Ticker

6/recent/ticker-posts

Waibuwar Masunta

Musa Shehu

Sashen koyar da harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.
07031319454

August, 2011

TSAKURE


Mak’asudin wannan bincike shi ne, gano irin waibuwar da masunta kan nuna musamman a lokacin wasu bukuwa nasu ko idan rana ta ‘baci ko in buk’ata ta taso. Galibi masu sana’o’in gargajiya na k’asar Hausa kamar mak’era da wanzamai da manoma da mahauta da masunta da sauransu, sukan nuna isa da mallakar sana’o’insu a wasu lokuta na musamman idan buk’atar hakan ta kama. Ganin cewa, sana’ar su sana’a ce mai had’arin gaske dangane da abubuwan da suke had’uwa da su lokacin su a cikin ruwa, ya tilasta su neman taimako iri daban-daban domin kariyar kai da kaya. Wannan ne ya sa babu wata dabbar ruwa komai girmanta komai k’uk’uwarta da za ta yi musu barazana. Haka kuma waibuwar tasu ba ta tsaya ga ruwa ko dabbobin ruwan ba, hatta ma idan wata matsala wadda ta shafi ruwa ta sami mutane kamar mak’akwar k’aya ko mutuwa a ruwa da sauransu, sukan nuna buwaya ko waibuwa don taimaka wa jama’a. Wad’annan al’amurra su wannan mak’alar ta nazarta.


1.0     Gabatarwa

Sana’ar su tana d’aya daga cikin manyan sana’o’in Hausawa na gargajiya da suke gudanarwa a lokaci mai tsawo da ya gabata. Sana’a ce da ta k’unshi yin ta’ammuli da ruwa. Wannan ya sa duk wurin da ruwa ke taruwa masu yawa ko wurin da ruwa ya ratsa a nan ake gudanar da wannan sana’a. Akwai Hausawa da yawa a k’asar Hausa wad’anda ba su da wata sana’ar da ta wuce su. Shi ne cin su da shan su da kuma hanyar biyan sauran buk’atun rayuwarsu ta yau da kullum. Samun irin wad’annan sana’o’i ga Hausawa ya sa mutanen kowane sashe suka yi fice a kan abin dogaro. Har ma sukan nuna buwaya da isa da mallakar sana’ar a wajen wani dandali na musamman. Mak’asudin wannan nazari shi ne, zak’ulo irin waibuwar da masuntar k’asar Yauri kan nuna a wasu lokuta na musamman da kuma taimaka wa mutane da suke yi na samun waraka ga wasu matsalolin rayuwa na yau da kullum, domin nuna isa da buwaya da mallakar sana’ar. Wannan waibuwa da sukan nuna bai tsaya ga nishad’antar da jama’a kawai ba, yakan taimaka ainun wajen ceto rayukan jama’a daga wasu masifu da kan tuzgo a rayuwa kamar matsalar had’arin jirgi a ruwa ko lak’ewar k’aya a wuya da makamantansu da dama. Irin waibuwar da masunta kan nuna a wasu lokuta ya sa mawak’a da dama kan yi musu wak’a tare da nuna buwayarsu a kan ruwa da halittun da ke ciki. Ga abin da wani mawak’i mai suna Mansur Muhammadu Maidume ke cewa dangane da masunta:

Jagora :        Ni kuma sai ka ban k’uk’uwa in noce

In tai k’asan Teku in yi ziyara

Sarkin ruwa Makwashe Argungu

........................................................

Don na iske dattijo Matanfada

Duba kada ya fito shan iska

Ya gaida manyansa ya gaishe mu

Sarkin ruwa Makwashe dattijo.

 

2.0   Su Wane Ne Masunta


Calvin (1991) ya bayyana ma’anar su da cewa “ su ( kamun kifi ) wata farauta ce ta ruwa wadda ake yi domin a kama kifi da wasu halittun ruwa. Alhassan da wasu (1982) cewa suka yi “su sana’a ce da ake shiga ruwa da hannu biyu ko da taru ko da koma da mamari ko ma da fatsa, don a kama kifi don a ci ko don a sayar. Sana’ar su sana’a ce da ake gudanarwa a cikin koguna da gulabe da tekuna a duk fad’in duniya baki d’aya. Masunta kuwa mutane ne da sana’arsu ta danganci kamun kifi da sauran halittun ruwa. Masunta ba su da wata sana’a da ta wuce ta shiga ruwa, sai dai akan samu ‘yan k’alilan da sukan had’a da noma wanda bai taka kara ya karya ba. Galibi akan kira masuntar k’asar Hausa da suna sarkawa. Sarkanci kuma sunan sana’arsu ta kamun kifi. Dangane da asalin wannan sana’a a k’asar Hausa kuwa, wani ra’ayi ya nuna cewa, wasu mutane ne arna mabiya addinin Gundari wad’anda suka fito daga k’asar Firzan tare da Muhammadu Kanta. (P.G Harris 1942). Ya ci gaba da cewa, bayan da aka sauya hedikwatar Kabi daga Surame zuwa Birnin Kebbi, sai wani mutum da ake kira Magaji Alfa wanda ya fito daga k’asar Songai tare da jama’arsa ya shigo k’asar Kabi wad’anda su ne a yanzu ake kira “Sarkawa”, kuma mabiya addinin Islama ne. A nan suka ci gaba da rayuwarsu tare da arnan da suka iske a wurin suna kamun kifi ba tare da tilasta musu musulunta ba. Ra’ayin ya ci gaba da cewa, kalmar “Sarkawa” wadda ake kiran masu sana’ar da ita ta samo asali ne daga kalmar “Sorkos” wato sunan k’abilar da suka fito daga k’asar Songai suka zauna a k’asar Kabi, inda daga baya suka watsu a sassa daban-daban musamman a yankin arewa maso yammacin Nijeriya. Yau da gobe har kalmar ta koma Sarkawa a Hausance. Ra’ayin ya k’ara da cewa, wannan k’abila ta Sorkos su ne asalin Kabawa. Wato daga Sarkawa aka samu Kabawa.

Fitattun masuntar k’asar Yauri su ne Kabawa wad’anda suka fito daga k’asar Argungu suka zauna k’asar ta Yauri domin su ci gaba da sana’arsu ta gado (su). Sai kuma wasu k’ungiyar Hausawa da suka fito daga k’asar Taraba suka za’bi su zauna a k’asar ta Yauri, su ma don su ci gajiyar da ake iya samu a a wannan ruwa na kwara. Wad’annan Sarkawa ne ( kabawa da ‘yan Taraba ) suka shahara wajen kashin manyan dabbobin ruwa kamar su Dorina da Kada da Ayyu da makamantansu. Sauran sarkawan kuwa sun tak’aita ne kawai ga kamun kifi manya da k’ananansu.

3.0   Makaman Su (Kamun Kifi)


Kowace sana’ar Hausawa ta gargajiya akwai kayayyakin da ta tanada wad’anda take amfani da su domin samun sauk’in gudanar da sana’ar kamar yadda ya kamata. Haka ma sana’ar kamun kifi ba a bar ta a baya ba wajen tanadar makamai ko kayayyakin da ake amfani da su wajen kamun kifi. Daga cikin makaman da ake amfani da su wajen su a k’asar Yauri sun had’a da gwangu ko saran d’amba da dalan tcereke da k’awuri da taru da birgi da gura da d’ankara da mamari da k’ugiya da bilili da makamntansu. Kusan kowane daga cikin wad’annan makamai da nau’in kifin da ake kamawa da shi. Akwai wanda kowane nau’in kifi ya ci karo da shi yana kamawa. Akwai kuma  zago ko mashi wanda da shi ne ake kashe dorina ko kada da makamantansu.

3.0   Waibuwar Masunta

A k’amusun Hausa na Jami’ar Bayero da ke Kano, an bayyana ma’anar waibuwa da yin wani abu wanda ya shallake tunanin mutane. Waibuwa wata hanya ce da mutum ko wata halitta kan yi wani abu na ban mamaki kamar canzawa daga yanayin da aka san shi zuwa wani yanayi ko kuma ya ‘bace sam.(Argungu 2007). Ke nan waibuwa na nufin nuna buwaya ko siddabaru ko sihiri a kan wani abu ko wata sana’a domin nuna isa da mallakar wannan abin ko sana’ar. Galibi waibuwa aiki ne na sihiri wanda ake had’awa da iskoki domin su biya wa d’an Adam wata buk’ata, shi kuma ya rik’a yi musu wata hidimar da suka buk’ata. Masu gudanar da sana’o’in Hausawa na gargajiya musamman irin su mak’era da manoma da wanzamai da mahauta, sukan nuna buwayarsu a fagen sana’arsu a wajen wani taro kamar bukin nad’in sarautunsu ko makamancinsa. Su ma masunta ba a bar su a baya ba wajen nuna irin nasu waibuwar da ta shafi sana’arsu ta su. Ana iya kallon wannan waibuwar masunta ta fuskoki daban-daban dangane da yadda suke aiwatar da su.

‘Daure Ruwa Da Kwance Shi: Wannan ma na daga cikin manya-manyan waibuwar da masunta kan nuna. Galibi sarkin ruwa ya fi aiwatar da irin wannan waibuwa na d’aure ruwa da kwance shi musamman a lokacin bukin kamun kifi. Yadda wannan waibuwa ke gudana shi ne, idan za a yi wani bukin kamun kifi, sarkin ruwa kan taho ya yi wasu ‘yan surkulle na tsafe-tsafe da ‘yan siddabaru kafin a fara su a cikin ruwan da za a gudanar da bukin. Sukan yi haka ne domin a d’aure duk wani mugun dabban ruwa da suka san zai iya cutar da masunta da kuma samun sa’ar kama kifi. Don haka, idan ya yi wannan d’aurin ruwa, duk wani mugun dabba kamar dorina da kada ko wani mugun kifi ba zai motsa a wannan lokacin ba idan an ci karo da shi. Idan aka k’are buki sai sarkin ruwa ya kwance d’aurin da ya yi domin samun walwala ga halittun ruwan da aka d’aure. Su ma d’aid’aikun masunta suna da irin nasu waibuwa na d’aure ruwa idan za su fita su musamman ‘yan gora wad’anda ke lalabe a k’asan ruwa. Yadda nasu d’aurin ruwan yake shi ne, duk wani abu mai rai da suka ta’ba ba zai motsa ba balle ya cutar da su. Don haka, duk kifin da aka lalabo ba zai motsa ba sai an jefa shi cikin gora.

Kira : Idan aka ce kira ana nufin kamar a kira wani abu don ya zo a tattauna da shi ko a aike shi ko saboda wani dalili na musamman. Kira a sana’ar su yana daga cikin manya-manyan buwaya ko waibuwar da masunta kan nuna musamman idan rana ta ‘baci, ko wani halittan ruwa ya yi musu ba daidai ba. A nan, za a kira wata dabban ruwa ne ta fito da kanta daga cikin ruwa zuwa bakin ganga ta kwanta sai yadda aka ga dama aka yi da ta. An nuna misalin wannan ya ta’ba faruwa a wani k’auyen Yauri, inda wani kada ya kama d’an wani basarke a bakin kuwara. A nan ne mahaifin yaron ( basarke ) ya nuna irin nasu waibuwa na sarkawa, ya zo bakin kwaran ya yi sihirce-sihircensu na masunta. Daga nan ya fara kiran kadoji d’aya bayan d’aya suna fitowa daga cikin ruwa suna zuwa ganga suna kwantawa, har wanda ya kama d’ansa ya fito sai ya sa zago (mashin ruwa) ya soke shi, nan take shi ma kadan ya mutu.

Kirari : Kirari a nan yana nufin a wasa makami don ya shiga jikin dabba ba tare da an wahala ba. Wannan wata waibuwa ce da masunta kan nuna musamman a lokacin da suka zo kashe manyan dabbobin ruwa kamar su Kada ko Dorina. A lokacin da aka caka wa dabban zago ya d’an kama jikinsa ko yaya, daga nan za a fara yi wa zagon kirari yana shigewa jikin dabbar har sai zagon ya ci k’arfin dabbar sa’annan a koma gefe ana kallonta. Sai dai abin lura a nan shi ne, kirarin da ake yi wa zagon ba kirari ne wanda aka saba da shi kamar wanda ake yi wa mutane ba. Kirari ne na surkulle wanda ba a iya fahimtar abin da ake fad’i kai tsaye.

Su (kamun kifi) A Bisa Fak’o : Wani waibuwa ne da masunta kan nuna musamman a lokacin wani k’asaitaccen buki kamar bukin nad’in sarkin ruwa ko sarkin gari gaba d’aya. Masunta za su sa homa ne a fak’o jama’a sun taru suna kallo, sai kawai a d’ago homan sai a gan shi cike da kifaye masu rai tamkar dai yadda ake yi a cikin ruwa. An nuna irin haka ya ta’ba faruwa a lokacin nad’in Sarkin Yauri Abduulahi.

Baduhun Ruwa : Baduhu wani magani ne da ake yi na tsafi ta fuskar amfani da tayin dabbobi, da kyanwar da ba ta bud’e ido ba, da suturar makaho ko makauniya.(Bunza 2006). Mai baduhu yakan ‘bace ga ganin mutane gaba d’aya, ko da ga shi ga su yana magana ana jin sa. Ba kowane masunci ke da baduhun ruwa ba, sai wad’anda suka shahara wajen kashin dorina ko kada ko ayyu da makamantansu. Baduhun ruwa baduhu ne da ake yi a lokacin da aka zo kashe wani mugun dabban ruwa. Sau da yawa idan aka zo kashe dorina ko bayan an daka mata zago, takan yunk’uro ta nufo mutum da nufin kashe shi, to a wannan lokacin ne baduhun ruwa yakan yi aiki ta hanyar ‘bacewa ga barin ganin dabban ruwan. Wato da ta yunk’uro ba za ta ga mutum ba sai dai ta yi ta haukarta har dafin zago ya kama ta ta gaji ta mik’a wuya.

Basanyi : Basanyi wani sihiri ne da ake yi na karya lagon abokin fad’a. ‘Yan dambe da ‘yan kokuwa da maharba da mayak’a su suka fi amfani da basanyi. Abin da basanyi ke yi shi ne, ya saka wa jikin abokin adawa sanyi, jikinsa ya yi la’asar, ya ji ba shi da sauran kuzari ga ga’b’bansa da tsokokinsa. Bahaushe ya yi imani da samuwar basanyi, kuma yana ganin da jinin d’an Adam da fitsarinsa ko kashinsa ake had’a shi. (Bunza 2006). Basanyin masunta ba ga mutane yake aiki ba, yana aiki ne a lokacin da masunci ya nuta cikin ruwa wajen lalaben kifi. Duk kifin da ya ta’ba ba zai motsa ba sai an jefa shi cikin gora sa’annan ya yi motsi. Haka ma duk wata dabban ruwa da aka ci karo da ita aka ta’ba ta cikin rashin sani ko ma ana sane, ba za ta motsa ba balle ta cutar da mutum.

Nuta : Nuta na nufin shiga cikin ruwa a noce k’asa ga barin ganin mutane. Sau da yawa masunta kan nuna wata waibuwa ta hanyar nuta cikin ruwa musamman idan mutum ya mutu a ciki. A irin wannan yanayi, sukan nuta cikin ruwa na k’imanin awa d’aya suna neman gawar mutum ba tare da sun taso sun nunfasa ba. A wasu lokuta har gasa ma akan yi na nuta a lokacin wasanni domin a ga wanda zai fi dad’ewa idan aka yi nuta.

Gyandi/Gindi : Gyandi kalma ce da ke nufin wasu maganganu da masunta ke yi suna sassark’a su, suna kuma sauka d’aya bayan d’aya cikin sauri, sai dai babu wata ma’ana da mai sauraro zai iya kamawa balle ya k’arar. Gyandi tamkar surkulle ne wajen k’umshiya da yadda ake sarrafa shi, sai dai yana iya kasancewa a bayyane ko a asirce. Masunta sukan sarrafa gyandi gwargwadon irin waibuwar da suke son nunawa. Ga dai yadda suke sarrafa shi kamar haka :

Idan k’aya ta mak’ale wa mutum a wuya aka yi juyin duniya ta k’i wucewa, da zaran suka yi gyandi a ruwa aka ba mutum ya sha sai dai wata k’ayar ba wannan ba. Wannan ya faru ga wata mata da k’aya ta kama ta a wuya har aka tafi asibiti amma abin ya faskara. Da aka kai ta wani k’auye da ake kira “Bunzawa” wajen wani masunci ya yi gyandi a ruwa ya ba ta ta sha, kafin ka ce kwabo ba k’aya ba labarinta.

Haka ma wasu masunta suna ik’irarin cewa, idan mutum ya mutu a ruwa matuk’ar bai yi amai a ciki ba, ko shakka babu rayuwarsa za ta dawo idan aka yi masa gyandi. Wannan ma ya sha faruwa ba sau d’aya ba. Haka kuma za a iya d’ebo ruwa a kwanu ko a wani abu a tofa gyandi a ciki, sai a rufe da k’yalle. Da zaran aka bud’e za a ga kifaye masu rai da lafiya suna yawo a ciki.

Akwai wani gyandi da ake yi domin a hana mutum shan ruwa, ko a hana shi had’iye yawu. Wannan yakan faru ne idan ana wasannin raha tsakanin masunta da mahauta. A duk lokacin da mutum ya d’auko ruwa zai sha sai kawai ya ga k’ananan kifaye na yawo a ciki, tilas ya fasa shan ruwan.

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/hoton-tsafin-maguzawa-cikin-littafin-karshen-alewa-kasa/

6.0    Kammalawa


Ba da gaskiya da bugun gaba da Hausawa suka yi wa sana’o’insu na gargajiya, shi ya haifar da matsayi da k’imar da suke da shi a idon mak’wabtansu na gida da ma sauran k’asashe na duniya. Wannan ne kuma ya ba su damar shiga da fita wajen ganin sun mallaki sana’o’in nasu ciki da wajensa. K’ok’arin yin hakan ne ya haifar da waibuwoyin da sukan nuna a lokuta daban-daban. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kusan mafi yawan abubuwan da aka bayyana a wannan nazari baya na waibuwa sun gushe ainun a sakamakon tasirin addinin musulunci a rayuwar masuntar.‘Yan k’alilan ne daga cikin ire-iren wad’annan waibuwa suka saura da rayuwa musamman wad’anda ke da alfanu ga jama’a, kamar gyandin da ake yi idan k’ayar kifi ta kama mutum da ire-irensu. Duk da yake cewa wani lokaci masuntan kan tayar da tuba idan rana ta ‘baci, ko wani ya ta’ba su, kamar dai yadda ya faru ga masuncin da kada ya kama d’ansa

                                                 MANAZARTA


Argungu,  I. A. ( 2007 )  “Samuwar wak’a da kirari  a cikin bikin  kamun  kifi  na

Argungu”.  Kundin digiri   na  biyu,  Jami’ar   Usmanu   ‘Danfodiyo,

Sakkwato.

Bawa, I. ( 2004 )  “Dabarun  Kamun  Kifi A K’asar  Argungu”. Kundin  digiri na

d’aya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (2006 ) Gadon Fed’e Al’ada. Tiwal Nigeria Limited  Surulere

Garba, C. Y. ( 1991 ) Sana’o’in Gargajiya A k’asar Hausa. Baraka press  limited,

Kaduna.

Harris, P. G. (1930) “Notes On Yauri” (Sokoto Province, Nigeria). The  Journal 

                   of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland

                   volume XL.

Harris  P.G.  (1942)  “The   Kebbi Fishermen”  (Sokoto Province, Nigeria).  The

Journal of the Royal Anthropological  Institute of  Great Britain and

Ireland. Voloume 72.

Jelani A.    (2005 )  The   Socio-economic   Development  Of   Fishing  In  Yauri

Emirates. Kundin   digiri na  d’aya,  sashen   nazarin  tarihi,   Jami’ar

‘Danfodiyo, Sakkwato.

K’ofar Soro, S. S. (2007)  “Dabbobin Ruwa A Idon Bahaushe”. Kundin  digiri na

d’aya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Madabo, M. H. ( 1979) Ciniki da Sana’o’i a K’asar Hausa. Printed in Great

Braitain Thorbay press limited Rayleigh Essex.

Sanda, U. M. ( 1999 )  “Sana’ar  Su  A Madatsar Ruwa Ta Kanji”. Kundin digiri

na d’aya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Yahaya,  I. Y. (1992) Darussan  Hausa Don  Makarantun  Sakandare. University

press Ibadan.

Zantawa da Alhaji Usman,  unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan Fabrairu, shekara ta dubu biyu da goma (2010).

Zantawa da Alhaji Ibrahim, unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan Fabrairu, shekara ta dubu biyu da goma (2010).

Zantawa da Ataka-sisi da abokansa a k’auyen Bunzawa na garin Yauri, a watan       Fabrairu, shekara ta dubu biyu da goma (2010).

Zantawa da malam Umaru mai geme, unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan Fabrairu, shekara ta dubu biyu da goma (2010).
www.amsoshi.com

Post a Comment

2 Comments

Post your comment or ask a question.