https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

 


NA


KUDU MUHAMMAD SALIHUKUNDIN DIGIRI NA FARKO A HAUSA (B.A HAUSA) DA AKA GABATAR A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO


 

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

 

BABI NA BIYAR


5.0 Shimfid’a


Babi na biyar, babi ne da ke buk’atar gabatar da sakamakon wannan bincike da abubuwan da aka gano a yayin gudanar da binciken wad’annan abubuwa aka ci karo da su wajen bincike wanda kuma ya sa’bawa tunanin mai bincike. Sannan kuma a kammala shi bayan kammalawa kuma sai shawarwari daga k’arshe kuma a zayyano manazarta.

5.1Sakamakon Bincike


Wannan bincike da na gudanar a kan dangantakar Hausawa da Nufawa, an sami cikakken haske a game da wad’annan al’ummun guda biyu irin huld’ar da ya shiga tsakaninsu na tsawon lokaci musamman abin da ya shafi tarihinsu. Haka kuma an sake samun haske a kan fuskokin danganta musamman yadda bayani ya gabata cikin wannan bincike na wasu sana’o’i irin su sabulun salo, da daddawa, idan mai karatu zai iya ziyarci wannan k’undin bincike, zai sami cikakken haske na yadda ake aiwatar da su tare da bin matakai, zai iya gabatar da sana’ar a sauwak’e. A k’arshe kuma an sami haske a kan tasirin ararrun kalmomi daga harshen Hausa zuwa Nufe da kuma na Nufe zuwa Hausa.

5.2 Kammalawa


Kamar yadda dai aka karanta daga farko, wannan aikin bincike an raba shi zuwa babuka biyar inda babi na farko ke d’auke da shimfid’a da manufar bincike da farfajiyar bincike da muhimmancin bincike da dalilan bincike da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar bincike sannan kuma nad’ewa.

A babi na biyu, an yi k’ok’arin fitowa da tarihin huld’ar Hausawa da Nufawa inda aka nuna tarihin kowanne daga cikinsu da mazaunin Nufawa da kuma nad’ewa.

A babi na uku kuma an yi bayani a kan dangantakar Hausawa da Nufawa tare da ba da ma’anar dangantaka da fuskokinta kamar ta addini irin su almajirci ko neman ilimi da malanta da jihadin tutar Shehu da kuma fatauci da zuwan Turawa da yak’e-yak’ensu da dangantaka na wasu al’adu kamar kayan k’walamar Bahaushe irin su k’osai da guguru da dakkuwa da gyad’a da kuma sana’ar d’inki da noma da kamun kifi da sabulun salo da daddawa da k’ira na fari da bak’in k’arfe da k’arau da kuma dangantaka ta auratayya kamar bikin aure da bikin haihuwa sannan kuma nad’ewa.

A babi na hud’u kuma an yi bayanin tasirinsu wato Hausawa da Nufawa inda aka fara gabatar da shimfid’a da ma’anar tasiri da yanayin tsarin aron kalmomi da dabarun aiwatar da aro da kashe-kashen aro da dalilan aro da matsalolin aro da kuma tasirin ararrun kalmomi tsakanin harsunan da kuma nad’ewa.

A  babi na biyar kuwa, babi na k’arshe, da farko an yi wa babin shimfid’a sannan sakamakon bincike da kammalawa da shawarwari da kuma manazarta.

 

5.3 Shawarwari


Akwai buk’atar ba da shawarwari na musamman ga al’ummun wad’annan harsuna guda biyu wato Hausawa da Nufawa a game da wannan aikin bincike nawa, don kuwa yana da kyau matuk’a su tunkari hanyoyin da zai wayar musu da kai  ta amfani da basira don inganta al’adunsu.

Ga kad’an daga cikin shawarwarin da za a bada:

  • Yana da kyau matasan wad’annan al’ummun su yi yunk’urin wayar da ‘yan uwa da abokai wajen nemo tarihin dangantakan da ke tsakaninsu domin yara masu tasowa su sami tarihin cikin sauk’i.

  • Haka kuma yana kyau su rik’e sana’o’insu na gargajiya musamman noma da d’inki kada su yi sakaci wajen dogara ga aikin gwamnati, su yi amfani da k’arfin basirarsu wajen dogaro ga kai don akwai alfanu masu d’imbin yawa a ciki.

  • Yana da matuk’ar kyau idan masu karatu ko kuma idan masu harsuna su kansu za su tuntu’bi wannan aiki wajen bin matakai na wasu sana’o’i musamman sana’ar sabulun salo da sana’ar daddawa, zai kawo musu amfani sarai ko kuma ya zamo mabud’in arzikinsu.

  • Akwai buk’atar al’ummar Nufawa su tashi tsaye wajen yi wa harshensu aiki ta yadda za a koyar da yara asalin kalmomin harshensu domin su rabu da irin barazanan tasirin da harshen Hausa ta yi a kansu, su kuma fara koyar da harshen musamman a makarantun firamare da kuma sakandire.

  • Haka kuma, yana da kyau matuk’a ga al’ummar Nufawa su yi taka tsan-tsan wajen yin amfani da kalmomin asali na harshensu, kuma su guji yin aro barkatai daga wani harshe daban wanda kuma na iya zamo sanadiyar mutuwar harshensu.

  • Har wa yau, yana da matuk’ar kyau ga al’umma ta Nufe da su da su taskance kayan tarihinsu don gudun ‘bacewa musamman irin su k’amusun harshen da kuma wasu aikace-aikace makamantan hakan.


A k’arshe ina mai k’iran wad’annan al’ummun wato Hausawa da Nufawa da babbar murya da cewa sun sami gagarumin k’ima a idon duniya kuma suna al’adu makusanciya irin ta addinin musulunci, don haka, su yi k’ok’arin kare addininsu domin girma da d’aukaka ya ci gaba da gudana kada su sake su gu’bata da tasirin zamani.

 

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/