NA
ALIYU MUSTAPHA
BABI NA HUDU
NAZARIN HAUSAR SHIRIN LABARIN WASANNI
Samuwar karin harshen Hausa na rukuni wani ingantaccen tsarin kare-kare ne wanda ya yi trasiri sosai a harshen Hausa. Babu ko shakka ire-iren ayi wad’annan kare-kare da rukunonin Hausawa suke sarrafa harshensu ya bada daman haifar da k’irk’ie-k’irk’iren sababbin ma’anoni tare da zuba hikimomi masu ma’ana da kuma k’ayatawa. Sannan kuma masu amfani da ire-iren wad’annan kare-kare hanyoyi masu sauk’i da tsari kuma sukan yi amfani da masu ban sha’awa wajen sarrafa harshen Hausa.
Hausar shirin labarin wasanni cike take da kalmomin Hausar rukunin masu kallon k’wallon k’afa. Shirine da yake nishad’antar da masu sha’awa da kuma sauraro, a dalilin haka ne yasa ake k’irk’ira sababbin kalmomi, da ma’anoni iri daban-daban domin k’ayatarwa da kuma nishad’antarwa. Kamar yadda kowane rukuni na al’umma ke da wani ke’babben karin harshe da wannan al’umma ke amfani da shi wajen sadarwa ko gudanar da harkokinsu na yauda kullum, wanda kuma ba kowa ne zai fahimci ma’anar ire-iren kare-karen harshen ba, face wanda yake cikin wannan al’umma ko rukunin na mutane.
Yanzu ga wasu daga cikin Hausar shirin labarin wasanni:
Kalma | Ma’ana | |
1. | Lallasa/Lallasawa | Nasar |
2. | Zura/Zurawa | Ci |
3. | Kunnen doki | Canjaras/Daidai |
4. | Doke/Dokewa | Cin galaba/nasara |
5. | Boge | Rashin cancanta/dacewa |
6. | Kontoragi | Kwangila |
7. | Ya ‘ballo ruwa | Yayi kuskure |
8. | Gidauniya | Lallasawa (ci uku) |
9. | Rad’e-rad’e | Jita-jita |
10. | Koci | Mai horar da ‘yan wasa |
11. | Kulob | Wungiya |
Baya ga Hausar shiin labarin wasanni, rukunin Hausar masu kallon k’wallon k’afa na samar da k’irk’irarrun kalmomi da sunaye ga ‘yan wasa ko k’ungiyoyin ‘yan wasa ta la;akari da yana yinsu, ko siffarsu, da k’wazonsu, da kuma salon yadda suke buga wasanni. Ga misali:
- Ronaldo - Doki:- wannan d’an wasa ya samu sunanne a sakamakon yadda yake da gudu tamkar doki mai gudun ‘yan tare.
- Messi - Aljani/Kiriku:- wannan sunnan ya samu ne ta dalinin yadda d’an wasan ke buga k’wallo da zafin nama, ga sauri kamar iska wajen gudu da kuma iya cin k’wallo.
- Bale - Roba-Roba:- d’an wasan k’ungiyar Real Madrid ne, ya ci wannan sunan ne sabo da jikinsa bashi sa k’wari, abu kad’an ya isa yas shi tafiya injury (watau jinya na tsawan makonni).
- Kulob d’in ‘Arsenal’: ‘Yan Dakon Kofa:- k’ungiyar ta ci wannan sunan ne sabo da rashi nasarar da suke yi na cin kofin gasa na rukunin Premier League na Ingila.
- Modrich - Monitor/Monita:- d’an wasan tsakiya ne (Midfielder) n akungiyar Real Madrid a Spaniya. Ana ce mas a’Monita’ domin ya iya rarraba k’wallo ga ‘yan uwansa na kulob, kuma yana tsare muhallin da aka aje shi yadda ya kamata.
- Kulob d’in Real Madrid - ‘yan Madara:- sunci wannan sunan ne kasancewar kallar kayan buga wasansu farare ne.
Sai kuma k’irk’irarrun kalmomi da aka samar.
Ga ma’anar k’irk’ira a nazarin Harshe da kuma sigarta kamar haka:
K’irk’ira
An bayayyana k’irk’ira da yanayin k’irk’iro sababbin kalmomi domin amfani ga abubuwa daban-daban. A nan k’irk’ira ta d’an banbanta da aro, domin ita tana iyar shafar kalmomi ‘yan gida ko had’a ka ta wata kalma daban da kuma kalma ‘yar gida.
Dalibai da dama kan haddasa samuwar sababbin kalmomi. Wad’anna dalibai sun had’a da:
- Tasirin adddinin musulunci
- Tasirin bak’in al’adu
- Zamananci ko yayi
- Fassara
Akan yi amfani da hanyoyi daban-daban domin k’irk’ira k’kalmomi a harshen Hausa:
- Fad’ad’a ma’anar kalmar asali.
Misali:
- Yaji
- Jirgi
- Kumbo
- Fad’ad’a ma’anar kalmar aro.
Misali:
- Pancake-fankeke (Hoda)
- Theater-Tiyata (Fid’a/Aiki)
- K’irk’ira daga kalmomin asali.
Misali:
- Tauraron D’an Adam
- Kafi zabo
- K’irk’ira ta had’in gambiza.
Misali:
- Lashemoni
- Hantsi kwaleji
- Sarrafa kalmomin aro.
Misali:
Turanci/Larabci | Sunan k’irk’ira | Aikatau | |
1. | Karam | Karimi | Karamta |
2. | Assaum | Azumi | Azumta |
3. | Salah | Salla | Sallata |
4. | Set | Saiti | Saita |
5. | Copy | Kwafe | Kwafa |
6. | Patch | Faci | Face |
Yakasai, (2005) ya bayyana yadda tasirin wurin zama ke taimaka wajen k’irk’iro sababbin kalmomi domin sadarwa tsakanin al’umma. Ga misali, yanayi da tsarin barikin ciginya ya haifar da samuwar k’irk’irarrun kalmomi kamar haka:
Ingilishi | Hausa | |
1. | As you are | Aje waya |
2. | About turn | Abatuwa |
3. | Attention | Had’e-k’afa-caan |
4. | Wrong/Mistake | Allah-ya-isa |
5. | Tr’beling by plane | Hau-isaka |
6. | Bank alert | Galan-galan |
7. | Teargas | Barkonon tsohuwa |
8. | Payment of salary | Motsi |
Daga bayanan ga suka gabata, mun ga yadda ake samar da k’irk’irarrun kalmomi ta hanyoyi daban-daban. A Hausar rukunin masu kallon k’wallon k’afa kuwa, ana samun k’irk’irarrun kalmomi kamar haka:
Kalma | Ma’ana | |
1. | Ya cire | Takura/Matsuwa |
2. | ‘Yan bak’in gida | ‘Yan adawa |
3. | Ya ‘ballo ruwa | Yayi kuskure |
4. | Fatan | Salon dabara |
5. | Gidauniya | Lallasawa (ci uku) |
6. | Sarkin yak’i | Gwanin k’wallo |
7. | Ya yi masa tsaki | Kama ruwa/Zire |
8. | Yayi mod’i | Kuskuren bugu |
9. | Yayi masa o’ber head | Yankan sama |
Akwai kuma wasu kalmomin k’wallon k’afa ya yawa da aka fassara daga harshen Turanci zuwa Hausa. Ga misali:
Turanci | Hausa | |
1. | Football (Game) | K’wallon k’afa |
2. | Ball | Bal/K’wallo |
3. | FIFA World Cup | Kofin k’wallon k’afa na duniya |
4. | K’uarter Final | Kwata fainal |
5. | Semi Final | Wasan kusa da k’arshe |
6. | Final | Wasan k’arshe |
7. | Draw | Kunnen doki/Canjaras |
8. | Match | Karawa/Fafatawa |
9. | Coach | Mai horar da ‘yan wasa/Koci |
10. | Referee | Rafali/Alk’alin wasa |
11. | Linesman | Matai makin rafali/Lasman |
12. | Tournament | Gasar wassani iri-iri |
13. | Champions | Zakaran wasa/Zakarun wasa |
14. | African cup of Nations | Kofin k’wallon k’afa na k’asashen Afirka |
15. | Goal-keeper | Gola/Mai tsaron gida |
16. | Striker | Mai kai hari |
17. | Defender | Dan wasan baya |
18. | League | Rukunin gasa |
19. | Football fan | Masu kallon bal |
20. | Team | K’ungiyar ‘yan wasa |
21. | Player | D’an wasa |
22. | Captain | Kyaftin |
23. | Midfielder | D’an wasan tsakiya |
24. | Score (‘B) | Ci/Zuri |
25. | Score (N) | Cin k’wallo/Zurawa |
26. | Football field | Filin k’wallo |
27. | Penalty kick | Fanareti |
28. | Red card | Katin kora |
29. | Yellow card | Katin jan kunne/Ktin kashedi |
30. | Attack | Hari |
31. | Goal | Gol |
32. | Cup | Kofi |
33. | Jersey | Jesi/Rigar ‘yan wasa |
34. | Off-side | Satar fage/Ofsaye |
35. | Substitution | Sauyi/Maye gurbi |
36. | Net | Raga |
37. | Throw | Jifa |
38. | Direct kick | Buga falan d’aya |
39. | Medal | Lambar yabo |
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.