Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari A Kan Bangar Siyasa A Matsayin Tushen Gur’batar Halayyar Matasa A Garin Gusau

NA

YASIRA ABUBAKAR                8167

SUWAIBA LAWAL                    8594

HAUWA’U MUSA GUSAU         8780

KUNDIN BINCIKE WANDA AKA GABATAR A SAHEN HAUSA NA TSANGAYAR HARSUNA A KWALEGIN ILMI DA K’ERE-K’ERE TA GARIN GUSAU, JIHAR ZAMFARA

www.amsoshi.com

Sadaukarwa


Mun sadaukar da wannan bincike ga iyayenmu bisa ga kyakkyawar tarbiya da suka ba mu tun daga farkon rayuwa zuwa yau. Iyayen namu sun had’a da: Alhaji Abubakar S.Pawa Dambo da Alhaji Musa Gusau da Alhaji Abubakar Aliyu Gummi tare da iyayenmu mata gaba d’ayansu.

Jinjina


Muna masu jinjinawa babban malaminmu kuma jagoran wannan bincike wanda ya kula da mu wato malam ‘Dahiru Hussaini Sankalawa na tsangayar harsuna sashen Hausa. Saboda nuna k’wazonsa wajen duba wannan kundi tare da mayar da hankalinsa wajen wannan aiki tun farkon lokacin da aka fara har Allah ya kawo mu a wannan lokaci. Allah ya saka masa da mafificin alheri. Amin.

 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

Godiya.


Muna godiya ga tabbataccen Sarkin wanda bai haifa ba, ba a haife Shi ba. Kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halittu annabi Muhammad (SAW).

Haka kuma muna mik’a kyakkyawar godiyarmu zuwa ga iyayenmu, mazanmu da sauran ‘yan’uwanmu da suka taimaka a cikin wannan karatu namu kamar Alhaji Abubakar S. Pawa Dambo Da Alhaji Musa Umar Gusau Alhaji Abubakar Aliyu Gummi. Tare da wasu da suka taimaka da addu’o’insu kamar su, Abdulmalik da Shafi’u da Bello don bamu tarbiyya tun tasowarmu har zuwa yau da kuma ba mu gudunmuwa da suka yi wajen ci gaba da karatunmu.

Haka kuma muna mik’a kyakkyawar godiyarmu zuwa ga malam Haruna Umar Bungud’u( H.O.D) na sashen Hausa a Tsangayar Harsuna Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau Jihar Zamfara, kuma muna mik’a godiyarmu ga dukkan malaman wannan sashe, mun gode ga baki d’aya Allah ya bar zumunci ya sa ma karatun da muka yi albarka ya sa abin da za mu taimaki wannan jiha da k’asa baki d’aya.

Ba za mu manta da abokan karatunmu ba kamar su Asma’u Ahmad Bungud’u da Maryam Ibrahim da Fauziya Abdurrahman da Hibbatu Nura Sidi.

 

K’umshiya



  1. Shedantarwa ii

  2. Sadaukarwa -        -        -        -        -        -        -iii



  • Jinjina -        -        -        -        -        -        -        iv



  1. Godiya -        -        -        -        -        -        -        v

  2. K’umshiya -        -        -        -        -        -        vi



  • Babi Na ‘Daya


1.0. Gabatarwa      -        -        -        -        -        -        -        -        1

1.0.1 Manufar Bincike    -        -        -        -        -        -        -        2

1.0.2 Muhallin Bincike   -        -        -        -        -        -        -        3

1.0.3 Hanyoyin Gudanar Da Bincike   -        -        -        -        -        3

1.0.4 Matsalolin Da Suka Taso           -        -        -        -        -        4

1.0.5 Matsalolin Da Aka Fuskanta                -        -        -        -        5

2.0    Babi Na Biyu

2.0.1 Waiwaye (Ayyukan Da suka Gabata)   -        -        -        -        7

2.0.2 Salo, Zubi Da Tsarin Bincike     -        -        -        -        -       10

2.0.3 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        -       11

3.0    Babi Na Uku

3.0.1 Tak’aitaccen Tarihin Garin Gusau       -        -        -        -12

3.0.2 Ma’anar Siyasa       -        -        -                  -        -        -15

3.0.3 Ire-Iren Siyasa        -        -        -        -        -        -        -17

3.0.3.1 Siyasar Ak’ida     -        -        -        -        -        -        -17

3.0.3.2 Siyasa Don Mulki -        -        -        -        -        -        -18

3.0.3.3 Siyasa Ta Rayuwa         -        -        -        -        -        -19

3.0.4 Tarihin Samuwar Siyasa A Garin Gusau        -        -        -19

3.0.5 Yadda Lamarin Bangar Siyasa Ya K’azanta A Gusau        -22

3.0.6 Kamfe A Lokacin Yak’in Neman Za’be         -        -        -        -24

3.0.7 Muhimmancin Fita Kamfe         -        -        -        -        -26

3.0.8 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        -27

Babi Na Hud’u


4.0.1 Ma’anar Bangar Siyasa     -        -        -        -        -        -28

4.0.2 Dalilan Da Ke Haifar Da Bangar Siyasa         -        -        -30

4.0.3 Masu Yin Bangar Siyasa  -        -        -        -        -        -31

4.0.4 Yadda Ake Yin Bangar Siyasa   -        -        -        -        -32

4.0.5 Muhimmancin Bangar Siyasa     -        -        -        -        -      33

4.0.6 Gudummuwar Bangar Siyasa Wajen Gur’bata Halayyar Matasa 34

4.0.7 Hanyoyin Da Za A Bi Wajen Magance Matsalar Bangar Siyasa 35

4.0.8 Kammalawar Babi  -        -        -        -        -        -        -        37

Babi Na Biyar


5.01 Jawabin Kammalawa        -        -        -        -        -        -        38

5.0.2 Shawarwari  -        -        -        -        -        -        -        -        40

Manazarta    -        -        -        -        -        -        -        -        -        42

 

Babi Na ‘Daya


Gabatarwa


Wannan aiki ya k’unshi nazari a kan bangar siyasa, a matsayin tushen gur’batar matasa a garin Gusau. Haka kuma wannan aiki mun gudanar da shi a kan tsari na babi-babi har zuwa babi biyar kamar haka:

Babi na d’aya ya k’unshi, Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallan Bincike, Hanyoyin Gudanar da Bincike, Matsalolin Da Suka Taso da kuma Matsalolin Da Aka Fuskanta.

Babi na biyu kuwa ya k’unshi Waiwaye ga Ayyukan Da Suka Gabata, sannan da irin Salo Da Zubi Da Tsarin Marubutan suka yi amfani da shi.

Babi na uku a nan ne za mu yi bayani a kan Tak’aitaccen Tarihin Gusau, Ma’anar Siyasa, Ire-Iren Siyasa, da kuma tarihin samuwar siyasa a garin Gusau.

A babi na hud’u kuwa za mu yi tsokaci a kan Ma’anar Bangar Siyasa, Dalilan da ke Haifar Da Bangar Siyasa, Masu Yin Bangar Siyasa, Yadda Ake Yin Bangar Siyasa, Muhimmancin Bangar Siyasa Ga Matasa, Gudummuwar Bangar Siyasa Wajen Gur’bata Halayyar Matasa, da kuma Yadda Za A Magance Matsalar Bangar Siyasa.

Babi na biyar nan ne muka k’ulle zare wannan bincike, wato nan ne muka kammala wannan aiki. A babin dai mun kawo: Jawabin Kammalawa da Shawarwari ga mai nazarin aikinmu.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 

Manufar Bincike


Wannan aiki namu yana da manufar samar da sahihan bayanai da suka danganci Bangar Siyasa da yadda bangar ta taimaka wajen gur’bata halayyar matasa a garin Gusau, tare da kawo hanyoyin da za a bi wajen magance wannan matsala, a kuma taskace su a matsayin kundin bincike.

Haka kuma aikin zai taimaka wajen gudanar da bincike na k’ashin Kanmu a duk inda muka samu kanmu.

Har wa yau aikin zai bamu damar kar’bar takardarmu ta shaidar malanta ta k’asa wato (N.C.E) Sannan ya kuma shedi zamanmu a wannan makaranta.

 

 

Muhallin Bincike


Babu shakka mun yanke shawarar yin wannan bincike a kan “Nazari A Kan Bangar Siyasa A Matsayin Tushen Gur’bata Halayyar Matasa A Garin Gusau”, saboda haka binciken namu zai ta’allak’a ne a jihar Zamfara kuma a garin Gusau. Wannan bincike zai taimaka wa manazarta da masu sha’awar karatun wani rubutu domin samun wani darasi a kan abin da ya shafi bangar siyasa.

A wannan binciken za mu yi iya k’ok’arinmu na ganin cewa, manufofin da wannan binciken ya k’unsa sun fito a fili. Amma ba za mu fita daga cikin muhallin da ake gudanar da wannan binciken ba. Za mu shiga garin Gusau da kuma wasu wurare da muka san cewa akwai matasa da kuma ‘yan siyasa kansu domin mu tattaro bayanai dagare su.

Hanyoyin Gudanar Da Bincike


Kamar dai yadda aka sani cewa kowane bincike da za a gabatar to ya zama wajibi a san hanyoyin da za a bi wajen yin sa. Wannan  ya sa muka fito da wasu hanyoyi guda biyu saboda manufar wannan binciken ta kammala.

Hanya ta farko da muka bi domin cimma nasara wajen gudanar da wannan bincike ita ce, ta tattara bayanai daga littatafan da aka wallafa masu dangantaka da wannan aiki, da mujallu da kundaye da muk’alu da dai makamantansu wad’anda suka shafi sha’anin siyasa.

Sai hanya ta biyu wato ta ganawa ko tattaunawa ido da ido tsakanin mu da wad’ansu mutane da suke da masanniya a kan wannan lamari na bangar siyasa.

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

Matsalolin Da Suka Taso.


Danagane da matsalolin da suka taso kuwa, mun yi la’akari da cewa, duk wani wanda ya kasance ba ya da wata sana’a sai ya je gidan ‘yan siyasa yana zubar da mutunci ko ya d’auki wani makami yan a yin  ta’addaci da shi ya zama d’an bangar siyasa. Wannan lamari ya yawaita a cikin fad’in k’asar nan kusan a ce ko’ina ana yi, sai dai na wani wuri ya fi na wani. A garin Gusau babban birnin Jihar Zamfara lamarin ya k’azanta, amma hukuma ta yi ko oho da wannan lamari. Wannan ya sa muka ga ya dace mu fito da wannan batu a cikin aikinmu ko da Allah ya sa a ci nasarar rage ta’addaci ko a fito da wata hanya da za ta rage wannan ta’addanci ko ma ta hana ga baki d’aya.

Matsalolin Da Aka Fuskanta


Bisa ga al’adar bincike irin wannan , duk lokacin da aka ce za a yi wani bincike to lallai ba za a rasa wasu ‘yan matsaloli da suke yin barazana ba. Wannan ya tabbatar muna da cewa, lallai ya dace mu yi la’akari da matsaloli da za mu fuskanta. Tabbas a cikin wannan aiki na gudanar da wannan kundin mun had’u da matsaloli daban-daban da suka had’a da:

  • Matsalar rashin samun isassun littatafan da za mu nazarta don gudanar da wannan bincike.

  • Matsalar ganawa da wasu daga cikin wad’anda muke buk’atar zantawa da su.

  • Matsalar “masu gida rana” wato kud’i kenan wad’anda suke su ne abokan tafiya a cikin wannan aiki namu.

  • Matsalar wutar lantarki na daga cikin matsalolin da muke fuskanta saboda sanin jama’a ne cewa a k’asar ma baki d’aya babu wadatacciyar wutar lantarki yanzu-yanzu duk an d’auke wutar wannan ya kawo ma wannan aiki tafiyar hawainiya.

  • Wata matsala da muke fuskanta ita ce, a lokacin da muke gudanar da wannan binciken muna da buk’atar tattaunawa da wasu mutane da suke da masaniya dangane da wannan aiki da muke da k’udurin yi.


 

Babi Na Biyu


2.0.1 Waiwaye A Kan Abubuwan Da Suka Gabata.


Wajibi ne ga duk wanda ke son aiwatar da bincike irin wannan ya waiwayi baya don ganin irin ayyukan da suka gabata, wannan zai ba shi damar sani inda aka kwana da inda za a tashi.

Shi wannan waiwaye ya zama tilas domin ta wannan ne mai nazari zai san inda ya dosa, wato yana da masanniya game da wasu ayyuka da suka shafi binciken da zai aiwatar, don haka, sai ya d’ora a kan su ko ya rushe su ya gina nasa tsarin ko ya d’auki wad’ansu abubuwa ya watsar da wasu, gwargwadon yadda ya fahimta ko ya d’ora daga inda aka tsaya.

A wannan binciken mun yi k’ok’ak’arin bincika ayyukan da suka gabata na masana da manazarta daba-daban da suka had’a da bugaggun littattafai da kundaye da jaridu wad’anda suke da alak’a da namu aikin. Ga dai wasu daga cikin ayyukan da suka gabata na wasu masana da manazarta da muka ci karo da su yayin gudanar da wannan bincike.

Jamila (2002) ta rubuta kundin a Kwalijin Ilimi da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Gusau, mai taken “Nazari A Kan Siyasa Da Tasirinta , A K’asar Hausa Musamman A Garin Gusau” wannan kundin ya taimaka ainun wajen gudanar da wannan aiki namu. Jamila ta rubuta shi don samun takardar shaidar malanta ta k’asa wato N.C.E kuma a cikin kundin ta yi magana a kan ma’anar siyasa, da muhimmancin siyasa, da tsarin mulki da siyasa a k’asar Hausa da yadda ake gudanar da Mulkin suyasa a k’asar, manazarciyar ta yi bayanin nad’in shuwagabannin gwamnati wad’anda ba su dace ba, da musgunawa duk wanda aka ga dama a cikin sha’anin mulkin.

Wannan aiki da Jamila ta yi yana da alak’a da namu aikin musamman idan aka kalli abin da ya k’unshi siyasa da yadda ake gudanar da ita, da yadda mulkin yake gudana a yau. Wannan kundin a wani gefen daban yana da bambanci da namu aikin saboda su suna magana ne a kan siyasa da tasirinta a k’asar Hausa, duk da yake sun ke’bance aikinsu a garin Gusau. Mu kuma aikinmu yana kallon bangar siyasa ne da irin yadda yake taka rawa wajen lalacewar matasa a garin Gusau.

Ruk’ayya A. K. (2005), ta rubuta kundinta na samun takardar shaidar malanta ta k’asa wato N.E.C. a Kwalejin Ilimi Da K’ere-K’ere Ta Gwamnatin Tarayya Da Ke Garin Gusau. Manazarciyar ta rubuta kundi mai taken, “Siyasa Da Tasirinta Ga Al’ummar Garin Gusau”. A cikin wannan kundin manazarciyar ta yi bayanin siyasa da yadda ake gudanar da mulki da  ‘Yan siyasa a addinance da ‘Yan siyasa a Al’adance, ta kuma kalli siyasa a k’asar Hausa. A babi na hud’u kuwa ta yi tsokaci a kan yanayin ‘yan siyasa da fa’idar siyasa ra’ayin jama’a a kan siyasa da muhimmancin siyasa da illolinta.

Wannan kundi na Ruk’ayya Abubakar Kanoma ta taimaka muna sosai wajen samun madogara ga aikinmu. Kuma shi wannan kundin yana da alak’a da namu aikin saboda yana bayani a kan siyasa, yayin da muma namu aikin yana da alak’a da siyasa. Inda kuwa muka sha bamban shi ne ita ta fi mayar da hankali ga siyasa ne kawai mu kuma mun mayar da hankalinmu ga bangar siyasa da irin rawar da bangar take takawa wajen lalata halayyar matasa.

Umar, (2013) a cikin Jaridar Aminiya ya yi bayanin bangar siyasa inda ya kawo ma’anar bangar siyasa ya kuma yi bayani dangane da illolin bangar siyasa kamar shaye-shaye da matasa suke yi su gusar da hankalinsu har su aikata wani aiki na ‘barna.

Wannan bayani da Umar ya yi a cikin Jaridar Aminiya yana da alak’a da namu aikin, saboda shi yana magana ne a kan bangar siyasa, yayin da mu ma namu aikin yana da alak’a da bangar siyasa. Inda muka sha bamban kuwa shi ne namu aikin zai ta’bo har wasu bayanai da shi Umar bai ta’bo ba.

2.0.2 Salon Nazari Da zubi Da Tsarinsa.


Salo shi ne hanyar wanzar da wani al’amari, wato hanya ce ta bayyana tunanin mutum. Salo muhimmin abu ne a cikin labari ko jawabi, haka kuma duk aikin da aka gudanar ba cikin tsari ba to, ba zai cimma nasara ba. Don haka domin samun nasarar gudanar da wannan aikin cikin sauk’i, mun yi amfani da salo mai sauk’i, mai jan hankalin mai karatu. Mun kuma yi amfani da za’ba’b’bun kalmomi masu sauk’in ma’ana saboda mai karatu ya ji sauk’in karantawa.

Haka kuma mun yi amfani da gajeru da matsakaitan jimloli, sannan muka gudanar da bayananmu d’aya bayan d’aya a cikin sakin layi mai sauk’in fahimta.

Aikin kamar yadda aka sani mun zuba shi ne a kan babi-babi har zuwa babi biyar saboda mu samar wa mai karatu sauk’i wajen nazari, kuma kowane babi da zamu gabatar sai mun yi masa shimfid’a kana idan muka kai k’arshe sai mu nad’e mu shiga babi na gaba.

2.0.3 Kammalawar Babi


Kamar dai yadda aka gani a wannan babi mun yi gabatarwa inda muka fad’i cewa a ciki ne za mu yi waiwaye a kan ayyukan da suka gabata, sai muka kawo wasu ayyuka da magabata suka rubuta, masu alak’a da namu kuma muka fad’i inda suka samu bambanci da aikinmu. Mun kuma kawo salo da zubi da tsarin wannan kundin inda har muka fad’a cewa za mu zuba wannan aikin bisa ga tsari na babi-babi kuma zai k’unshi babi biyar.

 

 

Babi Na Uku


3.0.1 Tak’aitaccen Tarihin Gusau


Gusau tana cikin garuruwan da aka kafa tun a lokacin jihadin Shehu Usmanu ‘Dan Fodiyo, kuma k’aramar daula ce wadda ta k’unshi mafi yawan garuruwan da suke cikin Katsina ta Yamma kafin mulkin Turawa.

A can da ‘bangaren da Gusau take yanzu yana a k’ark’ashin mulkin daular Katsina ta Yamma wadda Uban Dawaki yake rik’o a yanzu wato a birnin ‘Yandoto yana kula da garuruwan da ke wannan ‘bangaren.

A wajen k’arni na 17 da na 18 garin ‘Yandoto ya zama birni babba wanda mutane daga wurare daban-daban suke zuwa d’aukar karatu da kuma harkokin kasuwanci a cikinsa. Don haka garin ya k’unshi manyan malamai da kuma d’alibai da sauran mutanen da suke zuwa d’aukar karatu da kuma bayar da karatun, a inda ‘Yandoto ta zama kamar jami’a inda mutane suke had’uwa don k’arawa juna ilimi. Alhaji Mustapha (Mahaifin Alhaji Umaru) da Malam Abdurrahman (Mahaifin Malam Ashafa) Fulani ne wad’anda suka zo ‘Yandoto suka zauna tare da dukkan iyalansu da nufin jiran bayyanar Shehu Usmanu da suka samu labarinsa tun da dad’ewa.

Wad’annan Fulani sun shiga huld’ar auratayya a tsakaninsu bayan kasancewarsu ‘yan’uwa makusanta, ta hanyar aure ne aka had’a Aminatu ‘yar Alhaji Umaru aure da Malam Ashafa, sai suka samu haihuwar Malam Muhammadu Sambo.

A wajen shekara ta 1774-1775 Shehu Usmanu ya fara karantarwa da wa’azi ‘Dagel inda aka samu mutane da yawa suka dinga zuwa d’aukar karatu ciki kuwa har da Alhaji Umaru da jikansa Malam Sambo ‘Dan Ashafa. Tun lokacin da Alhaji Ummaru da jikansa Malam Muhammadu Sambo ‘Dan Ashafa da sauran jama’arsu suka nuna goyon bayansu da yarda ga karantarwar Shehu Usmanu ‘Dan Fodiyo. Sai matanen ‘Yandoto musamman Ha’be suka hana su zaman lafiya. Saboda tsanantawa ga wad’anda suka yarda da Shehu Usmanu ya tilasta su suka yi hijira daga garin ‘Yandoto zuwa wani wuri gaba da gulbin Sakkwato ya kafa birni. Wannan hijira ita ce ta farko da Malam Muhammadu Sambo ‘Dan Ashafa ya yi da jama’arsa wadda ta fara a cikin shekarar (1799), amma a wannan lokaci ba a samu zama na sosai ba saboda yawan hare-hare da kae kai masu wanda yake ba su da k’arfin karewa. Amma duk da haka sai da suka yi shekara bakwai a wannan wurin. Kuma wad’annan shekaru an yi su ne a tsakanin shekara ta 1799 zuwa 1806, bayan cinye ‘Yandoto, sai shaihun Muhammadu Bello da Umurnin Shehu Usmanu ya raba daular Katsina zuwa ‘bangaren Yamma da Gabas, aka ba Malam Muhammadu Sambo ‘Dan Ashafa izinin ya aiwatar da jihadi a yankin Katsina ta Yamma, wato Katsina Algharbi ko Katsinar Laka. Malam Ummarun Dallaje kuwa aka ba shi Katsina ta Gabas, daga nan sai malam Muhammadu Sambo ya kafa daular jihadin musulunci wadda take kula da wasu garururwa da suke nahiyar Katsina ta Yamma wadda a k’arshe Gusau ta zama Hedikwata.

Da aka canye ‘Yandoto sai Muhammadu Sambo ya mayar da Ced’iya ta k’asar Tsafe sansanin yak’insa a shekarar 1807 zuwa 1811. A shekarar 1811 ya sake komawa garin Gusau har zuwa shekarar 1818. lokacin da suka ji labarin zuwan yak’in Banaga d’an Bature, sarkin Zamfara Morai sai suka tashi zuwa Bungud’u suka shekara biyu daga 1818 zuwa 1820. daga nan kuma sai suka koma Kamani a shekarar 1820 zuwa 1822. Bayan haka kuma sai malam Muhammadu Sambo d’an Ashafa da jama’arsa suka kafa garin Wonaka a shekara ta 1822.

Allah ya yi wa malam Muhammadu Sambo d’an Ashafa rasuwa a garin Wonaka a shekarar 1827. sai sarki musulmi Muhammadu Bello ya nad’a babban d’an Malam Muhammadu Sambo sarkin Katsinan Yamma wato Abdulk’adir. Ya shekara talatin da uku (33) a Wonaka daga shekarar 1827 zuwa 1869. Sai sai sarkin Katsina na Marad’i da na Gobir da na Tsibiri suka so su kawo yak’i a nan Wonaka, don haka suka fita nan zuwa birnin Rawayya. A Rawayya kuma saboda wasu matsaloli sarkin Katsinan Yamma Abdulk’adir tare da jama’arsa suka yi shawarar su komo wurinsu na Gusau. Da sannu- sannu suka dawo Gusau

3.0.2 Ma’anar Siyasa


Masana da manazarta da dama sun taka rawa muhimmiya wajen samar da ma’anar siyasa, ga dai wasu daga cikinsu.

Hombe A.S (1948), ya ce, “ Siyasa wata hanya ce ta amfani da ra’ayoyin jama’a, domin samar da kyakkyawan shugabanci a tsakanin al’umma. Haka kuma siyasa tana nufin nazarin yadda za a mulki a k’ark’ashin za’ba’b’bun wakilai a tutar jam’iyyu daban-daban. Herreps, (1981).

Siyasa a Hausance tana nifin jawo ra’ayin wasu mutane da su had’a k’arfi wuri guda, su za’bi wasu ko wani mutum don ya shugabance su bisa ga tsarin dokokin k’asa. ‘Dangulbi (2003)

 

Dangane da ma’anonin da suka gabata za mu ga cewa, Siyasa lamari ne da ya shafi za’ben shuwagabanni da za su gudanar da mulkin k’asa tare ta tsari na tafiyar da tattalin arzikin k’asa yin ayyuka samar da ‘yanci, samar da abubuwan more rayuwa ga al’umma. Wannan ya nuna cewa mulkin siyasa ba k’aramin al’amari ba ne, saboda mulki ne na ‘yanci da ake yi wa lak’abi da mulkin farar hula. Sanin jama’a ne cewa a wasu k’asashe can dauri mulkinsu yana hannun sojoji, amma yanzu saboda samun ‘yanci mulki ya dawo hannun farar hula.

Hausawa suna cewa siyasa rigar ‘yanci wannan ya nuna cewa, a mulkin siya akwai ‘yanci. Wato dai ba a hannun kaki mulkin yake ba.

Mulkin siyasa ba kamar na sarauta ba ne. mulki ne mai k’ayyadadden lokaci, kamar nan k’asar Nijeriya ana yin tsari na kar’ba-kar’ba, kuma kowane d’an takara ya yi shekara hud’u sai ya sauka a sake za’be, idan ya yi sau d’aya to yana da damar ya sake na biyu. A wasu kujerun na mulki idan ka aka za’bi shugaba sau biyu to bai da damar ya sake na uku, sai dai in zai tsaya wa wasu.

3.0.3 Ire-Iren Siyasa


Wasu masana da manazarta sun bayyana siyasa iri uku, ga abin da suka fito da shi a matsayin ire-iren siyasa.

  1. Siyasar Ak’ida

  2. Siyasa Don Neman Mulki

  3. Siyasa Ta Rayuwa


Ga dai bayaninsu bi-da-bi don ganin yadda suke.

3.0.3.1 Siyasar Ak’ida


Siyasar Ak’ida siyasa ce da wasu ‘yan siyasa kan kasance a cikin jam’iyya guda kuma su jam’iyyar ita ce gurinsu ko da kuwa ba su samun komai, in an ci fani’ima in kuma ba a ci ba dai duk suna nan a ciki ba gudu ba ja da baya. Kuma su ba sa yin canjin shek’a ko wanka zuwa wata jam’iyya don tasu ta fad’i.

Galibi wannan ana yin ta ne saboda ra’ayi kuma wasu sukan yi ba don su samu wani amfani ba sai dai don su gudanar da adawa da ke tsakaninsu da jam’iyyar da ake adawa da ita.

3.0.3.2 Siyasa Don Neman Mulki


Shi wannan nau’in siyasa ana yin sa ne don neman mulki ko shugabanci ta fanni daban-daban na siyasa tun daga kan shugaban k’asa har ya zuwa kansila, sai dai su ra’ayinsu na d’an lokaci ne a cikin jam’iyyar da suke ciki. Koyaushe su wad’annan ba su da wani buri sai na samun shugabanci. Idan suka fuskanci rashin kafa gwamnati wato babu nasara sai su yi wanka daga jam’iyyar da suke zuwa jam’iyyar da suke ganin za ta iya kafa gwamnati.

Galibi a cikin irin wannan nau’in babu ak’ida a ciki saboda su don lada suke salla. Ma’ana don samun mulki na wata kujera suke yin siyasar idan babu alamun nasara wajibinsu ne su canza shek’a daga jam’iyyarsu ta asali zuwa wadda suke ganin za ta yi nasara.

3.0.3.3 Siyasa Ta Rayuwa


Siyasa Ta Rayuwa dai tana cikin ire-iren siyasa, wannan bai shafi mulki ba ko ak’ida sai dai ya k’unshi zamantakewa ta rayuwa wato yadda mutum zai gudanar da rayuwarsa a cikin zamantakewa da wasu mutane. A matsayin mutum mai huld’a da tarayya da jama’a sai ya gudanar da halayensa na rayuwa cikin jama’a tare da kwatanta adalci da kayautatawa ga jama’a da bin ra’ayinsu ko da shi ba ya son ra’ayin kuma ba zai bari su san cewa shi ba ya tare da su ba.

Wani wanda yake da siyasa ta rayuwa yana gudanar da rayuwarsa tare da jama’a ba su san takamaiman ra’ayinsa ba. Sai dai a kullum suna tsammanin cewa, shi tare yake da su, amma shi a cikin zuciyarsa ba ya tare da su. Kuma bai bari sun sani ba. Haka kuma mutum yana iya daidaita tsarin rayuwarsa ta zama daidai da ta jama’ar da yake tare da su.

3.0.4 Tarihin Samuwar Siyasa A Garin Gusau


Garin Gusau gari ne da mafi yawan mazauna garin Hausawa ne, kuma kashi tisi’in da tara dukkansu musulmai ne.

Dangane da samuwar siyasa a garin Gusau kuwa tun da Nijeriya ta samu ‘yanci. Kuma tun a lokacin aka fara siyasa a Nijeriya Gusau ta samu shiga ciki ana damawa da ita, duk da yake a wannan lokaci ba ta zama babban birnin Jiha ba. Amma tana matsayinta da babban gari mai jama’a.

A shekarar 1996 ne aka ba Zamfara ‘yanci ta zama jiha wato aka fitar da ita daga Sakkwato.

Bayan da aka k’irk’iro wannan jiha soja ne mai suna Jibril Bala Yakubu ya shugabance ta da farko. Amma da mulki ya dawo hannun farar hula Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura ne ya fara zama Gwamnan wannan jiha na farar hula. Bayan ya sauka sai ya bayar da ragamar mulkin ga mataimakinsa Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi shi kuma ya yi shekara hud’u wato wa’adi na farko, da aka kai ga na biyu bai samu cin za’be ba Allah ya ba Alhaji Abdul’Aziz Yari Shettiman Mafara sa’a ya kar’ba tare da goyon bayan su Yariman Bakura Sanata Ahmad Sani tsohon gwamnan jihar.

A can baya farko jam’iyyar ANPP ce take mulkin jihar kuma a tsohon gwamnan Sanata Ahmad Sani ne ya lashe za’ben a wannan lokaci. Bayan da ya sauka sai mataimakinsa Mamuda Aliyu Shinkafi Dallatun Shinkafi ya nemi kujerar a k’ark’ashin jam’iyar ta ANPP kuma Allah ya ba shi sa’a tare da goyon bayan Yariman Bakura. Bayan Dallatu ya yi shekara biyu sai ya canza shek’a daga ANPP zuwa PDP kuma ya nemi ya koma zama a kan kujerar sai Allah bai ba shi sa’a ba Abdul’Aziz Yari ya lashe za’be. A k’ark’ashi inuwar jam’iyyar ANPP.

Sha’anin jam’iyyun siyasa yanzu abin ya canza zane, saboda jam’iyyun adawa sun had’e a wuri d’aya sun yi maja, jam’iyyun da suka had’e sun had’a da ANPP, CPC, ACN. Wad’annan jam’iyyun sun had’u wuri d’aya suka samar da sunan fati d’aya wato APC kuma wannan jam’iyyar ta APC tana da alamar Tsintsiya. Jam’iyyar ta had’u ne saboda ta k’wace mulki ga hannun jam’iyar PDP mai mulkin k’asar.

A zamfara kuwa jam’iyyun biyu sun fi k’arfi su ne suke jayayya a tsakani da APC mai mulkin jihar da kuma jam’iyyar PDP a matsayin jam’iyyar adawa a wannan jiha. Jam’iyyun biyu dukansu suna da k’arfi tare da mabiya da yawa kowa yana da yak’inin cewa shi ne zai lashe za’be mai zuwa a shekarar 2015. wasu daga cikin ja’iyyar da ke mulki suna canza shek’a zuwa jam’iyyar PDP daga APC sakamako wasu dalilai. Daga cikin wad’anda suka canza shek’a akwai Injiniya Ibrahim Shehu Bak’auye ‘Dan majalisar Tarayya Abuja mai wakiltar Gusau, da Malami Aliyu ‘Yandoto da dai wasu daga cikin jam’iyyar ta APC. Wannan ya sa wasu suke ganin cewa, akwai alamun cewa gwamnatin tana da k’alu bale a cikinta.

3.0.5 Yadda Lamarin Bangar Siyasa Ya K’azanta A Garin Gusau


Garin Gusau dai kamar sauran garuruwan da ke wannan k’asa ta Nijeriya, ana gudanar da bangar siyasa kuma ana yinta ne kamar yadda sauran jihohi ke yi. Kwanci –tashi yau an wayi gari lamarin ya k’azanta har ya kai ga ana samun kashe-kashe kuma ana samun rasa dukiyoyi da rashin kwanciyar hankali.

Matasa na garin Gusau sukan je gidan wani d’an siyasa su mayar da garkarsa dandali ko ko kuma shi d’an siyasar ya bud’e masu wani ofis na gudanar da lamurransa na siyasa, sai matasan nan su koma a can suna aikata wasu halaye na banza kamar shaye-shaye da neman matan banza da tare jama’a suna yi masu k’wace. Ko bayan wad’annan halaye na banza, shi wanda ya aje su a nan yakan ba su kud’i su sha kayan maye ya kuma saya masu makamai da za su rik’a tayar da hankalin jama’a da su suna zage-zage da rashin mutunci a duk inda suka biya.

An wayi gari yau lamarin ya k’azanta a garin Gusau, saboda matasan da ke a wannan yanayi na shaye-shaye sukan aikata shaye-shaye sai su nufi inda abokan hamayyansu suke sai su kai samame su kashe wani sai su watse hukuma ta je ta d’auke gawar da aka kashe. Nan kwanan baya ba da jimawa ba matasa suka shiga gidan wani mutum a shiyar Unguwar Yarima suka yi wa amaryar wani fyad’e suka gudu.

Wasu ‘yan bangar siyasar wad’anda aka fi sani da ‘yan trowe sun kai samame a shiyar Tudun wada da ke nan Gusau a jihar Zamfara suka fad’a wani da sara har sai da suka kashe shi suka bar shi kwance a cikin jini, aka kira ‘yan sanda suka zo suka d’auki gawarsa. Matasan sun aikata irin wannan ya fi a k’irga ko bayan sa kuma sun kai wa wani samame suka kashe shi a mak’abarta a lokacin da ya raki gawar kakarsa zuwa wajen jina’iza.

Wannan kad’an kenan daga cikin abin da yake faruwa a garin Gusau ta jihar Zamfara. Kuma idan hukuma ba ta d’auki matakin da ya dace ba lamarin zai iya fin haka muni.

3.0.6 Fita Kamfe A Lokacin Yak’in Neman Za’be.


        Duk lokacin da aka bud’e fagen yin yak’in neman za’be wato Kamfe, ‘yan siyasa sukan nemi jama’a kuma kafin su shiga wannan yak’in sukan samu matasa masu jini a jika su rika su ana tafiya suna yin kuwace-kuwace da shaye-shaye suna d’aga makamai masu had’arin gaske. Haka kuma su wad’annan matasan idan aka biya ta inda ‘yan adawa suke galibi ba su cika wucewa ba sai an yi tashin hankali wannan lamari yana da had’arin gaske kuma su matasan ba a cikin hankalin kansu suke ba.

‘Dan siyasa ne ke neman wad’annan matasa kuma shi zai basu kayan maye ko kud’i su siya kayan mayen ya kuma basu makamai ko kud’i su saye da kansu. Wannan shi yake ba matasan k’warin guiwar su aikata duk abin da suka ga dama. Idan kuma suka yi ta’addanci sai ya je ya yi tsaye ya kar’bo su in ya buk’aci su yi wani abu na ta’addanci sai ya basu umurni su je wajen wani ko wasu ‘yan adawa su aikata wani abun k’yama na ‘barna.

Galibi a yayin kamfe akan fita wasu k’ananan hukumomi da wasu k’auyikka. Duk inda za a je matasan nan ne suke biye da d’an siyasa ko d’an takara suna tafe suna kuwace-kuwace da barazana da ruri da kad’e-kad’e da dai duk wasu halaye na assha. Sukan kama tayar da makamansu sama ko su dinga sare-saren iska ko su kama kwantar da wannan makaman suna kod’a su a saman titi ko wani abu na daban.

Idan kuwa aka isa garin da za a yi kamfe sai d’an takara da sauran ‘yan siyasa su sauka suna kira ga jama’a da su za’be su. Su kuwa matasan nan ‘yan mangar siyasa sukan kama zagayawa suna kuwace-kuwace suna yabon jam’iyyarsu da ‘yan takararsu da manyan ‘yan siyasarsu. Haka kuma duk a wannan lokacin sukan kama zagin jam’iyyar hamayya da abokan adawa na karawar ‘yan takarar.

 

3.0.7 Muhimmancin Fita Kamfe


Fita yak’in neman jama’a dai shi ne kamfe kuma shi kamfe yana da muhimmanci sosai saboda ta nan ce dukkan d’an takara ke bayyana ra’ayinsa ya kuma jayo ra’ayin wasu jama’a su ji suna son ya shugabance su. Don haka muna iya cewa muhimmancin fita kamfe ya k’unshi:

  1. neman jama’a

  2. jin ra’ayoyin masu za’be

  3. bayyana ra’ayin d’an takara

  4. tallata d’an takara

  5. ba da kud’i ga masu za’be


 

3.0.8 Kammalawar Babi


Wannan babi na uku nan ne muka yi bayani a kan tak’aitaccen tarihin garin Gusau, inda har muka kawo bayani tun daga Muhammadu Sambo d’an Ashafa kuma muka kawo dukkan gwagwarmayar da ya sha, kana muka kawo bayanai a kan wasu ayyuka da ya yi inda har muka ce ya fatattaki wasu kuma ya mayar da Cid’iya ta yankin Tsafe sansanin yak’insa. Mun kawo ma’anar siyasa daga masana daban-daban kamar Samuel da Adebayo da Abubakar inda muka fad’a cewa ita siyasa salon mulki ne na za’bi da kanka. Mun kawo ire-iren siyasa inda har muka yi tsokaci a kan iri uku da suka had’a da siyasar ak’ida, da ta neman mulki da ta rayuwa. Sai muka yi tarihin samuwar siyasa a garin Gusau inda muka ce ta samo asali ne tun daga lokacin da aka fara siyasa a k’asar Nijeriya. mun kuma kawo yadda lamarin bangar siyasa ya k’azanta a garin Gusau, inda har muka ce ana samun kashe-kashe a garin Gusau da hasarar dukiyoyi sakamakon bangar siyasar. Fita kamfe da kuma muhimmancinsa ya biyo baya duk a cikin wannan babi na uku.

 

Babi Na Hud’u


4.0.1 Ma’anar Bangar Siyasa


A yunk’urinmu na neman abin da ya shafi bangar siyasa ba ci karo da wasu littattafai da suka yi magana a kan bangar siyasa ba, amma hakan bai sa muka yi k’asa a guiwa ba saboda mun tuntu’bi wasu mutane sun bayyana muna daidai da tunaninsu. Ga dai wasu da suka bamu irin tasu gudummuwa dangane da ma’anar bangar siyasa.

Sani (2014), ya bayyana cewa, ‘yan siyasar wannan k’arni ne suka kawo bangar siyasa domin samun cimma burinsu, wanda ya haifar da babbar illa a cikin rayuwar matasanmu, wanda ya k’unshi saka matasa ga harakar shaye-shaye, da saran juna da cin zarafin al’umma.

Ya k’ara da cewa, ya kamata iayayen yara da malaman addini da masu gari su yi kira ga matasa da su guji wannan bak’ar d’abi’a, domin su zama manyan gobe abin koyi ga al’umma.

Manu (2014), ya fassara bangar siyasa da cewa, wani al’amari ne da matasa suka sa kansu na d’aukar makamai da shaye-shaye a lokacin siyasa domin su ci ma mutane da abokan adawa mutunci, ko zarafi a lokacin kamfe ko za’be. Mafi yawan wad’annan halaye sun samu asali ne daga abin da ‘yan siyasa suke taimaka wa matasan da shi ne kamar makamai da kud’in shaye-shaye.

Sama’ila (2014), a tasa fahimta ya bayyana bangar siyasa da cewa, “wata d’abi’a ce da ‘yan siyasa suka k’irk’iro a cikin wannan k’arni na ba matasa makamai da kud’i su yi shaye-shaye na kayan maye domin su ci mutunci abokan hamayyarsu.

Ya ci gaba da cewa, wannan al’amari na da ban tsoro k’waran gaske, ganin cewa al’amarin sai dad’a k’aruwa yake yi, kuma matasa na dad’a tsunduma a cikin wad’annan miyagun halaye na shaye-shaye.

Bisa ga jin ra’ayoyin wad’annan mutane da muka yi, mun gano cewa, bangar siyasa ba wani abu ba ce illa, ‘yunk’urin da matasa ke yi na zuga d’an takara da kuma kururuta shi da tallata shi ba ta hanyar wak’a ba, haka kuma akwai suka ga abokan adawa, tare da yin ‘batanci a gare su domin dushe tauraronsu’.

Wannan yanayi na banga a wannan lokaci ba abu ne mai kyau ba saboda ya surka da cin zarafin jama’a, shaye-shaye, sata, rashin kunya, ta’addanci da dai wasu haramtattun abubuwa da doka ba ta yarda da su ba.

4.0.2 Dalilan Da Ke Haifar Da Bangar Siyasa


Akwai dalilai da yawa da suke haifar da bangar siyasa da suka had’a da:

  1. Rashin ilimi ga matasa: Da yawa matasa da suke wannan lamari ba su da ilimin zamani kuma babu na addini. Rashin ilimi na daga cikin manyan dalilan da suka rardasa wannan bala’i.

  2. Rashin tarbiyya ga matasa: Da yawan matasan da suke wannan sana’a ta bangar siyasa ba su da tarbiyya, wannan daga iyaye ne su suka kasance masu rauni da rashin tsawatawa har yaran suka samu kansu a cikin wannan sana’a.



  • Talauci: Talauci yana daga cikin manyan dalilan da suka saka matasa cikin wannan yanayi na bangar siyasa. Idan matashi yana da wadata to lallai ba zai so ya zama a cikin wannan yanayi ba.



  1. Rashin aikin yi ga matasa:A wannan lokaci sanin jama’a ne cewa, dayawa za ka ga matasa ba su da aikin yi sai zaman banza zaman kashe wando. Wannan yanayi na rashin aikin yi ga matasa ya taimaka sosai wajen bunk’asa wannan lamari.

  2. Son kai ga shuwagabanni da neman duniya ko ta wane hali: Mafi yawan ‘yan siyasa sukan bayar da kud’i ga matasa su kuma umurce su da su je su cutar da wani abokin adawa, kuma su ko matasan ba za su iya zuwa haka kawai kai tsaye su aikata wannan d’anyen aiki ba, wannan ya sa suke amfani da kud’in su saye muyagun k’wayoyi da za su kawar da hankalinsu sai su aikata duk abin da aka umurce su.


4.0.3 Masu Yin Bangar Siyasa


Mafi yawan masu yin bangar siyasa matasa ne kuma da yawa a cikinsu ba su da aikin yi ba su da wata takamaimiyar sana’a, tare da rashin samun tarbiyya ta gari.

Matasa sukan je gidan d’an siyasa su zubar da mutunci shi kuma ya basu kud’i ya kuma ba su makamai. Su kuma su yi amfani da kud’in su sayi kayan maye wato k’wayoyin da za su haukata su ko su kawar da hankalinsu domin su ji dad’in yin ta’addanci.

Akwai wasu da ake ganin cewa, suna bangar siyasa amma su ba su shaye-shaye da ta’addanci, sai dai suna yin duk wata magana da ke iya hardasa jidali. Irin wad’annan ‘yan bangar siyasa sun fi yin bangar su a fili ko a kafafen yad’a labarai da suka had’a da rediyo da talabijin da jarida da dai makamantansu.

4.0.4 Yadda Ake Yin Bangar Siyasa


Galibi bangar siyasa takan samu ne a lokacin da ake gudanar da wani taro na ‘yan siyasa, kamar kamfe ko ranar za’be ko wajen wani d’aurin aure, ko zanen suna ko bukin sarauta ko dai wani taro da za a iya samu wani d’an siyasa ya halarta.

Matasa wad’anda suke cikin wannan sha’ani suke zuwa su yo shaye-shaye su rik’o makamai suna tayar da hankalin jama’a, wani lokaci ma har suna iya saran wani da makami, ko su buga ma wani sanda ko dai su samu wani aibu su yi wa wani. Matasan sukan fara wannan ta’addacin tare da kuwace-kuwace da zage-zage da fad’in “sai wane ko ba a wa Allah” suna kuma iya yin amfani da lafazi kamar haka, “sai wane ko ran dubu zai ‘baci” ko su ce, “Sai wane ko a sha adda” wato gwaninsu (d’an takara).

Matasan za su rik’a yin rawa suna jujjuyawa suna fad’in sai wane, tare da jujjuya makamai ana tayar da hankali da nuna k’in jinin wanda ake adawa da shi.

4.0.5 Muhimmancin Bangar Siyasa


Kamar yadda aka riga aka sani cewa, kowane irin abu yana da irin nasa muhimmanci haka ita ma siyasa tana da muhimmanci. Amma wannan muhimmanci bai wuce ‘yan kud’ad’en da ake ba su da kuma ababen hawa kamar babura/mashin da motoci da kuma wasu kayan amfani da za su iya had’awa da injimi da kuma kekunan d’inki da dai sauransu.

Haka kuma bangar siyasa tana taimakawa wajen kare mutuncin jam’iyya da ‘yan jam’iyya. Bangar siyasa tana da muhimmanci idan aka yi la’akari da yadda su ‘yan bangar suke yaba d’an jam’iyyarsu da jam’iyyar kanta. Wad’annan su ne manyan muhimmancin da ke ga bangar siyasa.

4.0.6 Gudummuwar Bangar Siyasa Wajen Gur’bata Halayyar Matasa


Bangar siyasa dai kowa ya sani cewa, rashin amfaninta ya fi amfaninta yawa. Wannan ya sa masu yinta galibi ba su cika daraja a idanun jama’a ba. Sau da yawa duk wanda aka gani a cikin bangar siyasa bai cika k’ima a idon mutane ba. Wad’annan halaye su ne suka ‘bata ‘yan bangar siyasa kuma su ne suka taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar halayen matasa:

  1. Bangar siyasa ta zama sanadin lalacewar halayyar matasa ta hanyar saka su cikin shaye-shaye.

  2. Bangar siyasa ta saka matasa cikin halin sare-saren mutane da kuma kisan juna.

  3. Bangar siyasa tana hardasa matasa gaba a tsakaninsu ko kuma su saka al’umma gaba d’ayanta a cikin gaba da juna.

  4. Bangar siyasa tana saka matasa tayar da rikici a wajen kamfe ko taron ‘yan siyasa.

  5. Bangar siyasa na saka matasa cin zarafin al’umma.

  6. Bangar siyasa na sa matasa su zamo silar hasarar dukiyoyin al’umma.

  7. Banagar siyasa na saka matasa su zama ‘barayi su kama sace-sace

  8. Bangar siyasa tana sa matasa su kasance ‘yan ta’adda ko ‘yan fashi da makami.

  9. Bangar siyasa na hardasa mutuwar zuci ga matasa.


4.0.7 Hanyoyin Da Za A Bi Wajen Magance Matsalar Bangar Siyasa


Akwai hanyoyi da dama da za a iya bi wajen magance matsalolin bangar siyasa da matasa kan yi su tayar da hankalin mutane. Wd’annan hanyoyi sun had’a da:

  1. ilimantar da matasa dangane da illar bangar siyasa, da kuma rayuwarsu a matsayinsu na manyan gobe.

  2. Jan kunnen su ‘yan siyasa don su daina tara wad’annan matasan suna ba su kud’i kuma suna tura su wajen tayar da hankalin abokan adawa.

  3. Hukunta duk wani d’an siyasa da aka kama da hannu dumu-dumu a cikin sha’anin bangar siyasa ko taimaka wa masu yin bangar siyasar.

  4. ‘Daukar mataki mai girma kuma mai tsanani ga duk wanda aka kama a cikin bangar siyasa.

  5. Kula da tarbiyyar matasa daga uwaye. Wannan ya k’unshi hani da horo da ya dace iyaye su yi ga ‘ya’yansu.

  6. Koya wa matasan sana’o’i da samar masu da aikin yi da zai hana su zaman banza har su yi tunanin su aikata wani abin assha! A cikin al’umma.


 

4.0.8 Kammalawar Babi


A cikin wannan babi na hud’u kuwa a nan ne muka yi tsokaci a kan ma’anar bangar siyasa inda har muka kawo ra’ayoyin masana dangane da bangar siyasar. Mun kuma fad’a cewa bangar tana haifar da babbar illa a cikin al’umma. Mun kawo masu yin bangar siyasa inda muka fad’a cewa, da yawansu matasa ne kuma mun bayar da dalilan da suke haifar da bangar siyasa inda muka ce da talauci da rashin aikin yi duk suna ciki. Mun kawo yadda ake yin bangar siyasa da muhimmancin bangar suyasa da gudummuwar da bangar siyasa take bayar wa wajen lalacewar halayyar matasa da hanyoyin da za a bi wajen magance wannan matsala ta bangar siyasa.

 

 

Babi Na Biyar


5.0.1 Jawabin Kammalawa.


Alhamdulillahi godiya ta tabbata ga Allah Mad’aukakin Sarki Mai Kowa Mai komai, Mahaliccin sammai da k’assai da ya bamu ikon kammala wannan aikin Bincike. Yabo da jinjina ga AnnabinSa Muhammadu (SAW) Imamin Manzanni Cika makin Annabawa Muhammadu d’an Abdullah, da iyalan gidansa da Sahabbansa da magoya bayansa tun daga farko har k’arshe.

Hausawa kan ce, “Komai nisan dare gari zai waye” wannan ko shakka babu haka yake. Saboda a nan ne za mu nad’e tabarmar wannan bincike. Kamar yadda aka gani a baya mun raba aikin nan namu gida biyar bisa ga tsarin babi-babi har babi biyar.

Babi na farko ya k’unshi, Gabatarwa, Yanayin Bincike, Muhallin Bincike, Hanyoyin Gudanar Da Bincike, Matsalolin da Suka Taso da Matsalolin da aka fuskanta.

A babi na biyu kuwa kamar yadda doka ta tanadar mun kawo Gabatarwar wannan babi, sannan muka biyo da Waiwaye A Kan Ayyukan da Suka Gabata kana muka yi byanin Salon Nazari da Tsarinsa.

A babi na uku kuwa nan ne muka yi bayani a kan tak’aitaccen tarihin garin Gusau, inda har muka kawo bayani tun daga Muhammadu Sambo d’an Ashafa kuma muka kawo dukkan gwagwarmayar da ya sha, kana muka kawo bayanai a kan wasu ayyuka da ya yi inda har muka ce ya fatattaki wasu kuma ya mayar da Cid’iya ta yankin Tsafe sansanin yak’insa. Mun kawo ma’anar siyasa daga masana daban-daban kamar Samuel da Adebayo da Abubakar inda muka fad’a cewa ita siyasa salon mulki ne na za’bi da kanka. Mun kawo ire-iren siyasa inda har muka yi tsokaci a kan iri uku da suka had’a da siyasar ak’ida, da ta neman mulki da ta rayuwa. Sai muka yi tarihin samuwar siyasa a garin Gusau inda muka ce ta samo asali ne tun daga lokacin da aka fara siyasa a k’asar Nijeriya. mun kuma kawo yadda lamarin bangar siyasa ya k’azanta a garin Gusau, inda har muka ce ana samun kashe-kashe a garin Gusau da hasarar dukiyoyi sakamakon bangar siyasar. Fita kamfe da kuma muhimmancinsa ya biyo baya duk a cikin wannan babi na uku.

Babi na hud’u kuwa man ne muka yi tsokaci a kan ma’anar bangar siyasa inda har muka kawo ra’ayoyin masana dangane da bangar siyasar. Mun kuma fad’a cewa bangar tana haifar da babbar illa a cikin al’umma. Mun kawo masu yin bangar siyasa inda muka fad’a cewa, da yawansu matasa ne kuma mun bayar da dalilan da suke haifar da bangar siyasa inda muka ce da talauci da rashin aikin yi duk suna ciki. Mun kawo yadda ake yin bangar siyasa da muhimmancin bangar suyasa da gudummuwar da bangar siyasa take bayar wa wajen lalacewar halayyar matasa da hanyoyin da za a bi wajen magance wannan matsala ta bangar siyasa.

Sai a wannan babi na biyar inda muka yunk’urin nad’e tabarmar wannan bincike namu, ga shi kamar yadda aka tanada muka yin jawabin kammalawa daga shi kuma sai shawarwari da za mu bayar ga mai karatu da wad’anda wannan sha’ani ya shafa.

5.0.2 Shawarwari


Muna son mu yi amfani da wannan damar mu ba ‘yan’uwanmu d’alibai shawara su mayar da hankali wajen gudanar da sha’anin karatunsu tare da yin k’ok’ari gwargwadon hali, su kasance masu gwazo ga karatunsu. Idan kuwa Allah ya kai su ga lokacin da za su gudanar da bincike in suka ci karo da wannan aiki namu to su yi k’ok’ari su d’ora daga inda muka tsaya na wannan bincike.

Muna kira ga wasu wad’anda ba nazarin wannan kundi sukai ba da su yi k’ok’ari su koyi darussan da ke cikin wannan kundi kar su yi k’asa a guiwa su kasance masu kyautatawa da neman ilimi da kauce wa wannan hali na shiga bangar siyasa

Haka kuma idan da wata hukuma da za ta ji kiranmu da ta d’auki mataki da za hana wad’annan miyagun halaye suna faruwa a cikin gari har ma k’asar ga baki d’aya.

 

Manazarta.


https://www.amsoshi.com/contact-us/

Post a Comment

0 Comments