NA
ALIYU MUSTAPHA
BABI NA BIYAR
KAMMALAWA
5.0 Shimfid’a
Wannan babin zai yi wiwaye ko tak’aita bayanan da ke cikin babukan da suka gabata a dunk’ule, sai kuma mu kawo sakamakon bincike irin ababen da za a iya hangowa a cikin binciken wannan shiri na labarin wasanni, sai daga k’arshe mu kawo shawarwari dangane da shirin labarin wasanni daga masu sauraro dangane da abin da ya shafi shirin.
5.1 Tak’aitawa
Kamar yadda bayani ya riga ya gabata a cikin babi na d’aya, mun yi k’ok’arin kawo irin gudummuwar da magabata suka bayar a matsayin ayyukan da suka gabata a kan shiraruwan gidajen rediyo. Da kuma yin tsokaci a kan tarihin gidan rediyon BBC Hausa. Sai babi na biyu, inda muka yi bayi kan tsarin rukunin jama’a, nau’o’in Hasua da kuma matsayin da harshen Hausa ya kai a kafafen yad’a labarai na duniya. Sai babi na uku wanda ya k’unshi manufar shirin labarin wasanni, zubi da tsarin shirin, da kuma yadda ake shiryawa da gabatar da shirin musamman ta fuskar nishad’antarwa, da kuma samun masaniyar irin wainar da ake toyawa a dunyar wasanni.
A babi na hud’u kua, an yi nazari ne a kan Hausar shirin labarin wasanni. Sai babi na biyar, wanda ya k’umshi kammalwa ta hanyar tak’aita bayanan da suka gabata, da sakamakon bincike, da kuma shawarwari, sai manazarta da kuma rataye.
https://www.amsoshi.com/2018/01/07/aladun-mutuwar-maguzawan-kambari-na-birnin-yawuri/
5.2 Sakamakon Bincike
Mun fahimci cewa jinsin maza da mata dun suna sauraren shirin labarin wasanni. Amma kuma, cikin kashi d’ari (100%), kashi casa’in (90%) maza ne inda aka bar jinsin mata da kashi goma (10%). Hasashe ya nun acewa, kowanne mataki na shekaru gwargwado musamman ma matasa suna sha’awar wannan shirin. Saboda haka, wannan shirin na labarin wasanni ya kasance abokin hira ga masu saurarensa. Musamman don samun nishad’i, tare a samun labaran irin wainar da ake toyawa a duniyar wasanni wanda ya shafi sana’ar wasan k’wallon k’afa da ma sauran wasanni na ciki da wajen k’asashen duniya.
Haka kuma, mun fahimci cewa matasa na samun nishad’i sosai, a yayin da suke kallo ko sauraren shirin labarin wasanni. Bugu da k’ari, mun fahimci cewa shirin labarin wanni yana k’arfafa guiwar masu sha’awar sana’ar wasan domin su rik’i sana’ar da muhimmanci kuma us ba da himma domin su samu abin dogaro da kai.
5.3 Shawarwari
Wannan aikin yana ba da shawara ga manazarta Hausa dukansu (malamai da d’alibai), da ma’aikatan watsa labarai na gidajen rediyo daban-daban da su duba wad’annan matsalolin da kyau, domin a san ta inda za a ‘bullo musu. Tawannan fuskar wanan kundin yake ganin ya kamata:
- A rik’a bin k’a’idojin rubutu wajen tsara labaran da ake yad’awa a shafin intanet.
- A rik’a amfani da alamomin rubutun Hausa domin inganta rubutu.
- A rik’a amfani da kalmomi amsu k’ugiya domin samun daidaituwa da kumka fito da ma’ana ta asali.
- Ya kamata a rik’a raba kalmomi da ba su kamata a had’e ba, a kuma had’e kalmomin da ba su kamata a raba ba domin cika k’a’idojin rubutu.
- Masu sauraro na k’orafin a k’ara lokacin shirin a kuma daina yin sa a gurguje domin samun sauk’in fahimta.
4.4 Nad’ewa
Masu hikimar magana kan ce: “Komai nisan dare gari zai waye” haka kuma komai nisan jifa k’asa za ta dawo, Bugu da k’ari komai ya yi farko, to zai kai k’arshe. Wannan zancen aka yake, domin kuwa nan ne muka kawo k’arshen wannan babin. Babi na biyar, babi ne na kammalawa wanda yake waiwaye ko tak’aita bayanan abubuwa da suka gabata a cikin babukan da suka gabata a dunk’ule. Sai a kawo sakamakon bincike, inda aka gabatar da irin abubuwan da aka gano ko aka fahimta dangane da abin da aka yi bincike a kai. Sai kuma aka ba da ‘yan shawarwari ga manazarta da suka had’a da malamai da kuma d’alibai da kuma ma’aikata da lamarin ya shafa.
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
Rataye
Manchester city ta lalalsa Real Madrid da ci 4 – 1 a los Angeles a wasan sada zumunci da suka buga domin shirin tunkarar kakar was ta bana. Kocin mancity pep Guardiola ya ce Benjamin mendy wanda ya saya kan kud’i fam miliyan 52 ba zai taka leda na mako biyu ba bayan wasan na Amurka.
Mutum 93,000 ne suka kalli yadda city ta samu ansararta ta farko a wasannin shirin sabuwar kaka da kwallaye daga Niceolas otamendi da Reheem Sterling da johnestones da kuma d’an shekara 17 Barahim Diaz. A rashin mendy Danilo ya buga wasansa na farko a filin wasa Los Angeles memorial Coliseum inda mai shekara 26 din wanda dan asalin kasar Brazil ne ya buga baya ta gefen hagu. Ya dai fuskanci tsohon kulob dinsa bayan mancity ta saye shi kan kudi fam miliyan 26.5.
Manchester city ta kashe sama da fam miliyan 200 a lokacin bazarar nan kan kyle walker (familiyan 45) da Bernardo Sil’ber (fammiliyan 43) da Ederson moracs (fam miliyan 43) da Benjamin mendy (fam miliyan 52) da kuma Danilo (fam miliyan 26.5).
Real madrid da barcelona za su fara El-clasico a ranar 30 ga watan yuli a Amurka:- Real madrid da Barcelona za su fafata a wasan hamayya da ake kira el-clasico a filin wasa na Hard Rock dake miami a birnin floridan Amurka a ranar 30 ga watan Yuli. Kungiyoyin biyu za su sake karawa a ranar 13 ga watan Agusta a spanish super cup wasan farko a camp Nou. A kuma rana ta 16 ga watan Agusta za a buga wasa na biyu tsakanin Real madrid mai rike da kofin laliga da Barcelona mai copa delrey a santiago Barnabeu.
Mancity ta lalalsa Hull city da ci 3-1:- kulob din manchester city ya lallasa Hullcity da ci 3 – 1 a fafatawar da suka yi ranar Asabar din nan a gasar premier ta Ingila 8 Aprilu 2017.
Man United ta doke sunderland da ci 3 – 0 :- kungiyar kwallon kafa ta manchester united ta yi nasarar doke sunderland da ci 3 – 0 a karawar da suka yi ranar lahadin nan a gasar premier ta Ingila 9 Aprilu 2017
Dan wasan real madrid Cristiano ronaldo shi ne yafi kowa zura kwallaye a gasar turai inda a yanzu ya ke da kwallaye 100 sakamakon biyun da ya zura a ragar Bayernmunich a ranar laraba.
Ina nan daram a Chelsea Conte:- kocin Chelsea Antonio Conte ya nanata sha’awarsa ta ci gaba da zama a Chelsea duk da rade-radin da ke cewa zai koma italiya.
Feneretin Atletico madrid na boge ne:- kocin leciester city craig shakespeare ya ce fenaretin da aka bai wa Atlentico madrid na boge ne 13 Aprilu 2017.
“shaw ya yi amfani da kwakwalwata ne” mourinho:- kocin manchester united jise mourinho yace mai tsaron gidan kulob din luke shawi na amfani da gangar jikinsa ne kawai amma kwakwalwar mourinho ya ke buga kwallo da shi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.