Nazarin Littafin Dakika Talatin A Bisa Ra’in Mazahabar Zahiranci (3)

    Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

    NA

    ADO MAGAJII MUSA

    BABI NA BIYU

    TAKAITACCEN TARIHIN MARUBUCIN LITTAFIN DAKIKA TALATIN DA RUBUCE-RUBUCE

    • Shimfid’a


    Wannan babi ya yi magana ne a kan tarihin Ado Ahmed Gidan Dabino a tak’aice da gudummuwarsa a fagen Adabin Hausa da kuma ire-iren tafiye-tafiyensa da matsayin da ya rik’e a rayuwarsa.
    • Takaitaccen Tarihin Ado Ahmed Gidan Dabino

    Ado Ahmed Gidan Dabino (MON) shahararren marubucin littattafan Hausa ne a Arewacin Nijeriya, sannan kuma mai shiryawa da bayar da umarni a shirin fina-finan Hausa. Haka zalika d’an jarida ne mai zaman kansa.

    An haifi Ado Ahmed Gidan Dabino a shekara ta 1964, a garin D’anbagina da ke k’aramar hukumar mulki ta Dawakin Kudu. Ya girma a unguwar Zangon Barebari a cikin birnin Kano. Ya fara karatun allo (Alk’ur’ani) a makarantar marigayi Malam Rabi’u a unguwar Zangon Barebari tun yana yaro, da kuma karatun littattafai na Islamiyya a makarantar marigayi Shehu Tijjani na ‘Yanmata a shekarar 1971. Bai samu damar yin karatun boko ba yana k’araminsa, sai da ya girma, sannan ya shiga makarantar ilimin manya ta Masallaci (Adult E’bening Classes Kano) a shekara ta 1984 zuwa 1986.

    Ya yi makarantar sakandire ta dare (GSS Warure E’bening Session), a Kano a shekara ta 1987 zuwa 1990. Ya shiga Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) inda ya sami takardar shaidar difilomar k’warewa a kan yad’a labarai, wato (professional Diploma in mass communication) a Sashen Koyar da Aikin Jarida, a shekara ta 2004 zuwa 2005. Ado Ahmed Gidan Dabino yana da mata d’aya da kuma ‘ya’ya shida (6). K’aramar cikinsu ita ce Halimatu Sadiya wadda aka haifa a shekarar 2017.
    • Gudummuwar Ado Ahmed Gidan Dabino a Fagen Adabin Hausa

    Adabi fage ne babba da ya shafi kawo hoton rayuwar al’umma. A fagen adabin Hausa Ado Ahmed Gidan Dabino mutum ne da ya ba da gudummawa sosai da tarihi ba ya mantawa da shi. Ya rubuta littattafai da dama, da suka shafi rubutattun k’agaggun labarai (zube) da kuma wasannin kwaikwayo da tsara fina-finan Hausa  da gabatar da shirye-shirye a gidajen rediyo gida da waje domin bunk’asa adabin Hasua.

    • Rubutaccen Kagaggen Labari


    Rubutaccen k’agaggen labari wani fad’ad’d’en labari ne watau labari ne na zube wanda ake rubutawa da yake bayani game da mutum da yanayin zamantakewa, tare da kawo wani abu da yake faruwa a rayuwar al’umma. Haka ma abin yana iya kasancewa ko bai faru ba, amma ana hasashen faruwarsa (Bunza, 2011). Shi wannan nau’in rubutaccen adabin Hausa an fara samar da shi ne a shekarar 1933. Adabin ya bunk’asa a tsakanin shekarar 1984 zuwa 2010 lokacin da aka k’iyasta akwai littattai sama da 3,500 (Malumfashi, 2010). Daga wannan lokaci 1984 zuwa yau matasa masu yawa sun yi rubuce-rubucen k’agaggun labaran Hausa kan fannonin rayuwa masu yawa, aka kuma sami masu nazari da suka ba adabin nasu sunaye daban-daban. An kira rubuce-rubucen adabin da sunaye kamar Adabin Kasuwar Kano da littattafan soyayya da Adabin Hausa na zamani da Hadisan ‘Yan Kano da kuma Rayayyen Adabin Hausa (Malumfashi, 2002 da Adamu 2013). Ado Ahmed Gidan Dabino yana d’aya daga cikin matasan da suka kawo ci gaban wannan fanni na adabin Hausa.

    Ado Ahmed ya fara rubuta k’agaggen labari ne da wani littafi mai suna Inda So da K’auna 1,2 a shekarar 1991, wanda a halin yanzu ya mayar da shi littafi d’aya  a maimakon na 1 da na 2, kuma littafin yana d’auke da jigon soyayya. Tun daga wannan lokaci Ado Ahmed Gidan Dabino ya ci gaba da rubutun k’agaggun labarai har zuwa yau yana kuma bugawa mad’aba’a mai suna Gidan Dabino Publishers wanda ke Birnin Kano. Ya buga littattafai wad’anda suka had’a da:

    1. In da So da K’auna (1991)

    2. Hattara Dai Masoya (1992)

    3. Masoyan Zamani (1993)

    4. Wani Hanin ga Allah… (1994)
      • Wasannin Kwaikwayo (Rubutacce)


    Rubutaccen wasan kwaikwayo na d’aya daga cikin rassan rubutaccen adabin Hausa. Anfara samar da shi ne daga aikin wani Bature mai suna Dr. R. M. East. Shi wannan Bature ne ya rubuta wani littafin wasan kwaikwayo mai suna Sid’ Hausa Plays a shekara ta 1930, amma duk da haka Hausawa suna da wasan kwaikwayo na gargajiya (wanda suka gada iyaye da kakanni) kamar su langa da tashe da sauransu.

    Daga cikin ’yan k’asa, wato Hausawa, wanda ya fara rubuta wasan kwaikwayo shi ne Abubakar Tunau Mafara. Ya rubuta littafin wasan kwaikwayo mai suna Wasan Marafa a shekarar 1949 mai jigon tsafta. Haka zalika Ado Ahmed Gidan Dabino ba a bar shi a baya ba a wajen rubutun wasan kwaikwayo na zamani wad’anda suke d’auke da darussa daban-daban kamar su ilimantarwa da fad’akarwa da dogaro da kai da makamantansu. Littattafan wasan kwaikwayo wad’anda ya rubuta sun had’a da:

    1. Duniya Sai Sannu! (1997)

    2. Ina Mafita

    3. Malam Zalimu (2009)

    4. Dak’ik’a Talatin (2015)
      • Fim


    Fim wani ‘bangare ne daga kafar sadarwa ta lantarki wadda take samar da gani da ji da motsi, domin amfanin mutane masu yawa (Gidan Dabino da Yakasai, 2004). Tarihi ya nuna an fara samar da fim na Hausa a tsakanin shekarar 1980 zuwa 1984 a garin Kano da wasu k’ungiyoyi suka fara aiwatar da shi.  Al’amarin fim na Hausa ya ci gaba ya bunk’asa daga shekarar 1999, lokacin da marubuta matasa da dama suka mai da hankali ga shirya fina-finai da aiwatar da su (Malumfashi, 2002).

    Ado Ahmed Gidan Dabino yana d’aya daga cikin marubuta da suka taka muhimmiyar rawa a wajen samar da fina-finai na Hausa baya ga gudummawar da ya bayar ta fannin rubutaccen adabin Hausa. Wannan yana samuwa ne ta hanyar juya rubutun da ya aiwatar musamman na wasan kwaikwayo (rubutacce). Ya yi finafinai kamar haka:

    1. Malam Zalimu

    2. Ina Mafita?

    3. Dak’ik’a Talatin
      • Shirin Gidan Rediyo


    Shirye-shiryen rediyo suna da kusanci da dangantaka makusanciya da adabin Hausa, musamman idan aka yi la’akari da buk’atar labarai da zantukan hikima. Don haka ne ma Ado Ahmed Gidan Dabino ya dad’e yana gudanar da shirye-shirye a gidajen rediyo na gida da waje. Wani abun farin ciki shi ne duk wad’annan shirye-shiryen yana gudanar da su ne kyauta (ba tare da an biya shi kwabo ba). Shirye-shiryen nasa na gidajen rediyo sun had’a da:

    1. Alk’alami ya fi takobi (Freedom Kano)

    2. Duniyar Masoya (FM Shukura Nijar)

    3. Ji Ka K’aru (Rediyon Deustche Welle Germany)
      • Nadewa


    Wannan babi na biyu ya tattauna ne a kan tak’aitaccen tarihin Ado Ahmed Gidan Dabino da kuma ire-iren gudummawar da ya bayar a ‘bangaren adabin al’ummar Hausawa wanda suka shafi rubuce-rubucen k’agaggun labarai da na wasan kwaikwayo da shirin fina-finan Hausa da shirin gidajen rediyo da shirya mak’alu domin k’ara wa juna sani ko ilimi tare da inganta ayyukansa. Wanan shi ne d’an tak’aitaccen tarihin Ado Ahmed Gidan Dabino.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.