Ticker

6/recent/ticker-posts

Usama Bn Laden: Gwarzo ko Ɗan Yaƙi? Laluɓen Ma’aunin Gwarzo a Hangen Makaɗan Hausa

Takardar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato, Juli, 2011
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato

Tsakure:


Mak’asudin wannan bincike shi ne, tantance yadda Bahaushe ke kallon jaruntaka da yadda Bature ke fassara ta’addanci. Takardar ta yi garkuwa da Usama bn Laden ta fuskar yadda duniyar Turai ke kallonsa. An yi k’ok’arin d’ora gutsattsarin maganganun Turai kan Usama ta fuskar zarginsa, da farautarsa, da cewa da suka yi, sun kashe shi, a ma’aunin awon jaruntaka a Bahaushen hankali. Na yi k’ok’arin la’bewa ga zantukan mawak’an baka domin su mutane suka fi sauraro, kuma su maganganunsu suka fi naso a zuciyar Bahaushe. Don haka, na gayyato mawak’a fitattu shahararru goma sha d’aya su raka ni a fahinta. An tsinto d’iyan wak’a ashirin da hud’u daga cikin wak’ok’insu domin yi wa bayanai nagartaccen turke. An za’bo mawak’an daga rukunin mawak’an sarauta da mawak’an maza da mawak’an sana’a da fand’ararun mawak’a (makad’an sata). An share fagen nazari da gabatar da ma’aunin gwarzo a al’adar Bahaushe ta fuskar gabatar da sunaye ashirin da Bahaushe kan kira gwarzo/jarumi da su. Daga nan aka gabatar da makaman tantance gwarzo irin su suna (fice), da kar’bar taron dangi, da rashin tsoro da rashin raki da wuce gudu. An kakka’be wannan bincike da fito da burin kowane gwazo a rayuwarsa cikin gwagwarmayarsa. Hak’ik’a, akwai buk’atar shugabannin duniya su san, kasancewar duniya gida d’aya a kimiyyance, ba shi ne kasancewarta gida d’aya ba a fahinta. Yadda yatsun d’an Adam suke, haka fahintocinsu suke. Yadda rana da wata ke sa’ba wa juna, tunanin ‘yan Adam da hasashensu ya zarce haka. Idan haka ne, ina laifin fad’an da ya fi k’arfinka ka mai da shi wasa?

Madalla da Makad’a ‘Dan’anace da ke cewa:

Jagora: Waye idonka Audun wawa,

: Ba kai d’ai an ka fara wa sababi,

: Ko ka yi dariya ba komai.

 Gabatarwa:

Hausawa kan ce, lokacin abu a yi shi. Rashin gwama darusanmu da abubuwan da ke aukuwa a duniya zamaninmu wani cikas ne ga basirarmu da ci gabanmu. Abubuwan da ke aukuwa a duniyar zamaninmu sun shafi kowane irin darasi da muke koyarwa domin daidaita akalar bincike da karatu. Domin samun makamar sanin rayuwarmu ya sa k’asashen Turai suka bud’e kafafen yad’a labarai irin su BBC, VOA, Jamus, da dai sauransu. Ko kusa, bai kamata a bar mu a baya ba wajen auna nauyin abubuwan da ke aukuwa a zamaninmu da darusan da muke koyarwa na harshenmu. Idan muka tashi tsaye, muka yi wa abubuwa susa gurbin k’aik’ai darusanmu za su gwada tsawo da kowane irin darasi da ake koyarwa a jami’o’in duniyarmu. Mak’asudin wannan rubutu shi ne, auna nauyin gwarzo da d’an ta’adda a Bahaushen sikeli ta bakin masana harshe (mawak’a). Na za’bi yin haka domin abokaina d’alibai su san, kowa da buk’in zuciyarsa mak’wabcin mai akuya ya sai kura. Don haka, kowane mutum na da ‘yancin kallon abubuwa ta fuskar al’adarsa.

Tak’aitaccen Tarihin Usama Bn Laden:


An haifi Usama bn Laden a Jedda, Saudi Arebiya ranar Lahadi, 1 ga watan Mayu, 1957, a babban gida na daraja da arziki. Mahaifinsa fitaccen tajiri ne, sanannen d’an kasuwa, amintaccen d’an k’asa. Usama shi ne d’a na goma sha bakwai ga Laden mahaifinsa. Usama ya yi ilmin addinin Musulunci sosai ya kuma karance boko farin karatu a fannin fasahar zayyanar muhalli. Mutum ne mai kamun kai da kawarci da kishin addininsa matuk’a. Yana da mata uku da ‘ya’ya fiye da ashirin. Gidansu sun mallaki tsabar kud’i na jari fiye da dala miliyan d’ari hud’u ($400million).

Kasancewarsa wayayyen d’an kishin addini ya yi huld’a da k’asashen duniya da yawa kamar Sudan da Misra da Afgan da Syriya da UK da France da makamantansu. Ya fara huld’a da k’asashen Turai a shekarar 1979. Ya had’a k’arfi da Amurka (US) aka gargad’i sojojin Rasha aka yak’e su suka fita daga mamayar da suka yi wa Afganistan. Da ya ci nasarar haka, ya kafa cibiyarsa ta jihadin kare addinin Allah da masu yin sa a shekarar 1988. Da dakarun Rasha suka mik’a wuya bori ya hau a shekarar 1989, ya koma Makka da zama. Daga Makka ya sake fita zuwa Syria a shekarar 1990. Da Gwanatin Saudiyya ta gayyato sojojin Amurka a k’asarta, sai Usama ya yi hijira zuwa wata k’asa. A shekarar 1994 Gwamnatin Saudiyya ta soke sunansa daga cikin ‘yan k’asarta. Daga nan ya koma Sudan da yammacin Misra (Masar) yana kai da kawo.

A rahotannin Gwamnaitn Amurka, Usama ya fara yak’ar k’asarta da masoyanta da masu jin tsoronta a shekarar 1995. Daga wannan shekarar Gwamnatin Amurka ke ganin cewa, lallai Usama ne ya yi tsare-tsaren ta’addancin:

  1. i) Hari a ofishin jakadancinta a shekarar 1996.

  2. ii) Harin da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka a Kenya a 1998.


iii)     Harin da aka kai wa jirgin yak’in ruwan Amurka a Tanzaniya 1998.

  1. iv) Harin da aka kai wa Yemen, 2000.


Tabbas, Usama ya fito ya gaya wa duniya cewa, wad’annan aika-aikar duk ba ya da hannu a ciki. Duk da haka, Amurka ta ba da tukuicin dala miliyan biyar ($5 million) 1999 ga duk wanda ya kawo mata shi. Bayan shekara biyu, 11 ga Satumba, 2006 aka kai mummunan hari a Cibiyar Kasuwancin Duniya da ke Amurka, Usama ya zama wanda ake tuma na farko. Don haka, aka sake ba da ladar dalar Amurka miliyan ashirin da biyar ga wanda duk ya kawo shi a raye ko a mace. Da kyautar ta kasa ciyuwa a shekarar 2011, shugaban k’asar Amurka Obama ya yi sanarwa sun kashe shi a k’asar Pakistan.

Idan har a Pakistan aka kashe shi a shekarar 2011, ya mutu yana d’an shekara hamsin da hud’u (54) a duniya. Idan kuwa hirar da aka yi da shugaban k’asar Pakistan Musharraf a shekarar (wajajen 2005) a CNN da BBC ta tabbata, Usama ya yi shekara shida da rasuwa a yau 2011, domin ya ce cutar k’oda ta kashe shi a shekarar 2005. Idan kuwa sakamakon muhawarar majalisar Amurka za a d’auka, ba a kashe Usama ba, har yanzu tana k’asa tana dabo. A ra’ayin masu fashin bak’in al’amurran yau da gobe na duniyar zamaninmu, suna ganin sanarwar kashe Usama da Obama ya yi, wani majigi ne aka shirya na yaudarar ‘yan kallo da ya ci nasarar sace hankalin masu ganin Amurka na iya komai, ga su nan dai.

Ma’aunin Gwarzo A Hausance:


Awon gwarzo a idon Bahaushe ya k’unshi abubuwa biyu: na farko shi kansa gwarzon da aka son tabbatar da gwarzantakarsa, na biyu abubuwan da ya yi da suka tabbatar da zamansa gwarzo. A ma’aunin Bahaushe, ba dole sai gwarzo ya zama jibgegen k’aton ba, domin sanin ba girma ba dominsa ba azaba. Haka kuma, ba dole sai gwarzo ko jarumi ya buwayi kowa duniya ba, domin makashi maza, maza ke kashe shi. A ganin Bahaushe abubuwan da gwarzo ya aikata za a bi diddiginsu a tabbatar da, ba su sa’ba wa daidaitacciyar al’adar rayuwar Bahaushe ba. Idan mutum ya ci nasarar hawan wad’annan matakai na Bahaushe, za a iya d’ora shi a kan kalmomin yabo na nuna tabbacin kasancewarsa gwarzo/jarumi.

Idan sunan mutum ya gota na tsaran zamaninsa. Ya rinjayi na abokan gwagwarmayarsa. Ya gagari na abokan adawa. A al’ada ko da bai fito ya yi kirari ba, za a ji ana yi masa kirari ko ana yabonsa da kalmomi irin su: Namiji, Jarumi, Gwarzo, d’a, Sadauki, Dakare, Kasko, Katakore, Wandara, Zaki, Giwa, Barde, Gak’i, ‘Baleri, Buwaye, Gagara Kundila, Gagara badau, Giye, Makaye, Jigji, wad’annan kalmomi ashirin da aka za’bo ba su kad’ai Bahaushe ke yi wa gwarzo/jarumi kari da su ba, na kawo su a matsayin misali kawai. A ganin masana al’adar Bahaushe, abubuwan da Turai ke danganta wa ga Usama Bn Laden maimaikon su ci fuskarsa da mutuncinsa, sai su dad’a k’ara masa lamba ga idon wasu al’ummomi na duniya musamman Afirka.

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/littafin-ruwan-bagaja-maaunin-matakan-rayuwar-bahaushe/

Usama Bn Laden Da Ta’addanci:


Laluben tushen kalmar ta’adda a harshen Hausa wani abin so ne ga irin wannan nazari. Wasu masana na hasashen tushenta daga Larabci ne, watau, “ta’ad” wanda nassoshin Alk’ur’ani da Hadisai da dama suka ambata. Wasu masana na ganin, tun kafin a haifi uwar mai sabulu belbela tana da farinta. Don haka, kalmar “ta’adda” Bahausa ce kai tsaye, tushen ta daga “ta Adda” ne, wani Bafadan Sarkin Kano. An ce, sunan Bafaden “Adda”. An sa ya kira wani talaka cikin hushi, ya tafi da gatari ya sassare shi, ya zo da gutsattsarinsa ya ce wa sarki, ga aikinka an cika. Tun daga wannan lokaci, idan za a tura wani bawan sarki aiki akan ce, kar ka yi irin, “ta Adda”, watau yadda Adda ya yi wa wancan talaka.

Idan aka rairaye wad’annan ma’anonin za a ga: A nassoshin shari’a ta’addanci na nufin, wuce gona da iri, zarce makad’i da rawa, shisshigi, k’etare haddi, wanzar da ‘banna da fasadi da bala’i da waba’i da hasara da rashi da ta’bewa mai haifar da salwantar rayuwa, da dukiya, da hana wa zaman lafiya da lumana gindin zama, da share wa k’addara da hasara fagen mik’e k’afafu. Irin wannan ma’anar ta yi canjaras da yadda Turai da duniya ‘yan boko ke kallon ta’addanci. A can da, mai irin wannan rayuwa shi ne d’an yak’i mai son a koyaushe ana fitina da fad’a da yak’i.

Wurin da gizo ke sak’a a nan shi ne, ma’anonin da Turai ke bai wa ta’addanci a yau haka yake, ko yana son gyaran fuska? Babu shakka, duk abin da zai ta da zaune tsaye, babu mai hankalin da zai yi na’am da shi. Duk da haka, ya kyautu a gano abin da ya sa na zaune ya tashi tsaye domin shi ne, Kafurkafur zakaran tsafi wanda ya fi kafiri kafirci. Makaftar da duniyar ‘yan boko ta yi ga zurfafa bincike a kan haka, shi ya sa fassararsu ta ta’addanci ta mamaye duniya aka wayi gari a yau aka yi, kamun kurar kurma, kura kuka, kurma kuka. Da wannan fassarar ta’addanci haka take a kan wad’anda ake kira ‘yan ta’adda a yau, da ba za a samu mai mara musu baya ba. Wa zai so mutuwa? Wa zai so ya kashe wani rai da gangan? Wa zai yi so hasara? Wa zai so rashin zaman lafiya? Wa zai so fitina da yak’i da hayaniya da hayagaga?

Kalmar “ta’addanci” ta yi kusan ta shige wa Bahaushe duhu domin ta tsufa k’warai har an yi kusan a manta da ita. Kalmomin hari, farmaki, alkafura da k’undumbala sun mamaye haskenka. Harin da aka kai wa Amurka da jiragen sama biyu a watan Satumba, 9/11 watau 11/9/2006. Amurka ta yanke hukuncin Usama bn Laden ne jagoran harin. Da haka aka zartar da hukuncin kisa a kansa da yak’ar duk wata k’asa mai zaman mutunci da shi. Bisa ga wannan zato Amurka ta dinga amfani da kalmar “ta’addanci” ga Usama da duk wani mai kama ko sifa ko ra’ayi irin na Usama ido rufe. Ba burina bitar harin da aka kai ba, domin masana sun yi rubuce-rubuce da yawa a kai. Burina a nan shi ne, yadda gargajiyar Bahaushe ke kallon yadda Amurka da Turai ke nuna Usama. Haka kuma, yadda Turai ke farfagandar fallasa Usama ya taimaka wajen jawo wa Usama farin jini da k’auna da so da yarda a zukatan ma’abota addini irin na Usama a bangon duniya. Idan a ganinsu Usama d’an ta’adda ne, a ganin wasu gwarzo ne, jarumi ne, sadauki ne, domin:

  1. Ba a bayyana wa duniya laifin da ya yi ba, yak’arsa kawai ake yi;

  2. An kasa a kama shi da hannu kamar yadda aka kama wasu shugabannin k’asashen duniya da aka yak’a;



  • Ya k’i ya mik’a wuya bale a yi masa tuannuti;



  1. An kasa gano wurin da yake, duk da barazanar cewa, duniya a hannunsu take;

  2. Bai rufe bakinsa ba tun ranar da aka fara yak’i da shi har ranar da aka ce, k’ila an kashe shi,

  3. Abubuwa da suka gudana lokacin da aka ce an kashe shi, sun k’ara sa wasu mutane yanke shawarar lallai dai gwarzo ne ba d’an ta’adda ba;



  • Cece-ku-ce da suka wakana bayan da aka ce an kashe shi sun k’ara sa mutane jin tsoron rahotannin da kafafen yad’a labarai na Turai ke bayarwa.


A kan wad’annan abubuwa bakwai na so in d’ora tunanin Turai da tunanin Bahaushe a kan matsayin Usama bn Laden a mahangar Bahaushe. Zan tak’aita bayanan a kan abubuwan da Turai suke fad’a a rubuce-rubucensu a kan Usama bn Laden.

Asali:

Bahaushe na ganin, asali wani babban abu ne a rayuwa. Mutumin da ba ya da asali nagari ba zai yi nagartaccen aiki ba. Mai asali nagari ana sa ran ya yi aiki nagari. A fad’ar Amurka Usama ya tashi wadataccen gida babba. Gidansu shahararrun masu kud’i ne ‘yan kasuwa ne da duniyar zamaninsu ta san da su. A wajen uwa da uba da kakani son kowa k’in wanda ya rasa. A ganin makad’a ‘Dan’anace tun a nan ake samun d’an k’warai wanda Hausawa ke ce wa “d’a”. Ga abin da ya ce:

Jagora:Mai son miya ya auri tsohuwa,

:Mai son shimfid’a ya auri budurwa

:Mai son d’an k’warai ya auri isassa.

Suna:

A al’ada Hausawa na cewa, suna linzami ne, wannan linzami idan mutane da yawa suka ja shi ya fi d’aukaka. Maimakon Amurka ta yi ta fama da yak’in sunk’uru har sai ta gano wad’anda suka yi mata ta’addanci, sai ta cire mutum d’aya, ta ce shi ne. Masu goyon bayanta da masu ra’ayinta da masu tsoronta suka mara mata baya. Cikin d’an lokaci kad’an sunan Usama ya fi na Amurka da dukkanin tarayyar Turai d’aukaka a duniya. Da ma Narambad’a na cewa:

 

 

Jagora: Da k’auye da birni,

: Na buk’atar ganin dokin ga,

: Da yay yi suna,

Yara  : Ga talitta komiy yi suna,

: Ana tilas shagalin ganinai,

Gindi: ‘Dan Mallam ci k’wallo sarkin gudu,

: Na yarda da d’an Hilinge.

 

Taron Dangi:

Yadda aka gudanar da farautar Usama da jama’arsa na taron dangin sojojin duniya abin lura ne ga Bahaushe. A k’a’idar Bahaushe, da Balarabe, a fagen daga an fi son a yi d’ai bayan d’ai, gudu guda domin a gane gwarzo, ai don haka ne ‘Dan’anace ke cewa Shago:

“‘Baleri ba guda da guda ba”.

 

A ganin Bahaushe, sai an yi gaba-da-gaba za a gano gwarzo. Don haka ne, Sani Aliyu ‘Dandawo ke cewa a wak’ar Hashimu:

Jagora: Harsashe makarinka a duka,

Yara: Amma ba gaba da gaba ba.

 

Idan aka yi wa mutum d’aya taron dangi, ko an ci nasara a kansa kirari kunya ne domin kashin bak’i sai taro. Idan ko har ya tsaya ya yi daga da su, ya zama gwarzo ko an so, ko ba a so ba, dubi yadda Narambad’a ke yabon sarkin Kwatarkwashi Alu da cewa:

Jagora: Ba shawagi sa maza yawon duniya,

Yara  : Suna sai da abin hwad’i ga ‘yan’uwa.

Gindi: Yai halin mazan jiya

: ‘Dan Sanda mai Kwatarkwashi.

 

A ma’aunin Bahaushe, gwarzo da dubu yake yak’i ba da mutum d’aya ba. Fitaccen gwazon nan Janborodo da sarkin Gwandu Halilu ya yi wa wak’a, Sambo Wali ya yi mata tahamisi cewa yake yi:

“Dubu kaka taryewa su kasa wurin zuwa,

Baka da baka doki da doki ka ta ruwa,

Ka kwana cikinsu gaba gak’i babu garkuwa”.

Idan gwarzo bai kai haka ba, yana da saura, ko da kuwa gwarzon sata ne, kamar yadda Gambo ke wasa Manu Dahin Gumbire cewa:

Jagora: Ko bataliyas soja,

: Tas shiga daji in gaya maka,

: Manu Dahi na d’an taya ta.

Artabo:

Ga alama, idan dakarai suka yi wa gwarzo taron dangi, ba makawa sai an gwabza. Sa’banin al’adar Turai da ta Bahaushe, da an yi wa mutum d’aya taron dangi an nuna ya buwaya. Idan haka ta auku, buri ya cika an yi ban kwana da duniya, an ce wa lahira, salamu alaikum. Idan abu ya kai gargare haka, suna ya d’aukaka, an hau buzun zama gwarzo, sai a yi hak’uri da wuya, a fuskanci maza gadan-gadan komi taka zama ta zama. Dubi yadda Narambad’a ke gaya wa sarki Ibrahimu:

Jagora: Rik’a da gaskiya Ibrahimu,

: Mai taimakon Allah na nan,

Yara  : Zan ka wa maza gurmani,

Gandi: Madogara na Mallam Iro

: Uban Yari mai gida Shinkafi.

 

Da an fara ba hamuta iska, batun sulhu da ban hak’uri ya k’are. Da dai Turai sun fahinci haka, da ba su yi tunanin fara yak’i ba. Da an fara yak’i an rufe k’ofofin tunanin tausayi da tausayawa. Haka kuma, kowane gwarzo so yake kowa ya d’ebo da zafi ya sa bakinsa irin yadda Narambad’a ke ce wa Sarki ‘Dankulodo na Marad’i:

Jagora: Gadan-gadan na Maid’aki

Yara  : Mai kwana wurin da yas so shi kwana.

Jagora: Awartaki rik’a ko da zahi

Yara: Sauran maza ka mai she su mata.

Gindi: Ciwon cikin maza ‘Dankulodo.

: Na Yari mai halin Tcagarana.

 

Babu wani jarumi da zai yarda ya je fagen yak’i ba da shirin mutuwa ba, domin ya san, d’ayan biyun ne, in a dawo, in a mutu can. Rinjayar da mutuwa ya sa Bahaushe ke gani, gwarzo shi ne wanda a fagen artabu an yi haihuwan guzuma d’a kwance uwa kwance. Idan aka yi kirarin bindigar ‘yan tauri, ke gawa, mai ke gawa, abin da an ka nuna gawa, gawa uku jere ga juna, to, abu ya yi. Madalla da Kassu Zurmi da ke ce wa Nomau Namagarya:

Jagora: Kyawon fad’a a yo accakwama,

: A kwa’ba ta bak’i k’irin

: Ta k’are muku can.

 

A fagen artabo, samun accakwama ba ta’addanci ba ne, a idon Bahaushe. Idan kuma tsuntsun da ya kirari ruwa, ruwa suka ci shi ba a yi ta’addanci ba a fannin yak’i. Rashin sanin haka ya sa Hausawa suka kasa fahinta Turai a kan yunk’urinsu na yak’i da ta’addanci cikin salon ta’addanci. Idan aka bari magabta suka had’a jiki, to, za a ga abu uku sun kau ga gwarzo da jarumi watau tsoro da raki da gudu.

Tsoro:

Gwarzo shi ake tsoro, shi ke ba da tsoro, shi ke sa raki, shi ke sa a ruga a guje. A halin da muka ciki, duk da ganin da Turai ke yi ta gama da tarihin Usama Bahaushe bai ganin haka, tsoron Usama na nan a k’irazansu har abada domin gwarzo ne. Tsoron da suke ji na Usama a ganin Bahaushe, shi ya ba Usama darajar zaman gwarzon wannan k’arni, kamar yadda Narambad’a ke gaya wa Sarkin Gobir Amadu cewa:

Jagora: Jikan Bubakar ba su tsoro,

Yara  : Wad’anga mazaizai na yau

: Babu mai imai,

Gindi: Amadun Bubakar gwarzon Yari,

: Dodo na Alkali.

 

Idan aka yi wa namiji taron dangi, ya k’i ya nuna razana ya cika namiji. A koyaushe, mai yi wa gwarzo kirai yana son ya d’ebe tsoron mutuwa da wahala a zuciyarsa (gwarzo). Dubi yadda Gambo ke kiran tauraronsa da cewa:

 

 

 

Gambo: Mi kaka shakka,

: Ga ni ga ka,

: ‘Dauri ka ka shakka ko kashewa?

 

Idan namiji ya kantare wuri d’aya, ya yanke shawarar ga abin da zai yi, to ba ja da baya bale neman shawara. A ko’ina gwarzo yake, idan ya tsai da k’afarsa wuri d’aya, sai dai a mutu. Narambad’a ya ba mu wannan fatawar da yake cewa:

Jagora: Dus sarkin da kas sani,

: Basaraken da kas sani,

: Amadu ya hi shi k’ane shiryayye,

: Babu batun banza.

Yara: Kuma babu sakewa,

: Kuma in yai tsaye,

: Ba mai kausai”.

Gindi: Na rik’a ka da girma,

: Audu k’anen mai daga,

: Kan da mu san kowa,

: Kai mun ka sani Sardauna.

Raki:

Hausawa na cewa, kowa ya ce, ya ce sai ya ce, bai ce ba. To, fad’ar ba a ce ba, shi ne raki. Namiji ko an fi shi gaskiya a fagen artabo, tsaye yake yi ya kare ‘yar gaskiyarsa, ba da razana ba, bale raki ko a doka ya kauce, ko ya zuk’e, ko ya kasa rama duka. A kid’in sata Gambo ya fito da wannan hasashen lokacin da aka koro Bawa Makau garin Gumi ana jifa da duka Gambo ya ce:

Gambo: Ko kan da akai,

: Mugun mijin k’asa,

: Ya kashe kanu sun yi maitan.

 

Haka ma, a cikin wak’ar Hantsi Hore (‘barawon damma) da aka zuga shi ya je ya sato hatsin mutane aka koro shi, ga abin da makad’a yake cewa:

Gambo: Hancti shi jefa,

: Su su jefe shi

:Har aka zo hilin kid’inmu.

Mak’asudinmu a nan shi ne, gwarzo ba ya mik’a wuya kamar akuya. Tattare da taron dangin da Turai suka yi wa Usama, ya k’i ya ba da kai bori ya hau wanda a ganin Bahaushe haka gwarzo ya kamata ya yi, komi taka zama ta zama. Da ba a yi tunanin yi masa taron dangi ba, da za a ci nasara idan aka fuskanci Bahaushe da bayanin Usama a matsayin d’an ta’adda. Ga al’ada ko akuya aka matsawa tana cizo. Idan tura ta kai bango babu wane na san wane. Rashin tsayawa a kula da ire-iren wad’annan shi ya sa har yanzu Amurka ba ta gamsar da Bahaushe ba a kan bayanin Usama.

Gudu:

Hak’ik’a, a bayanan Bush na farkon a yak’in ya nuna, Usama ya gudu, ya tsere, ya ‘boye. A maganar al’ada gudun abin kunya ne ga gwarzo. Abin lura a nan shi ne, idan gwarzo ya yi gaba da gaba da abin da yake tunkara, nan ne gudu yake akan kunya gare shi a al’adance. Yak’i a abokan yak’i sun fi duba, a ko’ina gwarzo ya garzaya ba guda ya yi ba, farmaki ya je kai. Da, da mutum d’aya suke fad’a, kamar dambe ko kokuwa, to nan kam gudu ya zama kunya. Alhaji Muhammadu Narayau (makad’in Dambe) a wak’ar wani tauraronsa Almu yana cewa:

Jagora: Kai dai ban da gudu,

: Ko na gangara gebe na,

Yara : Ko da mutuwa za ta zo ta kwasa.

Gindi: Ya sa maza le’bewa

: Almu ‘yan maza ka tsoro.

 

Ranar Wanka Ba A ‘Boyon Cibi:


Abin da ya ba ni sha’awar rubuta wannan takarda shi ne, karatun rahoton kashe Usama da Amurka da Pakistan suka wallafa a intanet. Daga cikin abubuwan da suka fad’a sun had’a da cewa:

  1. Sun tarar da Usama cikin gida da iyalansa

  2. Da aka kai masa farmaki, ya k’i ya mik’a wuya.



  • Matarsa ta k’i ba da had’in kai, aka harbe ta ga k’afa.



  1. Sojojin Amurka da na Pakistan suka kai harin a gidansa na Islamabad.

  2. An harbe shi ga kai, wajen idonsa ta dama, aka kashe shi.

  3. Sun isa gidansa da k’anana jirage sama uku, d’aya ya lalace aka yi amfani da biyu.



  • An k’i a nuna gawarsa, saboda irin munin kisar da aka yi masa na iya haifar da wata sabuwar fitina.

  • Ya k’i aminta da ya yi saranda ya mik’a wuya (kamar akuya), shi ya sa aka kashe shi.



  1. An saka gawarsa teku bayan an yi masa salla.

  2. An kama iyalansa, ana ci gaba da bincike.


Wad’annan abubuwa goma su suka fi shahara a kan bayanan kisan Usama. Ga mai hankalin nazari, akwai abubuwan cewa da yawa a ciki, da yake ba su suka dame mu ba, za mu mayar da hankali a kan zuciyar takardarmu. Rahotannin da Amurka ta bayar kan kisan Usama a ganin Bahaushe kamar kirari ne ta ke yi wa Usama na zamansa barde ba kushe shi take yi ba. Da ya yarda aka yi sulhu ko ya mik’a wuya kai tsaye Bahaushe na hangen wata kasawa a ciki.

Ga al’adar Bahaushe, kyawon gwarzo ya mutu ga hannun gwaraje irinsa don haka ne yake cewa, mutuwa kashe mutane ki mutu. Dan’anace ya warware wannan matsalar a wak’ar Shago da yake cewa:

Jagora: Ta fi a kashe ka gaba d’ai,

: Wandara mi kakai da rai ga arna,

: Ai ko an kashe ka ban ji haushi,

: Don ‘bannar da kay yi ta aka gyara,

: In ko ka kashe su ka yi gaba d’ai.

 

Fatar kowane gwarzo ya mutu a kan abin da ya yarda da shi. Idan da so ne samu a kai shi cikin kushewa da kayan fad’ansa. Mutuwar Usama a fagen daga ba abin kushewa ba ne a wajen Bahaushe, ai ‘Dan’anace ce wa Shago ya yi, da dai ya ja da baya ga mazajen fama a fage.

Jagora: Gara ka je lahira,

: Kana da nad’ad’d’en hannu,

: Ko can a samu abokin fama.

 

Rahoton Amurka ya nuna an yi musayar wuta ta ‘yan mintoci kamar arba’in, sabanin na Pakistan da ya ce, an yi awowi ana luguden aradu. A ma’aunin Bahaushe ko da minti d’aya aka yi ana ‘barin wuta namiji ya yi namiji.

Buri Ya Cika:

Ga abinda Amurka ta nuna Usama d’an ra’ayin rik’au ne na addinin Islama. Ita kuwa Amurka ‘yar ra’ayin rik’au ce ta damokrad’iyyar da ke takin sak’a da manufar Usama. A al’adance, d’an Adam na son ya mutu a kan ak’idarsa ko da an rinjaye shi. Da dai Amurka ta samu sa’ar jawo ra’ayin Usama ya fahince ta, a ci gaba da tafiya tare, kamar yadda suke a da, da za a ce, ta ci nasara. Yanzu da yake an yi kare jini biri jini, ta ci nasarar rik’e ak’idarta, shi ko ya ci nasarar mutuwa da ak’idarsa. A ganin Bahaushe, a ci gwarzo da yak’i a kama shi, shi ne kasawa, ba a kashe shi ba. Domin makad’a ‘Dan’anace ya ce:

Jagora: Yak’i ya ci annabawa Shago,

: Balle ‘baleri mai nad’e hannu”.

Gindi: Kai maza suka sauna,

: Kiro mak’i gudu mai ban haushi.

 

Makad’a ‘Dankwairo ya k’ara wa takwaransa k’arfin guiwa da cewa:

 

Jagora: Da wulak’anci gara shahada,

: Ga Musulmi ba illa ne ba,

Gindi: Ya wuce raini ba a yi mai shi,

: Amadu jikan Bello Sadauki.

 

Wannan d’an wak’ar ya ci canjaras da wak’ar Gatarin ‘Dagutu a wani baiti da yake cewa:

“Shahada muke buk’ata,

Ba dogon rai ga wanga tsari ba.”

An ce, a tarihin k’asar Hausa an samu mazaje masu irin ra’ayin Usama a fagen yak’i. A shekarar 1906 da Turawan taron dangi suka ci birnin Satiru ta k’asar ‘Dancad’i Lardin Sakkwato da yak’i mazajen Satirawa sun k’i mik’a wuya a kama su kamar akuya, sun za’bi shahada, Allah Ya yi wasu. Da turnuk’un yak’i ya kai ya kawo, ga abin da turayen yak’insu ke cewa:

Taro: Marafa ya dad’e bai zaka ba,

: Waziri ya dad’e bai zaka ba,

:Balle Nasara mai d’an wando,

:Babban mutum da wandon yara,

: Ku sa kid’i mazaizai mu gani,

: Ko can gida fad’a mun ka sani,

: Ba mu san gudu ba sai dai a mutu.

 

Bukatar kowane gwarzo shi ne, in an d’ebi na gashi ya d’ebi na dahuwa, don haka, duk da yake an k’ona garin Satiru mai kimanin mutane dubu goma (10,000) su kuwa sun kashe sojojin Biritaniya tare da jagoran rundunar sojan Major M.G. Hillary don haka suke cewa:

“: Ko an kashe mu babu hasara,

: Ko yanzu mun kashe Hilleri”.

 

K’arshen wasan dai shi ne,+ burin kowa ya cika. Burin Amurka na dasa manufofinta a k’asashen da ta ke da jin tsoron ak’idojinsu ya cika, burin Usama na samun shahada ya cika. K’arshen Turai a cikin sak’onninsu na taya Obama murna suna nuna masa, yanzu yak’i yake, ba a ce komai ba, an rak’i bak’o ya dawo. Tabbas, da gaskiyarsu, domin makad’a ‘Dan’anace cewa ya yi:

Jagora: Bari murna karenka na kashe kura,

: Wata rana ka tsinci bindi hanya.

 

Don haka, har yanzu sai an koma ga tunanin nan na Bahaushe a shafe jini a koma wasa. Dole sai an nemi wata hanyar zaman lafiya a duniya ba ta yak’i ba. Babu yak’in da zai iya k’are duniya, kuma ba ta fuskar yak’i kawai ake tabbatar da ak’idojin wasu mutane a kan wasu ba.

 

Sakamakon Nazari:


Ya kyautu a ce, majalisar ‘Dinkin Duniya ta fito da wasu nagartattun hanyoyi na sasantawa tsakanin k’asashe ba ta k’arfin soja ba. Amfani da k’arfin soje, bai ta’ba kashe wuta sai dad’a turara ta a zukatan wad’anda ke ganin an ci da hak’k’insu. Haka kuma, tilas, a daina harin bisa kan mai uwa da wabi wajen kwantar da tarzoma da zanga-zanga da tawaye. Bugun gaban da UN ke yi da Amurka shi ke harzuk’a wasu gwaraje su jarraba sa’arsu, in til, in kwal rinin mahaukaciya. Yin hukunci cikin duhu, da zartar da shi lullu’be, wata hanya ce ta haifar da ta’addanci a duniyarmu ta yau.

Irin fafatawar da gwamnatoci biyu na Amurka Bush da Obama suka yi da Usama ta k’ara d’aukaka shi bisa ga d’aukakar da yake da ita a idon Musulman duniya. Maganar kashe shi kuwa wata sabuwar lamba ce aka k’ara danna masa duk da kasancewar ba a yarda sun kashe ba. A tak’aice, wannan fafitikar ta nuna da wuya mutum ya yi kirari da bugun gaba ya ci nasara ga abin da ya sa gaba.

Nad’ewa:


Muradin wannan takarda shi ne, jawo hankali masu mulki cewa, duk abin da aka gaya wa mutane yadda yake, suna da damar kallon abin gwargwadon hankalinsu. Ba dole ba ne a ce, fassarar da mai ba da labari zai yi, ita ce wadda mai saurarensa zai yi ba. Haka kuma, al’adun mutanen duniya sun sha bamban. Yadda Bature zai hangi nasara da buwaya da jaruntaka da k’wazo, ba haka Bahaushe zai hange su ba. Wannan ishara ne ga ma’aikatan jaridun duniya domin su tabbata sun k’oshi da al’adun harsuna biyu da suke fassara labarai. A ganin Bahaushe, gwarzo ko jarumi shi ne, wanda ya yi tsayin daka ga fahintarsa ko da za a ta jawo masa hasarar rayuwarsa. A Hausance, Usama gwarzo ne da ya mutu da ‘yancinsa. A ak’idar Larabawa cewa suka yi:

Man lam yamut bis saifi maata bi gairi hi,

Tanawwa’atil asbaabu wal mautu waahidun.

Manazarta:


 

Ali, M.A. (2010) “Effect of War on Terror by the West on Islam and

Muslims” (Sick) Being a draft of M.A Dissertation Submitted to the Department of Islamic Studies, FAIS, UDU Sokoto.

 

Ali, T. (2002) The Clash of Fundamentalism: Crusades, Jiahd and

Modernity, Verso, London.

 

Awake, (1987) The New Look of Terrorism, Watch Tower, Lagos.

 

Bunza, A.M. (2006) Gadon Fed’e Al’ada, TIWAL Nigeria Ltd, Lagos,

Nigeria.

 

Bunza, A.M., Ibrahim, S.S. Usman B.B. (2007) Daular Sakkwato,

(Fassarar Sokoto Caliphate na Murray Last). Ibrash, Lagos, Nigeria.

 

Bunza, A.M. (2009) Narambad’a, Ibrash. Lagos-Nigeria.

 

Gunaratna, R. (2002) Inside Al-Qa’eda, Berkley Books, New York.

 

Revero, M. (2002) Fake Terror: The Road to Dictorship.
www.amsoshi.com

 

Post a Comment

0 Comments