Ticker

6/recent/ticker-posts

Kudi A Idan Mawakan Hausa Na Baka Da Rubutattu, Wakar Kudi Ta Alhaji Audu Wazirin Danduna Da Ta Alhaji Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
NA
Shu’aibu Murtala Abdullahi 

BABI NA HUDU
SALON WAKAR KUDI

4.0 Gabatarwa


A wannan babi nazarin zai yi k’okari wajen kawo ma’anar salo da sauraran abubuwan da salo ya kunsa, kamar salon zubi da tsari, amsa-amo, awan kalmomi da kambamawa da kuma dabarun janhankalin da ke cikin wak’okini

4.1    Ma’anar Salo


Masana da manazarta sun tofa albarkacin bakinsu dangane ada abun da ya shafi salo misali; kamar k’amus na jami’ar bayero kano (2006:385) ya bayana salo ta hanyyoyi iri-iri kamar yayi ko sauyi ko launi k’oce.

Dangane da ma’anar salo, suma masana sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar salo misali:

Sa’id (1981:35) ya bayyana salo da cewa “salo shi ne yadda mawak’i ya zana tunaninsa a takarda. Za a dube shi a ganui shin tana da manufa, bayanin Yana da k’arfi ko rarrauna ne ana kuma fahimtarsa cikin sauki ko kuma sai an yi lalube a gane manufard’a. Haka kuma za a dubi kwarewarsa da gwanintarsa wajen sarrafa harshe da ya yi amfani da shi”.

Danganbo (1981:2-3) yana ganin cewa “salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da sako. ya dad’a fad’ada tunanin sa da cewa lalle ne salo ya kunshi za’bi, kuma kyan salo ko maninsa  ya danganta ga yadda kowane mutum ya za’bi abubuwa da ya yi amfani da su cikin rubutunsa to furucinsa don isar da sakonsa kuma salo yakan yakan ta’allak’a ne dangane da yadda mutum yake tunani cikin da cewa.

Guban (1993:54) ya bayana salo a wakok’in baka da cewa “salo a wak’okin baka wata hanya ce wadda makad’i yake kyautata zaren tunanainsa, ya sarrafa shi cikin a zancidan ya cimma burinsa na isar da sak’o ko wak’a. Salo awak’okin baka abu ne wanda yake dad’a fito da ainihin kyansu ko muninsu ta haka za’a iya gane wak’oki masu karsashi, masu hikima da balaga da kuma wak’oki marasa ma’ana marasa inganci. Salo kenan ma’auni ne na rarraba zak’in wak’a ko d’acinta, salo kuma wata dabara ce da za a iya yiwa harshe ado da ita kuma hanya ce ta sarrafa harshe a jujjuya shi ta yadda za a iya tak’aiita manufa ka sakaya ma’ana ko kuma a karfafa tunani”

A.B. Yahaya (2016:30) ya bayyana ma’anar salo da cewa

“Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin wak’a wadda mawak’i ya bi domin isar sa sak’on da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa wak’a kwalliya ta yadda sak’on wak’ar zai isa ga mai saurare ko karatun wak’a”

Ta la’akari da wadannan ma’anoni da masana suka bayar za a iya  cewa salo shi ne zaren da mawak’i kan yi amfani da shi domin su sami kar’buwa a wirin jama’a ta hanyar wak’a.

4.2    Salon Zubi da Tsari


Zubin wak’a wani bangare ne daga cikin salon zubi:- Zubin wak’a ya shafi bayanai kan yadda siffar wak’ar take. Wato bayyana yawan baitocin da ta kunsa. Haka kuma zubin ya kunshi bayyana ko wak’atana da amshi ko bata da shi, da kuma amsa-amo da ta kunsa. Wace irin wak’a ce  dangane da suna kwar biyu ce ko uku da sauransu. Wane baiti ne mafi tsaryi, kuma wane ne mafi gajarta ko dangogin  wak’a gajajjera nre ko kuma dagoye? Wannan nau’i na salon zubi yana da muhimmanci k’warai da gaske a cikin wak’a a wajen na zarin rubutattar wak’a da kuma sauran wurare.

4.2.1 Zubi da Tsarin Wak’ar Kud’i ta Gambo Hawaja


Wak’ar kud’i ta gambo hawaja tana da zubi da tsari da farko wak’ar tana da yawan baitocin da suka kai (d’ari biyu da ashirin da d’aya 221) sanna kuma wak’ar ‘yar kwar biyu ce ma’ana layuka biyu ta kunsa, sannan wanna wak’a ta gambo hawaji wak’a ce wadda ba ta ada amshi, saboda rubutacciya ce ba ta  baka ba. Haka kuma baitocin da ke cikin wannan wak’a gajeru ne amma akwai wasu baitoci masu tsayi da kuma wadanda ba su da tsayi misalin masu tsayi da gajeru.

4.2.1.1 Baitoci Masu Tsayi


Baiti na (20)

(20)   Diriba ‘1’ ja mu sannu don kar ta k’wance,

Mu tai tafiya mui ta nunan kudi.

 

(106) Na-Erode, wa-makan a Jos sai su zauna,

Su ce isan, basu neman kudi.

 

(122) Tsaya zan yi zan ce da fulfulde malam,

M shaida wa ‘yan fulbe ranar kudi.

 

(76)   Ka shisshiyar zancen ka ko kwai da babu,

A kar’ba a zauna a kai dan kudi.

 

(86)   Mu tashi mu bar gyangayadi mui ta niyya,

Mu zage damatsu mu nemo kudi.

4.2.1.2 Gajerun Baitoci


 

(22)   Fatauci, giya, caca, neman kilaki,

Adar yin su in dai ana son kud’i.

 

(51)   ku sai ya da a daji jami’a,

Kud’i “cede belde” mu nemoo kudi.

 

(82)   Idan ka ga sarki akwai d’an dalili,

Idan ba fad’a, ka yi satar kud’i.

 

(123) Da ad liyan da “cede”,

Wuri “cambe” sunansa babba kud’i.

 

(151) Ta zauna cikin bata ko kara yafi,

A kayi, a kayi, mijin ba kud’i.

Wannan wak’a ta Gambo Hawaja tana da amsa-amo wanda take tafiya da shit un daga farkonta har zuwa karshen ta k’ato Kalmar (kud’i) wanda shi ne amsa-amon wak’ar.

4.2.2 Zubi Da Tsarin Wak’ar Kud’i Ta Audu Wazirin D’anduma  


Zubi da tsari na wak’ar audu Wazirin D’anduna ana iya cewa yana jera tunanin sa, a wajen isar da sak’onsa ga masu saurarensa, kuma ta hanyar da zza su iya fahimtarsa abin da yake son ya isar ba tare da wata wahala ba. Audu Wazirin D’anduna yakan maimaita wasu kalmomi da ya fad’a acikin wak’arsa. Wato ya fadesu har sau biyu kafin ya ci gaba da wani baiti misali. A baiti na (86)

(86)   Jagora! Kud’i,

Y/Amshi! Tsakanin D’an Adam da kud’i.

 

(87)   Jagora! ABH! Kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin D’an Adam da Kud’i.

 

(109) Jagora!Ooh! Kud’i.

‘Y?Amshi Tsakanin D’an Adam da kud’i.

 

(110) Jagora! Ooy! Kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin D’an Adam da kud’i.

 

Dan haka ana iya cewa zubin da tsarin wak’ok’in sa yana samuwa ne daidai da yadda yake son ya samar da baitin wannan wak’a. Haka kuma, tana da amshi irin amshin da ake kira amshin shata “Tsakanin D’an Adam da kud’i” kuma wanna wak’ar, ta ba mai d’ango d’aya ce sannan ta na da yawan d’iyoyi d’ari d’aya da sittin (160) haka kuma d’angon da ya fi tsawo a cikin wak’ar shine:- baiti na (23)

(23)   Jagora! Yanzu da wata harka sai kana da kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin D’an Adam da kud’i.

 

(24)   Jagora! Hakan ga ba ka da girma sai kana da kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin D’an Adam da kud’i.

 

(26)   Jagora! Kuma akan sabon harka saboda kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin d’an Adam da kud’i.

 

(35)   Jagora! Kai mu duba Tsakanin d’an Adam mu gani,

‘Y/Amshi! Tsakanin d’an Adam da kud’i.

 

Haka kuma d’iyan da suka fi gayarta a cikin baiti na (40)

 

(40)   Jajora! Ummh! Kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin d’an Adam da kud’i.

 

(41)   Jagora! Aah! Kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin d’an Adam da kud’i.

 

(86)   Jagora! Kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin d’an Adam da kud’i.

 

(87)   Jagora! Abh! Kud’i,

‘Y/Amshi! Tsakanin d’an Adam da kud’i.

4.2.3 Zubi Da Tsarin Wak’ar Kud’i Ta Alhaji Mamman Shata


Zubi da tsarin wannan wak’a ta “kud’i a kasha su ta hanya mai kyau”

Da farko wannan wak’a tana da yawan d’iya ashirin da hud’u (24) haka kuma tana da anshi wadan da ake kira amshin shata wato “kud’i a kasha su ta hanya mai kyau” sannan wannan wak’ar bat a da daidaiton layuka acikinta saboda wani d’an yafi wani yawa. Haka kuma akwai dan da yafi kowane tsayi da kuma wanda yafi gajarta.

Misali:-

D’a na (17)

(17)   Muddin dukiya ta taru

Muddin dukiya ta taru

Ka zan na

Kuma ka huta tsaf

Ka yi tunani can daga zucci

In dai kai niyyar ‘baddasu

Jeka kasha su ta hanya mai kyau

 

(21)   In zan alheri in sanifa

In zan sayo

In je in sani fa

In zan sayar

In rink’a tunani

In san riba

Fitar da uwa

Kud’i a kasha su ta hanya mai kyau

Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau

 

(8)     Ko ni Alhaji sarkin wak’a

In nai wak’a kyakkyawa

Na sami kid’i mai k’wari

Wa tara has sun kari

Ba ashararu

Ba sakarci

Sai in kasha su ta hanya mai kyau

Kud’i a kasha su tahanya mai kya

 

4.2.3.1 Gajerun D’iyoyi


 

Ad’a na (6)

(6)     A kasha su ta hanya mai kyau,

Kud’i a kasha su ta hanya mai kyau.

 

(24)   Tunda mun/san bai shiga shashanci ba,

Kud’i a kasha su ta hanya mai kyau.

 

(5)     Tun da sai kai gumi ka sami abin ka,

A she ko kasha shit a hanya mai kyau,

Kud’i akashe su ta hanya mai kyau.

Daga karshe wannan shi ne irin zubi da tsarin da wak’ok’in suke dashi, wato abin day a shafi yawan baitoci do d’iyoyin wak’ok’in da kuma nuna cewa ko wak’ok’in suna da amshi ko bas u das hi, da kuma irin baiitoci ko d’iyoyin da suke da tsayi ko wad’anda suke gajeru daga cikin wak’ok’in.

4.3    Aron Kalmomi


A wannan fage mai nazari zai yi k’ok’ari ya fito da yadda makad’i yake zabo kalmomin da yake zubawa a cikin d’iyan ko baitocin wak’ok’insa. Za a duba a gani, kalmomin nan tsofaffi ne ko sababbi ne ko kirkirarru ne ko kuma bak’i ne wad’anda suka shigo harshen Hausa daga wasu harsuna Gusau (1993:63). A nan nazari ya yi k’ok’ari wajen kawo bak’i ko ararrun kalmomi da mawak’an suka yi amfani da su. Misali Gambo Hawaja a cikin wak’arsa ta ‘kud’i’ ya yi amfami da ararrun kalmomi a wasu baitoci na cikin wak’ar in day a aro kalmomin da Larabci ta Turanci da Fulatanci. Misali

A baiti na (20)

(20)   Din-ba “I” ja mu sannu dan karta kwance,

Mu tan tafiya mui ta neman kud’i.

 

A wannan baitin mawak’in ya yi amfani da Kalmar din-ba wadda kuma kalma ce ta Turanci (dri’ber) ya d’anko ta ya yi amfani da ita.

 

(43)   Illori su ce :Olie” Hausa “‘barawo”

Fulani su ce “Gujju” kayan kud’i.

 

A wannan baitin kuma ya yi amfani da kalmomi na yarbanci da fulatanci wato Olie da Gujju. Wanda suke nufin ‘barawo.

 

(95)   Tilawa izu arba’in sai ta rushe,

Ta dawo bakwai ko biyar don kud’i.

 

A nan kuma ya yi amfani da kalmomin larabci kamar (tilawa) da “hizb” da kuma arba’in (arba’in) wadda dukkan su asalin su daga larabci ne to suma ya yi amfani dasu.

Alhaji Audu Wazirin D’anduna shi ma ya yi amfani da kalmomi kamar na turanci da larabci misali:- baiti na (109)

 

(109) Ooh! Kud’i,

Tsakanin D’an Adam da kud’i.

 

A wannan d’an ya yi amfani da Kalmar Turanci ta Ooh wadda take da alamar mostsin rai.

(86)   Aah! Kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

 

A wannan baitin ma ya yi amfani da Kalmar Aah wadda ita ma Turanci ne.

(56)   Tsakanin D’an Adam da kudi,

Tsakanin D’an Adam da kudi.

 

A wannan baitin ya yi amfani da Kalmar larabci wato D’an Adam wadda ta samo asali daga (Adam)

(117) Sai Alhaji ya zo sai kana da kud’i,

Tsakanin D’an Adam da kudi.

 

(118) Alhaji ko bay a nan don saboda kudi,

Tsakanin D’an Adam da kudi.

 

A wannan d’iyan wak’a mawak’in ya yi amfani da wato (Hajj) da bahaushe yake kira Alhaji wadda ita ma larabci ce.

Shima Mamman Shata ya yi amfani da aron kalmomi na larabci a cikin wasu d’iyoyi na wak’arsa. Misali:_

A d’a na (7)

(7)     Malam du cinikin da kake yi

Du wuyar shi dud dadin shi

In dai kai niyyar d’adda su

Je ka kasha ta hanya mai kyau

Kud’i a kasha su ta hanya mai kyau.

 

A wannan d’an ya yi amfani da kalmar malam wadda asalinta Kalmar larabci ce wato (mu’allim)

4.4    Salon Kambamawa


Masana sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abunda suke ganin shi ne kambamawa. D’angambo (2007:47) ya bayyana kambamawa da cewa “ita wannan wani lafazi ne ko furuci da mawak’a kan yi wanda sai a ga abu ne mai wuya haka ta auku. Sukan fad’i abin dab a zai yiwu ba, su nuna ya auku ko zai auku. Ko kuma suce in ma ya auku to ba zai hana haddasa wani abu ba. Wannan dabara ce kambamawa dan jawo hankali” misali Gambo Hawaja a cikin wak’arsa ta “kud’i” ya kambama kud’i a wasu daga cikin baitocin wak’ar kamar haka;-

A baiti na (40)

(40)   Gama lafiya dai da rai sun fi komai,

A kan ba da su don a samo kud’i.

 

A wannan baitin kambamawa ce cewa lafiya da rai sun fi komai to amma a akan bayar da su dan kud’i.

(55)   Idan ban da rayi kud’i ya fi komai,

Abokin zaman lafiya rai kud’i.

 

A wannan baitin ma ya kambama kud’i cewa abin da ya fi kud’i shi ne rai, sannan kuma kud’i shi ne abokin zaman lafiya.

(87)   Kud’i shi ya kan sa’a saba da arne,

Musulmi akan kishi in ba kud’i.

 

A wannan baitin ya kambama kud’i cewa shi ne zai sa asaba da arne mara addini. Sannan ya sa akwaimusulmi saboda bashi da kud’i

4.4.1 Alhaji Audu Wazirin D’anduna A Cikin Wak’arsa Ta Tsakanin D’an Adam Da Kud’i


Shi ma acikin wasu d’iyan wak’ar ya yi kambamawa misali

A d’a na (14)

(14)   Kana ‘ya komai don saboda kud’i

 

(16)   Matuk’ar dai ka sha wuya kas samu

In za ka ‘batar

Kai imani

Zo ka kashe su ta hanya mai kyau

Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

 

A wannan d’an ya kambama kud’i cewa idan da kud’i to komai ma kana ‘ya yi ba wani abu.

(23)   Yanzu du wata harka sai kana da kud’i,

Tsakanin dan Adan da kud’i.

 

A wannan d’an yana nuna cewa yanzu babu wata harka da zaka iya yi ko ta kasuwanci ko ma maye sai kana da kudi.

(36)   A na zare ido sabo da kudi,

Tsakanin d’an Adam da kudi.

 

A wannan d’an ya nuna cewa idan mutum yana da kud’i zaka ga yana zare ido yana muzurai saboda kawai yana da kudi. A nan ma kambamawa ce.

Alhaji mamman sahata a cikin wak’arsa ta “kud’i a kashe su ta hanya mai kyau” ya yi amfani da wasu d’iyoyi wajen kambama kud’i.

Misali:-

A d’a na (11)

(11)   Tsaya dukiya abin nema ce

Su kud’i abin nema ne

Ciccije nemi abunka

Ba za karki nemi kud’inka

In kuma ka tashi kashewa

To ka kashe su ta hanya mai kyau.

 

A wannan d’an  yana nuna cewa su kud’i ba’a samunsu sai an nema kuma sai an dage an yi amfani da karfi sannan ake samun su .

Ta la’akari da wadanna baitoci ko d’iyoyi da nazarin ya fito da su za’a gane irin kambamawa da mawakanan suka yi wa kud’i a cikin wadannan baitoci ko d’iyoyi in da nazarin ya yi k’okarin fito da su.

4.5    Dabarun Janhankali


A wanna ‘bangaren nazarin zai yi k’okari wajen fito da wasu baitoci da d’iyoyi da mawak’an suka yi amfani da su wajen janhankali kan yadda ya kamata a nemi kid’iu misali:-

4.5.1 Dabarun Janhankali a Wak’ar Kud’i ta Gambo Hawaja


Gambo Hawaja ya yi amfani da wasu baitoci wurin janhankali misali

A baiti na (4)

(4)     Kusa hank’uri kui kawai ku fahimta,

A yau zan gaya muku ranar kud’i.

 

A wannan baitin janhankali ne yake yi cewa mytane su yi hakuri su zo su fahimci ranar kud’i da zai gaya musu.

(8)     Jama’a mu daure, mucije, mu jure,

Mu tayar wa aiki da neman kud’i.

 

A wannan baitin ma janhankali yake cewa jama’a sai an daure, ancije, an jure, sannan sai an yi aiki sosai wajen neman kud’i.

(16)   Ka lura da bai d’an-dako sai ka bi shi,

Idan kai/sake babu kayan kud’i.

 

A wannan baitin yana jawo hankalin jama’a cewa idan zaka bawa d’an dako kayanka to ka lura kuma ka bishi dpomin idsan kayi sake to zaka rasa kayanka.

4.5.2 Dabarun Janhankali A Wak’ar Tsakanin D’an Adam Da Kud’i Ta Audu Wazirin D’anduna


Shi ma Alhaji Audu Wazirin d’anduna ya yi amfani da dabarun na janhankali a wasu daga cikin d’iyan wakansa misali:-

(6)     Yanzu ba wata harka sai kana da kud’i,

Tsakanin D’an Adam da kud’i.

A wannan d’an yana janhankalin jama’a ne cewa yanzu babu wata harka sai in da kud’i.

(11)   Ba ai maka komai sai kan da kud’i,

Tsakanin D’n Adam da kud’i.

 

A wannan d’an shi ma jawo hankalin mutane cewa yanzu fa ba aimaka wani abu idan baka da kud’i.

(37)   Nima gashi ina wak’a saboda kud’i,

Tsakanin d’an Adam kud’i.

 

A wannan d’a ma janhankali mutane ya yi cewa shi ma gashi yana yin wak’a don ya sami kud’i, saboda jama’a su tashi su nemi kud’i.

4.5.3 Dabarun Jan Hankali a Wak’ar “Kud’i a Kashe Su ta Hanya Mai Kyau” ta Mamman Shata


Shi ma Ahaji Mamman Shata ya yi amfani da dabarun janhankali a wasu daga cikin d’iyan wannan wak’a tasa. Misali:-

(4)     Ka tuna yanda kasamu kud’in ka

Ka sha wuya ka samu kud’inka

To ka kashe su ta hanya mai kyau.

https://www.amsoshi.com/2018/01/27/kudi-idan-mawakan-hausa-na-baka-da-rubutattu-wakar-kudi-ta-alhaji-audu-wazirin-danduna-da-ta-alhaji-mamman-shata-da-kuma-gambo-hawaja-1/

A wannan d’an yana jawo hankalin jama’a cewa su tuna yadda suka sami kud’i, sun sha wuya sannan suka samu to su kashe su tahanya mai kyau.

(5)     Tun da sai kai gumi ka sami abinka,

Ashe ko kashe su ta hanya mai kyau.

 

A nan ma yana janhankalin mutane cewa tun da sai da aka yi gumi aka sami kud’i to a kashe su ta hanya mai kyau.

(8)     ko ni Alhaji Sarkin wak’a

In nai wak’a kyakkyawa

Na sami kud’i mai k’wari

Wa tara har sun kauri

Ba ashararu

Ba sakarci

Sai in kashe su ta hanya mai kyau

Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

A wannan d’an ma yana jawo hankalin jama’a cewa ko shi sarkin wak’a in ya yi wak’a mai kyau ya sami kud’i mai kauri, sannan kuma ya tara suka taru, to sai ya kashe su ta hanya mai kyau.

Ta la’akari da wadannan baitoci da d’iyoyin wad’annan wak’ok’i nazarin ya yi k’okarin fito da wasu baitoci ko d’iyoyi da mawak’an suke yi amfani da su wajen janhankalin mutane kan yadda ya kamata a nemi kud’i da kuma yanda ya kamata akashesu.

4.6    Nadewa

Wannan nazari ya yi k’ok’ari wajen fito da wasu abubuwa a cikin wannan babi da suka had’a da salo tare da ma’anar sa  daga madsana da kuma abin da ya shafi zubi da tsarin da ke cikin wakokin in da nazarin ya yi k’ok’arin bayyana na kowace wak’a, haka kuma akwai abin da ya sha fi mawak’an su ka yi amfani da su kamar kalmomin larabci da filatanci, sannan akwai abin da ya shafi kambamawa in da nazarin ya yi k’ok’ari wajen fito da wasu baitoci ko d’iyoyin da aka yi kambamawar sun yi amfani da dabarun janhankali kan yadda ya kamat a kashe su da kuma irin abubuwan da kudi yake sawa.

       

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments