Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako Ta Alhaji Musa Danba’u GidanBuwai

Sauraro Da Rubutawa
Hirabri Shehu Sakkwato
08143533314

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

Jagora: D’an Lamid’o uban Lamid’o,

Mai gaskiya na difiti gwamna,

Muntari bawan Allah,

Yara:    Kwaj ja da kai sai ka gyara mai zama.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Shi aiki ya zo ga jahatai,

Ba ci da ceto na kawo shi ba,

Balle ya danne abin talakawa,

Yara:    Abin nufatai aikin gaskiya.

 

Jagora: Safe duk,

Yara:    Abin nufa tai aikin gaskiya.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Masu hwad’in Ali ba ka gwamna,

Ku ‘yan adawa yaya za ku yi?

Kun ci kare ba wanki hannu,

Yara:    Alk’awali Allah bai tashi,

Aliyu kai ag gwamnan Sakkwato.

https://www.amsoshi.com/2018/01/12/na-tinkari-tsautsayi-da-shirin-yaki-tawakkali-ta-tsai-da-ni/

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Ga wasu sun ci amanar Allah,

Wane amana ta kama su,

An yi gidaje gandam-gandam,

Ga hwa gida daidai jin dad’i,

Yara:    Ba a dama zamnawa ciki.

 

Jagora: Bak’in ciki ya kai musu geji,

Yara:    An bar su sai dai yawo ta-zubar.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Ni ‘yan DPP nika kallo,

Sun shiga za’be an kashe su,

Sun k’ara kuma sun hwad’i,

Saboda sun san dad’in mulki,

Yara:    Wanda duk a ba ya da dangana,

Wanan rabonai kunya safe duk.

 

Jagora: Cikinsu kowa ya k’i ya hank’uri,

Wanda duk a ba ya da dangana,

Yara:    Wannan rabonai kunya safe duk.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Shi ik’irari ba ya da kyawo,

Du wanda ka ga yana ik’irari,

To k’yale shi kurum ka yi kallo,

Yara:    Ka bar shi sai ta gyara mai zama.

 

Jagora: Wawa,

yara:     Ka bar shi sai ta gyara mai zama.

 

Jagora:  Saga,

Yara:    Ka bar shi sai ta gyara mai zama.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Ka zama  gaba ka ci da aiki,

Mahassadanka suna da baya,

Yara:    Mu je gabansu suna lalata,

Saboda ka hau dokin gaskiya.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Wane giyam mulki ta d’ibai,

Hay ya je Gada ya sha wallah,

Ya ce ko hullatai ya aje k’asag ga,

Sai tai gwamnan Sakkwato,

Yara:    Mai bindiga iskan ga talo-talo,

Bana ya hau dokin rantsuwa.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Babban-da-jika uban k’uma sheri,

To bana ya yi tayatai ya gaji,

Da tsahe-tsahe da yanke-yanke,

Da tsahe-tsaye da yanke-yanke,

Da tsahe-tsahe da yanke yanke,

Sai nic ce mishi dori ka dangana,

Yara:    Ba yadda ya so Allah ya yi ba.

 

Jagora: Wawa,

Yara:    Ba yada ya so Allah ya yi ba.

 

Jagora: Jahili,

Yara:    Ba yada ya so Allah ya yi ba.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

 

Jagora: Ka ga mutum-mutumi da kamar mutum,

Da ka ganai ka ga tsumma ne kurum,

Bai hana komai bai tare komai,

Ka yi shi don ya tsare ma goda,

Yara:    Bai hana tsuntsu ‘bata ma ita.

 

Jagora: Wannan,

Yara:    Bai hana tsuntsu ‘bata ma ita.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Allah wadan gurun kolo,

Da d’ai bai saba kashin kunya ba,

Shi bai saba kashin kunya ba,

Ba ka sani sai ka je gaisai,

In ya yi ma kyauta ka duba,

Ka dubi girmanai ka ga kyautar,

Yara:    Abin akwai abin ban kunya ‘yan uwa.

 

Jagora: Wannan,

Yara:    Abin akwai abin ban kunya ‘yan uwa.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Kwamishinan idikeshin Arzika,

Ka yi ciyaman kowa ya yaba,

To har yanzu da sauran aiki,

Yara:    Muna da raunin ilmi Sakkwato.

 

Jagora: Arzika ka sani,

Yara:    Muna da raunin ilmi Sakkwato.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Kwamishinan wasanni Ahmed,

Kwamishinan wasanni Amadu,

D’an Aliyu Sadaukin d’a kake,

Ma’aikata sashen wasanni,

Duk inda kai magana ta zauna,

Yara:    Ba su da dama canza ma ita.

 

Jagora: Na san,

Yara:    Ba su da damar canza ma ita.

 

Amshi: Maganin wargi d’an Garba,

Aliyu sabon gwamnan Sakkwato,

Ba a kai ma reni ko kusa.

 

Jagora: Sai godiya Zabira ka yi d’a,

Yara:    Abin da yai man ya kyauta k’warai.

 

Jagora: Gai da Mu’azu Zabira Sakkwato,

Yara:    Abin da yai man ya kyauta k’warai.

Jagora: Gai da mijin Alhajiya Arziki,

Mai hana k’arya angon Murja,

Gai da mijin Alhajiya Arziki,

Mai hana k’arya angon Murja,

Jikan Umaru kai dai gayya,

In sun so im ma ba su so ba,

Yara:    Aliyu kai ag gwamnan Sakkwato.

 

Jagora: In sun so im ma ba su so ba,

Yara:    Abin da yai man ya kyauta k’warai.

 

 

 

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.