Gudummawar Zauren Sakkwatanci Na Gidan Rediyon Vision F.M. Wajen Adana Kalmomi Da Jumlolin Karin Harshen Sakkwatanci (2)

    Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya
    NA 
    MAINASARA ABDULKADIR

    BABI NA ‘DAYA:              

    GABATARWA

    Wannan bincikemai take, “Gudummawar Zauren Sakkwatanci Na Gidan Rediyon Vision F.M. Wajen Adana Kalmomi Da Jumlolin Karin Harshen Sakkwatanci”, aiki ne da aka gudanar bisa tsarin babi-babi. A babi na d’aya bayan shimfid’a, an gudanar da bitar ayyukan magabata don samun damar gudanar da shi. Daga nan sai aka fad’i dalilin da ya haifar da gudanar da nazarin. An bayyana hanyoyin da nazarin ya bi don samun nasarar kammaluwar sa. An bayyana mahimmanci binciken bayan kammaluwar sa. Babi na biyu daga shimfid’a sai ma’anar jumla da ire-irenta. Bayan nau’o’in jumla sai nazarin ya ba da misalan jular Hausa aka kuma nad’e babin a kaso na 2.3. A babi na uku kuwa nazarin ya yi k’ok’arin kawo tak’ataccen bayani game da karin harshen Sakkwatanci, sannan ya kawo tsarin kalmomin karin harshen Sakkwatanci a zauren Sakkwatanci na gidan rediyon Vision F.M. A k’ark’ashin wannan kaso ne nazarin ya zak’ulo kalmomi masu bambancin furuci amma ma’ana d’aya da masu ma’ana d’aya amma akwai bambancin tsarin sauti. Nazarin ya kawo yadda tsarin jumlolin karin harshen Sakkwatanci a kaso na 3.3. A ka nad’e babin a 3.4. A babi na hud’u mai take “Wasu Mahimman Kalmomi na cikin Jumlar Karin Harshen Sakkwatanci da aka tattauna a zauren Sakkwtanci” nazarin ya dubikamomin lokatak’ da mafayyaciya. A kalmomin lokatak’ karin harshen Sakkwatanci yana da yanayin lokatak’ biyu, wato na shud’ad’d’en lokatak’ da lokatak’ mai ci. An nad’e babin a kaso na 4.3. Babi na biyar an tak’aita nazarin ne babi bayan babi. Sai manazarta ta zo daga k’arshe

    1.0    SHIMFI’DA

    An dad’e ana gudanar da bincike a kan abin da ya shafi lamarin karuruwan harshen Hausa, tun daga rabe-rabensa har ya zuwa nazarin d’aid’aikun karuruwan harshen, kamar su: Sakkwatanci da Katsinanci da Zamfaranci da Kabanci da dai sauran kare-karen harshen Hausa. Da farko dai kafin a ce komai, ya kamata a san k’unshiyar wannan babi da ke k’ok’arin bayyana abubuwan da suka shafi nazarin da ake son gudanarwa. A wannan babi na farko yana da bayanan abubuwa da suka had’a da, bitar ayyukan da suka gabata, da dalilin yin bincike, da hanyoyin gudanar da bincike, da kuma muhimmancin bincike. Don haka wad’annan abubuwa da aka ambata, su ne za a gabatarwa, a kaso na gaba in da za a fara da bitar ayyukan da suka gabata kamar haka:

    1.1    BITAR AYUKKAN  DA SUKA GABATA

    Ganin irin muhimmancin da ke akwai wajen duba ire-iren rubuce-rubucen da magabata suka rubuta da nufin yin bitar wad’ansu daga cikin su, musamman wad’anda suke da alak’a da wannan binciken, tun daga kundaye da muk’alu da mujallu da litattafai in har akwai.

    Amfani, A. H. (1984) ya gabatar da mak’ala mai suna “Aspects' of Hausa Dialectology,” ya yi bayanin ke’ba’b’bun siffofin (idiosyncractic features) wasu kare-karen harshe Hausa. Ya yi bayani kan yadda wasu kare-karen harshen Hausa suka sha bamban da juna wajen amfani da lokatak’ (tense aspect).

    Hamma'ali B.M. (1985) A cikin nasa aikin ya kwatanta Sakkwatanci da daidaitacciyar Hausa a fannin furuci da tsarin Kalmomi da kuma tsarin jimloli. Haka kuma, ya yi k’ok’arin kawo bayanai dangane da Sakkwatanci da kuma bambancinsa na Kalmomi da Ma'anoni duk a tak’aice.

    Abubakar, B. (1990) ya yi k’ok’arin yin zuzzurfan bincike kan karin harshen Sakkwatanci, inda ya yi k’ok’arin gano bambancin sunaye tsakanin Sakkwatanci da daidaitacciyar Hausa. Kuma ya yi magana kan yadda karin harshen Sakkwatanci ke samar da suna na jinsin mace, wanda ya sa’ba wa na daidaitacciyar Hausa. Ya nuna cewa ana iya k’irk’iro suna ta hanya biyu, wato ta amfani da tushen kalma, da kuma d’afi. d’afin zai iya kasancewa d’afa-goshi da kuma d’afa-k’eya ko kuma d’afa-k’eya kawai. Misalin irin wad’annan Kalmomin su ne:

    Tushen kalma                 d’afa-k’eya                     cikakkiyar kalma

    kan-                                - o                                  - Kano

    d’afa-goshi            tushen kalma         d’afa-k’eya  cikakkiyar kalma

    ba-                        kan -                     - o               Bakano

    ba-                        kan -                     - uwa           Bakaniya     D.H.

    ba-                        kan -                     - a               Bakana   KH. SK.

    Wani aiki da nazarin ya gudanar da bitar sa shi ne, aikin da Mashegu, (1994),  ya gudanar. Mashegu ya yi aikinsa ne kan kalmomin tsigalau na Hausa, inda ya nazarci yanayin zuwan su a matakai daban-daban. A babi na d’aya Mashegu ya yi k’ok’arin kawo ma’anonin mahimman kalmomin taken bincike, wad’anda suka had’a da; ma’anar kalmar nahawun “functionalist”, sannan ya ba da ma’anar tsigalau “Diminitive” da hanyoyin amfani da tsigalau a harshen Hausa, tare da nuna cikakken amfani da tsigalau a cikin jumlar nahawun Hausa. A babi na biyu Mashegu ya tsttsafe kalmomin tsigalau tun daga rabe-raben su har zuwa guraben da sukan fito a nahawun Hausa. Babi na uku shi kuma manazarcin ya dubi kalmomin tsigalau ne ta fuskar ilimin ma’ana a nahawunce. Ya kawo rabe-raben ma’ana a nahawu, sannan ya dubi yadda kalmomin tsigalau suke samun tasarifi wanda ke haifar da samuwar sabuwar ma’ana a lokacin ginin jumla. Cikin babi na hud’u Mashegu ya nazarci kalmomin tsigalau ne a cikin wasu litattafan adabin Hausa. Ya dubi yadda aka yi amfani da kalmomin tsigalau a cikin littafin “Jatau Na K’yallu” da wak’ar “Allah Ka Ba Mu Sawaba” da littafin “Jiki Magayi”. Babi na biyar shi ne marfin aikin nasa inda ya kammala aikin ya kawo manazarta tare da rataye. Wannan aikin ba shi da alak’a ta k’ut-da-k’ut da wannan nazarin, alak’ar da suka had’a ita ce, dukkan su an gudanar da su ne bisa tafarkin nahawun Hausa.

    Fagge, da Yakasai (1986), wannan aikin an gudanar da shi ne a kan ilimin kwatanci, amma a harshen Ingilishi. Aikin mai take “A Comparative Study on Phonological and Morphological Aspect Between Kananci and Standard Hausa”. A cikin wannan aikin an tattauna game da su wa ye Hausawa? Sai aka dubi karin harshen Hausa da rabe-rabensa, sai kuma aka gabatar da taken aikin watau daidaitacciyar Hausa da Kananci, duk a babi na d’aya. Cikin babi na biyu kuwa sun tattauna ne kan kwatancin bambanci na tsarin sautin daidaitacciyar Hausa da Kananci. Sannan suka dubi tsarin naso a tsakanin daidaitacciyar Hausa da Kananci. A babin na biyu manazartan sun dubi yadda wasulla kan sallace da kuma tsari wasulla masu goyo ko tagwan wasulla. Babi na uku manazartan sun dubi yadda ake samun bambanci tsakanin daidaitacciyar Hausa da Kananci ta fuskar tasarifi, inda suka nazarci yadda ake jam’inta kalmomi da tsarin jinsintawa da ginin kalma da kuma samar da sabuwar kalma sai suka rufe aikin gaba d’aya. Wannan aikin yana da alak’a da wannan nazarin, saboda dukkan su a kan karin harshen Hausa aka d’ora su, sai dai wannan aikin ya ke’banta ne a kan karin harshen Sakkwatanci, sannan an gudanar da shi ne ta hanyar za’ba masa muhallin bincike da gidan rediyon Vision F.M.

    Abdu, (1991). Aiki ne da aka gudanar kan matsayin harshen Hausa ga k’abilun kudancin Zariya. Aikin an yi shi ne da harshen Ingilishi, wanda aka yi wa take da “Hausa as a Lingda Franca Among the Southern Zaria monority Linguistic Dialects Group”. A cikin aikin Manazarcin ya za’bI wasu daga cikin k’abilun ya ba da misalan yadda suke sarrafa harshen Hausa a lokacin da suke gudanar da ma’amala a tsakanin su da sauran k’abilun. Ya yi tsokaci kan Kataf da Kaje da Morwa da wasu da dama. Inda ya nuna yadda suke furta kalmomi da wasu sassan jumlar Hausa. An kasa aikin zuwa babuka biyar don samun sauk’in kammala aikin. Wannan nazarin ba shi da alak’a ta k’ut-da-k’ut sai dai don dukan su a kan harshen Hausa aka gudanar da su.

    Yakasai, (2001). Yakasai ya gudanar da aikinsa ne mai take “Gudummawar Gidan Talbijin Na STV Kano Wajan Bunk’asa Harshen Hausa Da Raya Al’adun Hausawa”.  A cikin wannan aikin an kawo tarihin kafuwar gidan talbijin na STV Kano tare da dalilin kafa shi. Daga nan sai Manazarcin ya bayyana mahimmancin gidan talbijin d’in, a babi na biyu. A babi na uku Manazarrcin ya kawo wasu mahimman shirye-shiryen da ake gabatarwa a gidan talbijin d’in. Wad’annan shirye-shiryen ana yin su ne don bunk’asa harshen Hausa da raya al’adun Hausawa. Yakasai ya nuna yadda gidan talbijin d’in yake gudanar da shirin wasan kwaikwayo da wasa k’wak’walwa da yadda ake kawo rahotanni. A babi na hud’u an gabatar da irin gudummawar da gidan talbijin na STV Kano ke bayarwa wajen bunk’asa harshen Hausa da raya al’adun Hausawa. An kammala binciken ne a babi na biyar. Wannan nazarin yana da alak’a da wannan binciken domin dukkan su, sun yi tarayya kan muhallin gudanar da su, wato kafar yad’a labaru. Amma akwai bambanci saboda shi wannan an yi shi ne kan kafar talbijin, inda nawa binciken, sai dai wannan aikin ya ke’banta ne a kan karin harshen Sakkwatanci, sannan an gudanar da shi ne ta hanyar za’ba masa muhallin bincike da gidan rediyon Vision F.M. Sakkwato.

    Muh’d, (1986). Wannan Manazarcin ya yi aikinsa ne kan kwatanci tsakanin Daidaitacciyar Hausa da Katsinanci; inda tun a babi na farko ya gabatar da aikin nasa inda ya kawo bambance-bambance da ake samu a karin harshen katsinanci. Ya bayyana irin hanyoyin da yake son amfani da su wajen gudanar da bincikensa. A babi na biyu Manazarcin ya kawo tak’aitaccen asali tarihin rubutun harshen Hausada matsayin Daidaitacciyar Hausa kan hanyar rubutun. Babi na uku Muhammad ya bayyana tarihin Katsina da Katsinanci,  sannan ya sake kawo tarihin tsohuwar daular Katsina da kuma Katsina a lokacin jihadin Shehu ‘Danfodiyo. Manazarci ya yi k’ok’arin bayyana matsayin Katsina a lokacin da ya gudanar da binciken nasa (1986). A kaso na 3.4 Manazarcin ya bayyana ko me ake nufi da Katsinanci? Wanda ya zama shi ne k’arshen babin na uku. Babi na hud’u ya d’auke da bayanai kan ire-iren bambance-bambancen da ake samu tsakanin Daidaitacciyar Hausa da Katsinanci ta fuskar furuci da nahawu. A 4.1 Muhammad ya yi k’ok’arin bayyana bambance-bambancen da ake samu ta fuskar bak’ak’e. Haka kuma a 4.2 ya fito da irin bambance-bambancen da ake samu a wasulla. A 4.3 Manazarcin ya yi bayani kan nahawu inda ya dubi wasu mahimman sassan jumla na Daidaitacciyar Hausa da na Katsinanci. A 4.4 Manazarcin ya yi kyakkyawan bayani kan wasu ‘yan bambance-bambance da ake samu a karin harshen Katsinancin kansa, tsakanin kudancinsa da arewacinsa. Inda ya dube su t fuskar furuci kuma ya kwatanta su da kalmomin Daidaitacciyar Hausa. An kammala binciken ne a kaso na 4.5, tare da yin ratayen kalmomin karin harshen Katsinanci da yin k’arin bayani da kalmomin Daidaitacciyar Hausa. Wannan nazarin na Muhammad (1986) yana da alak’a da wannan nazarin domin dukan su a kan karin harshe aka yi su, sai dai wannan aikin ya ke’banta ne a kan karin harshen Sakkwatanci, sannan an gudanar da shi ne ta hanyar za’ba masa muhallin bincike da gidan rediyon Vision F.M.

    Muharazu, da Wasu (2008), sun yi aikin binciken su ne kan “Zamfarci” inda suka kawo rabe-raben Zamfarci tare da kawo tarihin k’asar Zamfara a tak’aice, sannan suka dubi Zamfara a zamanance. Inda suka yi amfani da tsarin k’ananan hukumomin jahar ta Zamfara. Sun za’bI k’aramar hukumar Tsafe inda ta zame masu ma’aunin karin harshen Zamfarci. Muharazu da Wasu sun yi k’ok’arin tattauna batun Hausawan jahar Zamfara da watsuwar su zuwa wasu sassan jahar, inda wasu k’abilu suke da zama. Sun nazarci tsarin sautukan Zamfaci da tsarin furucin Zamfarci tare da ba da ingantattun misalai. Wasu daga cikin tsari sautin da suka tattauan a cikin aikin nasu akwai /ts/ da /tc/ lokacin da wasalin /aa/ ya biyo bayan su, da /Ø/ da yake koma wa /hw/ da kuma /s/ da ke komawa /sw/ da /z/ da ke koma /zw/ da kinin wasalin /y/ da /w/. Sun nazarci tsarin naso a karin harshen Zamfarci, haka kuma sun dubi le’bantawa da jam’intawa. Manazartan sun dubi tsarin kalmomin mallaka tun daga doguwar mallaka har zuwa gajera. Sun nuna yadda k’wayar ma’anar mallaka ta “-rsa” take komawa “tai” a karin harshen Zamfarci Maharazu da Wasu sun yi k’ok’ari k’warai da gaske wajen bayyana tsarin karin harshen Zamfarci. Wannan bincike na su Maharazu (2008) yana da alak’a makusanci da wannan nazarin, domin duk a kan karin harshe ake magana, sai dai wannan aikin ya ke’banta ne a kan karin harshen Sakkwatanci, sannan an gudanar da shi ne ta hanyar za’ba masa muhallin bincike da gidan rediyon Vision F.M.

    Duk wad’annan ayyukan na wad’annan masanan suna magana ne a kan abin da ya shafi kare-karen harshen Hausa a ciki har da Sakkwatanci, inda suka bambanta da wannan aikin shi ne, wannan aikin ya ke’banta ne kan wasu muhimman kalmomi, na karin harshen Sakkwatanci da ake wasa k’wak’walwa da su a gidan rediyon Vision F. M. inda wannan nazarin yake k’ok’arin adana su a rubuce don gudun salwantar su nan gaba. Wato nazarin na son ganin karin harshen Sakkwatanci ya sami wata taska ta adana kalmomi da sassan jumlar da ake hasashe ‘bacewar su nan ba da dad’ewa saboda barazanar zamani.

    1.2 DALILIN BINCIKE

            Dalalin da ya haifar da wannan binciken shi ne, a lokacin gudanar da bitar ayyukan da magabata suka aiwatar ba a sami wani aiki da ya yi daidai da wannan nazarin ba ko da kuwa ta fuskar taken bincike ne. Wani dalilin kuma shi ne don cika k’a’idar da Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato ta shinfid’a kan cewa duk d’alibin da ya kawo shekarar k’arshe dole ne ya gudanar da bincike na nazari a fannin da ya yi karatu don ba da gudumuwa a Sashen da ya yi karatu. Dalili na uku kuwa shi ne yin wannan bincike zai taimaka wajen warware matsalar da akan samu na fahimtar karin harshe Sakkwatanci ga sauran jama’a musamman ma mutanen da suka fito daga rukunin karuruwan Hausa na gabashi don su iya bambance shi da takwarorinsa kamar Zamfarci da Gobiranci da Kabanci.

    1.3 HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE

            An gudanar da wannan bincike a kan matakai daban-daban. Da yake aiki irin wannan ya shafi cud’anya da jama’a da ziyartar wurare muhimmai da ake iya samar da shiga d’akunan karatu da kuma huld’a da mutane don samar da ingantattun bayanai. Don haka nazarin ya yi k’ok’arin shiga sak’o da lungu tare da ziyartar masana, da yin nazarin ayyukansu domin cimma burin ganin anyi aikin bincike mai inganci.

    1.4 MUHIMMANCIN  BINCIKE

    Wannan binciken ba zai rasa rawar da zai taka ba a gaban manazarta, wato ma'ana ba zai rasa kasancewa mai muhimmanci ba ga masu karatu ko nazarin abin da ya shafi karin harshe, musamman ma tsakanin Karin harshen Sakkwatanci da kuma daidaitacciyar Hausa, da sauran kare-karen harshen Hausa.

    Wannan binciken zai kasance mai alfanu ga manazarta masu bincike kan abin da ya shafi karin harshen Sakkwatanci, musamman  kan abin da ya shafi azuzuwan kalmomi a Sakkwatanci. Haka kuma, zai taimaka ga masu son su san Sakkwatanci, da kuma masu nazarin bambance-bambancen da ake samu tsakanin Sakkwatanci da dangogin karin harshen Hausar Yamma.

    Muhimmancin wannan binciken ga manazarta kuwa, bai wuce su yi amfani da shi wajen sanin bambancinsa da sauran karuruwan harshen Hausa ba, ta yadda za su iya tantance shi tsakanin sa da sauran karuruwan harshen Hausa. Haka kuma zai taimaka wa mai nazarin rubuce-rubucen mak’alu da kundayen digiri da litattafai musamman masu aiki kan tsarin ginin jumla, don sanin k’a’idar yin amfani da kalmomin karn harshen na Sakkwatanci.

    A k’arshe wannan binciken zai kasance mai muhimmanci a gare ni. Domin shi ne zai kasance abin bugun gaba gare ni, da kuma makami, a duk inda na shiga ko na kasance ya rik’a nuna ni domin in kasance a cikin wad’anda suka d’an ce wani abu a cikin harshen Hausa. Kuma zai k’ara muhimmanci ga masu son cigaba da bincike kan karin harshen Sakkwatanci da su k’ara zurfafa bincike na wasu abubuwa makamantan wad’annan a cikin harshen Sakkwatanci. Kuma zai k’ara k’arfafa k’warin guiwa ga wasu masu nazari don zak’ulo hanyoyi domin bunk’asa harshen Sakkwatanci.

    1.5 NA’DEWA

    A wannan babin na d’aya an yi bayani kan bitar ayyukkan da suka gabata da kuma dalilin yin bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike tare da kuma muhimmancin bincike, haka kuma an nuna tsarin gabatar da aiki. Babban muhimancin wanannan binciken shi ne na kulawa wasu muhimman kalmomi da zantukan Karin harshen Sakkwatanci dan gudun salwantar su, saboda barazanar sauyawar zamani da ake samu kan harsunan duniya da harshen Ingilishi yake yi musu.

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.