USMAN ADAM ROGO


 

https://www.amsoshi.com/2017/10/30/nazarin-littafin-kibiya-ratsa-maza-na-abdulaziz-sani-madakin-gini/

Gabatarwa


Wannan bai kammala har sai an yi dogon waiwaye a kan kafuwa da kuma yad’uwar addinin musulunci a duniya da kuma kafuwar jami’o’i na “Cardo’ba da Alk’ari’a” tun lokacin mulkin Abasit.

Musulunci ya fara zuwa Afirika tun zamanin Annabin Rahama lokacin da ya turo tawagan farko ta musulmi masu gudun hijira daga Makka zuwa Habasha a k’ark’ashin jagorancin Ja’afar Ibn Abu-Talib.

Don haka, wannan littafi mai suna “Jarumin Jarumai” yana d’auke da shafi saba’in da biyu (72) wanda a cikin sane za a ga yadda ake aiwatar da dabaru iri-iri. Kuma yana d’auke da taurari kashi-kashi kusan guda bakwai ko takwas. An kuma yi amfani da dabbobi irin su:

 • Dawaki – kamar Doki Sarkas

 • Garuruwa – birnin Jehur, birnin Teheren


Wato dai littafi ne mai d’auke da tashin-tashina na Abdul’aziz Sani Madakin Gini. Sannan kuma labari ne mai d’auke da “jigin jayayya”. Wannan littafi na jarumin jarumai yana d’aya daga cikin irin littafan da ya wallafa.

https://www.amsoshi.com/2017/10/20/mene-ne-bori-fashin-bakin-maanarsa-cikin-taskar-harshe-adabi-da-alada/

Ma’anar Jigo


Jigo na nufin sak’o ko manufa ko bayani ko ruhin da littafi ya k’unsa wanda kuma shi ne abin da littafin ke son isarwa ga mai saurare ko karatu ko nazarinsa.

Misali: kamar a cikin wannan littafi na “Jarumin Jarumai” yana d’auke da “jigon tashin hankali” . dalili kuwa shi ne, ana gaba ne tsakanin masarauta biyu.

Ma’anar salo


Salo hanyace da ake bi a isar da sak’on littafi ko kuma a wani k’auli shi ne dabarun jawo hankali da sarrafa littattafai a cikin littafi.

Don haka, amfani da Hausa mai kyan armashi ta hanyar za’ben kalmomi da jumloli ingantattu kansa a yi kwad’ayi a yi karatun littafi tare da fahimtar jigo cikin sauk’i. A wanna littafi na Jarumin Jarumai an yi amfani da wad’annan salailai kamar:

 • Aron kalmomi

 • Karin magana

 • Zance cikin zance

 • Labari cikin labari

 • Hikima da harshe


Wad’annan salailai na daga cikin abubuwan da suka sa littafin ya yi kwarjini da farin jini.

Misali:

 • A shafi na bakwai (7) akwa inda aka yi “aron kalma” da ambaton “al’ajabi”.


Ga abin da labarin ya ce har aka samu wannan kalma:

“Shi kansa gashin k’irjin dokin wani iri ne na musamman mai ban al’ajabi da ban sha’awa.

 • A shafi na arba’in da bakwai (47) akwa inda aka samu “karin magana” da cewa – mai laya ya kiyayi mai zamani.


Ga abin da labarin ya ce har aka samu wannan karin magana,

“Ya kai abba na hak’ik’a na yarda da duk abin da ka fad’a amma ka sani cewa masu iya magana sun ce mai laya ya kiyayi mai zamani.

 • A shafi na goma (10) akwai inda aka samu “zance cikin zance” da ambaton wannan kalma – ‘dumu-dumu’


Ga abin da labarin yake cewa har aka samu wannan zance cikin zance,

“Wani akasi da aka samu shi ne cikin wani ta’bo gimbiya Amrita ta fad’o ta yi dumu-dumu a cikinsa”.

Saboda haka wannan ya nuna salo a cikin wak’a shi ne irin dabarun da marubucin ya yi amfani da su domin jawo hankalin mutane su saurari labarin cikin raha tare da fahimtar sak’onsa a cikin sauk’i. Shi salo a cikin labari ya kasu kamar haka:

 • Salon zubi da tsari

 • Salon kwalliya ko sarrafa harshe

 • Salon kinaya

 • Salon kamance


Zubi da tsari


Salon shi ne wanda ake duba yadda marubuci ya zuba ya kuma tsara labarinsa. Shi ya sa wasu ke ce masa salon zubi da tsari. Yana da shafi saba’in da biyu (72). Wasu manazarta sun fi so a k’ira shi “tsari”, a nan zubi da tsari sun shafi wad’annan abubuwa, sune kamar haka:

 • Bud’ewa da rufewar littafi

 • Dabarun k’ulla labari

 • Tsarin babi-babi ko lambobi ko kan labari


Akwa mabud’in jayayya, da marufin matsayar da aka cimma jayayya.

Salon Kwalliya:


Ana amfani da wasu za’ba’bbun kalmomi masu ratsa zuciya da marubucin littafi ke amfani da su cikin hikima da basira.

Kamance:


Shi ne wajen da marubucin wak’a ke kwatanta wani abu da wani.

Misali, “Ran jahili da kare daidai suke”

 • “Amrita tsaye da wannan bak’on jarumi kuma ga ta dumu-dumu a ta’bo”

 • “A daidai wannan lokacin ne dakarun dake tsaron lafiyar gimbiya Amrita su arba’in suka iso wajen”.


Wannan magana an yi ta ne a shafi na goma sha d’aya (11), sakin layi na  farko.

Kinaya:


Shi ne inda marubucin littafi zai k’ira wani abu musamman mutum da sunan wani abu daban da ba nasa ba.

Misali,

 • “Kare ya tono magana”


Wannan magana an yi ta ne a shafi na ashirin da biyu, sakin layi na biyu

“Inda sarki Kailus ya dubi Aisar cikin murmushi ya ce, abin nan dai ga ma’ana, kare ya tono magana”.

Masu nazarin littafi sun sakawa wad’annan salailai sunaye domin banbance kowane nau’i na salo. Fitattu daga cikin nau’in salo akwai: Kinaya, Kamance, Jisantarwa, Alamtarwa, Zayyana, Hira, Labari da kuma Shillo.

Taurari:


A wannan littafi na Abdul’aziz Sani Madakin Gini mai suna “Jarumin Jarumai”, yan d’auke da taurari ne kamar haka:-

 1. Gimbiya Amrita

 2. Sarki Kailus

 3. Sadauki Janwar

 4. Jarumi Aisar

 5. Sarki Ihsan

 6. Laziya

 7. Sarkin Gidan Garin Jehur

 8. Baiwa Zarsilat


Ita gimbiya Amrita ita ce ‘yar sarki Kailus na k’asar Jehur. Shi kuma sarki Kailus shi ne mahaifinta ita Amrita. Sadauki Janwar kuma shi ne sarkin yak’in k’asar Jehur. Sannan shi kuma Jarumi Aisar wani Jarumi ne na k’asar Teheren, wato garin sarki Ihsan, mahaifin Aisar. Shi kuwa sarki Ihsan shi ne mahaifin Jarumi Aisar abokin gaban sarki Kailus na k’asar Jehur. Shi kuma sarkin gida shi ne sarkin gidan k’asar Jehur wanda wanda komai za a yi a gidan, shi maigida zai fara fad’awa sai ya sanar, ko in maigida bayanan shi zai zama tamkar maigida. Laziya kuma ita mahaifiya ce ga Jarumi Aisar wato uwar gidan sarki Ihsan na k’asar Teheren. Ita kuma Zarsilat wata baiwa ce wadda aka turo domin ta yaudari Jarumi Aisar da surar jikinta.

Garuruwa


A cikin wannan littafi na Jarumin Jarumai akwai garuruwa kamar haka:

 • Garin Jehur

 • Garin Teheren

 • Garin Rum

 • Garin Misra


Shi dai wannan gari na Jehur, wato gari ne inda sarki Kailus yake mulka. Garin Teheren kuma shi ne inda sarki Ihsan yake mulka wato mahaifin Jarumi Aisar. Garin Rum kuma shi ne garin da aka gudanar da  gasa ta farko tsakanin sarki Kailus na garin Jehur da sarki Ihasan na garin Teheren. Sannan shi kuma garin Misra a nan ne za a ci gaba da gudanar da gasa, inda za a kara tsakanin sarki Kailus da Jarumi Aisar d’a ga sarki Ihsan.

Shi wannan littafi na “Jarumin Jarumai” littafi ne da ya ke magana a kan masarautu guda biyu, babu zaman lafiya sai tashin hankali wato masarautar garin “Jehur da garin Teheren”. Shi yasa jigon littafin ya zo da jigon tashin hankali. Sannan kuma wannan littafin yana d’auke da shafi tun daga d’aya (1) har zuwa saba’in da biyu (72).

Kammalawa


Wannan littafi mai suna “Jarumin Jarumai” na labarin zube na gargajiya. An rubuta shi ne da jigon jayayya. A cikin wannan littafin an kawo ma’anar jigo da salo da zubi da tsari. An kuma kawo sunayen taurarin ciki da garuruwan dake ciki.