Gaskiya: A Tunanin Bahaushen Karin Magana

 

Daga


 


Aliyu Muhammad Bunza


Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya


Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto


mabunza@yahoo.com 08034316508


 


 


Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato k’ark’ashin kulawar Dr. Umar Aliyu Bunza wanda shugaban Sashe Farfesa Abdulhamid ‘Dantunbishi ke jagoranta, Alhamis 9 ga Satumba, 2015 da misalin k’arfe 10:00 na safe a babban d’akin taron Tsangayar Fasaha da Nazarin addinin Musulunci.


 


 


 

Gabatarwa:


Tunanin Bahaushe na fad’ar: “Lokacin abu a yi shi,” wata babbar makaranta ce mai fannonin karatu da yawa. Ga al’adar d’an Adam, kowa na son gaskiya, don haka dukkanin fafutukar d’an Adam a duniya, gaskiya yake yi wa ita. Ma’anar gaskiya a kowace al’umma bai sa’ba ba. ‘Dan yunk’urin da nake son in yi shi ne, lek’o inwar gaskiya cikin wani d’an sashen adabin baka wato “Karin Magana”. Kayan cikin tunanin Bahaushen Karin Magana suna da dangantaka ta k’uk’ut da al’adarsa da tunaninsa a duniyar zamaninsa. Ganin irin halin da k’asarmu take ciki, na k’ok’arin yi wa gaskiya babban masaukin alfarma, ya ba ni sha’awar in d’an ambaci gudunmuwar Hausawa na k’ara wa Borno dawaki a kan goyon bayan gaskiya. Ba zan yi mamakin a ce, wannan takarda ta yi canjaras da wani aiki irinta ba, domin gaskiya sananniyar aba ce, mai farin jini, da jan hankalin ma’abota hankali. Duk da haka, ni dai, a iya d’an bincikena, ban kai ga wani aiki da suka yi zozo-zozo ba.

Warware Taken Takarda


Babu wani sashe na rayuwar Bahaushe da Gaskiya ba ta yi naso ba. Na za’bi in kalli karin magana domin kasancewar karin magana wata fitacciyar duniyar adabi da ta mamaye duniyar masu magana da harshe. Tunanin da ke cikin karin magana na masu harshen ne, domin su suka k’agi karrruwan maganganunsu. Yadda karin maganan Bahaushe ke kallon gaskiya shi ne gaskiyar yadda Bahaushe ke kallon gaskiya a duniyar tunaninsa. Na tak’aita fad’in bagiren bincike a kan Bahaushen karin magana domin a kowane harshe akwai karuruwan maganganu da suke yi wa gaskiya kirari da godiya. Kasancewar karin magana k’ololuwar tunanin masu magana da harshen, idan aka nazarci “gaskiya” a ciki an kai matuk’a ga tunanin masu harshe a kan yadda suke kallon gaskiya. Abubuwan da za a tattauna a cikin wannan ‘yar takarda tantagaryar tsabagen Bahaushe tunani ne na kowane Bahaushe, a kowace nahiya yake ciki a duniyar k’asar Hausa, wannan tunanin ya wakilce shi.

Ma’anar Gaskiya


A tsarin nahawu “gaskiya” suna ne. Daga cikin rukunin sunaye yana daga cikin sunayen da ba a gani. A wata fassara sunan na d’aukar “nake yi” wato a ce: “Gaskiya nake yi”. A koyaushe za a fassara gaskiya, dole a yi la’akari da abu biyu: furuci da aiki. A tunanin Bahaushe gaskiyar furuci ita ce:

A darkako zance yadda aka ji shi cikin ruhin kalmomin da aka ji shi ba tare da an sauya su ba, ko a sassa’ba musu muhalli ga yadda suka sauka ba. A tabbata ba a k’ara komai ba, ba a rage komai ba, ba a kururuta ko gid’ad’a komai ba, kuma ba a rage nauyin sassakan kalmomi ba, kuma ba a k’ara musu nauyi ba. Zancen, da an furta shi, mai shi zai ce: “Haka na fad’a”,  wanda aka yi gabansa ya ce: “Haka na ji shi”. Idan ta tabbata haka, wannan shi ake ce wa, “gaskiya magana” yadda aka ji ta, haka aka fad’e ta.

 

A tunanin Bahaushe, ba baki kad’ai ke da hak’k’in gaskata gaskiya ba. A ayukka ma ana iya rarrabe na gaksiya da akasinta. Aikin gaskiya shi ne:

Aikata abu yadda aka shata a aikata shi. Aikin da aka aikata, ya yi canjaras da tunanin al’adar rayuwa da ak’idarta ba ragi ba k’ari. A aikata aikin da gaskiya, a kan gaskiya, bisa gaskiya, ba tare da yin takin sak’a da kowane irin ma’aunni na gaskiya ba.

 

Wad’annan fassarori na gaskiya k’unshe suke cikin tunanin Bahaushe na fad’ar: “In za ka fad’i, fad’i gaskiya”. A nan, gaskiyar magana ta fito. A fassarar gaskiyar aiki kuwa, za mu harari: “A dad’e ana yi sai gaskiya”. A dad’e ana me? Ana aikata wani aiki ba ja da baya, ba tsoro, ba razana bale tsangwama sai gaskiya? Da furucin da aka furta, da aikin da aka aikata na gaskiya, duka sunansu “gaskiya” bisa ga zurfin tunanin Bahaushe na rad’a mata suna “Gaskiya sunanta gaskiya”.

Jinsi Gaskiya:


Ga d’an tunanina na d’alibin al’ada, na so in kalli a tsarin nahawun Hausa gaskiya wane jinsi take? Me za a ce a kan jinsin a al’adance? A k’a’idar zumuntan suna da lamirinsa, gaskiya mace ne. Dalilina na fad’ar haka shi ne, ga al’adar zantukan yau da kullum, akan ji Bahaushe na fad’ar:

Gaskiya ta yi halinta.

Gaskiya mugunyar magana

Gaskiyar fad’a harsashe

Gaskiya nagartar namiji.

Fad’in gaskiya ya fi mugunyar salla.

Daidaiton shigan lamirin jinsin mace na ta da –r wata hujja ce ta tabbatar da jinsin mace ga gaskiya. Yarda da ba Bahaushe ya yi na kasancewar gaskiya “magana” wata hujja ce ta zamowar gaskiya mace. Idan mun daidaita a kan kasancewar gaskiya “mace” a al’adance, tana da martabobi goma sha d’aya:

 1. Mace ke haihuwa matuk’ar ana haihuwa gaskiya ba ta k’arewa.

 2. A awon shekaru mata sun fi maza makara, tabbacin gaskiya ita ce k’arshen kowane al’amari.

 3. A kowace al’umma, mace ake nemi ba ita ke nema ba. Wa gaskiya ke nema? Kowa nemanta yake.

 4. Mata sun fi maza fice da haiba idan sun tsatsanta a matsayin mutane. Haka gaskiya take ko’ina.

 5. Mata su aka fi sani da kyau irin na fuska da jiki. A koyaushe gaskiya ba ta da muni ga Bahaushe.

 6. Mata sun fi cin adon kintsi da tsari mai jan hankali. Gaskiya da adonta aka gan ta, don haka ba ta neman wani ado.

 7. Mata sun fi maza zak’in murya da yauk’in tafiya. Muryar gaskiya rarara ce.

 8. Mata sun fi maza hak’uri idan aka dubi kishi da haihuwa. Mai gaskiya kan dafa dutse.

 9. Mata ke hak’a tarkon kama mutum. Tarkon gaskiya k’arya ba ta ta’ba tsallake shi ba.

 10. Mata ake nema ba su ke neman maza ba. Kowa gaskiya yake nema domin a ce masa mai gaskiya.


Irin tunanin Bahaushe ga mata na yau soyayya, gobe k’iyayya, shi ke ga gaskiya a kirarin, da ake yi mata na: “Gaskiya a k’i ki a so ki”. An yarda mace na tsufa ta kai munzalin da za a tabbata haka, amma ita gaskiya ta fi da haka, dalilinsa ke nan na ce mata: “Gaskiya ba ta tsufa”.

Fitattun Sofifin Gaskiya:


Kasancewar gaskiya suna, ba dole sai an gan ta da ido ba domin ‘boyayyen suna ce. Tattare da haka, sifoffinta da halayenta da karuruwan magana suka fuskanta abin duba ne ga kowane masoyinta. A hangen Bahaushe, gaskiya aba ce da ta tattaro abubuwa kamar haka:

Farin jini:   A ko’ina gaskiya da masoyinta yake/suke za a tarar da su

masu farin jini ga mutane. Ashe babu laifin karin maganan da ke cewa: “Gaskiya ina laifinki”? Farin jini shi ne ku’butar illar abu ga masu kallonsa saboda tsananin son da suke yi masa.

Hak’uri: A koyaushe, gaskiya da mutanenta, an shaide su da hak’uri domin

sun san kul ba dad’e, kome nisan dare gari zai waye; don haka, a dad’e ana yi sai gaskiya.

Wayo: Ba a ta’ba samun ma’aboci gaskiya wawa ba, sai dai ma’auri

k’arya ya ga wautarsa na biya wa gaskiya sadaki mai tsada. Kafirce wa k’awace-k’awacen k’yalk’yali da gaskiya ta yi dole ne, domin ita ba ta neman ado ko zak’in muryar zabiya.

 

K’wazo: A al’adance, raggo abin kushewa ne don haka, ragganci ba ya

daga cikin sifofin gaskiya. A ganin Bahaushe, mai gaskiya shi ne managarci don haka yake cewa: “Gaskiya nagartar namiji”. Idan an ci karo da ita baibai ta gwak’e abokin adawa ya ce: “Gaskiya dokin k’arfe”.

Kunya: Gaskiya kunya gare ta, don haka kowa ke sha’awar huld’a da ita.

Idan an zaune ta, zantukan ladabi da kunya za su rik’a fita a baki domin maganar gaskiya baki ba shi rawa. Idan aka rasa ta, babu wani abu da zai maye gurbinta na kare kunya. Tunanin Bahaushe ke nan na cewa: “Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi ji’bi”.

Cika Ido: Mai gaskiya komai k’arancin zatin jikinsa a idon wad’anda suka

san shi da ita ya fi toron giwa cika ido a dokar daji. Komai k’arancin shekarun mai gaksiya Bahaushe bai d’auke shi yaro ba saboda cewa yake yi: “Yaro da gaskiya abin tsoro ne”. Idan gabaci ya zure mata ta yi halinta akan ce: “Gaskiya ba ta da kad’an”.

Basira: A kowace irin al’umma ma’abota basira ake ba tsaron gaskiya.

Duba zuwa ga manzanni da annabawa da mala’iku wani dogon karatu ne. A tsakaninmu ‘yan Adam, ma’abota basira daga cikinmu ke kula muna da tsare-tsare dokokinmu da zartar da hukunce-hukuncenmu. A koyaushe gaskiya ta bayyana, k’in ba da kai bori ya hau rashin basira ne domin an ce: “Da k’in gaskiya sai ‘bata”.

Kyawo: A ji abu, a ga abu, a tabbatar da abu ya yi abu, sai gaskiya. A

lafazance da aikace, Bahaushe bai ta’ba kwatanta gaskiya da muni ba. A koyaushe a wajensa fara ce fes! Mun kuwa san cewa ya yi: “Komi ya yi fari yana kyau in ban da kurkunu”. Komai munin magana a bagiren da aka furta ta ko munin aiki a wurin da aka aikata shi, in dai a kan gaskiya yake zancen muni bai taso ba, sai dai a ga manya suna na k’adangare suna cewa: “Ka ji farar gaskiya”. ‘Dank’ari! Wato gaskiyar da ke ciki ta kore komai sai dai a biyo da gyaran fuskar fad’ar: “Gaskiya ciwo gare ta”.

Tsufa: A ma’aunin d’an Adam na addini da al’ada da cigaban zamani,

tsufa ga rayuwa wata martaba ce, domin an ga jiya, an ga yau. A tunanin Bahaushe, gaskiya ba ta tsufa irin ta mutane, a koyaushe aka lalubo ta za a same ta sabuwa garas kamar yanzu aka yi ta. Maganar gaskiya ba ta tsufa, aikin gaskiya ba ya tsufa. Hak’ik’a, Hausawa sun dace a fad’arsu na cewa: “Gaskiya ba ta tsufa”.

Magani: Bahaushe ya d’auki gaskiya wata babbar magani ga cutukan

zukata da na ga’b’bai da rigakafi da waibuwa. A hangensa shi kansa magani sunansa “gaskiya”. Ko’ina mabuk’aci yake yawo da wata buk’ata maganinta yake nema ya rabu da ita ko ya shawo kanta ko ya rage ta ko ya yi mata barazana. Bahaushe na ganin, gaskiya ita ce ganmon d’aukar dukkanin wad’annan buk’atoci. A fagen artabo da marasa gaskiya, gaskiya ‘yar tauri ce ta hak’ik’a domin Bahaushe ya yanke hukunci cewa: “Ciki da gaskiya wuk’a ba ta huda shi”.

Fitattun Halayenta:


Hali a nan, ina son in ce, abin da za a iya gani k’uru-k’uru a kan wanda ta shafa ko wurin da ta bayyana ko aikin da ta k’arasar. A kadadar adabi, babu abin da ya samu babbar shaidar k’warai kamar gaskiya. Wannan shi ya sa babu wani bayanin da zai iya kewaye dukkanin halayenta, sai dai a d’an kwatanta gwargwadon abubuwan da aka tuna. Mu tsura wa wad’annan halaye ido mu nazarce su a ma’aunin gaskiya mu gani:

 1. Bahaushe ya ce: “Idan ka ji shuru lafiya ce, gaskiya ta bayyana, idan ta d’aga ko ita ake neman dole a ji muryoyi na tashi.

 2. Idan ka ga ana gudu, ta bayyana ko wurinta za a je neman agaji. Ban ga laifin Rarara ba da ya ce: “Masu gudu su gudu”!

 3. Hausawa na cewa, “Labarin zuciya a tambayi fuska”. Idan an yi canjaras da gaskiya, za a ga fuska na haske da dariya ko murmushi, tamkar kurma na cikin mota ya tsinkayi matarsa.

 4. Idan an tarar da fuskoki gintse cikin k’ura, watak’ila an zartar da ita ga wanda ya sa’ba mata. Haka kuma, idan lokacinta ya yi dole a gintse, Bahaushe ya ce: “Gaskiya mai d’aci”.

 5. Kuka akasin dariya ne, amma kuma gaskiya yake rakowa a ko’ina aka ji shi. Idan ta bayyana tana sa kuka ga wanda ta ratsa. Haka kuma, da kuka ake neman zartas da ita ga wanda aka yaudara.

 6. Bahaushe ya ce: “In ka ga barci da dogon hansari gaskiya aka taka ta ba da damar a kwanta a huta a yi barci”. Wanda ya rasa ta zancen barci sai abin da hali ya yi.

 7. Ga al’ada, idan aka kasa barci gaskiya aka kwance wa bante. Wanda ke matse neman gaskiya ko ya sa’ba mata, bai ga idon barci ba.

 8. A ko’ina aka tarar da ana fad’a, kowane ‘bangare ita yake da’awar yana da, don haka yake tsayin daka sai ta tabbata, an tabbatar masa da ita.

 9. Ma’abota basira sun ce: “Gaskiya ta tsayar da hukuma”, a ko’ina aka ga kotu don k’wato gaskiya da tabbatar da gaskiya aka kafa ta. Wanda duk ya kai k’ara ita yake son a ba shi. Wanda duk aka kai k’ara ana zarginsa da rashinta.

 10. Makarantun da ‘yan Adam ke yi na kowace irin ak’ida da fahimta da fasaha, gaskiya ce ake son a gano a ciki.

 11. Ba a ta’ba samun zaman lafiya ba face sai da gaskiya. A ko’ina gaskiya ta k’i kai ziyara zaman lafiya ya k’are.

 12. Rigingimu da tashin hankulkula da zub da jinainai tushensu rashin gaskiya. Mai musu ya tambayi wad’anda ke k’ark’ashin inwar gaskiya.

 13. Magabata sun ce: “In ka ga lafiya a tsufa tun a k’uruciya aka bauta wa gaskiya”. Idan aka ga tsufa cikin wuya ba a ba gaskiya hak’k’inta cikin k’uruciya ba.

 14. A ko’ina tsoro ya yawaita banga-banga aka yi da gaskiya, in an yi taho-mu-gama da ita, dole tsoro ya yi ban kwana da k’irji.

 15. Gwarzo a ko’ina yake gaskiya ya rako sau da k’afa.

 16. Masana da mad’aukakan duniya kafad’ar gaskiya suka dafa suka yi zara aka gan su, aka ji su, aka yarda da su, suka samu kar’buwa.

 17. In suna ya dashe, ba a jin d’uriyar mai shi a ko’ina, da wuya in ba dugadugan gaskiya aka ci ba.


https://www.amsoshi.com/2017/11/05/zawarci-da-auren-bazawara-maguzance/

Nahawun Sunan Gaskiya:


A nazarin nahawun sunan gaskiya babban abin kulawa shi ne fad’ar Bahaushe na: “Gaskiya sunanta gaskiya”. Sunan gaskiya kad’aitacce ne a farfajiyar tunanin Bahaushe. A tsarin daidaitaccen nahawun Bahaushe gaskiya ba ta da jam’i, tilonta ta “gaskiya”, jam’in ta ‘gaskiya’, ba a ta’ba jin “gaskiyoyi” ba. Dalili kuwa ita kad’ai ce, ta ishi kanta, da kanta, ba ta da na biyu, ba ta da mai kama da ita. Abu in dai ya kasance ita, in ko ya kasance akasinta. Na yarda da karuwa da ta ga noman d’an koli ta ce “Abu kamar da gaske”, wai, domin ta san ba gaskiyar ba ce. Abin ban sha’awa d’ofanenta da ake yi wa kalmar koyaushe gaba yake idan aka nazarci:

Gaskatawa

Gaskacewa

Gaskanta

Gaskatacce

Gaskatacciya

Gaskatattu

Magaskanta.

A wata mahanga, a cikin tsarin sunayen itace da tsirrai na k’asar Hausa, tare da k’wari da dabbobi da tsuntsaye babu mai suna “gaskiya”. Da na lura cikin wannan tunanin, sai na ga akwai ice mai suna “k’arya”. Dalili kuwa shi ne, a tsarin nahawu gaskiya ta fi k’arfin duk wani abu da ba d’an Adam ba. A iya sanina, babu wata halitta mai sunanta.

Gaskiya A Duniyar Dabbobi:


Wannan aikin a kan karuruwan maganganun gaskiya aka tsara su. Duk da haka, na yi aron hannu domin fashin bak’in ma’anonin wani labari da gidan Rediyon Rima ya ta’ba gabatarwa a shirinsu na kacici-kacici. Labarin na cewa:

Wai mene ne dalilin akuya na a ko’ina ta ga mota ta ruga a guje? Shi kuwa kare me mota ta yi masa da ya gan ta ya ruga aguje yana bin ta da haushi? Akwai mamaki jaki komai odar da mota ke yi masa, ba ya ta da kansa, bale ya d’aga wurin da yake. Mafasa bak’in suka ce: “kowanensu na kan gaskiyarsa. Ita dai akuya, rashin gaskiya ta yi, ta shiga ba ta biya ba. Kare kuwa, ya biya kud’insa, ba a ba shi canji ba, don haka yake bin gaskiyarsa”. Jaki (DPO’n) hanya, gaskiya ta yi masa yawa; ya biya ba a d’auke shi ba, ba a ba shi kud’insa ba. Don me zai yi wa maras gaskiya gudu shi da gaskiyarsa? Ashe sunan wannan labari a farfajiyar karin magana: “Gaskiya ka fad’a ba sanda ba”.

 

Akuya ta tabbatar da maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi ji’bi. A fahimtar kare, gaskiya ka fad’a ba sanda ba, ko an fi shi gudu ba zai daina bi ba, sai an biya shi. A tunanin jaki, ciki da gaskiya wuk’a ba ta huda shi. Jaki gaskiya ya taka, to, k’asa ta gudu ta je ina?

Tasirin Karin Maganganun Gaskiya ga Dimokrad’iyyar K’asarmu:


Da gangan na kawo wannan d’an fasali domin mu rik’a daidaita karatunmu da halin da muke ciki na rayuwa. Demokrad’iyya wani ruwan dare ne a duniyar mutanen k’arninmu. A k’asarmu, gaskiya ta tarar da k’arya ta tara miyagun makamai fiye da goma sha biyar (15) wanda take ganin kowane d’aya daga ciki ya ishe ta yak’ar gaskiya. Daga cikin makaman akwai:

 

Kud’i:                  Na cikin gida da k’adarori da na waje. Su ne k’uri’a in ba su,

ba ci.

Mulki:        Ita ta kafa daula ita ke da masarauta. Mai sanda ke da fasalin

bugu.

Yawa:         A ko’ina ta hanga ta yi wa gaskiya rata mai yawa. Ba ta

zaton kowace matsala.

Magud’i:    Da shi ta kafa daula kuma ta shirya shi matuk’a.

Banga:       Bayan wakilan tsaro na yi mata kore ga ‘yan ta’adda da ta

yaye bila adadin.

Addini:       Cikin yaudara ta kutso da shi domin in dama ta k’iya a koma

hagu.

K’abilanci: Aka raba hankalin ‘yan k’asa da sunan k’abilu domin samun

damar ribantarsu.

‘Bangaranci:        Aka raba k’asa kudu da arewa bisa cin amana.

Zumunci:    K’arya ta yi tsaye ta ‘bata zumuncin masu gaskiya domin ta

hana su zama su fahimci bambance-bambancensu.

Tsoro/Barazana: An ba gaskiya tsoro da k’arfin iko, an yi mata barazana

da wakilan tsaro, ta dai yi tsaye ta k’i ta sake suna ta ce: “Gaskiya sunanta gaskiya”.

Tsafe-Tsafe:         K’arya ta haifar da k’ungiyoyin asiri barkatai ta fito da k’arfin

tsafi ta fargagi gaskiya. Ina! Gaskiya ta yi tsayin daka ta tabbatar da mai gaskiya yana tare da Allah.

K’arya:      Ta gaji da sari-ka-rok’e, ta fito ta soki gaskiya da rashin

takardun shaidar karatu. Ta kushe gaskiya da cewa ta tsufa. Ta zarge ta da ham’bare wata daula irin ta. Ta aza mata laifin zanga-zanga. Duk aka k’are ta bisa doron karin maganan “kowa ya yi cinikin k’arya ya yi biyan gaskiya”.

Wad’annan abubuwa kad’an ne daga cikin zagon k’asa da taron dangi da k’arya ta yi gangami domin a yi wa gaskiya ature. In ban da gaskiya dokin k’arfe ce, wa ke kar’be mulki ga mai mulki ba tare da ya kafa mulki irin mulkin mai mulki ba? Duk da kasancewar tsafi gaskiyar mai shi, ya tsaya ga mai shi, ya bar gaskiya tama. A tarihin demokrad’iyyar Afirka, gaskiya ba ta ta’ba ba mutane mamaki ba kamar yadda ta bayyana a za’ben shekarar 2015 a Nijeriya. Sakamakon za’ben ya sabunta wa ‘yan k’asa tunani, da dama suka dawo da rakiyar fahimtar mai sanda ke da fasalin bugu. Zancen cewa: “Gaskiya ta gama aiki”, a Nijeriya an k’aryata shi. In ba gaskiya, babu abin da ke had’a kan mutane mabambanta addini da ak’ida da al’adu wuri d’aya, a fuskanci abu d’aya a yi tsaye a kansa, a tabbatar da shi, sai mai kushe ta ya ji kamar mafarki yake.

Baje Kolin Gaskiya A K’unshiyar Karin Magana:


Tunanin wannan takardar ya tattara ga irin yadda Bahaushen tunani ke kallon gaskiya a k’unshiyar karin maganganunsa. Bayan an yawata da karuruwan maganganun a wurare daban-daban na baje kolin gaskiya, na ga ya dace a tattaro su gaba d’aya a d’ora su kan zango-zango na gaskiya da suka baje koli.

Suna:

Bahaushe bai ta’ba bai wa kowane irin abu sunan gaskiya ba. Sunanta d’aya ne, ita kad’ai ke da shi, da shi aka san ta, baya da jam’i ba ya ninkuwa don haka yake da:

 1. Gaskiya sunanta gaskiya

 2. Gaskiya da gaskiya ake gaishe ta.


 

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/falsafar-daurin-auren-maguzawa/

Lafazinta:

Sanin cewa, ga lafazi ake fara kirdadon gano gaskiya Bahaushe ya fi bai wa maganganun gaskiya muhimmanci. Sanin haka ya sa wasu sassa daga karuruwan maganganun ke cewa:

 1. In za ka fad’i, fad’i gaskiya

 2. Maganar gaskiya a yi ta da wando

 3. Maganar gaskiya harshe ba ya rawa

 4. Fad’in gaskiya sai namiji.


Muhallinta A Harshe Da Kunne Da Zuciya:


Idan aka furta gaskiya a tunanin Bahaushe mafad’inta gwarzo ne domin ya yak’i harshensa. A kunne za a fara jin irin nauyinta, zuciya ta ba da labarin launinta, d’and’anonta, rad’ad’inta, ga su nan dai:

 1. Gaskiya mugunyar magana

 2. Gaskiya mai d’aci

 3. Abu da ciwo kamar gaskiya

 4. Farar gaskiya

 5. Bak’ar gaskiya (ba a cika fad’ar haka ba)

 6. Gaskiya mai ciwo

 7. Fad’in gaskiya ya fi mugunyar salla

 8. Gaskiya mai dad’i


Zatinta da K’arfinta:

Duk da yake gaskiya a nahawu ‘boyayyen suna ne, Bahaushe na ba ta zati da ruhi irin na mai rai domin ita ke rik’e da kafad’un masu rayuwa. Duk wani k’wazo da mazakuta da dabara sai da gaskiya ake yin sa. Harari wad’annan karuruwan magana da idon basira:

 1. Gaskiya dokin k’arhe

 2. Gaskiya mai nauyi

 3. Gaskiya ka fad’a ba sanda ba.

 4. Gaskiya ta yi halinta.


Dangantakarta Da Mutane:

Daga cikin karuruwan maganganun da suka baje wa gaskiya koli akwai wad’anda da kallonsu suna da alak’a da mak’agan su domin kowane irin adabi masu shi suka k’ago shi. Dubi wad’annan sosai:

 1. Gaskiya a k’i ki, a so ki.

 2. Da k’in gaskiya sai ‘bata

 3. Ciki da gaskiya wuk’a ba ta huda shi.

 4. Na d’aure mene ne gaskiyar maza? Ya ce: “Gaskiyar maza a sake su”.

 5. Mai son gaskiya ka fad’a maka gaskiya.

 6. Tsafi gaskiyar mai shi.

 7. Gemu babu gaskiya ko na bunsuru ya fi shi.

 8. Kowa ya k’i gaskiya rabo nasa k’unya.

 9. Da k’arya ta raba ka da mutum gara gaskiya ta raba ku.

 10. Gaskiya mazan tsaye taka so.


 

Dangantakarta Da Akasinta:

Wasu karuruwan maganganun Bahaushe raba k’afa suke yi, ido ga kifi, ido ga bado. Bayan sun kar’bi bak’uncin gaskiya suka kar’bo uzurinta na k’in k’ulla abota da k’arya. Karuruwan maganganun da suka yi wannan hasashe sun had’a da:

 1. Gaskiya mai korar k’arya

 2. Abu kamar gaskiya karuwa ta ga noman d’an koli

 3. Maras gaskiya ko cikin ruwa ya yi ji’bi

 4. Gaskiya ba ta neman ado ko zak’in muryar zabiya

 5. A dad’e ana yi sai gaskiya.

 6. Gaskiya ina laifinki?

 7. Ba gaskiya awo a d’aki

Hana Rantsuwa:

A cikin kowane irin al’amari na ilmi, ba za a rufe k’ofar abu ba gaba d’aya. Dalilin da ya sa ake raga tazara domin d’an Adam d’an tara ne bai cika goma ba. Tattare da irin k’imar da ke ga gaskiya a kowane al’amari ana d’an samun wasu karuruwan maganan da suka d’an zarge ta da yawan hak’uri da rashin wayo irin na yaudara. A ganina, wad’annan su ne hana rantsuwa da cewa, gaskiya ba ta ta’ba samun zargi ga kowa ba. Ga hana rantsuwa.

 1. Fad’a da gaskiya tsoro ne.

 2. Ba gaskiya ba ce ga shari’a kai dai a samo sa’a.


Takin Sak’ar Zamaninmu da K’unshiyar Karuruwan Maganan Gaskiya:


Adabi k’awataccen asirin gudanar da tsarin rayuwa ne da aka gada kaka da kakani. Yadda gaskiya ta samu baje koli a karin maganan Bahaushe, bai kyautu a ce, akwai zamanin da za a yi mata barazana ba. Taskar adabinmu ta tababtar da gaskiya dadaddiyar abu ce a k’asarmu. Babu shakka, mun gaji gaskiya ga magabatanmu. Lallai tun gabanin saduwa da kowace al’umma da addini da ak’ida da wayewa Bahaushe yake da gaskiya. Ga irin k’unshiyar karuruwan maganganunmu na gaskiya da wuya a sami wata al’umma a farfajiyar duniyar yankinmu da za su gwada tsawo da mu a kan tafiyar da gaskiya da yarda da ita. Idan haka ne, yaya aka yi yau an wayi gari:

 1. A huld’od’in zamantakewarmu gaskiya ta yi ‘batan dabo?

 2. A al’amarin gudanar da siyasar mulkinmu an k’i ba gaskiya kujera ko d’aya? An bar a tana shawagi, wai dole in ta gaji ta san wurin da dare ya yi mata?

 3. Wurin masu addini da gaskiya take a rubuce, yau shafin ya ‘bata cikin shafuka, wanda ya ce, zai binciko shi, a barkace masa tunani?

 4. Manyan da, da su ke k’wato wa gaskiya hak’k’inta, a yau wajensu ake karatun dabirta gaskiya?

 5. Tsarin ilminmu da aka kafa bisa gaskiya, yau har d’alibi ya kar’bi takardar shaidar sauke karatu ba su ta’ba kuren hanyar had’uwa da gaskiya ba?

 6. Me ya sa masu gaskiya a yau suka kasance ‘yan tsiraru, k’auyawa, marayu, marasa galihu, talakawa, wawaye, toshon yayi ko tsohon alkawali?


Wanda duk ya san irin gurbin da ke ga gaskiya cikin adabinmu musamman cikin karuruwan maganganunmu, tilas, ya girka tagumi a kan halin da Bahaushe yake ciki a yau. Abin ban mamaki, babu wanda ya ta’ba jarraba gaskiya a kowane al’amari ya kasa samun biyan buk’ata. Babu wanda zai zargi gaskiya da wani muni a ta’ba masa. Babu mai ganin laifinta ba a ga laifinsa ba. Babu mai takin sak’a da ita, ya cika muna ido da zuciya. Ba mu ta’ba jin d’an kokuwan da ya yi k’arfinta ba wajen mugun kaye. Cikin ‘yan dambe, ba a samu mai mak’etacin bugu ba irin nata. Ma’abota sharo sun san sandarta ta fi ta kowa tsawo da nagartaccen k’arfi da nauyi ga hak’ark’ari. Wai a ce, duk da sanin wad’annan abubuwa, gaskiya ta tsawwala cikinmu, idan ta tunkaro mu, mu yi malle, idan ta riske mu, mu yi na bushiya, idan ta lalabo mu, mu zama kunkuru, sai ta d’aga mu fitar da k’afafu da hannuwa.

Ga alama, abubuwan da suka sa muka rafashe ga rik’on gaskiya irin yadda magabata suka tabbatar a karuruwan maganganunsu ina ganin akwai:

Kwad’ayi: Hausawa sun ce: “Shi ne mabud’in wahala”. Ga mu nan a

cikinta. Yaushe za mu fita? Sai mun sallami tsohon nan kwad’ayi.

Son kai:      Hausawa sun ce: “Mai sa son banza”. Yau son banza ya kai

mu ga aikin banza da maganganun banza. Me ke sa ma’aikatan hukuma rashin gaskiya? Son kai ke sa sata.

Son girma: Hausawa sun ce: “Mai kashe girma, yau ga girman nan

gingira’bai ta kasa tayar da kanta bale a dafi kafad’arta a tashi.

Rashin mutunci: Mutuncinmu ga kowa shi ne abin duniya da muka tara,

wanda bai tara ba, ba kowa ba ne. A k’arshe, ga mu mutane wad’anda ba mutane ba na shugabantar mu. Dole gaskiya ta gudu.

Sakamakon Nazari:

A kowane zamani, adabin mutane na tasiri a kan rayuwarsu. Idan ana son a daidaita abubuwan da suka lalace a cikinsu, a harari adabinsu cikin natsuwa a ga yadda za a ceta musu da shi. Na tabbata ban yi son kai ba, idan na ce, duba cikin karuruwan maganganun Hausawa da suka fuskanci gaskiya wata shaida ce ta cewa, Bahaushe gaskiya gwaggonsa ce domin ya gaje ta, kuma ya sha ta a nono. Idan aka yi duba cikin manyan sarakunan Hausa tun na gargajiya ya zuwa yau, za a tabbatar da haka. Ashe gaskiyar Shawith Smith da ya rubuto ta’aziyyar Sarkin Gwandu Yahya cikin jimla d’aya da cewa “K’ur’ani don gaskiya ake tsoron ka”. Tirk’ashi! Ba Muhammadu Buhari kawai ne sojan da ya rik’i Nijeriya ba. Idan lokacin da, yana soja, bindiga ake tsoro, yanzu da ya sa farin kaya, me ake tsoro? A d’an nawa tunani, gaskiyar Buhari ake tsoro ba sunansa ba, ba muk’aminsa ba, ba tsawonsa ba, ba addininsa ba, ta harshensa ba, ba k’abilarsa ba, ba jam’iyyar siyasarsa ba. Wannan kad’ai wata madogara ce ta cewa, adabinmu ya yi tasiri ga magabatanmu domin Muhammadu Buhari ya tabbatar da haka. A wannan d’an bincike na lura da abubuwa kamar haka:

Gaskiya buwayayyiya ce tun a sunanta da sifarta da halayenta. Babu shakka, ta ci ragon sunanta domin babu wanda aka haifa a duniya da ba ya son a danganta shi da ita. Babu mai rai da ke son a zarge shi da rashin ta. Wanda duk ba ya da ita tsoron kowa yake yi. Wanda ya rik’e ta ya wuce tsoro, dole a tsorace shi. Dalilin da ya sa ake tsoron gaskiya da masu ita a yau, domin marasa gaskiya sun yawaita, aikin rashin gaskiya ya mamaye duniya. Gaskiya ta fi mulki k’arfi, ta fi hukuma iko, ta fi ilmi farin jini, ta fi lafiya amfanin mai ita, ta fi wayo da hankali kare martabar suna, ta fi dukiya d’aukaka suna, ta fi kyauta tagomashi. Domin tabbatar da ita ake yak’i, ganin ta ke sa aje makamai, d’ammahar ta ke sa a yi sulhu. A kan kowace irin tahiya gaskiya ita ce godabe. Idan an yi d’emuwa ita aka baro, idan an kai ga zango an yi dace da ita. Na dai yarda da tunanin Bahaushe, gaskiya ina laifinki?.

 

Malamaina da abokanin aikina da d’alibanmu (in da su) ina son in yi ‘yar tambaya. Wai wane laifi gaskiya ta yi wa ilmin boko na rashin sama mata darasi mai cin gashin kansa a kowane fannin ilmi mai suna “gaskiya”? A d’an nawa gani, in kowa zai manta da haka, bai kamata d’an Nijeriya ya manta ba, musamman idan aka dubi takardarmu ta kud’i naira ashirin da shugaban k’asarmu na 2015. Don haka na ba da shawara mu fara tunanin k’ago darasi mai take “Gaskiya”.

 

Nad’ewa:


c da waiwaya tana maganin mantuwa. A tunanin magabatanmu in abu ya ‘bata bai kamata hankali ya ‘bata ba don haka suke ganin, in rak’uminka ya ‘bata babu laifi ko cikin akurki (-n kaji) a rega domin d’ebe kokanto. Gaskiyar magana ita ce, ana dare ga dara ya yi, sai aka ci nasara ana cikin gina ga wutsiya. Tattare da sanin cewa, aiki ya yi wa kurege yawa, amma dai aikin Magaji ba ya hana na Magajiya. Ban yarda da cewa, wanda ya yi nisa ba ya jin kira ba, sai dai idan mai kira bai d’aga murya ba, ko iska bai buga gefen wanda ake kira ba, ko wanda ake kira bai san kiransa ake ba, ko kuma ba ya d’ammahan a kira shi. A cikin halin da k’asarmu ta shiga har mun fara zaman dako a aza ranar zaman makoki. Da malamai da bokaye da likitoci kowa ya yi abin da ya sani, aka sa wa mai yi ido. Buwayayye, zama d’aya ya aiko buwayayyiyar baiwarSa “Gaskiya” marasanta suka ce, “In ba ku yi ba mu wuri”! Tabbas, sanin wurin bugu shi ne k’ira. In ka ji rik’a mini kayana, Hausawa sun ce: “Ba zawo ya koro mai kayan ba”. Wanda duk ya ga duhun dare, ba a d’aure shi ya kucce ba. Hak’ik’a, wurin da babu k’asa nan ake gardamar kokuwa. Aradu! Gaskiya ta san a ko’ina k’arya ta ‘boye kayanta, ku tambayi Malam Muhamamdu Gambo Fagada ku ji:

 

Jagora: Kaicon na kai na!

: Halin duniya na ba ni tsoro!

: Wai ga maciji ana ta/.

: Biyas shayi da sanda!

: Wai ga ‘barayi

: To, mib bid’i mai wak’ar ‘barayi?

Amsa ita ce: Rashin gaskiya.

 

          GASKIYA MUNA GAISHE KI.

 

Manazarta


 

Aliyu, M.S. (1980) “Sharotcomings in Hausa Society as Seen by

Representative. Hausa Islamic Poets from Ca 1950 to Ca 1982” M.A. Thesis, Knao: Bayero University.

 

Bunza, A.M. (1996). “Gaskiya Ina Laifinki? Tsokacin Diddigin

Musabbabin Karyewar Arzikin Nijeriya Cikin Wak’ar “Gaskiya Mugunyar Magana” ta Alhaji muhammadu Sambo Wali Basakkwace” Sokoto: Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo.

 

Bunza, A.M. (2000). A Dad’e Ana Yi Sai Gaskiya: Laluben Gurbin

Gaskiya Cikin Adabin Hausa,” Mukala: Sokoto: Jami’ar usmanu ‘Danfodiyo.

 

Burji, B.S. (1997). Gaskiya Nagartar Namiji, Kaduna: Baraka Press.

 

Dangambo, A. (1984). Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga

Rayuwar Hausawa, Kano: triumph Publishing Co.

 

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa,

Edinburgh: University Press.

 

Muhammed, I. (1996). “Gaskiya Da Raha A Cikin Littafin Ruwan

Bagaja, Sharhin Ciki da waje” Kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.

 

Muktar, D. (1983). In Za Ka Fad’i Fad’i Gaskiya, Zari’a: Huda-Huda

Publishing Company.

 

Mustapha, S. (2003). “Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”. Kundin

MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo.

 

Skinner, N. (1971). Realism and Fantasy in Hausa Literature, in MAN.

 

Umar, M.B. (1987). Dangantakar Adabin Baka Da Al’adun Gargajiya, Na

Hausawa, Kano: Triumph.

 

4 comments: