Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Alhaji Aliyu Magatakarda (Alhaji Musa Danba’u Gigan Buwai)

Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.

www.amsoshi.com

Rubutawa: Shehu Hirabri 
08143533314


Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ka yi biyu yau saura biyu,

Ga ka difiti gwamna ga ka sarkin Yamma,

Sai in ka zama gwamna a Sakkwato,

Yara:   Sannan a ba ka Barade cikin gida.

 

Jagora: Sai in ka zama gamna a Sakkwato,

Yara:    Sannan a ba ka Barade cikin gida.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ka ga sarautar sarkin Yamma,

Ba fa sarautar yaro ce ba,

Ba ko sarauta wargi ce ba,

Sai an zaɓi mutum mai kirki,

Yara:    A ba shi sarkin yamman Sakkwato.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Na yi mahwalki jiya mai daɗi,

Amma hwa ban magana sai yaz zamo×2

Yara:    Allah ya sa ya zame ma gaskiya.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

Jagora: In Allah ya so ya yarda,

Tutawuzan sabin in ta zo,

Yara:    Kai za ka gwamna jaharmu ta Sakkwato.

 

Jagora: Ko mu masu adawa mun bari,

Yara: Saboda mun ga alamun gaskiya.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ran Juma’a na kwan mamaki,

An yi sarautu Sakwkato bunni,

Mai kurin shi ad da mutane,

An yi naɗi kowa ya watce,

Mai jama’a ya kwashi abinai,

Sai nib biya garkar wani sarki,

Ni ishe ‘yan banga sun taru,

Yara:    Da haka ‘yan sholi ɗai nig gani.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Wannan duk aka ci da haƙƙi nai,

Allah shi kai mai sakayya,

Makircin da sukai ma Sakkwato,

Aliyu kar ka ji tsorran komai,

Yara:    Bar su akwai Allah shi ya gani.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Aliyu kai ka gadi sarauta,

Ka yi naɗi daidai da sarauta,

Wanda duk bai gadi sarauta ba,

Yara ko ga naɗi sai mun ganai,

Yara:    Wane naɗinai ya cika girma,

Wanga uban huni sai ‘yan dako.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: I taƙamarka Alu daidai,

Taƙama sai ɗan sarki,

Jan biri in dai ya yi taƙama,

Yara:    Tabbata hwadaman nan ya gani,

Yana nuhwa ya kare geron wani.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Na gaishe ka Italin Nasiru,

Shugaba na matasan Sakwkato,

Kai ne anka sani duk Sakkwato,

Duk wanda anka naɗa shirme ne,

Yara:    Nasiru naka naɗi ag gaskiya.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Bello na Gwiwa masoyin Ali,

Ni na gane kana ƙaunatai,×3

Yara:    Alhaji tun ga naɗi nit tabbatar.

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Ahmed Aliyu ku gaisai,

Ahmad Aliyu ya ban mota,

Yara:    Saboda Sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Nasiru Itali ba mu sitalet,

Yara:    Saboda sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Kai bari dai in tada gwanina,

Bari dai in wasu ubana,

Ɗan Barade jikan umar,

Baba gizago ba ka da sabo,

Yara:    Masassaƙi ya tsara hannu ƙwarai.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora:  Musa Damo ya ban gero,

Musa Damo ya ban dawa,

Musa Damo ya ban kuɗi,

Da riguna Musa ya ba ni×2

Kaf Illela Lokal gamun

Yara:    Duk wanda ke son sarkin Yamma,

Alhaji babu irin Musa Dama.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

 

Jagora: Magatakarda Difiti Gwamna,

Maza su ƙara shiri sai ka zamo,

Hankalinka ya kwanta Sakkwato,

Tun mulkin gargajiya Aliyu don Mulkin ga,

Na zamani inda duk Allah ya ce a yi,

Yara:    Babu wanda ka ce ba a yi.

 

Amshi: Ƙi sake bajini gwarzon maza,

Ali sarkin Yamman Sakkwato.

 

Jagora: Dole in yi yabon gogana,

Tunda garinmu guda da shi,

Shehu Adamu birnin Rana,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Shehu na sani ɗan Adamu,

Yara:    Irin abin da ya kai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Gwamnan jahar Yobe,

Gwamnan jahar Yobe,

Abba Bukar ɗan Ibrahim,

Yara:    Irin abinda ya kai ma.

 

Jagora: Matiamakin sifika Sakkwato,

Rai ya daɗe Alhaji Maigwandu

Yara:    Irin man ya yi da.

 

Jagora: Nasiru mai mai birnin Wurno,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi ɗa.

Jagora: Haji Mu’azu Zabira ka yi ɗa,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi ɗa.

 

Jagora: Mustapha Haji Maigandi,

Yara:    Irin abin da yakai man ya yi ɗa.

Post a Comment

0 Comments