Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatanci Na Kamanci Da Bambanci Tsakanin Jimlar Tambaya Da Jimlar Korewa Ta Hausa Da Ta Fulatanci (6)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

DAYI RILWANU

BABI NA HUDU

TAKAITAWA DA KAMMALAWA

4.0  TAKAITAWA


A babi na farko an nuna yadda tsarin binciken ya gudana. A farkon babin an fara ne da shimfid’a sannan aka kawo bitar ayyukan da suka gabata, wad’anda suke da nasaba da wannan binciken. An gabatar da bitar ayyukan da suka gabata ne da muhimman kundaye da muk’alu da kuma littattafai da aka rubuta masu alak’a da wannan nazarin. Sannan aka kawo dalilin bincike, a ciki an bayyana dalilan da suka sa aka gudanar da wannan bincike, haka kuma sai aka bayyana manufar binciken, a nan an nuna manufofin wannan bincike ta la’akari da harsuna biyu, musamman harshen Fulatanci (Fulfude). Haka kuma an bayyana farfajiyar wannan bincike, ta la’akari da yadda tsarin aiki yake, daga nan kuma sai hanyoyin gudanar da bincike, wanda shi ma aka fito da hanyoyin da aka bi don samun nasarar kammaluwar aikin. Daga nan kuma sai muhimmancin bincike inda aka yi la’akari da irin huld’ar da mu’amala da tsarin zamantakewar harsunan biyu da yadda ake aiwatarwa a cikin nazarin ilimin harshe. Daga k’arshe sai aka biyo da nad’ewa a tak’aice.

A babi na biyu ya na d’auke ne da ma’anar jimla a harshen Hausa kamar yadda masana suka kalle ta, haka kuma an waiwayi ma’anar jimla a harshen Fulatanci (Fulfulde). An kawo ire-iren jimla a harsunan biyu, inda aka jero jimlolin kamar irin su; jimlar tambaya da jimlar korewa da jimlar umurni da kuma sassauk’ar jimla, domin ganin yadda tsarin kowace jimla take a harsunan biyu. Daga k’arshe sai aka nad’e babin da jawabin kammalawa.

Babin da ya ta’bo zuciyar wannan bincike shi ne babi na uku, kamar yadda aka ambata tun a farko, babi na uku babi ne da aka nuna kamanci na jimlar tambaya ta Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde) inda aka samu cewa a dukkan harsunan biyu, kalmar tambaya ta zo a farkon jimla, sannan alamar tambaya ta zo a k’arshen jimla. A nan, binciken ya fahimci cewa akwai kamanci tsakanin tsarin jimlar tambaya ta harshen Hausa da tsarin jimlar tambaya ta harshen Fulatanci (Fulfulde). Ta fuskar bambanci tsakannin jimlar korewa kuwa, wannan bincike ya gano cewa harshen Hausa ya tanadi wasu muhimman kalmomi da ake amfani da su domin nuna korewa a cikin jimla; amma a ‘bangaren harshen Fulatanci, kalmomin korewa suna da yawa wad’anda ake amfani da su wajen nuna korewa a cikin jimla. A nan kuwa, bincike ya gano cewa akwai bambanci tsakanin tsarin jimlar korewa ta Hausa da tsarin jimlar korewa ta harshen Fulatanci (Fulfulde). Daga k’arshe sai aka rufe babin da jawabin kammalawa, wato nad’ewa a tak’aice.

4.1     KAMMALAWA


Hausawa na cewa, “duk abin da ke da farko to yana da k’arshensa” wannan zance haka ya ke domin wannan nazarin mai taken, “Kamanci ko bambanci tsakanin jimla biyu na harshen Hausa da na harshen Fulatanci (Fulfulde), nesa ta zo kusa” wato ya zo kan iyaka, domin Allah Maigirma da d’aukaka a cikin ikonSa da baiwarsa da k’addarawarsa da taimakonsa ya kawo mu k’arshen wannan binciken wanda za a yi jawabin kammalawa a kan wannan aiki.

Wannan bincike ya tattaro abubuwa da dama, da suke da alak’a da ginin jimlar harsuna biyu wato harshen Hausa da na Fulatanci (Fulfulde). A cikin wannan d’an k’aramin kundin an bayar da ma’anar jimla na harsuna biyu ne, wato harshen Hausa da kuma harshen Fulatanci, wad’anda suke a matsayin ginshik’in ginin jimla.

https://www.amsoshi.com/2018/01/25/sautukan-hausa-bakin-jukunawa-5/

Ta ‘bangaren da aikin ya nazarta don k’ara ba da haske a kan binciken, aikin ya dubi jimloli biyu na harsuna biyu, wato harshen Hausa da harshen Fulatanci (Fulfulde) ne a tak’aice. Haka kuma, aikin ya dubi jimlar tambaya da yadda take a harshen Hausa da harshen Fulatanci (Fulfulde) duk domin ganin yadda tsarin ginin jimlar harsunan yake.

Sannan aikin ya nuna kamanci ko bambanci na jimlar tambaya ta Hausa da Fulatanci (Fulfulde) da kamanci ko bambanci na jimlar korewa ta Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde) haka kuma an nuna kamanci na jimlar tambaya ta Hausa da ta Fulatanci inda aka nuna cewa harsunan kowanensu dole kalmomin tambaya su zo a gaban jimla kafin abin da ake tambaya ya biyo baya, sai kuma,aka nuna bambanci na jimlar korewa na harsuna biyu, cewa, harshen Hausa yana amfani da bak’in “b” ko kalman ‘b’ domin nuna korewa amma harshen Fulatanci (Fulfulde) na amfani da kalmomi da yawa domin nuna korewa a cikin jimla.

4.2     SHAWARWARI


Wannan aikin ya ci karo da matsaloli kad’an ta ‘bangaren samun littattafai na harshen Fulatanci. A gaskiya akwai k’arancin littattafai na dubawa a harshen, duk da ya ke akwai wasu kad’an da aka wallafa, to amma yawancinsu a cikin harshen Ingilishi ne aka wallafa su, wad’anda aka wallafa a cikin harshen Fulatanci sun k’aranta sosai. Shawara ta a nan ita ce: Idan har ba a yi k’ok’arin magance wannan matsala ba, a gaskiya haka zai iya haifar da durk’ushewar harshen Fulatanci a fagen nazari. Don haka ya kamata malamai da d’alibai Fulani Su ta shi su yi aiki tuk’uru domin farfad’o da martabar harshen Fulatanci a fagen nazari, da kuma ku’butar da harshen daga fad’awa cikin jerin harsunan da ke hanyar mutuwa. Martabar kowane harshe shi ne, masu shi su gudaar da nazari a kansa tare da inganta hanyar sadarwa tsakanin al’ummar harshen da mak’wabtansu. Duk lokacin da aka rasa masu magana da harshen to kuwa harshen zai mutu. Kamar yadda sauran harsuna na duniya wad’anda masu magana da su suka yi sakaci ta fuskar nazarinsu har suka mutu.

Ina ganin idan har aka yi wallafe-wallafe da yawa a cikin harshen Fulatanci za a sama masa gata da kuma daraja a idon al’umma, domin an adana shi kamar yadda aka adana sauran ‘yan uwansa, irin su harshen Hausa.

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments