Dusashewar Wasannin Gargajiya A Kasar Yabo (3)

    Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Jahar Sakkwato, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
    NA
    Sufiyanu Abubakar
    Hassan Ladan
    Hassana Mustapha Ibrahim

    BABI NA BIYU

    Takaitaccen Tarihi Da Asalin Garin Yabo

    2.0 Gabatarwa


    A halin yanzu garin Yabo shi ne cibiyar mulki ta k’aramar hukumar Yabo, a nan ne kuma Sarkin Kabin Yabo yake zaune. Wannan masarauta ta had’a da garuruwa irin su, Bingaje; Dagawa; Fakka; Muza; Kibiyare; Dono; Gudurega; Ruggar Kijjo, Shiyar Ajiya, Shiyar Waziri. Wad’annan garuruwa suna da k’auyuka na masu unguwanni da dama, da ke k’ark’ashinsu.

    Idan mutum ya fito daga Sakkwato ta kudu zai d’auki kimanin kilo mita 45 zai tarar da Lambar Bojo a kan titin Birnin Kabi. In ko ta hanyar Shagari ya biyo akwai wata Lambar Yabo wadda ake kira (Lambar D’an Bayi). Wad’annan su ne hanyoyin da ake bi domin a shiga garin Yabo.

    Garin Yabo gari ne da ke shimfid’e a cikin yanayin Dutsi ta kowane gefe, kasancewar an gina garin ne a lokacin yak’e-yak’e. Sannan kashi 60 cikin 100 na k’auyukan Yabo haka za ka tarar da su. Baya ga haka, mafi yawan k’auyukan Yabo suna da yanayi na dausayi da kuma k’ananan gulabe. Sannan Yabo gari ne wanda ya had’a k’abilu daban-daban kamar Fulani, Hausawa da Gobirawa da kuma Kabawa (D’ancika, 2011).

    2.1 Tak’aitaccen Tarihin Malam Muhammadu Moyijo Sarkin Kabi Na Farko


    A k’arshen k’arni na 16 mafi yawancin Fulani sun mai da k’asar Hausa a matsayin wurin zamansu. Wasu daga cikin Fulani masu ilimin addinin Musulunci, sun ci gaba da shiga cikin k’asar ta Hausa domin karantar da addinin Musulunci. A sanadiyyar haka, a farkon k’arni na 19 a kowane sak’o ana iya samun Fulani malamai a k’asar ta Hausa.

    Muhammadu Dotti kakan Muhammadu Mojijo shi ne ya jagoranci jama’arsa domin shigowa daular Kabi ta wancan lokaci. A nan suka fara tsayawa a wani gari da ake kira Gigane lokacin sarkin Kabi Muhammadu Tomo a shekarar 1703-1707. An bayyana cewa su wad’annan jama’a ta Wolorbe (wani rukuni na Fulani) daga baya sun k’arasa zuwa Shema da kuma Gotomo a k’ark’ashin jagorancin Muhammad Sambo, wanda shi ne mahaifin Muhammadu Moyijo. Babban dalilin hijira ga jama’ar Fulani a wannan lokaci shi ne domin su samu wuri mai dausayi domin kiyo da kuma noma. Wasu dalilan sun had’a da fad’ace-fad’ace a tsakanin manoma da makiyaya.

    A k’ark’ashin jagorancin Malam Moyijo Fulani da yawa sun samu damar samun wurin zama a cikin k’asar Kabi. Sanadiyar wasu dalilai da suka bai wa Muhammadu Hodi damar zama sabon Sarkin Kabi. Shi kuwa Mojijo a dalilin wasu matsaloli na damuwa ya sa ya k’aurace wa wurin zamansa na farko wato Gotamo zuwa wani wuri wato Yabo ta yanzu saboda haka, wannan ne ya ba wa damar garin.. sai daiHolorbe ne suka kafa ta daga baya suka k’aura saboda ‘yan k’ank’anan fad’ace-fad’ace kusa da garin Yabo.

    2.1.1 Rayuwar Moyijo da Wuraren Zamansa


    Muhammadu Mojijo shi ne daga cukin na farko da suka fara kar’bar tuta ga Shehu Danfodiyo, wadda ta ba shi damar fara jihadi a yankin da kuma mak’wabtan k’asarsa. Muhammadu Mojijo an haife shi a wani gari da ake kira Sheme inda ya girma kuma ya yi karatun addini a wurin mahaifinsa. Muhamadu Mokiko ya kasance a matsayin babban sarki a daular Kabi. Sunan sarautarsa Magajin Sangaldi, wato shugaban Fulani a k’asar Kabi ta wancan lokaci, kuma fadarsa ta kasance a garin Gotomo kafin ya sassak’a garin Yabo.

    Kafin a fara jihadi Moyijo ya kasance sanannen magoyi bayan Shehu tun lokacin gangamin jihadin k’asar Kabi a shekarar 1780. Tun wannan lokaci aminci da abokantaka ta k’ullu tsakanin Shehu da Moyijo.

    2.1.2 Lalacewar Dangantakar Moyijo da Hukumomin Daular Kabi


    A wannan lokaci dangantakar Moyijo da hukumomin k’asar Kabi sai k’ara lalacewa take yi. Yayin da dangantakar k’asar Gobir da Shehu ta yi k’amari, inda Sarkin Gobir Yunfa ya jagoranci wata tawaga domin a yak’i Shehu da magoya bayansa a Gimbana. Inda aka kashe mutane, kuma aka kama wasu a matsayin bayi. Wannan shi ya sanya Shehu hijira zuwa garin Gudu a shekarar 1804.

    Magoya bayan Shehu sun nad’a shi a matsayin Amirul muminina kuma suka jaddada jihadi. A wannan lokaci hukumomin k’asar Kabi sun samu labarin cewa Moyijo tare da ‘yan uwansa, Ajiwa, Yamusa, Abubakar Ruwa, Ahmadu da sauransu duk sun mik’a wuya tare da ba da goyon bayansu d’ari bisa d’ari ga  jagorancin Jihadin tare da Shehu Usmanu D’anfodiyo.

    2.1.3 Mubayi’a Da Biyayyar Moyijo Ga Shehu D’anfodiyo


    Moyijo ya yi gangamin jama’arsa domin su amsa kiran Sheu da kuma yi musu bayani game da Jihadi. Moyijo ya yi wannan ne domin nuna goyon bayansa da biyayyarsa ga Shehu, tare da shi lokacin da ya je wurin akwai fiye da doki d’ari da d’aruruwan jama’a har ya sanya shakku a jama’ar Shehu. Bayan Moyijo ya wuce sai suka bayyana shakku ga Shehu saboda ganin yadda Moyijo ya yi biyayya, duk da irin wadatar da Allah ya yi masa, (k’arfin da yake da shi) sanadiyar wannan shakka ya sanya Shehu ya yi tunanin jarraba Moyijo a kan wannan biyayya ta shi domin d’ebe shakku. Shehu ya tura wani mutum da doki domin ya kira Moyijo kuma aka ce ya bari sai Moyijo ya isa gab da shiga cikin garin Yabo sannan ya kira Moyijo ya fad’a mai Sheu na kiransa.

    Jin haka ke da wuya sai Moyijo ya umurci sauran mutane da su isa Yabo su kwanta su huta saboda la’akari da nisan da yake tsakanin Gudu da Yabo, sai Moyijo da shi da k’anensa Abubakar Ruwa, Yamusa, Kamadu da Dudu suka juya zuwa Gudu domin kar’bar kiran Shehu. Ajiwa shi ne wa ga Moyijo, shi ya isa Yabo domin ya yi ban ruwan dabbobinsu.

    Lokacin da Moyijo da ‘yan rakiyarsa suka isa Gudu Shehu ya ji dad’i ya gode musu, ya yi musu addu’a kuma ya bai wa Moyijo tutar farko don jaddada addinin Allah. Sannan ya tabbatar da shi a matsayin Amirul-kabi. Moyijo shi ne mutum na farko da ya fara kar’bar tutar jihadi daga Shehu.

    2.1.4 Yak’ok’i da Jihadodin Moyijo


    Moyijo ya samu damar yin jihadi a k’asar Kabi lokacin da Moyijo ya dawo sabon mazauninsa na Yabo sai ya fara yak’ar k’ananan garuruwan da ke kewaye da shi kafin fara babban jihadin cin daular Kabi ta yankin gabas. Lokacin wad’annan jihadodin Moyijo ya yak’i garuurwa da k’auyuka wad’anda suka had’a da; Fakka, Birnin Asuma da Shimfiri da Muza da Gudale da Dankal da Bayawa da Yakurutu da kuma Dafashi, wanda ya ba Moyijo damar mai da garin Yabo wani wuri na musamman wajen gudanar da harkokin jihadi.

    Bayan k’are yak’in Tabkin Kwatto, Shehu da jama’arsa sun fuskanci matsaloli na k’arancin abinci a dalilin haka sai Shehu ya rubuta wa d’ansa Malam Muhammadu Bello takarda zuwa ga Malam Moyijo. A takardar ya shaida masa halin da jma’arsa ke ciki na k’arancin abinci, kuma Malam Moyijo ya tarbi Shehu tare da shi da dangoginsa. Ya kuma ajiye Shehu garin Magabci Gabas ga gulbi har tsawon wata biyu. An sami wannan a cikin wak’en Nanan Asma’u inda take cewa:

    Kabi ta yi kai duk ga tanyon Shehu

    Ko Moyijo ya za ka shi da dangogin nasa.

    (Nana Asma`u: Wak’ar Jahadi…)

     

    A nan Mugabci ne Shehu ya rubuta wa sarakunan Hausa takardu, inda ya yi kira gare su domin su taimaka wa addinin Allah. Sun had’a da sarakunan Kano. Da Katsina da Zazzau. Amma sarkin Zazzau Makau kad’ai ne ya kar’bi kiran Shehu. Shi ma fadarsa ba wanda ya bi shi, Kano da Katsina ya ga takardun su ka yi.

    Waziri Gid’ad’o ya bayyana Moyijo a matsayin mataimakin Shehu kuma a cikin wad’anda Shehu ya bai wa tuta kuma a cikin kwamandodin yak’i na Shehu, a cikin littafinsa mai suna Raud aljinan.

    Bayan samun nasara jihadi, Muhammadu Moyijo ya tabbatar da zamansa a garinsa na Yabo da sarautarsa ta Amirul Kabin Yabo kamar wasu manyan sarautun Kabi. Malam Moyijo ya rasu a shekarar 1818 kuma d’ansa Muhammadu Yalli shi ne ya gaje shi kuma har yanzu zuriyar Moyijo su ne suke rik’e da wannan sarauta ta Yabo. Manyan abubuwan da za a iya tunawa game da shi sun had’a da:

    1. Malam Moyijo shi ne Amirul Kabi na farko da Sheu Usmanu Danfodiyo ya bai wa wannan matsayi.

    2. Malam Moyijo shi ne farko da Shehu D’anfodiyo ya bai wa tutar jaddada addinin Allah a wurarensu.

    3. Malam Moyijo na d’aya daga cikin kwamandodin Shehu Usman D’anfodiyo.

    4. Malam Moyijo yana d’aya daga cikin manyan sarakuna k’araga da ke za’ben sarkin Musulmi.

    5. Malam Moyijo yana d’aya daga cikin ‘yan majalisar sarkin Musulmi da ke ba shi shawarwari.


    Duk wad’annan muk’aman sun rataya ne ga masarautar Yabo. Saboda ganin irin girman da d’aukakar da masarautar take da shi tun lokacin jahadin jaddada addinin Musulunci na Shehu Usmanu Danfodiyo da kuma irin gudummuwar da masarautar ta bayar ga samun nasarar jaddada addinin Allah (D’ancika, 2011).

    2.3 Ire-iren Wasannin Gargajiya


    A al’adance kowane gari na da nasa ire-iren wad’annan wasanni na gargajiya da suke gudanarwa. Don haka a garin Yabo akwai ire-iren wad’annan wasannin na gargajiya, wad’anda aka gada kaka da kakanni.

    Ire-iren wad’annan wasannin za mu ce, wasanni ne na gadin gadin, wad’anda suka samo asali daga rayuwar gargajiya tun shekaru aru-aru da suka wuce. Wato ba wanda zai ce ga wanda ko lokacin da aka fara wad’annan wasannin.

    Wasu daga cikin ire-iren wasannin gargajiya na garin Yabo sun had’a da:

    1. Afajana (karkaja)

    2. A shisshire

    3. A sha ruwan tsuntsaye

    4. ‘Yar bud’d’a

    5. Dungunge

    6. Jangiro-jangiro

    7. Jini wa jini

    8. Kuren kuskure (kurde)

    9. Kasko-kasko

    10. Langa

    11. Liyambo

    12. ‘Yar lunk’as

    13. ‘Yar k’usk’us

    14. ‘Yar ato (Bowajo)

    15. ‘Yar jayau

    16. ‘Yar waya

    17. ‘Yar k’etarau (wasan k’etare)

    18. ‘Yar dawaki

    19. Wasar karnuka

    20. Wasar teloli

    21. Wasannin ‘yan mata

    22. Wasan ‘yar tsana

    23. Yar goyo

    24. Tafa-tafa


      • Muhimmancin Wasa






    Wasannin gargajiya a gairn Yabo ba haka suke kara zube ba domin kuwa suna da matuk’ar amfani saboda kuwa, suna taimakawa wajen: Tarbiyyar yara da Motsa jiki (kiwon lafiya) da Rage dare (hira) da Koyar da harshe da K’arfafa zumunci da Neman abin masarafi da Koyar da dabarun zaman duniya.

    2.4.1 Tarbiyyar Yara


            Wasa tana da matuk’ar muhimmanci, domin kuwa tana koyar da tarbiyya ga yara. Domin kuwa, kamar yadda addinin Musulunci ke da dokoki na ladabtarwa da horo da hani, haka ma kowace al’umma ke da nata dokoki wanda take bi domin ladabtar da nata yara. Kowace wasa takan tsara nata dokoki ta kuma ladabtar da duk wanda ya sa’ba wad’annan dokokin. Wannan zai sa yara su tashi da sanin irin dokokin da aka shata a kan wani abu da kuma abin da zai faru ga wanda ya sa’ba wad’anan dokokin.

    2.4.2 Motsa Jiki (Kiwon Lafiya)


            Wani muhimmanci na wasa shi ne kiwon lafiya, domin kuwa a lokacin da yara ke aiwatar da wasa, suna yi ne ta hanyar motsa jiki, kamar guje-guje da tsalle-tsalle, ta wannan hanya kan sa jini ya yawata a ko’ina cikin jikin, wannan na taimakawa ga kiwon lafiya da kuma tashi da kuzari da dauriya.

    2.4.3 Rage Dare (Hira)


    Haka ma wani muhimmanci na wasa shi ne rage dare, domin kuwa a madadin yaro ya tafi wurin yawon banza a inda ba a san inda yake ba, sai ya tafi wurin wasa. Wannan zai sa ya samu abin da zai amfane shi ta hanyar motsa jiki da kuma sauraren wak’e-wak’e masu sha’awa da bandariya domin samar da raha da nishad’antarwa.

     

     

    2.4.4 Koyar da Harshe


    Wani muhimmanci kuma shi ne, koyar da harshe. Domin kuwa idan muka yi la’akari da irin kalmomin da ake amfani da su wajen aiwatar da wasanni, za mu ga cewa suna k’unshe da d’imbin hikimomi da salailai wanda wannan kan sa yaro ya tashi da sanin harshensa da kuma k’warewa a kan wasu zantuka na hikima. Wannan ya had’a da gagara-k’wari da salon magana ko zaurance da kacici-kacici da dai sauransu.

    2.4.5 K’arfafa Zumunci


    Babban muhimmancin wasa shi ne k’ara dank’on zumunci, ba ga yara kad’ai ba, har zuwa ga iyayensu. Wannan kan faru ne ta hanyar da yara ke taruwa a dandali guda, duk da kasancewar wuraren zamansu daban-daban ne wannan zumunci kan d’ore har girma. Kuma ta wannan ne yara kan zama abokan juna, har abin ya kasance sanadiyar zumuntaka a tsakanin iyayensu da ‘ya’yansu ta har abada.

    2.4.6 Neman Abin Masarufi


    Neman abin masarufi na daga cikin muhimmancin wasa. Domin kuwa idan muka yi la’akari da wad’ansu jama’a za mu ga cewa, suna yin wasa ne domin neman abin da za su ci, na yau da kullum. Ire-iren wad’annan jama’a sun hada da:

    1. Masu wasa da kura

    2. Masu wasa da maciji da kunamu

    3. Masu wasa da birai

    4. ‘Yan tauri


    Duk da kasancewarsu masu wasa da rayuwarsu, amma suna yi ne domin kariyar kai, da rashin nema ga wani.

    https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.