu Kalmomi


Yana da matuk’ar kyau mu d’an yi fasarar wasu kalmomi da muka yi amfani da su da zasu shige wa mai karatu duhu. Wad’annan kalmomi dai sun had’a da:

Hantsaki      -        -        wani k’arfe ne da wanzamai ke amfani da shi

Koshiya       -        -        wani icce ne da wanzai ke amfani da shi

Kalaba         -        -        k’arfe ne k’arami da wanzamai ke amfani da shi

‘Yartsaga     -        -        aska ce da wanzamai ke amfani da ita.

‘Yankara     -        -        wasu kara ne da aka amfani da su wajen kaciya

Kura ta cire hak’ori         -        k’arfe ne na wanzamai

Karkiya       -        -        kara ne na dawa da aka amfani da su

Zabira         -        -        jikka ce da wanzamai ke saka kayan aikinsu

Tankolo      -        -        jikka ce k’arama ta saka asake

Jijiya  -        -        -        jijiyar dabba ce wanzamai ke amfani da ita.

Kaciya         -        -        kuidu

Gurya -        -        -        wani ciyo da ke fita gaban mata

Beli   -        -        -        wani ciyo da ke fita cikin mak’oshi

 

 

Manazarta.


https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

Post a Comment

0 Comments