Bismillahir Rahmanir Rahim
وعن عبد الله بن عمرو بن
العاص رضي الله عنهما أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: خير الدعاء دعاء يوم عرفة،
وخير ما قلت أنا والنبيّون من قبلي: لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك، وله
الحمد، وهو على كل شيء قدير. رواه الترمذي (3585) وحسَّنه الألباني في " صحيح
الترغيب " (1536) .
Dubi da hadisin Abdullahi ɗan Amru ɗan As (Allah Ya yarda dasu), yace Manzon Allah (saw) yace: "Mafi alkhairi addu'a itace addu'ar ranar Arfa. Kuma mafi alkhairin abinda nace da ma duk annabwan da suka zo kafin ni, shine La'ilaha illallahu wahadaHu la sharika lahu laHul mulki wa laHul hamdu wa Huwa ala kulli shai'in ƙadeer. (Tirmizy ya ruwaito, kuma Albany ya Hassan shi).
GA samfur na
irin ADDU'O'IN da ya kamata mu riƙa muyi ta maimaitawa, musamman bayan La'asar
zuwa Magriba. Kamar yadda Abu Nu'aim ya ruwaito daga Aɗa'u ɗan Abi Rabahin
cewa, "idan mutum ya samu dama ya keɓa da maraicen ranar Arfa, toh ya
aikata" saboda ana sanya ran karɓan
addu'a yafi kaifi a wannan lokacin.
Toh shawari
anan shine, kada mu dage da roƙon kuɗi zalla (you know, ƴan Najeriya, damuwar
kenan 🤪). Kamata ya yi muyi
ADDU'O'IN wa kawukan mu da iyayen mu (rayayyunsu da matattunsu), sauran ƴan'uwa
da abokan arziƙi, al'umman musulmi baki ɗaya da ma ƙasar, jihohi mu da kuma uwa
uba, shugabannin mu. Kada mu manta, ƴan'uwan mu musulmai a Falasɗin musamman a
Gaza, suna buƙatar ADDU'O'IN mu na musamman.
Muyi nazarin
waɗannan adduoin;
1. La'ilaha
illallahu wahadaHu la sharika lahu laHul mulki wa laHul hamdu wa Huwa ala kulli
shai'in ƙadeer. Tunda Manzon Allah(saw) yace shine mafificin abinda za'a faɗi,
toh muyi ta maimaitawa.
2. Rabbana
atina fiddunya hasanatan wa fil akhirati hasanatan wa ƙina azaban Nar. Anas
(RA) ya ruwaito cewar Manzon Allah(saw) yana yawan maimaita wannan addu'ar.
Muyi ta maimaitawa, domin ta ƙunshi kusan duk abinda zamu roƙa a ɗaiɗai.
3. AllaHumma
inny as'alukal afwa Wal afiyata fiddunya Wal akhira. Saboda hadisin Anas da
yazo a Musnad Ahmad, Sunanut-Tirmizy da Sunan Ibnu Majah, cewar wani mutum yazo
ya tambayi Manzon Allah akan wani addu'a ne yafi falala, sai Manzon Allah Ya
gaya masa wannan addu'ar. (Shu'aibul Arna'uɗ yace Hasan ne ligairihi, Amma
isnadinsa me rauni ne).
4. Rabbi inni
zalamtu nafsy zulman katheeran, fagfirly magfiratan min indik, war hamny innaka
antal gafurur-Raheem.
5. la'ilaHa
illa anTa subhanaKa inni kuntu minazzalimin addu'ar annabi Yunusa.
6.
Hasbunallahu wa ni'ima wakil, alallaHi tawakkalna. Addu'ar Annabi Ibrahim.
7. Hakanan,
idan zamu roƙa wa shugaba ni shiriya, ko mu roƙi Allah Ya ƙwata mana wani
haƙƙin mu, kamar halinda ake ciki a ƙasar nan da jihohi dabam dabam na zalunci.
Ga tsadan kaya, ga kora daga wajajen kasuwa da sana'a, babu gaira babu dalili
aka hau ɗaga mutane a inda suke neman abinda suke rufa asirin kansu da na
iyalan su. Toh zasu iya addu'ar Allah Ya ƙwato musu haƙƙin su, kuma Allah zai
amsa. Amma zasu iya la'akari da wasu dalilan, kamar yadda ake cewa, shi
al'amarin Public Policy ko leadership and management, Abu ne sai wanda yake kai
ke iya fahimtar me yafi da cewa ayi a koda yaushe, ya yin irin wannan dokoki.
Koma meye, ai ana la'akari da halin ƙunci da talakawa kan iya shiga.
8. Ya Allah
ka ba mu lafiya da zaman lafiya a gidajen mu, anguwaninmu, garuruwanmu,
ynkunanmu da ma ƙasa baki ɗaya.
9. Ya Allah
Ka shiryi shugabanninmu, Kayi riƙo da hannuwa su zuwa daidai.
10. Ya Allah
Ka shiryi al'umman mu maza da mata, da matasa. Ka ɗauramu baki ɗaya a hanyar
daidai, Ka rabamu da aikin ashsha.
11. Ya Allah
Ka yaye mana duk wata damuwa, masifa, bala'i, matsala da jinya.
12. Ya Allah
kayi katangan ƙarfe tsakanin mu da duk wani mugu, azzalumi, maha'inci,
mayaudari.
13. Ya Allah
duk me nufin mu da sharri da hassada da ƙyashi, da cuta, da ƙulle ƙulle, da
makirci, da musgunawa, da tozartawa, Ka mana maganinsa. Ka shirye shi, idan ba
me shiryuwa bane, ka mana maganinsa, ka mayar masa da ƙullinsa kansa. Ameen
Yanada
muhimmanci mu sani cewar, wanda duk Allah Yaja kwnansa zuwa yau, toh Ya masa
falala, kuma Ya bashi babban rabo. Don haka kar ayi ƙasa a gwiwa, a himmatu da
ADDU'O'IN alkhairi. InshaAllah za'a dace.
Mu sanya juna
a ADDU'O'IN mu na yau. Ku tuna dani cikin ADDU'O'IN ku, ku roƙamin sabati da
cikawa da shahada da rayuwa mai amfani.
Allah Ya
datar damu, ameen, Ya zil Arshil Majeed, Ya Hayyu Ya Qayyum, Ya sami'ud Du'a.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.