1. Da sunan
Ilaahu gwani karatu ya fara,
Tsaya ɗan’uwana ga salati mu ƙara,
Buƙata mu samu
tabarraki gun Tabara,
Zaman duniyarmu da lahira mun biɗe shi.
2. Karatunmu
yau ga zaman abota ya raɓa,
Kiyaye zama
bisa ƙa’ida kar a saɓa,
Da hulɗa da zance kar a kwaso a kwaɓa,
A zan sese-sese zama wuya ke gare shi.
3. Abota zaman
yarda da ƙauna aminci,
Ka cuɗanni in cuɗe ka ne ba butulci,
A baki da zuci
a jittu shi ne zumunci,
A koyaushe ɗaya ƙaunar yakai ɗaya ya gan shi.
---------------------------
-------------------------------
1. Da sunan
Ilaahu gwani karatu ya fara,
Tsaya ɗan’uwana ga salati mu ƙara,
Buƙata mu samu
tabarraki gun Tabara,
Zaman duniyarmu da lahira mun biɗe shi.
2. Karatunmu
yau ga zaman abota ya raɓa,
Kiyaye zama
bisa ƙa’ida kar a saɓa,
Da hulɗa da zance kar a kwaso a kwaɓa,
A zan sese-sese zama wuya ke gare shi.
3. Abota zaman
yarda da ƙauna aminci,
Ka cuɗanni in cuɗe ka ne ba butulci,
A baki da zuci
a jittu shi ne zumunci,
A koyaushe ɗaya ƙaunar yakai ɗaya ya gan shi,
4. Mutuncinku
bakin gwargwado kun fake shi,
Ɗabi’u na juna gwargwado an sane shi,
Wuraren da an
ka yi canjaras ba a fashi,
Barafeshiya aka maƙura kar ta
tashi.
5. A kan
kowace matsala a zan sa fahinta,
Idan zuciya ta
zaburo kar a bi ta,
A sa hankalin
natsuwa a kore fushinta,
A bar bin halinta na son a yanka ta
tashi.
6. Abota ba za
ta yi kyau ba in ba kusanta,
Tana wargajewa
in ana sa husata,
Zama ba ya kyau
in godiya ta ƙaranta,
Zukata cikin gumuni gaba na ta nishi.
7.
Abota ta na fi
gabanka ta zan adawa,
Zaman ƙeta tarko ne
mafarinsa rowa,
Zaman ɗari-ɗari aboki ya zan katawa,
Zaman tsegumi da raɗa hasumi ka tashi.
8.
Abokin aboki
bai da babban muƙami,
Abokin
rashin samun abokin kalami,
Yawaitan
abokai don biɗan kai ga tsomi,
Yana sa a gane halinka kowa ya ƙi shi.
9.
Abotan biɗan a sani ka sa cin mutunci,
Abotan
rashin ra’ayi ka kawo butulci,
Abotan
maso wani ka ji raggon fatauci,
Kashe kanka za ka yi babu riba gare shi.
10.
Abota da manya
tsegumi ke shigowa,
Abota da
yara ga babba zargi ka zowa,
Abota da
macce ka sa a hango kusurwa,
Idan babu daudanci ƙazanta gare shi.
11.
Abokin buƙata lokaci ke
gare shi,
Idan ta
biya a ware a ture batunshi,
Idan ta ƙi jawo ruwa a
nan za a ƙi shi,
Abotan a so ka, a ƙi ka, ciwo gare shi.
12.
Abokin zaman ƙarya zaton za a
samu,
Idan an
ga ci sunansa Nasamu-namu,
Idan an
ka tsinka wuya a ce: “wa ka kai mu?”
Da an hangi zai zauna wuri sai a tashi.
13.
Abokin ƙabilanci
bala’insa kissa,
Idan kar
ta san kar, dole kowa ya ƙosa,
Maci
goro bai riƙa gandi in ya ga marsa
Zama kan ƙabilanci bala’i gare shi
14.
Abokan
munafucci da tsince da giba,
Zaman
zurmuguɗɗu da tsegumi bai da riba,
Zama
juddadun a cikin zato yai musiba,
Zaman an yi an ce, wa ka ƙaunar ya yi
shi?
15.
Abokin da ke mazarin
ya san tanadinka,
A
koyaushe burinai ya rege cikinka,
Da duk
za shi al’amarinsa bai son ganin ka,
Ka sa mai ido, ka bi taka hanya, ka bar shi.
16.
Abokin da
harshenai yake zazzalowa,
Wajen ba
da labarinka in ya ga sanwa,
Asirranka
duk ya baza su gun ‘yan adawa,
Ka kauce, Tabaraka zai yi ma maganin shi
17.
Abokin adawa ba
ya ƙaunar a dace,
Ijabar
da Jalla ya yo yake son ta noce,
Idan ya
ga baiwa gun ka tamkar ya ƙwace,
Hawaye kamar su zubo gaba na ta nishi.
18.
Aboki na
tserereniya ba shi hanya,
Abin duk
da kay yo, zan yi ya zan hamayya,
Ana tare
an ƙi rufe takaici a ƙurya,
Zaman so ya hurhura har ya koma na kishi.
19.
Zaman yaudara
cutar abokin amana,
Ana
zaune tare cikin gaba na ta kuna,
Da duk
yag ga mai ra’ayin ka zai zo shi zauna
Shi ɓata ka dama da
hanni, wai don a so shi.
20.
Aboki ba zai ƙi zama da kai
shawari ba,
Ba zai ƙulla
al’amarinsa bamban da kai ba,
Ba zai
so taɓin irlinka in ba ka nan ba,
Da an so a muzantaka kai ka ba da bashi
21.
Aboki na gaske
ba zai yi zargin mutum ba,
Ba zai
yarda gun ka a zo da mugun zato ba,
Magabcinka
bai ga wurin laɓawa garai ba
Ina zai ganin sarari da fuska gare shi?
22.
Wurin kankajeli
shirin abota ka ɓaci
Garin
kakkaɓi motar abota ka faci
Katsal
na zube wa zaman abota mutunci
Kisisiniya na sa aboki a bar shi.
23.
Ka ce ba gawani
a gare ka wa za ya so ka?
Rashin
moriyarka na sa ana zulluminka,
A shaide
ka ba ka da moriya ko ta tsoka?
Abota da kai ƙarfin hali ɗai ka yo shi.
24.
Abota da Daɗin-kowa ɗai ad da ciwo,
Ya hau ɗan rabonka da ci kamar zai yi zawo,
Idan ya
farauto nasa ya kama yawo.
Shi ɓoye abinsa
cikin akwatin gilashi.
25.
Abotar taho mu
yi gardama kar ka yi ta,
Zaman
tare ga a barambaram ba fahinta,
Ɗaƙoƙi su tashi kamar a miƙe a kwafta,
Jiɓi na zuba kumfa
ga baki na haushi,
26.
Abota da mai
son kansa ɗai kar ka fara,
Bale
zarumin rikici da dokin gadara,
Da wawa
da shashasha ina mai dabara?
Bale sakarai asheraru ƙarya gare shi.
27.
Da mai shishigi
da yawan zaƙewa ga amri,\
Da mai
faifeye abu dole sai ya ga sharri,
Da mai
ba ka, in ka ɗaga ya far ma da gori,
Da mai son a ce, ya fi ka kirki, ka bar
shi.
28.
Butulci ka ɓata zama ka zan mai fahimta,\
Ana
taimakonka kana ta ƙwazon ka cuta,
Tukuicinka
cin zarafin abokin fahimta,
Zaman ba ni in cuce ka ciwo gare shi,
29.
Tunanin da nay
yi a da fahimtar aƙida,
Yana
kankare gaba da mugun makida,
Wajen
‘yan abarba da masu lemo da gwadda,
Maɗi bai kirari ga
zuma na ganin shi.
30.
Ashe hadda
mallamai abin ya shige su,
Abota
kaman dai ta fi muni cikinsu,,
Faɗin na fi wane sani ka watse zamansu,
Karatun kirari babu lada gare shi.
31.
Ana mazhaba ɗaya ɗan shiri- sai shi ware,
Ɗarikunsu sun yi dubu wane za ka kare,?
Ga ‘yan ƙungiya da kwaɗai da son rai ya cure,
Ana tare ci bamban takaici gare shi.
32.
A tarbe ka
lablablab kaman babu kissa,
Idan an
ka miƙe ƙafa karatun darussa,
Ga filin
Ta’ala za a soko dasisa,
Ta giba da ɓata, fashin baƙi sai a ba shi.
33.
Idan an ga
haske gun samari na sunna,
Ƙira’a gwanin sha’awa da manya da gunna,
A fannin
hadisi ya ci murya rawanna,
Ana tare za ka ji gobe an sallame shi
34.
Abotar karatu
yanzu ya zan na kishi,
Idan na
karantarshe ka na ba ka bashi,
Abin duk
da nac ce, so da ƙi, za ka bi shi,
Kamar Rabbana kai ne ya aiko gare shi
35.
Wajen masu tinƙahon karatun
shahada,
Abota a
baki a zucci ƙllin makida,
Sanin
yaz zamo tamkar karatun jarida,
Abotar kwaɗai makasarta shagon farashi.
36.
Wajen masu
mulki dubi saddan Husaini,
Zamanai
da Tarikh munzu dogon zamani
A ƙarshenta yai
sanadin kashewar Husaini,
Tukuicin ga mai muni ina isalin shi?
37.
Hukuncin ga an
yi irinsa Borkino-fasso,
Tomas
shugabansu da shi da Kampore fasso,
Abotansu
tai tsanani a Barkino-fasso,
Ya harbe Thomas sai lahira babu fashi.
38.
A Nijar da
Mainasara da Danda ƙasarsu,
Abokan ƙuƙut a firamare
an ka san su,
Gari ɗai bukinsu guda ga sabgar garinsu,
Ashe can a ƙirji ba ya ƙaunar ganin
shi.
39.
Ya sa bindiga
ta faɗa da jirgin sama’u,
Ta watse
shi ɗaiɗai babu bakin buka’u,
Abota ta
zan sababin bala’i fasadu,
Ashe duk zaman da ake da ƙunshi cikin
shi.
40.
Gawon yai irin
ta ga Murtala kar ku manta,
Tsakanin
Buhari da Iro in kun fahimta,
Zumuncin
Abacha Husaini sun so kusanta,
A ƙarshen abotar shan bala’in burushi.
41.
Ɗa Nzegu shi da Firimiya ba husuma,
Ya mai
da shi tamkar ɗa ga aikin hukuma,
Da yag
girma al’amarin musiba ya koma,
Takaici daɗaɗɗe nan ya huce hushinshi.
42.
Riƙe wanga tarihi
misali gare ka,
Aboki
idan ya yi zamba yay yaudare ka,
Ka sa
mai ido ka yi ƙoƙarin yafe naka,
Tuwon yaudara tuƙinsa tilas ya tashi.
43.
Ka yafe ƙanana da
manya-manyan jaza’i
Da mai
yi duƙunce da wanda ke ta balli,
Ka
saurari ƙarshen masu tunƙa da ƙulli,
Da ‘yan sa’ido komai suke ba a fashi.
44.
Da Maula da Bn
Ladan abin na da tsari,
Zama ne
na Allah ba jiyewa da gori,
Zukatansu
babu kwaɗai da gurin tujuri,
Hakuncinsu kowane ittifaƙi gare shi.
45.
Suna nan a raye
walau su kwanta shahada,
Ƙasa tasu ce komai tsanancin makida,
Irin
shimfiɗar da sukai ta gyaran aƙida
Jiragen Amerika babu mai kakkaɓo shi.
46.
Alu hayya! Kak
ka aboci ƙaton bahili,
Ibadarku
kowane lokaci kan ƙala’i,
Da mai
tattalin Allah Ya koro bala’i,
Ganin bai aje ba, baƙin nuhinai shi bi shi
47.
Abota da
malammai tana sa muruwwa,
Karatu a
kwasai arha sai an yi kuwwa,
A ƙauli guda an
zargi laifinku rowa,
Muridanku sun ka faɗi ga hanya na ji shi.
48.
Abokanku
ladannai da ke ta da murya,
Da
uttazu masu rabon nasiha a hanya,
Suna ƙorafin sadaka
da zakka ta manya,
A ɗan marmasa musu
gwargwado don su san shi.
49.
Tsaya in taƙaita ma abokan
amana,
Da mai
son ka, mai sha’awar ka, kullum shi nuna,
Da mai
son ganin ka a kulluyaumin ga sunna,
Da mai kau da kai ga kurenka in ya yi
girshi.
50.
Da mai tattalin
ƙullum ka dace ga harka,
Da mai
taulahin auki wajen arzikinka,
Da mai
son ganin ka, kana cikin hayyacinka,
Ka sa min da mai fatar ka samu ka ba shi.
51.
Idan kaɗ ɗaga kirkinka zai fassarawa,
Idan ka
taho wa’azi yake nanatawa,
Da lurar
da kai haɗarin zama ɗan adawa,
Da tausan gabanka da hanƙuri don ka yo
shi
52.
Shina son ganin
ka cikin mutane na kirki,
Ga
jaruntaka bai son ka gwabce da raki,
Rigayanka
kuka zai yi in ya ga miki,
Ya shafe jininka da kyau ƙuda kar su bi
shi.
53.
Ku duba ga
Makau Bawa babban ɓarawo,
Da Gambo
ya gan shi cikin jini babu kyawo,
Ya rugo
da shi asibitti yak kama yawo,
Da rai ɓace ceton ran abokin zaman shi.
54.
Ashe Bawa baƙu yo ya lafe
abinsa,
Da yal
lura an watse ya niƙe jikinsa,
Ya ce:
“Mai tafashe jijjiga babu kissa,
Ka dahe su in suna ta gunza da nishi”.
55.
Abokin da duk
bai kutso kai nai wurin ka,
Idan ƙaddara ta zo ya
zo taimakonka,
Mutane
su ƙi ka ya murje fuska ya so ka,
Ya yo ma nasiha gwargwadon hankalinshi.
56.
Masoyinka ba ya
gudunka komai musiba,
Tsayi
zai yi sai an gane tsada da riba,
Abokanmu
yanzu haƙiƙa in za ku duba,
Ana zaune fuska goma kowa da nashi.
57.
Kirana gare mu
a dole gyaran halinmu,
Musibar
ga ta yi yawa haba ‘yan’uwanmu!
Haƙiƙan idan Ustazu
ya tsai da gemu,
Walankeluwa ga zama ya zan ya guje shi.
58.
A nan ɗan Naturai zai rufe ƙorafinsa,
Kwatancin
Aliyu na Bunza in an ka bi sa,
Ana kai
ga cin nasarar zama babu kissa,
Zaman nan na da, a fahinta, gyara gare shi.
Aliyu
Muhammadu Bunza.
Alhamis
24/07/2014
Sakkwato,
Arkilla, 6:04.pm
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.