Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummawar Zauren Sakkwatanci Na Gidan Rediyon Vision F.M. Wajen Adana Kalmomi Da Jumlolin Karin Harshen Sakkwatanci (1)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya

NA 

MAINASARA ABDULKADIR

TABBATARWA


Mun amince da cewa wannan kundin digiri na Mainasara Abdulkadir mai Lamba 1211106045, ya cika dukkan k’a’idojin da aka gindaya domin samun digirin farko (B.A. Hausa) a Sashen Harsunan Nijeriya, Na Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

 

-----------------------------                                          --------------------------------

Sa Hannun mai dubawa                                                  Kwanan wata

Malam Sama’ila Umar

 

 

 

-----------------------------                                          --------------------------------

Sa Hannun shugaban Sashe                                             Kwanan wata

Prof. Atiku Ahmad Dunfawa

 

 

 

-----------------------------                                          --------------------------------

Sa Hannun mai dubawa na waje                                      Kwanan wata

 

 

SADAUKARWA


Na sadaukar da wannan aikin ga iyayena da kakannina da duk wanda ya taimaka mini a rayuwata. Allah ya sa ya zama abin alfahari ga d’aliban Sashen HarsunanNijeriya.

GODIYA


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangiji mai kowa mai komai Mabuwayi gagara misali, wanda ba a kwatanta shi da komai sannan Ya sanar da mu abin da ba mu Sani ba. Tsira da amincin Allah su k’ara tabbata ga shugabanmu, kuma za’ba’b’ben Manzo, shugaban dukkan Annabawa babba d’an Amina da Abdullahi, Annabi Muhammadu (S.A.W) tare da IyalanSa da Sahabbansa da kuma wad’anda suka bi su ta hanyar shiriya har zuwa ranar k’arshe.

Ina mik’a godiyata zuwa ga mahaifana wad’anda suka tarbiyyantar da Ni, suka kuma d’auki d’awainiyar kulawa da Ni ta hanyar d’aukar saka Ni a makaranta domin ganin na zama mutum nagari cikin jama’a, wato Alh. Abdulk’adir Sa’idu Tambuwal, (CON) da Hajiya Hadiza Liman da Haj. Hadiza (mama Hajo) da Rabi (mummy) da Prof. A’isha Madawaki. Allah ya saka musu da mafificin alherinSa amin.

Ina mik’a godiyata ga Malamina, wato Malam Sama’ila Umar wanda ya d’auki nauyin duba wannan aiki nawa tare da ba Ni kyawawan shawarwari da kuma hak’urin duba wannan aiki da yi min gyare-gyare, ba tare da nuna gajiyawa ko k’osawa da Ni ba, har lokacin da Allah ya nuna mana kammaluwar wannan aikin, Allah ya saka masa da mafificin alherinSa duniya da lahira amin.

Wannan shafin ba zai kammalu ba, sai na cigaba da mik’a godiyata ga d’aukacin Malamanmu na wannan Sashe bisa ga irin namijin k’ok’ari da suka yi wajen koyar da mu da kuma ba mu shawarwari domin samun cigaban karatunmu. Ina rok’on Allah ya saka musu da gidan aljannarSa, amin. Ina mik’a godiyata ga ‘yan’uwana, Haj. Baila’u Lawal da Amina Bala da Zara’u Abdulk’adir da Muwadata Abdulk’adir da Ruk’ayya Abdulk’adir  da Hadiza Abdulk’adir da Nana Abdulk’adir da Mustapha Abdulk’adir da matarsa Haj. Yuhanazu Tukur da Alh. Labaran da Sa’idu Murtala da Ummul-khairi da Mushkuru Abdulk’adir da moyi da Alh. Ibrahim Abubakar (Baburo). Allah ya saka musu da mafificin alherinSa, ya k’ara musu d’aukaka amin.  Haka kuma ba zan manta da irin gagarumar gudummawar da su; Halliru Yahaya, H.O.D. Dept. of Geography, C.O.E. Maru Zamfara State, da Zaharaddeen Buhari, (C.B.N. Gombe), da Alh. Idris Adam, Chief Registrar, Shari’a Court of Appeal, Sokoto, ba ni ba don haka ina mai yi masu addu’a, Allah ya k’ara masu d’aukaka da kariya bisa ayyukansu, ya albarkaci zuri’arsu baki d’aya amin. Ina mik’a godiya tare da jinjina ga iyalaina da suka jure da yanayin da na saka su a lokacin gudanar da karatu, wato Haj. A’isha Abubakar da ‘ya’yanta Abdulk’adir (Adnan) da Hafsat (Hanan) da fatar Allah ya k’ara mana k’aunar juna da yawancin kwana, amin.

A k’arshe, ina mik’a godiyata ga dukkan d’aliban da muka yi karatu tare da fatar Allah ya ba mu ikon hak’uri da juna, Allah kuma ya sa mu zama jekadu nagari a duk inda muka tsinci kanmu, da fatar Allah ya sakawa kowa da alherinSa, amin.

 

 

K’UMSHIYA


Take  ………………………………………………………………………………..i

Tabbatarwa ………………………………………………………………………..ii

Sadaukarwa ……………………………………………………………………….iii

Godiya …………………….………………………………………………………iv

K’umshiya …………………………………………………………………………v

BABI NA ‘DAYA: GABATARWA


Gabatarwa……………………………………………………………………1

1.0     Shimfid’a …………………………………………………………………….2

1.1     Bitar Ayukkan da suka Gabata ……………………………………………...2

1.2     Dalilin  Bincike………………………………………………………….....10

1.3     Hanyoyin Gudanar da Bincike …………………………………………….10

1.4     Muhimmancin Bincike ……………………………………….....................11

1.5     Nad’ewa …………………………………………………………………….12

BABI NA BIYU: JUMLA DA IRE-IRENTA A HARSHEN HAUSA


2.0     Shimfid’a ………………………...…………………………………………13

2.1     Ma’anar jumla ………………..……………………………………………13

2.2     Ire-iren Jumlolin Hausa ……..……………………………………………..14

2.2.1  Sassauk’ar Jumla …………………………………………………………..14

2.2.2  Jumlar tambaya……………………………………………………………17

2.2.3  Jumlar umurni ………………………………………………….................18

2.2.4  Jumlar korewa …………………………………………………………….19

2.4     Nad’ewa ………………………………………………………….................20

BABI NA UKU: Gabatar Da Azuzuwan Kalmomi Da Jumloli A Karin Harshen Sakkwatanci


3.0     Shimfid’a ……………………………………………………………….…. 22

3.1     Karin Harshen Sakkwatanci………………………………………………..22

3.2 Kalmomin Karin Harshen Sakkwatanci A Zauren Sakkwatanci Na Vision F.M………………………………………………………………………………..24

3.2.1 Kalmomi Masu Bambancin Furuci Amma Ma’ana ‘Daya……………….….26

3.2.2  Kalmomi Masu Ma’ana ‘DAya, Amma Sauti Bamban……………………..27

3.3 Jumlolin Karin Harshen Sakkwatanci………………………………………...30

3.3.1  Sassauk’ar Jumla A Karin Harshen Sakkwantanci ………………….……. 30

3.3.2  Jumlar Tambaya A Karin Harshen Sakkwatanci ………………………… 32

3.3.3  Jumlar Umurni A Karin Harshen Sakkwatanci ……………………….….. 32

3.3.4  Jumlar Korewa A Karin Harshen Sakkwatanci  ……………………….…. 33

3.6     Nad’ewa …………………………………………………………………….34

 

 

BABI NA HU’DU: WASU MUHIMMAN KALMOMI NA CIKIN JUMLOLIN KARIN HARSHEN SAKKWATANCI DA AKA TATTAUNA A KAN SU CIKIN ZAUREN SAKKWATANCI


 

4.0     Shimfid’a …………………………………………………………………...35

4.1     Mafayyaciya………………………………………………………………..35

4.2     Mafayyaciya A Karin Harshen Sakkwatanci……...……………………….37

4.3     Lokatak’……………………………………………………..........................38

4.2.1  Shud’ad’d’en Lokatak’…………………………………………………..……40

4.3.2  Lokatak’ Mai Ci………………………………………………………….…41

4.4     Nad’ewa …………………………………………………………………….42

 

BABI NA BIYAR: KAMMALAWA

5.1     Tak’aitawa ………………………………………………………………….44

 

Manazarta…………………………………………………………………47

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.