Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Zaman Gandu A Garin Zazzau (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

SHEHU MUHAMMAD TAFIDA

BABI NA HUDU; Takaitawa Da Kammalawa

4.0 SHIMFI’DA


A cikin wannan babin na hud’u kuma na k’arshe ne aka kawo tak’aitattun bayanai dangane da aikin da aka yi nazarinsa, Daga shi sai jawabin kammalawa, da k’arshe aka rufe babin da shawarwari.

4.1  TAK’AITAWA


Komai nisan jifa, ance k’asa za ta fad’o. Kamar yadda aka fara wannan aikin ga shi Allah ya kawo k’arshensa. Kamar yadda aka fad’a a baya, an yi nazarin wannan aikin ne a kan zaman gandu musamman a garin Zazzau.

Saboda haka ne ya sa aka tsara binciken ya zuwa babuka hud’u , domin samun sauk’in fahimtarsa. A babi na farko an fi mai da hankali ne ga ayyukan magabata inda suka maganta dangane da zamantakewar iyali a k’asar Hausa. sai dalilin bincike, inda aka nuna cewa anyi shi ne domin zak’ulo wasu muhimman abubuwa da ta yiwu ba a kain gare su ba, ko ba a tsara su yadda ya dace ba. Yayin da farfajiyar binciken ta bayyana yadda Zagi- zage ke kula da rayuwar iyalinsu ko  zuriyarsu don ba da gudumuwa ga duk wata al’uma da ba ta da irin wannan fasali da tsari na kula da zuriya. A mahimmacin bincike kuwa aka ce saboda kulla zumunci  da kare zuriya daga gurbata daga wata mummunar  al’ada. Daga nan sa hanyoyin gudanar da bincike inda aka nuna cewa anbi diddigin ayyukan da suka gabata, musamman wad’anda suka shafi al’adar  zamantakewar  al’uma.

A babi na biyu kuwa nan ne aka kawo ma’anar kalmar zama, kamar yadda masana suka kalli kalmar haka kuma sun ba da ma’anar gandu bisa ra’ayoyin. Inda aka bayyana ma’anar kalmomin da cewa; zaman tare na zuriya ko  al’umma da suke k’ark’ashin jagorancin mutum d’aya, a matsayin shugabansu. Sai zamantakewar Bahaushe da iyalansa, inda aka nuna yadda maigida yake zaune da ‘ya’yansa da jikoki, da tatta’ba kunne, a k’ark’ashin jagorancinsa. Daga nan sai yanayin zamantakewar gargajiya, inda a nan ne aka nuna ingancin da zamantakewar  ke d’auke da shi, an bayyaa yadda fasalin zama yake da kuma ire-iren yanayin rayuwa. Kamar jaruntaka da d’a’a, da gaskiya, da rik’on amana, da zumunci da hak’uri a duk wanni halin rayuwa da mutum ya tsinci kansa a ciki. Sai yanayin zamantakewa na zamani, inda aka nuna cewa ; zamantakewar Hausawa  ta fara sauyawa ne sakamakon shigowar bak’in Larabawa da suka zo da addinin musulunci. Bayan had’uwarsu da Larabawa sai bak’in Turawa ‘yan mulkin mallaka da suka bar mana gadon al’adunsu, da d’abi’unsu, da ma yanayin zamantakewar tasu.

A babi na uku kuwa sai aka kawo yanayin zamantakewar  iyali a garin Zazzau har aka nuna yadda ake aiwatar a shi. Irin wannan zamantakewar a garin Zazzau ana kiranta zaman gandu. An kawo yadda jagoranci yake tare da ayyukan ci gaba da ake samu a zamantakewar gandu. Inda aka nuna  zuriya ce kan had’a kai don gudanar da wani aiki da zai kawo wa zuriyar ci gaba. Sai zummunci da matsayinsa a zaman gandu. An bayyana shi da cewa shi ne tushen rayuwa da yake kula da taimakon juna da ayyukan ci gaba na zuriyar wanda ya shafi taimakon kai da kai ta fuskokin rayuwa. Daga shi sai kimar matan ‘yan’uwa, an nuna k’annen miji kan d’auki matan yayyensu tamkar abokan wasa (taubashi), yayin da suke yi masu ba’a da maganganun barkwanci. Amma kuma sukan d’auki matan yayyensu tamkar iyaye yayi da suke neman wani abu na rayuwa, kamar nemar aure ko neman wata shawara da ta shafi wata matsala ta rayuwa.

 

 

4.2  JAWABIN  KAMMALAWA


‘Dan’Adam ko ina yake a duniya ba ya iya gudanar da zamantakewarsa shi kad’ai, wannan ne ya sa shi neman abokiyar  zama, ta hanyar aure. Wannan hanya ita ce tushen kafuwar al’umma, ta irin wannan hanyar zamantakewar  ne al’ummar Hausawa musamman na garin  Zazzau suka k’irk’ira ma kansu, zamantakewa irin ta gandu domin samun kariya daga abokan gaba, da taimakon juna, da samar da cikakkiyar tarbiyar ga al umma.

4.3 SHAWARWARI


Saboda inganci da muhinmaci zamantakewar Hausawa tare da irin rawar da zamantakewar yake take takawa wajen tsarin shugabanci, da kula da tarbiyar iyali, da cud’anyarsu da sauran jama’a. zai yi  kyau a cusa wannan a cikin manhajar karatu, tundaga firamare har zuwa ga jami’o’i. Wannan zai bai wa d’alibai damar fahimtar yadda ake gudanar da zaman tarayya tun daga gida da kuma irin rawar da al’umma kan taka.wannan zai  kawo k’arshen zaman daga kai sai ‘ya’yanka, domin a koma ga tsarin zamantakewar da aka gada kaka da kakanni.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments