Ticker

6/recent/ticker-posts

Gurbin Amana A Adabin Hausa

Takardar da aka gabatar a taron kara wa juna sani a sashen koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

NA

MUSA SHEHU

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya

Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

07031319454

msyauri@yahoo.com

1.0   Gabatarwa


Hausawa al’umma ce da ke rayuwa bisa kyawawan d’abi’u da al’adu abin koyi ga sauran al’ummu tun gabanin had’uwarsu da bak’insu na alhairi (Larabawa) da kuma bak’in dole da suka yi musu ci-da-k’arfi da babakere (Turawa). Hausawa mutane ne masu karimci da sanin ya kamata da gaskiya da rik’on amana da adalci da jarunta da biyayya ga na gaba da tausaya wa na baya da karrama bak’o, ga kuma hani ga zalunci da yaudara da cin amana da sauran munanan d’abi’u. Hausawa kan bi hanyoyi daban-daban domin koyar da ‘ya’yansu dukkan d’abi’u managarta domin su zama mutane nagari wad’anda za su jagoranci jama’a bisa turba madaidaiciya. Alal misali, sukan yi amfani da tatsuniyoyi da wak’ok’i wajen cusa tarbiyya ga zukatan ‘ya’yansu ta hanyar bayyana musu alfanun da ke tattare da d’abi’u kyawawa kamar gaskiya da rik’on amana da biyayya ga na gaba da tausaya wa na k’asa, da kuma bayyana musu munanan sakamakon da ke tattare da bijire wa wad’annan d’abi’u managarta.

Mak’asudin wannan mak’ala shi ne, waiwaye a kan d’aya daga cikin kyawawan d’abi’un Hausawa, wato amana. Mak’alar za ta yi nazari ne a kan matsayin amana na kyautata zamantakewa da bunk’asa soyayya da aminci da k’aunar juna tsakanin Hausawa. Bugu da k’ari, takardar za ta dubi yadda al’ummar Hausawa ke bayyana irin matsayi da amfanin rik’e amana, da kuma irin illolin da ke tattare da masu cin amana a cikin wasu sassa na adabinsu na baka da ma rubutacce.

1.1   Mene ne Amana?


            Kalmar Amana asali ba kalma ce ta Hausa ba, ararriyar kalma ce daga harshen Larabci wato ‘Amanat’. Da Hausawa suka aro ta ba su yi mata wani kwaskwarima ba dangane da bak’ak’en kalmar ba, da ma ma’anarta ta asali. A k’amusun Hausa an bayyana ma’anar Amana da cewa, ba mutum ajiyar kaya ko wani abu yadda zai adana shi kamar nasa ba tare da wani abu ya salwanta ko wani abu ya same shi ba.[i] A cikin k’amus na Advanced Leaner’s, bayyana ma’anar Amana aka yi da cewa, yarda da wani a kan kyawawan halayensa na gaskiya da adalci da kuma kauce wa zaluntar mutane ko zamba cikin aminci.[ii] A kan haka ana iya cewa, Amana wata d’abi’a ce na tsare gaskiya da adalci da bai wa kowa hak’k’insa yayin da aka ba mutum kula da wani abu ko shugabancin wani abu ko wasu mutane.

1.2   Ire-Iren Amana

1.3   Amana da Muhimmancinsa a Rayuwar Hausawa


            Ba shakka, duk al’ummar da ta rasa Amana ko ya yi mata k’aranci, lallai rayuwarta na cikin mummunan had’arin gaske na ta’bar’barewar al’amurra da shiga halin k’ak’a-nika-yi. A zamanin da ya gabata, rayuwar Hausawa ta kasance abin sha’awa musamman ta fuskar rik’on Amana a kowane fuska na rayuwarta. Alal misali, shugabanni sukan rik’e amanar da Allah ya ba su na kula da lafiyar talakawansu ko rayuwarsu da dukiyoyinsu. Sukan bai wa talakawa hak’k’ok’insu, ba su cin amanarsu ta hanyar babakere da ruf-da-ciki da dukiyoyinsu, bale barazana ga rayukansu da hana su sakewa da walwala. Wannan ne ya sa aka samu k’aunar juna a tsakanin talakawa da shugabanninsu a wancan lokaci. Shugabanni sun rik’e amanar talakawansu gwargwadon iko, su kuma talakawa suka kasance masu biyayya da yin kyakkyawar addu’a zuwa gare su.

Ta gefen ma’aurata kuwa kuwa, wato mata da miji, kowanensu yakan yi iya k’ok’arinsa na rik’e amanar da ke wuyansa na abokin zamansa. Miji kan rik’e amanar matarsa da ya yi alkawali gabanin aurensu na ba ta ci da sha da sutura da kula da lafiyarta. Ba ya k’untata mata ko cin zarafinta. Yakan yi hak’uri da ita kasancewarta mai raunin hankali da tunani. A koyaushe yakan tuna cewa matarsa amana ce gare shi, don haka ko ya yi niyyar hukunci mai tsauri a kan ta yakan sassuta. Haka ma abin yake ta fuskar matar, ita ma takan rik’e amanar mijinta gwargwadon iko, ta hanyar kula da dukiyarsa da ‘ya’yansa da kuma kauce wa almubazzaranci da abincinsa, da ma dukkan amanarsa da ke kan wuyanta. Irin wannan kyakkyawar zama na rik’e amanar juna tsakanin ma’aurata ya sa ba a faye jin tsakanin ma’aurata ba, bale yawan mace-macen aure ya wakana.

Amana tsakanin mak’wabta kuwa abin sai Alasambarka. Mak’wabci yakan zama tamkar d’an’uwa na jini saboda kyakkyawar zamantakewa. Mak’wabci ba ya zura ido yana kallon abin da zai cuci mak’wabcinsa sai inda k’arfinsa ya k’are. Mak’wabci kan kula da ‘ya’ya da ma duk wani abu da ya shafi mak’wabcinsa kamar ya dda yake kula da nasa ‘ya’yan. Yakan yi musu fad’a yayin da suke aikata ba daidai ba, ya kuma d’ora su bisa hanya. Wannan ne ya sa dank’on zumunci ya samu gindin zama a tsakanin mak’wabta saboda babu cin Amana ko ha’inci tsakaninsu a wancan lokaci.

Har wa yau, akwai Amana tsakanin iyaye da ‘ya’yan da suka haifa. Iyaye sukan yi iya k’ok’arinsu na sauke amanar da Allah ya damk’a musu na ‘ya’yansu gwargwadon hali. Sukan d’auki nauyin kula da ciyar da su da kuma ba su tarbiyya tagari da ilimi nagartacce. Irin wannan Amana ce da iyaye ke rik’ewa ya sa aka samu al’umma da shugabanni nagari masu Amana da kwatanta adalci tsakanin jama’a.

Amana tsakanin abokai kuwa takan kai ga mayar da su kamar ‘ya’uwa na jini babu mai bayyana asirin abokinsa komai wuya komai wahala. Idan d’aya ya ba d’ayan ajiyar wani abu ba zai ci amanarsa ba ko bayan rayuwarsa, bale yana raye. ‘Dayansu ba zai had’a kai da wasu mugaye ba don a cutar da abokinsa, hasali ma idan ya ga abin da zai cutar da shi sai ya ga abin da ya ture wa Buzu nad’i, abin dai sai wanda ya ji ko ya gani. A tak’aice, ana iya cewa, Amana tsakanin al’umma tana haifar da wasu kyawawan abubuwa na ci gaban rayuwar al’umma da suka had’a da:

  • Zaman lafiya

  • Had’in kan al’umma

  • K’aunar juna

  • Bunk’asa tattalin arziki

  • Kyautata jin dad’in rayuwar al’umma

1.4   Gurbin Amana a Adabin Bakan Bahaushe


Hak’ik’ Amana d’abi’a ce mai kyawo da Bahaushe yake son tabbatar da shi a koyaushe domin ci gaban rayuwarsa. Haka ma yakan k’yamaci duk wani mai d’abi’ar bijire mata,wato mai cin Amana. Domin ganin ya tabbatar da wannan muhimmin d’abi’a da d’orewarta a cikin al’ummarsa, yakan yi amfani da hanyoyi daban-daban na adabinsa na baka kamar wak’ok’insa da tatsuniyoyi da karin magana da kirari da sauransu, wajen bayyana muhimmanci da kuma kyakkyawar sakamako da masu Amana sukan samu a rayuwar yau da ma ta gobe, tare kuma da bayyana k’yama da mummunar sakamako ga maciya Amana tun a nan duniya har zuwa ranar sakamako.

[i]   Don k'arin bayani, a duba }amusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano, shafi na 15.

[ii]  Don k'arin bayani, a duba Oxford Advanced Leaner’s Dictionary bugu na bakwai, shafi na 1586.
www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments