Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko Mai Suna: Mai Ban Tsoro Magatakarda Wamakko (Alhaji Musa Danba’u Gigan Buwai)

Wannan da ɗaya daga cikin waƙoƙin gargajiya na mawaƙan baka.

Rubutawa: Shehu Hirabri 
08143533314 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Na gaya wa mutane d’auke dafi sai giwa,

Yara:    Maza tahi kauce zomo ba ka iyawa wa kai nan?

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ali d’an Lamid’o Ali uban Lamid’o,

Baba jikan Umar Sakkwato yau ta zama taka,

Yara:    Wahidun Allah mai ida nuhi kai yab baiwa.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Na sani Allah shi ka ba da mulki ya ba ka,

Don kak ka bi shawara katan keke,

Mai son a ƙi wa kowa komai,

Yara:   D’an Barade Alu kai ta wa mutane adalci.

 

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Mun sani Allah shi ka ba da mulki ya ba ka,

Don kak ka bi shawara buhun kowa,

Mai son a ƙi wa kowa komai,

Yara:    D’an Barade Alu kai ta wa mutane adalci.

 

Jagora: Don Allah d’an Barade Alu,

Yara:    Kai ta wa mutane adalci.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Mugun madambaci kake Ali,

Baba da kat tattako ka bugi bakin dogo,

Yat tahi ba ban kwana,

Yara:   Bar maganar guntu shi hag ga cikinai ya rude.

 

Jagora: In ka ji ƙi gudu ɗanba’u,

Sa gudu ne ab bai zo ba,

Ranaz zaɓenka d’an Barade na Wamakko,

Wad’ansu maza hay Yamai suna ɓoyo,

Yara:    Kahin a yi zaɓe sun tcere.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Wad’ansu maza sun yi rantsuwa kama sun ƙara,

Sun ce maka d’an Barade ba ka zama gwamna,

Allah ya yarda yau Alu ka zama gwamna,

Bamaguje kai kuma ya za ka yi zance kokonka,

Yara:   Du hatcin Sakkwato kaf ba su cire mai kahwara.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Tauraron gabas mijin Arziki gaishe ka na Murja,

D’an Garba farin wata Ali,

Yara:    Ka iske mutanen birni har da mutanen ƙauyuka.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Wane Sakkwato sun d’au kai mutumin kirki,

Dab baya ya yi lalata yat tabka abin kunya,

Yara:    Dan nan daraja tai tah hwad’i. ×3

 

Jagora: Mun gane shi mutunci madara ne,

Da ya zube a ƙasa,

Yara:    Ban san wani mai kwasa tai ba ×2

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ji wane d’an hwad’in rai,

Wai bai bid’ar sanata,

Shugaban ƙasa yaka so,

Bana ya yi bakan-baƙantantam,bai yi firesidan ba,

Kuma nan ga jaha tai ya hwad’i,

Ba zama Sakkwato,

Yara:   Sai dai ya tsaya kwatano,

Ko kuma ya wuce birnin Ghana.

 

Jagora: Wane ba zama Sakkwato,

Yara:    Sai dai ya tsaya kwatano,

Ko kuma ya wuce birnin Ghana.

 

Jagora: Yanzu ba zama binni,

Yara:    Sai da ya tsaya kwatano,

Ko kuma ya wuce birnin Ghana.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Mai jama’as siyasa,

Bana ya hwad’i ina magana?

Dan sakandare ya kasai ya shiga sabati,

Yara:    Bana ko magana tai ya noce.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Na difiti gwamna Muntari d’an Shehu,

Zaki na Alu A.A. na baba D’anda birnin Mana,

Kar ka ji tsoro,

Yara: Sa arna su shira kai ka shirya.

 

Jagora: Na baba D’anda birnin Mana ban da sakewa,

Yara:    Sa arna su shira kai ka shirya.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Gaisheka shugaba na matasa binni,

Har ƙauye gaishe ka Itali,

Yara:    Mai kwana da shiri ranar yaƙi.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

Jagora: Ahmed Aliyu ya ban mota saboda jin dad’i,

Yara:    Domin darajar sabon gwamna.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora:D’an da gabas ga Sakkwato gaishe Haji Gwanda Gobir,

Yara:   Bai maganar banza in yai magana ta bat tashi.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ambasada a gaishe ka,

Gai da Haji Ladan Shuni,

D’an masanin Sakkwato,

Yara:   Mai hora marasa imani.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Muntari baba maigona,

D’an Bello uwa yaƙi,

Ku an ka sani bunni,

Ku an ka sani ƙauyukka,

Yara:   Tun ana yaƙi an san da mutanen Yarlarɓe.

 

Jagora: Yanzu ko ana yaƙi,

Yara:   An san da mutanen Yarlaɓe.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Sai godiya ciyaman fati Arzika na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jaogra: A gaida tsalha Sidi Alhaji ya gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya ni kai Ila Gada Alahaji ya gode,

Yara:    Du yanda ya kan man ya kyauta.

Jagora: Gaishe ka Mai’akwai Yabo,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: D’angaskiya ina Ibrahim,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya nikai Loto ni Alhaji na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya Yahaya Haji D’an Buhari na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Muntari mafiya na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta,

 

Yaro: Dakata ɗanba’u akwai magana ni wajena,

Duw wanda yai alƙawali ƙila in ya mance,

Sai a tuna mai ubandawaki Shi’itu shi zai ba ni gida

ɗanba’u duka ni da mutane na,

Jagora/Yara: Ban koma zuwa kwana Loja.

 

Yara: Dakata ɗanba’u wanda yai alƙawali,

Sai a tuna mai wata ƙila takan yu ya manta,

Ubandawaki shi zai ba ni gida Sakwkato,

Kaf nida mutane na,

Jagora/Yara: Ban koma zuwa kwana Loja.

 

Jagora: Kaf ni da mutanena,

Yara:   Ban koma zuwa kwana Loja.

 

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ina Bala Musa,

Yara:    Du yanda yakai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya Bala Musa,

Du yanda ya kai man ya kyauta.

Amshi: Ƙara shirawa,

Aliyu zaɓaɓben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Yaro: Dama hanƙurin kwaram sai goga,

Wuyau ta sai ƙarfe,

Jure fari sai tofa,

Baba ruwa da kada ba a zuwa wanka,

Sai dai a tsaya kallo,

Yara: Wani ya shiga zai wanka,

Da ya shiga bai kai waje ba.

 

Jagora: Ba a zuwa wanka sai dai a tsaya kallo,

Yara:   Wani ya shiga bai kai waje ba.
 
www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments