Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Harshen Rubuce-Rubucen Hausa A Jikin Motoci

Daga

Nazir Ibrahim Abbas
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto
email: ibrahimabbasnazir@gmail.com
Gsm:  +2348060431934

Gabatarwa
Harshe yana da muhimmanci a cikin al’umma. Kowace huld’a da d’an’adam zai yi da harshe yake yin ta. Mutum kan bayyana tunaninsa da harshensa ko dai ta hanyar furta sautuka don yin magana ko kuma ta hanyar rubuta abun da yake buk’ata. Wannan mak’ala mai suna ‘Nazarin harshen rubuce-rubuce a jikin motoci’, za ta yi nazarin wasu rubuce-rubuce ne da ake yi a jikin motocin haya. Wad’annan rubuce-rubucen kuwa sun yi tasiri sosai a zukatan direbobi ta yadda da wuya ka ga babbar motar d’aukar kaya ko kiya-kiya ba ta d’auke da shi. Irin wad’annan rubuce-rubucen sun zama ruwan dare. Daga bayanan da na tattara, kowane direba kan rubuta abin da ke cikin ransa ko abin da yake sha’awa. Sai dai na lura da rubuce-rubucen sun k’unshi karin magana da habaici ko kirari da kuma wasu zantukan hikima. Akwai kuma wad’anda suka shafi addini, kamar addu’o’i da ayoyin Al’k’urani da Hadisai da ma wasu zantuka da ke nuna tawakkali.

1.1 Ma’anar Harshe


Masana da dama sun bayar da ma’anar harshe. Harshe a tak’aice hanya ce ta sadarwar d’an Adam wadda yake bayyana duk wani abu da ke cikin zuciyarsa ko tunaninsa ta hanyar magana, wanda kuma shi ne babban abun da ya bambanta shi da dabba. Harshe kan bayyana mutum ta fuskar asalinsa da addininsa da tunaninsa da al’adunsa da k’abilarsa da ma duk wani abu da ya shafe shi. Domin kuwa, da harshe ne mutum yake duk wata sadarwa wadda yake buk’ata a rayuwarsa. Ta hanyar harshe ne muke fahimtar junanmu da kuma al’ummar da muke ciki da wad’anda duk muke huld’a da su.

1.2 Tsakanin Harshe da Al’umma


Al’umma tana nufin wasu gungun mutane da ke zaune wuri d’aya. Wad’annan mutane kuma suna iya zama tare dalilin dangantaka ko muhalli ko zumunta ko al’ada ko addini ko kuma don suna amfani da harshe d’aya.

Al’umma kuwa, ba za ta had’u ba sai tare da cud’anya ta huld’a tsakanin mutane. Ita kuwa huld’ar ba za ta yiwu ba sai da sadarwa. Sadarwar nan kuwa, da harshe ake yin ta. A kan haka za mu fahimci cewa babu wani al’amari da zai gudana a cikin al’umma ba tare da harshe ba. Da harshe al’umma ke gudanar da duk wasu harkokinsu na rayuwa da zamantakewa da addini da kasuwanci da ilimi.

Kasancewar harshe hanyar sadarwa, shi ne makamin da ke bayyana al’adar mutum. Sa’arnan da shi ne mutum ke bayyana irin fahimtarsa da duniya. Bugu da k’ari, da harshe ne mutum ke bayyana al’adarsa da kuma yad’a ta ga sauran al’umma. Wad’annan rubuce-rubuce da direbobi ke yi a jikin motocinsu, wasu al’amurra ne da suka shafi imani da al’ada da ra’ayoyi da fahimtar su a harkokin duniya. Domin kuwa, kowane mutum da irin tunaninsa na rayuwa. Wannan kuwa, a bayyane yake  a cikin wad’annan rubuce-rubucen.

Alfanda (2008: 17-18) ta bayyana cewa daga cikin irin wad’annan rubuce-rubucen akwai wad’anda suka na inkiya da tunasarwa da wa’azantar da al’umma. Bugu da k’ari ta kawo nau’o’in rubuce-rubucen da ake samu a jikin rukunin motoci daban-daban da suka had’a da kiya-kiya da taksi da takai da tanka da kuma a daidaita sahu. Daga k’arshe ta yi nazarin nahawun rubuce-rubucen a jikin motocin haya a birnin Kano.

1.3 Rubuce-Rubucen Hausa a Jikin Motoci

Harshe hanya ce ta sadarwa ko dai ta hanyar magana (furuci) ko kuma ta hanyar rubutu. A nawa hasashe, irin wad’annan rubuce-rubuce da ake yi a jikin motoci sun dad’e a k’asar Hausa amma ba su yad’u ba, sai bayan da aka sami yawaitar motoci na haya da iya rubutu da karatun Hausa a cikin al’umma, musammam tsakanin direbobin tasha.

Bunk’asar sana’ar tuk’i da tashoshin mota a k’asar Hausa da kuma cud’anyar direbobi da masu motocin hayar, da kuma wasu al’amurra da suka faru gare su a rayuwa, da imani ko addininsu, sun taimaka wajen samarwa da bunk’asar irin wad’annan rubuce-rubuce a motocin nasu. Wani lokaci ma siffa ko yanayin mota yana tasiri ga irin sak’on da ake rubutawa a jikinta. Watak’ila tsohuwa ce tana tafiya a hankali, sai a rubuta wasu kalamai da ke nuna wa jama’a ka da fa a rene ta.

Daga cikin rubuce-rubucen da na tattara na kuma yi nazari a jikin motoci daban-daban da ake rubutawa a matsayin sak’onni ga jama’a akwai: (a) Karin magana, (b) salon magana/zantukan hikima, (c) kirari, (d) habaici, (e) rubuce-rubucen addini (wad’anda suka k’unshi ayoyin Al’k’ur’ani mai girma da fassarar hadisai da addu’o’i na neman tsari).

(a) Karin Magana

Yahaya da wasu (2001)sun bayyana karin magana da cewa: ‘Tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalak’a tare da bayar da ma’ana gamsasshiya mai fad’i, mai yalwa musamman idan aka yi bayani daki-daki’. Karin magana ke nan. Wasu daga cikin karin magana da ake rubutawa a jikin motoci, sun had’a da:

Bayan wuya....

Kowa ya sha kid’a....

Hana wahala....

Dogara da Allah....

Wani hani ga Allah...

Mahak’urci....

Sabo da maza jari.

Hali abokin tafiya.

(b) Salon Magana/Zantukan Hikima

Salon magana da wasu zantukan hikima suna daga cikin abubuwan da direbobin haya ke rubutawa a jikin motocinsu. Wad’annan ‘yan zantuka ne masu ban sha’awa da jan hankalin mai karatu. Duk da yake direbobin su suka fi sanin ma’anoni da dalilan rubuta su, amma dai muna iya kallon su a wannan ma’auni. Wasu daga cikin irin wad’annan rubuce-rubucen da na tattara kuwa, su ne:

K’arshen ado likkafani.

Duniya ba ta da tabbas.

Mota bayan uwa ce kowa ya hau ta sai ya sauka.

Ba gwani.

Uwa maganin kukan d’anta.

Sai a hankali.

Dariya ba so ba.

Zaman duniya sai hak’uri.

Iya tafiya ya fi gudu.

Baki yana kashe kore.

Agwagwa da buje.

Abin sirri ne.

Ya yi daidai!

A kwana a tashi.

(c) Kirari

‘Dangambo (1984) ya bayyana cewa: ‘Akwai hikimar sarrafa harshe cikin take da kirari. Take da kirari ya k’unshi yabo da zuga ne. Cikin irin wannan yabo da zuga ne ake amfani da sarrafa harshe’. Saboda haka, muna iya cewa kirari yana nufin kod’a kai ko kuma zuga da tunzurawa domin k’ara k’aimi.

Direbobin motocin haya sukan yi amfani da wasu kalmomi da suke yi wa kansu kirari, su rubuta su a jikin motocinsu a matsayin sak’o ga duk mai iya karantawa. Daga cikin irin rubuce-rubucen da suka danganci kirari a jikin wasu motocin, akwai:

‘Dank’walisa.

Sai ‘Danmusa.

Sik’afa.

Jinnu alk’alumman tafiya.

Jikan Gwamma.

Ijaba.

Haske.

Adon matasa.

Sani ji da naka.

Rayuwa ce gayu.

Ga naku.

Dawanau.

A sasanta.

Mai jama’a.

(d) Habaici

Yahaya da wasu (2001) sun ce: ‘Habaici kalmomi ne da ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum. Shi ma zance ne na hikima da ake amfani da shi a yi da mutum, a kaikaice’.

‘Dangambo (1984) kuwa ya bayyana habaici cewa: ‘Magana ce mai ‘boyayyar manufa. Akan yi maganar da niyyar nufin wani abu ga wanda aka yi maganar domin sa. Amma shi habaici idan ba mutum ya san kan zance ba, ba kasafai ake gane wanda aka yi habaici dominsa ba’.

Don haka, habaici ke nan yana iya d’aukar ma’anar gugar zana ko shagu’ben wani, a kaikaice. Irin wannan ma, direbobin haya suna amfani da shi wajen isar da sak’on zuciyarsu ga al’umma ta hanyar rubutawa a jikin motocinsu. Daga cikin irin wad’annan rubuce-rubucen da na ci karo da su akwai:

Oho dai!

Kai dai ka ga mutum.

Akwai hisabi.

Akwai Allah.

Yara ku bi a hankali.

Halin mutum sai Allah.

Kai ma haka.

(e) Rubuce-Rubucen Addini

A wannan rukuni, ana samun rubuta ayoyin Al’k’ur’ani mai girma da Hausa da fassarar Hadisai da addu’o’i da duk wasu al’amurra da suka danganci addini ko imanin mutum. Wasu direbobin da na zanta da su, sun ce suna rubuta ayoyin da sunan Allah ne, domin neman tsari da kariya daga had’ari.

Irin wad’annan rubuce-rubucen Hausa kuwa, sun fi kowane rukuni yawa a jikin motoci. Wasu daga cikin motocin da na ci karo da su d’auke da rubuce-rubucen addini, sun had’a da:

Fad’i alheri....

Falak’i da Nasi.

Sai addu’a.

Baiwa sai Allah.

Allah gatan kowa.

Salati goma ga Annabi.

Allah ya tsare.

Mujahida.

Allah ya sa alheri.

Sai ta Allah.

Haka Allah ke so.

Komai na Allah ne.

Fad’i alheri ko ka yi shiru.

Iyaka na’abudu.

Wallahu hairun ma’in.

Alhamdulillahi.

Innallaha ma’asabirin.

San Allah.

Mota sai addu’a.

Ya Salam.

Ya Allah.

Haza’amrulla.

https://www.amsoshi.com/2017/09/27/gabatar-da-ke%c6%83a%c6%83%c6%83un-kalmomin-intanet-na-hausa-da-na-fulfulde/

Duka wad’annan, rubuce-rubuce ne da ke isar da sak’onni daban-daban na zukatan direbobi zuwa ga al’umma ta amfani da harshe. Wannan yana k’ara tabbatar mana da irin dangantakar da ke tsakanin al’umma da harshensu.

Kasancewar sana’ar direbobin ta ta’allak’a ne da tuk’a mota da zirga-zirga a ko’ina, kuma sun sha gwagwarmaya a cikin sana’ar, ina hasashen cewa wannan ne ya sa suke da sak’onni da dama da suke son isarwa ga al’umma, sai suka ga hanya mafi sauk’i ta yin hakan, ita ce ta rubuta irin wad’annan sak’onni a jikin motocinsu da harshensu na Hausa don sak’on ya isa ga al’umma a sauk’ak’e.

Wasu daga cikin direbobibin da na zanta da su, sun ce suna isar da sak’onni ne ta rubuce-rubucen a kan wasu al’amurra na hak’ik’a da suka faru a rayuwarsu, da suka yi daidai da zantukan. A ‘bangaren addu’a kuwa, sun ce suna yin rubuce-rubucen ne don neman tsari da kariya. Wasu kuwa suka ce suna rubutun ne ta la’akari da nau’i ko yanayin motarsu, wasu kuwa har way au suka ce suna rubuta kalaman ne domin yi wa kansu kirari ko kod’a kai, kuma da zarar an ji kirarin ko an ga motar, an san su ne.

1.5 Kammalawa


A wannan takarda, mun ga yadda harshe yake yawatawa a maganganun al’umma wanda da wuya a iya raba su. Kasancewar kowace al’umma tana da harshe, kuma da harshen nan take isar da duk wani sak’o da take buk’ata, mak’alar ta tattauna dangantakar harshe da al’umma ta la’akari da rubuce-rubucen da direbobin haya ke yi a jikin motocinsu. Bayan nazarin rubuce-rubucen a yanayin karin magana da salon magana ko zantukan hikima da kirari da habaici da wad’anda da suka danganci addini, mun fahimci tasirin wad’annan rubuce-rubucen a kan tunanin direbobin kansu da kuma tasirinsu a kan  ga al’ummar da ke karanta su..

Bugu da k’ari, mun fahimci irin wad’annan rubuce-rubucen, sak’onni ne da ke cike da falsafa da tunanin masu rubuta su (direbobi) a kan wasu al’amurra na rayuwarsu da kuma sana’arsu ta tuk’i. Babu shakka, rubuce-rubucen, sak’onni ne da ke bayyana al’ada da addini da imani da fahimtar direbobin a kan harkokin rayuwa, wad’anda suke isarwa ta harshensu. Rubuce-rubucen, ko shakka babu suna taimakawa wajen bunk’asa harshe da adabin Hausa.

Manazarta


Alfanda, A.A. 2008. ‘Rubuce-Rubuce  A Jikin Motocin Sufuri A Birnin Kano Da Kewaye:          Manufarsu da Matsayinsu Ga Al’umma’. Kundin Digirin Farko Sashen Koyar da        Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A.M. 2005. ‘Arashi shi gogi Bak’auye: (Nazarin Karin Maganan Arashi Da ke jikin          Motoci). Mak’alar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani. Sashen Koyar da Harsuna        Nijeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.

 

Dangambo, A. 1984. Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa.        Kano: Triumph Publishing Company, Ltd.

 

J.O. Ojo da Wasu 2005. Introduction to Sociolinguistics. Oyo: Lektay Publishers.

 

Madauci, I. da Wasu 1986. Hausa Customs. Zaria: NNPC.

 

Ndimele, O. 2007. Readings On Language. Port Harcourt: M & J Grand Orbit Communication    Ltd.

 

Samsom, U.A. 2001. ‘A Sociolinguistic Study of Selected Inscriptions on Vehicles’. M.A.           Thesis. Dept of English, ABU, Zaria.

 

Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media

Services.

 

Yahaya. I.Y. da Wasu. 2001. Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. 1-3. Ibadan: University Press.

 

Yule, G. 1997. The Study of Language: An Introduction. Great Britain: University Press.

 

Hira da Ummaru Direba, Tashar Kabuga (15 ga Oktoba, 2013).

 

Hira da Shehu Kaihi, Sokoto (1 ga Afrilu, 2013).

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.