Wannan ɗaya ce daga cikin jerin waƙoƙin da aka yi wa Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko (ALU). A hasashen manazartan Amsoshi, ALU shi ne gwamnan ƙasar Hausa da ya fi kowane gwamna yawan waƙoƙi da aka yi masa.
Rubutawa: Shehu Hirabri
08143533314
Aliyu
sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Ɗan Lamiɗo uban Lamiɗo,
Mai gaskiya na difiti gwamna,
Muntari bawan Allah,
Yara: Kwaj ja da kai sai ka gyara mai zama.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Shi aiki ya zo ga jahatai,
Ba ci da ceto na kawo shi ba,
Balle ya danne abin talakawa,
Yara: Abin nufatai aikin gaskiya.
Jagora: Safe duk,
Yara: Abin nufa tai aikin gaskiya.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Masu hwaɗin Ali ba ka gwamna,
Ku ‘yan adawa yaya za ku yi?
Kun ci kare ba wanki hannu,
Yara: Alƙawali Allah bai tashi,
Aliyu kai ag gwamnan Sakkwato.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Ga wasu sun ci amanar Allah,
Wane amana ta kama su,
An yi gidaje gandam-gandam,
Ga hwa gida daidai jin daɗi,
Yara: Ba a dama zamnawa ciki.
Jagora: Baƙin ciki ya kai musu geji,
Yara: An bar su sai dai yawo ta-zubar.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Ni ‘yan DPP nika kallo,
Sun shiga zaɓe an kashe su,
Sun ƙara kuma sun hwaɗi,
Saboda sun san daɗin mulki,
Yara: Wanda duk a ba ya da dangana,
Wanan rabonai kunya safe duk.
Jagora: Cikinsu kowa ya ƙi ya hanƙuri,
Wanda duk a ba ya da dangana,
Yara: Wannan rabonai kunya safe duk.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Shi iƙirari ba ya da kyawo,
Du wanda ka ga yana iƙirari,
To ƙyale shi kurum ka yi kallo,
Yara: Ka bar shi sai ta gyara mai zama.
Jagora: Wawa,
yara: Ka bar shi sai ta gyara mai
zama.
Jagora: Saga,
Yara: Ka bar shi sai ta gyara mai zama.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Ka zama gaba ka ci da aiki,
Mahassadanka suna da baya,
Yara: Mu je gabansu suna lalata,
Saboda ka hau dokin gaskiya.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Wane giyam mulki ta ɗibai,
Hay ya je Gada ya sha wallah,
Ya ce ko hullatai ya aje ƙasag ga,
Sai tai gwamnan Sakkwato,
Yara: Mai bindiga iskan ga talo-talo,
Bana ya hau dokin rantsuwa.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Babban-da-jika uban ƙuma sheri,
To bana ya yi tayatai ya gaji,
Da tsahe-tsahe da yanke-yanke,
Da tsahe-tsaye da yanke-yanke,
Da tsahe-tsahe da yanke yanke,
Sai nic ce mishi dori ka dangana,
Yara: Ba yadda ya so Allah ya yi ba.
Jagora: Wawa,
Yara: Ba yada ya so Allah ya yi ba.
Jagora: Jahili,
Yara: Ba yada ya so Allah ya yi ba.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Ka ga mutum-mutumi da kamar mutum,
Da ka ganai ka ga tsumma ne kurum,
Bai hana komai bai tare komai,
Ka yi shi don ya tsare ma goda,
Yara: Bai hana tsuntsu ɓata ma ita.
Jagora: Wannan,
Yara: Bai hana tsuntsu ɓata ma ita.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Allah wadan gurun kolo,
Da ɗai bai saba kashin kunya ba,
Shi bai saba kashin kunya ba,
Ba ka sani sai ka je gaisai,
In ya yi ma kyauta ka duba,
Ka dubi girmanai ka ga kyautar,
Yara: Abin akwai abin ban kunya ‘yan uwa.
Jagora: Wannan,
Yara: Abin akwai abin ban kunya ‘yan uwa.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Kwamishinan idikeshin Arzika,
Ka yi ciyaman kowa ya yaba,
To har yanzu da sauran aiki,
Yara: Muna da raunin ilmi Sakkwato.
Jagora: Arzika ka sani,
Yara: Muna da raunin ilmi Sakkwato.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Kwamishinan wasanni Ahmed,
Kwamishinan wasanni Amadu,
Ɗan Aliyu Sadaukin ɗa kake,
Ma’aikata sashen wasanni,
Duk inda kai magana ta zauna,
Yara: Ba su da dama canza ma ita.
Jagora: Na san,
Yara: Ba su da damar canza ma ita.
Amshi: Maganin wargi ɗan Garba,
Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,
Ba a kai ma reni ko kusa.
Jagora: Sai godiya Zabira ka yi ɗa,
Yara: Abin da yai man ya kyauta ƙwarai.
Jagora: Gai da Mu’azu Zabira Sakkwato,
Yara: Abin da yai man ya kyauta ƙwarai.
Jagora: Gai da mijin Alhajiya Arziki,
Mai hana ƙarya angon Murja,
Gai da mijin Alhajiya Arziki,
Mai hana ƙarya angon Murja,
Jikan Umaru kai dai gayya,
In sun so im ma ba su so ba,
Yara: Aliyu kai ag gwamnan Sakkwato.
Jagora: In sun so im ma ba su so ba,
Yara: Abin da yai man ya kyauta ƙwarai.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.