Sauraro Da Rubutawa
Hirabri Shehu Sakkwato
08143533314
Amshi: D’antakarar zama gwamna,Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Wask’ar ga tamu mun soma ta,
Mun fara ta da rok’on SAllah,
In Allah ya so ya yarda,×2
Yara: Gwamnanmu mun yi mun k’are.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Baba in dai kana shirin yak’i ka fito,
In ka ga ba ka yi ka gaya min,
Siyasar jahar ga in bar ta,
Yak’i sai da uwa d’an Barade ×2
Yak’i babu uwa banza ne,
Yara: Har k’ara ma zaman karta.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Ni na tabbata kana da basira,
Na sani kana da tunani,
To amma fa ka k’ara kulawa,
Angulu munahukin Allah ne, ×2
Yara: In ka ganai wurin yak’i,
Shi ba da gaske ya zo ba.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Mun san masu takarar gwamna,
‘Yan takara zama mun san su,
‘Yan shaye-shaye mun san su,
Mun bar wane d’an wiwi ne, ×2
Yara: Can nig ganai cikin lungu,
Ya la’be ana yi mai moli.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Tun sadda wane yai gwamna,
Martaba jaharmu ta hwad’i,
Mai ilimi da marar ilmi,
Dole ne a samu bambanci,
Ku Sakkwatawa albishirinku,
Ga d’an uwanku nan d’anku,
Shi za ya takarar gwamna,
Ku daure ku ba shi goyon baya,
Yara: In Aliyu ya zamo gwamna,
Martabar jaharmu ta tashi.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Yanzu kowa ka cin amanar jama’a,
A kwan a tashi ‘Danba’u,
Sai ka ganai cikin tarko,
Tarkon da ba ya hishshe shi,
Ji wanda a cikin jama’atai,
Sai ga shi yanzu ya bar su,
Wad’anga nan da ya samu,
Ya bid’o abarba don ya raba musu,
Yara: Sai ga abarba tai tsutsa.
Jagora: Da ya bid’o abarba don ya raba musu,
Yara: Sai ga abarba tai tsutsa.
Jagora: Sakkwato mun canza masu suna,
Ba ‘yan abarba a sunansu ba,
Yara: ‘Yan tukuwa d’iyan d’id’i.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Tsaya abin ga na da mamaki,
Birnin da k’auye na duba,
Kuma manya da yara na duba,
Yara: Duk inda ka ishe d’an abarba,
Ya iya shirin munahucci.
Jagora: Wannan,
Yara: Ya iya shirin munahucci.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au wulak’anci.
https://www.amsoshi.com/2018/01/12/na-tinkari-tsautsayi-da-shirin-yaki-tawakkali-ta-tsai-da-ni/
Jagora: Ni ‘Danba’u hamdullahi,
Na yi godiya wajen Allah,
Siyasar su wane ta watce,
Yau shekara takwas suna mulki,
Girman sakarakuna sun kasai,
Ga d’an talakka ya sha k’waya,
Wai za ya kori sarkinmu,
Kahin ya kori sarkinmu,
Allah ya biya buk’atunmu, ×2
Yara: Sai ga sakamako ya yi,
Shi ya rigaye hisshe shi.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: A yanke mutum a yanke dabba,
Don tattalin bak’in tsahi,
Don d’ai a hau kujerar mulki ×2
Yara: In lokacinka ya k’are,
Tsahinka duk na banza ne.
Jagora: Wawa,
Yara: In lokacinka ya k’are,
Tsahinka duk na banza ne.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Ga magatakrda ga Muntari,
To amma fa ku k’ara kulawa,
In dai abin rabo ya samu,
A damk’a ma masu imani ×2
Don kada a baiwa kuraye shi ya,
Yara: In sun had’e shi an huta.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Mu Sakkwatawa sannu da aiki,
A gaishe ku Sakkwatawan Shehu,
Na gaishe ku Sakkwatawan Shehu,
Na tabbata kuna da d’iyauci,
Domin abarba kun k’i ta,
Sai yawo sukai suna k’arya.
Yara: Sun rikirkice musa,
Sai hwad’a sukai da junansu,
Harkarsu ta yi dameji.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: An tsaida wane takarar gwamna,
Kare mai bak’in jini da yawa,
Yara: Du inda ya bi ya hurce,
‘Yan yara na yi mai yihu.
Jagora: Yihu kare.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Ina d’an buga-buga wane,
Ya lek’a Gabas ya lek’a Yamma,
Ya lek’a Gusun ya lek’a Arewa,
Kullum wurin muna hucci,
Ba Sakkwato noz ba da Sakwkato,
Yara: Ko isa mun hi k’arhinsa.
Jagora: Wawa,
Yara: Ko Isa mun fi k’arfinka.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Kowa tasu tare da manya,
Ka san yana da tarihi,
Don haka manya sunka gaya mini,
Yara: Danginsu Maguzawa ne.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Na iske wane na ta jawabi,
Ya ce Sakkwato duk kaji muke,
Shi bai bid’ar mu sai ran za’be,
Nan take za ya jawo mu,
Yara: Yanzu talakawa sun gane,
Nerarka ba ta jawo su.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Ku k’ara shiri in za ku shirawa,
Ku ja d’amara in za ku shirawa,
An ce mahaukaci ya ratce,
Ya shedi ba ya kaffara,
Sai ya yi gwamna Sakkwato binni,
In kunka yarda yai gwamna,
Yara: Irinta dauri ta dawo,
Har yau muna cikin k’angi.
Jagora: Idan ka gane ni da manyan kud’d’i,
Aljihuna ya cika damfam,
Yara: To kar ka tambaya Malam,
Tambarin Tahida yab ba mu.
Jagora: Idan ka ga babura sababbi,
An lodo an kai Illela,
Har ana bid’ar gidansu ‘Danba’u,
Yara: To kar ka tambaya malan,
Yahaya Buhari yab ba mu.
Jagora: Idan ka ga riguna sabbi,
Aska biyu d’unkin Zazzau,
Yara: To kar ka tambaya malan,
Ladan na Shuni yab ba mu.
Jagora: Na gaishe ka ciyaman fati,
Arzika Tureta d’an girma,
Ka taimaka ma ‘ya’yan bunni,
Ka taimaka ma ‘ya’yan k’auye,
Gulbi babu jira sai kwalhwa,
Yara: Kowa ishe ka ya samu.
Jagora: Baba,
Yara: Kowa ishe ka ya samu.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au walak’anci.
Jagora: Idan ka gane ni da babba mota,
Kuma motar nan tsadadda ce,
Kuma motar nan mai tsada ce,
To Muntari ka sai mini mota,
Yara: To kar ka tamaya malam,
Na ishe mataimakin gamna.
Jagora: A gaishe ka mataimakin gwamna,
Ga jikan Mahmadu Gummi nan,
D’an malam kake jikan Malam,
Yara: Yak’inka ya yi rinjaye.
Amshi: D’antakarar zama gwamna,
Magatakarda Wamakko,
Aliyu kar ka d’au reni,
Kuma kar ka d’au wulak’anci.
Jagora: Na gode wa Haji Muntari d’an Bello,
Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.
Jagora: A D’alha Sidi Uban ‘Danba’u,
Duk yanda ya yi ya kyauta.
Jagora Alu A.A. Alu d’an boko,
Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.
Jagora: A gaishe ka mai matasan bunni,
A gaishe ka mai matasan k’auye,
Nasiru Itali na gode ma,
Yara: Duk yanda ya yi ya kyauta.
1 Comments
[…] Wak’ar Aliyu Magatakarda Wamakko, Mai Suna Gwamnanmu Mun yi Mun K’are Ta Alhaji Musa ‘Danba’… […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.