Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Rubutawa: Shehu Hirabri
08143533314
Amshi:
PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Ya Allah na kwan roƙon ka,
Allah ya gwada muna ran za’be,
An ƙirga PDP ta ci,
Yara: Amin, amin Haji ‘Danba’u,
Wannan magana babu kuskure.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: In Allah ya so ya yarda,
Mu za mu yi winin Nijeriya,
Lokal gammon da siteg gammon,
Yara: Mu ke winin had da federal.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Manufar fatinmu na PDP,
Mutunci fawa da walwala,
Ka yi yanda kake so Nijeriya,
Yara: Ban san wani mai takura ka ba.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Kai ji wane yai tahiyar kura,
Yana gaba ya koma baya,
Inda ya nuhwa ba a kar’bai ba,
Ya dawo bai ishe kowa ba,
Yay yi shiw ya riƙe baki,
Nac ce duk mai koraj jama’a,
Yara: Sai ya biɗi mai ba shi shawa.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Ku ji kyanwa mai saurin tahiya,
Ƙarƙarin takai ta ci kihi,
Dur rad da ƙaya tal laƙe miki,
Yau kowa bai tagaza miki,
Sai dai ki mace ‘yar damtcen uwa,
Yara: Don mu kula ‘barnarki tai yawa.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Mai ƙarƙarin hawan iccen kwakwa,
Idan ka hwaɗo kaƙ ƙalle,
Kai ciki dubu nika tona ka,
Yara: Baƙar magana wad da kai muna.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Haji Modi na Yabo a gaishe ka,
Zaki mai ƙarhin mutum dubu,
Ka gama da ‘yan kwakwa baya,
Yanzu kwakwa ba ta da tasiri,
Yara: Sai dai su yi bammi su sha giya.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: kowa ke zagin Shagari,
Da Iro Gusau ɗan Muhammadu,
Wannan ƙarshe nai jin kunya,
Yara: Don sai an gyara mishi zama,
Ya tabbata ba zarumi ba ne.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: in dai Allah ya yi abinai,
Kowa ya tsaya sai dai kallo,
Zubairu S. Magori a gaisheka,
Jagora/Yara: Ga allura mai shiga jiki,
Gaishe ka ni kai ɗan Attahiru.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Raƙumin Gwadabawa ya wahala,
Don ya ɗau kaya mai nauyi,
Yara: Ya hwara zuhwa har ga kunnuwa.
Jagora: General Ibrahim Babangida,
Lokacin da ka riƙa Nijeriya,
Wanda bai da mota yai mota,
Wanda bai da kuɗi yai kuɗɗi,
Talakawa duk sun gode,
Yara: Wannan magana zahiri take.
Amshi: PDP hasken Nijeriya,
Fati mai ƙarhi da martaba.
Jagora: Wada waziri mai komi dozin,
Wada waziri birnin Ɗanbatta,
Wada waziri baban soja,
Ka yi zarumi ko birni wa,
Har na ji mutane suna hwadin
Yara: Ka zam hitila maganin dugu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.