Ticker

6/recent/ticker-posts

Sassaka A Garin Dakin-Gari: Tasirin Zamani A Kan Gargajiya (6)

NA

ABUBAKAR ALIYU
1310106004


KUNDIN DIGIRI NA FARKO NA HAUSA (B. A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NAJERIYA. JAMI`AR USMANU DANFODIYO, SAKKWATO
www.amsoshi.com

BABI NA BIYAR

5.1 Kammalawa

Kamar yadda bayani ya gabata a cikin babuka da na kawo a can baya wannan ya na nuna sana’ar sassak’a ba abar yarwa ba ce. Sana’ar Sassak’a muhimmiyar sana’a ce a k’asar Hausa wadda ke kawo abubuwa da yawa na ci gaban al’umma da k’asa baki d’aya. Sana’ar sassak’a sana’a ce da al’ummar Hausawa suka gada kaka da kakanu kuma har yanzu al’ummar tana ta’ammali da ita haka ma har a nan gaba za a ci gaba da amfana da ita. Haka zalika har yanzu  zamani bai kawo wani canje-canje na a zo a gani a cikin sana’ar ba.

A wannan bincike nawa mai taken Sassak’a a Garin D’akin Gari Tasirin Zamani a kan Gargajiya na karkasa babuka ne zuwa gida biyar. A babi na d’aya na fara da shimfid’a da bitar ayyukan da suka gabata da hanyoyin gudanar da bincike da dalilin gudanar da bincike da muhimmancin bincike da farfajiyar bincike daga k’arshe na nad’e wannan babi. A babi na biyu kuwa na fara da shimfid’a sannan tarihin Garin D’akin-Gari da yanayin tattalin arzikin mutanen D’akin-Gari da yanayin k’asar D’akin-Gari daga k’arshe sai na rufe wannan babi da nad’ewa. A babi na uku na fara da kawo shimfid’a ta wannan babin sannan da gani ya kori ji da jerin kayan aikin sassak’a da ma’anar sassak’a da hanyoyin samun itace da masassak’a a garin D’akin-Gari da ire-iren itatuwan da ake amfani da su a wajen sassak’a da magungunan da ake samu ga masu sana’ar sassak’a. A k’arshe na rufe wannan babi da nad’ewa. A babi na hud’u kuwa na fara da shimfid’a da ma’anar zamani da kayan aiki da abubuwan da ake sassak’awa da tasirin zamani a kan sana’ar sassak’a da tasirin sana’ar sassak’a ga al’umma da matsayin sana’ar sassak’a a yau da kuma makomar sana’ar sassak’a nan gaba. A babi na biyar wanda ya ke shi ne k’arshe na kawo kammalawa da manazarta da kuma mutanen da aka yi hira da su a kan wannan sana’a ta sassak’a a garin D’akin-Gari tasirin zamani a kan gargajiya kuma da haka ne wannan babi ya zo k’arshe.

 

Manazarta

https://www.amsoshi.com/contact-us/

 

 

Post a Comment

0 Comments