Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Nazarin Jumla A Nahawun Hausa (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya

NA 

IBRAHIM HAMISU YUSUF

BABI NA HU’DU

TAKAITAWA DA KAMMALAWA

4.1 Tak’aitawa


Wannan kudin ya k’unshi babi hud’u, kuma kowane babi ya na da abubuwan da ya k’unsa game da nazarin. A babin na farko an nuna yadda tsarin binciken ya gudana. A farkon babin an fara da shimfid’a, sannan aka kawo bitar ayyuka, a ciki an yi bayyanin ayyukan da aka gudanar na wani sashen aikin nan, haka kuma sai aka kawo dalilin bincike, a ciki an bayyana dalilan da suka sa aka gudanar da binciken sai kuma hujjar ci gaba da bincike ya biyo baya, wannan binciken bai cin karo da wani aika ba, wanda dama shi wannan aikin ya shafi hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Bayan haka sai muhimmancin bincike, inda a nan ne a kawo amfanin wannan bincike ga masu nazari da matakan da aka bi wajen gudanar da bincike. Haka kuma an bayyana farfajiyar wannan bincike, wato fad’i inda binciken ya tsaya ta la’ak’ari da yadda tsarin yak’e inda binciken ya gudana a cikin nahawu a fanin ilimi ginin jumla. Nazarin ya tsaya a kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa. Daga nan sai kuma hanyoyin gudanar da bincike da aka bi don samun haske wajen gudanar da wannan bincike. Inda aka bi hanyoyin gudanar da binciken da kuma makamantansu, hanya ta farko shine kundaye da kuma hanya ta biyu shine littafai sai kuma hanyar k’arshe shine shawarwari masana ilimin nahawun Hausa musamman wad’anda suka san ilimin kimmiyar sashen d’ausa. Babi na biyu yana d’auke ne da shimfid’a wannan take amatsayin gabatarwa. A nan ne aka fito da azuzuwan kalmomi nahawun harshen Hausa. Inda a nan ne aka fito da nahawun taciya tare da nuna muhimmancinsa a harshe, an kuma bayyana matsayin azuzuwan kalmomi a cikin jumla daga nan kuma sai nad’ewa ya biyo baya.

A babi na uku an gudanar da aiki ne akan hanyoyin nazarin jumla a tak’aice kuma aka kawo dabarun nazarin jumla ta  hanyar azuzuwan kalmomi daga nan sai nazarin jumla ta hanyar azuzuwan kalmomi daga nan sai nazarin jumla ta hanyar yanki a nan ne inda aka bayyana su daki-daki, daga nan kuma sai aka kuma nazarin jumla ta hnayar bishiyar li’irabi, inda kuma daga baya nad’ewa ta zama murfin babin. Babi na hudu ya zo da tak’aitawa da kammalawa.

 

4.2 Kammalawa


A babi na d’aya an nuna yadda tsarin binciken, ya gudana. Babin ya fara ne da shimfid’a sannan aka kawo bitar ayyukan da suka gabaci wannan aikin wad’anda suke da nasaba da shi ko wasu sassa daga cikin aikin musamman ma na masana ilimin nahawun Hausa. Daga nan sai aka zo da dalilin bincike. An bayyana cewa a lokacin da ake kok’arin karance-karancen don samar wa binciken gurbin zama, ba a ci karo da wani aiki ba da aka yi irin wannan binciken ba. Bayan haka hujjar ci gaba da bincike ya biyo bayan dalili daga nan an kuma bayyana mahimmancin wannan binciken da cewa an aiwatar da shi ne domin a magance ire-iren matsalolin da ake cin karo dasu a wajen fahimtar nahawun Hausa. Aikin ya gudana ne ta hanyoyin tattaro bayyanai daga ayyukan da aka gabatar wad’anda suka shafi nahawun harshen Hausa, daga kundaye da littafai da aka wallafa; babi na biyu yana dauk’e ne da waiwayen azuzuwan kalmomin na harshen Hausa. Sannan kuma an gudanar da aikin akan nahawun taciya bisa ra’ayin masana. An kuma gudanar da aikin a kan matsayin azuzuwan kalmomin a cikin jumla.

Babi na uku, bayan shimfid’a aikin ya yi bayyani da ire-iren jumla ta hanyar yanki da kuma ta hanyar bishiyar li’irabi da kuma har wa yau ya yi bayyaninsu daki-daki ta yarda mai nazari zai fahimci abin cikin sauki tare da fito da tsarin da matakan gina jumlar Hausa kuma yadda suke zuwa a cikin tsari na musamman “suna” da “aikatau” da “k’arbau” ( S. A. K). Aikin ya gabatar da sassan jumlar inda aka kawo wasu manyan sassa guda shid’a da aka nazarce su. Sun had’a da; yankin suna (Ysn) da yankin harafi. (YHrf) da yankin bayyanau (Byn) da kuma yankin yadda fasalin wadannan sassan suke, an bayyana cewa dukkan sassan suna amsa sunan kalmomin da suke  jagorantar kowane yanki. A babin an gabatar da yankin suna (Ysn) wanda idan jumla ta zo ba suna tom wakilin suna zai wakilce ta. Wanda da ma nashi aikin wakilta suna yake yi a cikin jumla wanda dama shi wannan binciken ya fada ne kan hanyoyin nazarin jumla a nahawun Hausa.

Babi na hud’u, bayan shimfid’a aikin ya tak’aitawa ne inda ya yi bayyanin abubuwan da suka gudana a cikin nazarin tare da yin sharhinsu a tak’aice, amma bayan tak’aitawa sai kuma kammalawa ita ta biyo baya, inda aka yi bayani tare da yin sharhin abubuwan da binciken ya kunsa kuma ya samo a tak’aice, daga nan sai shawarwari.

 

 

4.3 Shawarwari


Dangane da binciken da aka gudanar a lokcin da ake k’ok’arin kamala wannan aikin, an fahimci cewa akwai wasu mahimman abubuwa daya kamata masana su mai da hankali game dasu. Kamar haka: ya kamata masana nahawun harshen Hausa, su k’ara k’ok’ari don a samar da k’arin k’amusun ingilishi zuwa k’ausa. Saboda ba wani k’amus mai irin wannan tsarin baya ga na Rozana da Newman, wanda ta wallafa a shekarar 1997. Samar da k’amus irin wannan zai taimaka wa masu nazari don samun sauk’in fassara wasu kalmomi na ilimin kimiyyar harshe a lokacin da suke gudanar da nazarin wani fanni na nahawu daga littafan ingilishi.

A fannin nazarin gini jumla, ya kamata masana ilimin ginin jumla su samar da wasu k’arin littafatn da aka gina su bisa sabuwar fahimta ta zamani. Yin haka zai taimaka wajen bunk’usa harshen Hausa ta bangaren littafan nahawu. Waiwayar ayyukan da suka dad’e da gudana zai taimaka wirin warware matsalar da wasu gurabe ke dasu don sauk’ak’a fahimtar ga masu nazarin nahawun Hausa. Misali sake waiwayar bngarorin nahawu, irin ilimin tsarin furuci da sauran sassan shi, kamar tsarin gaba. zai haska wa masu nazarta wannan fannin wajen fahimta.

Masana ilimin kimiyyar harshe da suke gudanar da ayukkansu a kan harshen Hausa ya kamata su lura da ire-iren sababbin kalomomi da suke shigowa na zamani zuwa cikin harshen Hausa. Ko dai an aro daga wani harshe ko kuma an k’irk’ire su ne. rashin lura da ire-iren sabbabin kalmomi da suke shigowa na zamani zuwa cikin harshen Hausa. Ko dai an aro daga wani harshe ko kuma an k’irk’ire su ne. rashin  lura da ire-iren wad’anna kalmomi na iya haifar da matsala na samun bacewar kalmomi na asali. Gudanar da nazarin wad’annan kalmomi zai taimaka wajen adana kalmomin Hausa na asali ba tare sun bace ba. Sannan kuma za a sami k’arin wasu kalomimin da za su dace da zamanin da ake ciki.

Post a Comment

2 Comments

  1. Muna dogiya ga aiyukan ku.
    da za a sa shekarar da ka buga maqala da kufayen binciken da ake watsawa da abun zai armashi ga dalibai domin samun damar yin madogara (reference). domin samar da source mai inganci mun gode.

    ReplyDelete
  2. Abu-Ubaida Sani11 May 2018 at 13:31

    Mun gode Malam A. Abdu

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.