Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Zaman Gandu A Garin Zazzau (4)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

SHEHU MUHAMMAD TAFIDA

BABI NA UKU; Zaman Gandu a Garin Zazzau

3.0 SHIMFI’DA


A cikin wannan babin an kawo yanayin yadda tsarin zamantakewar iyali yake a garin Zazzau domin fito da tsarin rayuwar Zagezagi. Sannan an nuna yadda jagoranci yake a k’asar Zazzau tare da bayyana ire-iren ayyukan ci gaban da ake gudanarwa domin raya iyali. An kawo yadda zumunci yake a rayuwar zaman gandu. Sannan aka nad’e babin da tak’aitaccen bayanin aikin da babin ya k’unsa.

3.1 ZAMANTAKEWAR IYALI A ZAZZAU.


Iyali  rukuni  ne na jama’a wad’anda suke zaune bisa tsarin shugabanci na miji (maigida) da mata (uwar gida) da ‘ya’ya da jikoki da duk  wani wanda ya kamata maigida ya d’auki nauyinsa na rayuwa.

Zamantakewar  iyali a k’asar Zazzau yana da tsari na musamman wannan tsari shi ake kira da zaman gandu. Zaman gandu shi ne inda maigida yake d’auke da nauyin dukkanin zuriyarsa. Tun daga matansa da ‘yan’uwansa da ‘ya’yansa da na dangi da duk wani mahaluki da maigida ke d’auke da nauyin kula da rayuwarsa.

Irin wannan  zaman ana gudanar da shi ne, a wani irin babban gida mai d’auke da fasalin sa-sa, wato kusan kowace k’usurwa ko bangon gidan akwai wani namiji mai aure da aka mallaka masa kula da wannan yankin (sa-sa), wanda yake d’auke da wani ‘bangare na zuriyar gida. Ana iya samun wani sashe na gida yana d’auke  da barorin gida wad’anda ba tsatso d’aya suke da zuriyar gidan ba. A cikin gida ana iya samun mutane da dama kamar kimamin mutane d’ari biyu ko ma fiye da haka ko kuma ya kasa haka. Abin ya dogara ne ga yawan zuriyar da ake da su a gidan.

A wannan zaman aikace-aikacen da ake gudanarwa, wad’anda suka shafi sana’ar da zuriyar suka dogara da ita, tana shafar ko wane d’aya daga cikin zuriyar gidan da barorinsu. Misali idan zuriyar tana aikin noma ne, to a gidan za a iske maigida yana da wasu gonaki da ake gudanar da aikin na bai d’aya a cikinsu. Noma da ake yi a cikin wad’annan gonaki shi ake kira noman gandu. Idan kuwa k’ira ne ko jima haka abin yake, domin akwai aikin da ake had’uwa a gudanar da shi gabad’aya mutanengidan. Irin wannan aikin shi ake kira da aikin gandu.

3.2 JAGORANCI  DA  AYYUKAN  CI  GABA  A  ZAMANTAKEWAR  GANDU


Domin sanin  irin ayyukan cigaba da ake samu  a jagoranci na zamantakewar gandu an duba ra’ayoyin masana domin samo cikakkiyar yadda suka bayyanata misali;

Skinner (1959), ya bayyana kalmar jagoranci da cewa:  ‘‘Tana nufin ba da shawara’’.

K’amusun jami’ar Bayero (2006) an bayyana jagoranci da cewa: ‘‘Shigewa gaba  ga wasu mutane a wata harka’’.

Daga bayanin da masana suka bayar dangane da jagoranci, ana iya fahimtar cewa jagorancin iyali, abu ne da ya k’unshi d’aukacin nauyin duk wani mahaluki da yake gudanar da rayuwarsa a k’ark’ashin juagoracin mutumin da aka za’ba don jagoranci. igidaMiasli kamar maatare da kulawar uwargida da sauran mataimaka na gidan da ake zamantakewar  gandu. Mutum bai da wani iko nasa na kansa, face sai wanda aka fitar daga gandu. Fita daga gandu kuwa ya ta’allak’a ne kan wanda ya kai ga wani mataki na rayuwa, inda ake ganin ya kamata a ware shi don ya kula da zuriyar da take k’ark’ashinsa. Tare da had’a shi da wasu daga cikin kannensa.

Ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a yanayin zamantakewar gandu suna da yawan gaske. kuma duk ana gudanara da su ne domin a samu cikkakiyar hanyar rayuwa ta zuriya, wadda za ta dogara da kanta da kariyar mutuncinta. Ire-iren wad’anan ayyuka sun had’a da irin sana’ar da gidan ya dogara da ita. Hanya na biyu ita ce ta tarbiya, domin kare zuriyar da aikata abin kunya ko fad’i. Da kuma ingata rayuwar zuri’yar don bamban ta ta da sauran al’umma na garin.

Akwai aikin ci gaba inda zuriya kan had’a kai don gudanar da wani aiki da zai kawo wa zuriyar ci gaba. Misali: Aikin gyaran muhallin da zuriyar take zaune a cikinsa. Kowa na barin sana’arsa da sauran ayyukan da yake aiwatarwa domin ganin an gyara muhallin da ake zaune a cikin sa don kare zuriyar daga shiga kunci na rashin muhalli, musaman ma lokacin damina. Wata hanyar kuma ita ce ta taimakawa ‘ya’yansu da ingantacen ilimi don kare zuriyar daga tarkon jahilcin rayuwa. Sanan ana gudanar da aikin ci gaba ta samawa jikokin ‘ya’ya mata sana’ar yi, musaman ‘ya’yan da suka tashi a hannun kakanni na uwa.

3.3  ZUMUMCI DA MATSAYINSA A ZAMAN GANDU


Zumunci abu ne mai muhimmancin gaske a rayuwar kowace al’uma ta  duniya. Masana da dama sun bayyana fahimtar su game da zumunci. Masana irin su :

Skinner (1959), ya bayyana zumuci da cewa: ’’Dangantaka ko abokantaka duk za a iya kiransu da zumunci’’.

Zumunci  ke nan shi ne tushen rayuwa da yake kula da taimako da ayyukan ci gaba na zuriya, wanda ya shafi taimakon kai-da-kai ta fuskokin rayuwa gaba d’aya.

Akwai wasu mahimman rukunoni na zumunci a rayuwar Bahaushe, wad’annan rukononin kuwa su al’ummar garin Zazzaun suke aiwatar da su.

-     Zumuncin jini

-    Zumuncin mak’wabtaka

-    Zumuncin abokantaka

-    Zumuncin sana’a

Kowaane d’aya daga cikin wad’annan rukunonin na zumunci yana taimakawa wajen inganta rayuwar  zuriya da ha’bakar t.a Sannan, kuma suna ba da kariya ga duk  zuriyar da ta rik’e su da muhimanci. Ga yadda ake gudanar da rayuwa a k’ark’ashin wad’annan rukunoni na zumunci.

3.3.1 Zumuncin jini:

Zumuncin jini shi ne inda ‘yan’uwa da suka fito daga zuriya guda suke kula da zumunci ta hanyoyi da dama. Misali; ta hanyar auratayya. Iyaye sukan had’a ‘ya’yansu aure don gudun ‘bacin zumunci. Kuma a nan  ne ake samun ‘yan’uwan jini da kan taimaka wa wani d’an’uwa da ya shiga wata matsala ta rayuwa kuma sukan sama wa wani d’an’uwa sana’a ko ilmi ko kula da lafiyarsa a lokacin da ya shiga wata matsananciyar  rashin lafiya  ko talauci. A takaice wannan zumuncin shi ne jagora ga sauran rukunonin zumunci.

A yanayin zaman gandu  na garin Zazzau irin wannan zumuncin yana aukuwa ne idan har akwai matasa wato, ‘yammata da samari da suka fito daga cikin gida d’aya , mai sa-sa da yawa Misali, idan aka samu d’an Wa da d’an k’ani ko’ya’yan ‘yan-uwa mata da aka aurar, Zage-zagi kan yi amfani da irin wannan dama su had’a su aure domin k’ara dank’on zumunci. Abin alfahari ga Bazazzagi ya had’a jinin zuriyarsa aure don ya dunk’ule zuriyarsa wuri guda. A zamanin da, da wuya ace d’an zuriya yana son ‘yar’uwarsa a hana masa a ba wani daya fito daga wata zuriyar ta daban aurenta.

3.3.2  ZUMUNCIN  MAK’WABTAKA


Mak’wabtaka shi ne duk magidatan da ke kewaye da gidanka na da hakkin kula da iyalinka ta hanyoyin da dama Misali, mak’wabci na da ikon hukunta ‘ya’yanka ko tsawatar musu  yayin da ya ga suna aikata wani abu na daban haka kuma makwabci kan d’auki ‘ya’yan mak’wabci tamkar yaran da ya haifa irin wannan yana faruwa ne musamman idan gidajen akwai yaran da suka taso tare.

Haka mak’wabci na iya shiga tsakani, idan wata matsala ta taso tsakanin mak’wabcinsa da iyalinsa, kafin ‘yan’uwan ma’auratan su sami labarin , irin wannan zumuncin ba nan ya tsaya ba a wani lokaci ma akan kai ga had’a ‘ya’yan mak’wabci da mak’wabci aure domin k’arfafa dank’on zumunci.

3.3.3 ZUMUNCI N ABOKANTAKA


Zumuncin abokantaka, zumunci ne da ake kulla shi tsakanin aboki da  aboki. Kuma yana taimakawa wajan gyara tarbiyar ‘ya’ya da ba wa juna shawara game da yanayin zamantakewa. A yayin aiwatar da wannan irin zumuncin idan ba an sanar da kai ba ka ce wannan zumuncin na jini ne domin duk abin da sauran ‘yan’uwa na jini ke yi lokacin da wani sha’ani ya taso za ka iske da su a ciki. Haka aboki na iya d’aukan ‘ya’yan abokinsa su zauna zaman gandu ba tare da wata matsala ba, ko kuma nuna bambanci tsakanin su da ‘ya’yan da ya haifa ba.

3.3.4  ZUMUNCIN SANA’A


Zumuncin sana’a zumnci ne da ke faruwa ta hanyar sana’ar mutum da abokin sana’arsa. Irin wanna za ka iske sauran abokan sana’ar mutun na sa ido ga kayan sana’ar  d’an’uwarsu  yayin da wata matsala ta same shi.

Haka sukan tafi har gida su diba lafiyarsa, a wani lokacin ma abokanan sana’a sukan taimaka wa d’an-uwansu  idan wata annoba ta fad’a wa d’a’uwansu da jari domin gudun fad’awa wani hali na daban.

3.4    KIMAR MATAN ‘YAN’UWA


A kaso na (3.3) an bayyana ire-iren rukunonin zumznci. Inda aka kawo rukunoni hud’u na zumunci. Wani babban abu da ake samu a zumuci cikn zaman gando shi ne yanayin da ‘yan’uwan miji kan d’auki matan ‘yan’uwansu.

Matan ‘yan’uwa suna taka muhimmiyar rawa waje inganta  rayuwar zuriyar gida suna taimakawa wajen ba da ingantacciyar tarbiyar ‘ya’ya. Wani abu kuma shine yayyen miji kan d’auki matan k’annensu  tankar su ne k’annensu na jini ba mazansu ba.

Wannan yana faruwa ne a lokacin da suka fahimci d’an’uwansu yana cuta wa matarsa ta fuskar zamantakewa. A nan sukan yi masa hukunci mai tsanani dan ya bar cuta mata. Haka kuma idan ita ce ke cuta masa za su fa’d’aceta kamar yadda zasu yi wa ‘yar’uwansu ta jini ko da kuwa ba daga zuriyarsu ta fito ba.

K’annen miji kan d’auki matan ‘ya’yansu tankar abokanan wasansu (taubasai). Inda suke yi masu ba’a da maganganun barkwanci. Amma duk da haka, sukan d’auke su tankar yayyensu a lokacin da suke tunkarar wanni abu na rayuwa kamar neman aure ko neman shawara kan wata matsala ta rayuwa. K’annen miji kan yi shawara da matan yayyensu  kafin su kai ga iyayensu. Wani lokaci ma su matan yayyen kan kai maganar ga magabata, idan sun kai matsaya da k’annen mazan nasu,maimakon wasu ‘yan-uwa.

 

3.5   NA’DEWA 


Kamar  yadda aka yi bayani a farkon wannan babin, aka nuna yanayin zamantakewar iyali a garin Zazzau cikin taswira domin sauk’ak’a fahimta. Samman sai yanayin yadda jagoranci da ayyukan ci gaba a zamantakewar gandu yake, bisa ga ra’ayoyin masane. An yi bayyanin zumunci da mutsayinsa a zaman gandu kamar yadda masana suke kallon sa . sai kimar matan ‘yan-uwa,  yayin zamantakewar gandu. Da k’arshe sai aka nad’e babin da tak’aita wad’annan bayanan.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments