Ticker

6/recent/ticker-posts

Gurbin Ilmi Ga Haɗin Kai Da Cigaban Al’umma

Zauro, Zauro Development Association (ZADA) da karrama wasu fitattun mutanenta, ranar Jumu’a 27 ga watan Disamba, 2013 a makarantar Dikko Aliyu Model Primary School, Zauro da ƙarfe goma na safe

Aliyu Muhammadu Bunza

Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya

Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina

Jahar Katsina, Nijeriya


Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai. Tsira da aminci su tabbata ga manzonSa Muhammadu ɗan Abdullahi (SAW) da iyalansa da sahabbansa da masu koyi da tafarkinsu.

Gabatarwa


Kowace al’umma da ci gaban magabatanta take bugun gaba. Magabata ba su da abin taƙama face alherin da suka shuka na baya na cin moriyarsa. Idan gaba ta yi kyau, ta gyara wa baya hanya nagartacciya. Rashin samun gabaci na gari ke haddasa wa baya doguwar masassara idan ba ta samu kyakkyawar kulawa ba, bakin wuta ya mutu a hannunta. To! Gudun haka ke sa, a koyaushe magabata suka hango baya na ƙwazo abin yabawa sukan shirya mata gagarumin buki na yi mata madalla irin wannan da muka hallara a yau. A mahangar addini da zamani, babu ci gaban da ya fi samun nagartaccen ilmi da zai ciyar da mai shi da al’ummarsa gaba. Naƙalin kafe ilmi a zuciya ya zauna daram! Shi ne ladabi da biyaya ga kogin da aka shawo shi, da masu tsaron kogin, da gabacin da kogin yake ƙarƙashinsa. Babu shakka, samun haka ya sa magabata cikin garin Zauro suka tara mu a yau mu shaidi taurarin garin Zauro a shekarar 2013.

Mene ne Ilmi?


Masana ilmin boko sun yi wa ilmi sanin damisar Bunu. A mafi rinjayen ra’ayoyinsu, sun fi fassara ilmi da fasahar “karatu da rubutu”. A ganin Shehu Usmanu ‘Danfodiyo, fahintar abu da naƙaltarsa da fasahar tantance daidansa da kuskurensa da dabarun rege barkwancinsa da yi masa kwanton ɓauna idan ya zo da burunsuwa, ilmi ne na haƙiƙa ko da yatsu sun kasa sarrafa alƙalami, zuciya ta kasa kiyaye rubutu. Na yi wannan tawili ne bisa ga faɗar Malam Usmanu ‘Danfodiyo na kiran wani Baduku Malami lokacin da suke tare da Malam Abdullahi a garin Magami. Idan muka auna waɗannan ma’anoni biyu muna iya harrarar su kamar haka:

“Ilmi shi ne sanin abu farin sani ba sanin tsoro ba, ba garaye-garaye ba, a kuma iya sarrafa shi gwargwadon basirar yadda aka san shi. A kiyaye shi a zuci ko da a mafarki ana iya rarrabe shi da waninsa. Ya lugudu a baki, leɓɓa da harshe su ƙware wurin furta shi da rera shi. Ya sarrafu a gaɓɓai, a koyaushe ya kasance hannu ya iya jiki ya saba. Ya tasirantu a jiki, ya zamo da motsi da rashin motsin mai shi karatu ne ga marashinsa. Idan karatu da rubutu suka haskaka a ciki, an yi tangam mai zuwa hajji ya gamu da Annabi (SAW).”

 

Idan aka yi katari da wannan ma’ana, to kwalliya ta biya kuɗin sabulu. A kowane gari aka samu mazaje masu wannan sifa garin ya tashi daga zama ƙauye ko da jiɓa ke hakincin garin. Garin duk da ya rasa ma’abota ilmi ƙauye ne. Sunan wayewar jama’ar da ke ciki ‘ƙauyanci’. Sunan yawansu ‘taron buwa’. Suna hankalinsu ‘haukan yaro’. Duk arziki da dukiyar da suka tara na masu ilmi ne domin farauta suka je da kulake, ba su da kare, ga shi sun tayar da gada da zomo, ga mai ilmi da ƙaton kare cikin bantsari, me zai wakana? Malam Ibrahim Tubali (Narambaɗa) ya ba da amsa:

Jagora: Banza sharanin maras kare

: Sai kuwwa

 

Yara: Sai ko wanda yak kasa

: Ya ce masa amshi rataya

 

Gindin: Ya ci maza ya kwan shina shire

: Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/kifi-na-ganin-ka-mai-jar-homa/

Mene ne Haɗin Kai?


Daga cikin maƙasudin taruwarmu a yau shi ne lalubo gudunmuwar ilmi ga ɗinke al’umma ta zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Haɗin kai ba yana nufin taruwanmu a nan, wuni ɗaya, zuciyarmu da manufofin na zaman ‘yan marina ba. Idan mun yi haka, mun yi haɗin kan kullummai cikin shalla, ɗan lalabe ɗaya ya zo da tankoliya, ba ya ganinsu, su ke ganinsa, amma ya ribace su. Haɗin kai kalma ce ta basira da falsafa ga tunanin Bahaushe.

A tunanin Bahaushe, ilmi a ƙirji yake amma rumbun adana shi a ƙwaƙwalwa yake. Za ka ji Bahaushe na cewa, na yi zucci-zuccin in yi abu kaza, amma ba zai ce, na yi ƙwaƙwalwa-ƙwaƙwalwar yin abu kaza ba. Ashe gaskiyar magabata da ke cewa, sai akwai kai wuya ke ciwo. Sun tabbatar muna jinin kai bai ƙetare wuya. Tabbas, ba don ɗaukar kaya kawai aka yi kai ba. Me ya sa ba ma cewa, haɗin baki ko haɗin zuciya ko haɗin ido ko haɗin hanci ba sai dai a ce: “Haɗin kai”? Dalili shi ne, fasahar da ke kimshe cikin ƙwaƙwalwa wadda ƙashin kai da fatar kai suke lulluɓe, ita ake son ta kusanci juna sai ra’ayi ya zama abu ɗaya a yi abubuwa da manufa ɗaya. Idan kowa ya ce, dahuwarsa ta ishe shi, ya sa gaba inda yake so. To fa! Akwai ranar ƙin dillanci, ranar da wayon mai wayo na son agaji. Ƙarfin majiyi ƙarfi ana buƙatar mataimaka. Tsoron irin wannan ranar da ba a san ranar da za ta zo ba ake neman haɗin kai domin a dace da hasashen Baba Wazirin Gwandu Alhaji Malam Umaru Nasarawa da yake cewa:

Kwaɗ ɗauki kaya sun fi ƙarfinai ga kai,

Yaf fara hanya tabbata masa ba shi kai,

Tafiya kaɗanna shi kai shi ɗora taƙaitaƙai,

Ko dai shi yas in ko shi faɗi su hau shi.

(Gargaɗi ga abokai)

 

Ai makaɗa Gambo ya yi irin wannan hasashe da:

 

Jagora: Komi aka yi in babu ceto

: Ana wahala ko ba a mace ba.

(Waƙar Bawa Makau a garin Gumi).

 

Muradin Haɗin Kai A Fagen Ilmi


A kowane fage na rayuwa ana buƙatar haɗin kai amma a fagen ilmi an fi. A fagen ilmi, haɗin kai shi ne daidaituwa ga abin da yake tabbas na lalura a yi masa tarnaƙi, da yin talala ga abin da yaƙe ƙila-wa-ƙala. Dubi yadda maƙera suka daidaitu a kan amfani da masaba wajen dukan ƙarfe, da zugazugi wajen turara wuta, da awartaki wajen tsamo gasasshen farshi. Me ya sa masunta suka yi ittifaƙi ga ƙaƙe ga iyon tsaye, gora a iyon kwance, makarmana a bakin gora, hilahili a tuƙin zaune, kala a tuƙin tsaye? Abin da duk ya ba manoma fasahar tausa na ramin shuka, sungumi a shuka, kwasa a noma, gatari a sara, barandami a sassabe, kwando da mangala ga jidar taki, shi ne muke ce wa “haɗin kan ilmi”. Babu wanda zai ce ya san ranar da aka yi wannan “haɗin kan” amma kowa ya tashi haka ya tarar, ya yi ɗa’a, ya bi, haka na baya za su yi. Idan haka ne, ƙalubalen da ke gare mu ga waɗanda za mu karrama a Zauro yau shi ne:

 

1.     i) Su yi amfani da karrama su da aka yi musu, su taimaka wa wasu na ƙasa su taso, kowa arziƙinsa zai ci, bai cinye na wani. Ka da ku manta, rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

 

2.     ii) Su yi amfani da ilminsu su ƙirƙiro abubuwan cigaba da za su hana wa jama’ar garin Zauro maraici da muzanta a farfajiyar jahar Kabi da tarayyar Nijeriya. Ku tuna samunku a garin Zauro tsintuwar guru cikin suɗi ne.

 


iii)     Haƙiƙa tinƙaho da ilmi ko muƙami a yi hasadar juna, da doro, da gwalo, ga wanda aka ba tazara tsohon yayi ne. Ku bari biyayyarku, da ƙasƙantar da kanku, ya ba wasu sha’awar zama irin ku. Haba! Kwana nawa loma ke yi a baki? Ai duk mai hankali ya san, ba a san tabkin da ke makara da ruwa ba.

 

1.     iv) Ku yi tsayin daka, ku yi wa jahilci ƙofar raggo. Ku yi wa ƙabilance rub-da-ciki. Ku yi wa hasada taron dangi. Ku sa mai tsegumi zamowa bebe. Ku tabbata wa zaman banza da shashanci da lalaci ba su da gidan gado a Zauro. Mun san Zauro a jiya, ga mu cikin Zauro ta yau, ta gobe Allah masani. Don haka, ku sani ba don kifin da ya wuce akan yi saba ba, don mai shirin komowa. Ku tambayi kabawa ƙarin bayani.

 

2.     v) A tsarin haɗin kan ilmi, dole shugaba ne jagora, ko an fi shi ilmi, ko muƙami, ko ƙarfin jiki, ko na aljihu, ko na siyasa. Biyayya gare shi ita kaɗai ce tafarkin ci gaba. Kada ɗan karatunmu, da ‘yar kujerar da muke a kai ko ɗan jallin da muka riƙa, su nuna mana rena gabaci da tozarta shi. Masu barkataccen tunanin cewa, girma ya kawo gabaci banza ne, Malam Ibrahim Tubali ya yi muƙabala da su kamar haka:

 


 

Jagora: Ga abu nan a faɗi

Yara  : Babu mai faɗi sai ƙus-ƙus-ƙus akai da shi.

 

Jagora: Wa ka faɗi?

Yara  : Kai ɗan baka faɗi.

 

Jagora: Wai baya ka ƙwazon tunkuɗe gaba

Yara  : Shi Allah ba yarda ya kai

: Mai sharri shi ɗai yake biya.

 

Jagora: Kai tashi biri tsohon maɓannaci

Yara  : Karen ɓuki bai ɗan shawararka ba

: Shi maganar giwa shika biya.

 

Yara  : Ku ce wa biri, “duk dabbar da ac

: Cikin daji giwa taka biya”

 

Gindi: Ya ci maza ya kwan shina shire

: Gamda’aren sarkin Tudu Alu.

 

Idan ilmi ya nuna maka wulaƙanta mutane da cin zarafinsu ya mai da ka biri maɓannaci. Idan kujerarka ta ruɗe ka ga raina mutane da yin banza da su, ka zama karen ɓuki, abokin shawarar biri. Haƙiƙa, al’umma kamar zubin dabbobi suke a dawa, jagoransu “giwa” in sun rasa ta sai ragaita. Mu taka sannu, mu yi biyayya ga gabaci, wanda duk bai bi ba, ba mai bin sa.

Taron Dangi


Da mutanen Zauro ba su yi tunanin haɗa kansu ba su kira wnanan taro, nasarar da waɗannan taurari suka ci za ta kasance, sussuka ɗaka shiƙa ɗaka, ruwa shu guga shu. Tunanin a haɗa kai, a yi wannan taro, ba na mutum ɗaya ba ne. Don haka, tunanin a samu haɗin kai na dukkanin jama’ar Zauro na kowane mutumin Zauro ne a ko’ina yake. Ko ba a faɗa ba, kuna cike da farin cikin samun matasan Zauro da digirin Ph.D da babbar ɗamarar gidan soja da kowa ke son ya gani a garinsu. Yaya za mu yi likkafa ta ci gaba? Yaya za mu agaza wa masu hazaƙar da muke da su a garinmu? Wane mataki za mu ba maƙwabta mamaki su yi ɗokin koyi da garin Zauro? A ɗan nawa Babunjen tunani:

 

1.     Masu hannu da shuni su buɗe asusu na musamman na tallafa wa haziƙan yara haifen Zauro zuwa karatun digiri da babban digirin MA da PhD. Wannan wani adashi ne da ranar kwasarsa ba za a yi adashin kurma ba.

 

2.     Babu laifi a samu makaranta ɗaya ta firamare ɗaya ta sakandare a garin Zauro da Zaurawa za su zuba jarinsu na wuri da basira a raya su gadan-gadan. A sama musu kayan aiki na a zo a gani. Malamai son kowa ƙin wanda ya rasa. A ba su kulawar shekarar biyar soma-taɓi, ku gani in Kabawa da Sakkwatawa ba su fara kamun gidajen haya na sa ‘ya’yansu makarantun Zauro ba. Ai mai maɗi ke talla! Mai zuma ido yake sa wa.

3. Dukkanin ‘yan Zauro masu koyarwa a manyan makarantu, da fitattun ‘yan boko, a ba su darusan da su za koya wa ‘ya’yanku a ƙalla sau ɗaya a wata. Da yin haka, maƙwabtanmu suka tsere mu ga ilmin boko da suke yi muna kallon hadarin kaji cikin ƙasarmu ta gado. Don me ba a fi mu tsawo ba, ake yi muna kuri da taƙama?

 

In ɓera da Sata ko Daddawa da Wari


Matsalolin da ƙananan hukumominmu da jaharmu da ƙasarmu ke fama da su a yau ta fuskar ilmi shi ne haihuwan guzuma ɗa kwance uwa kwance. An tura matasa sun je karatu tun a firamare da makarantun da ke gaba da su. Sun je manyan makarantu, sun karɓo takardun shaidar kammala karatu da yabo mai kyau, sun dawo gida jiran gawon shanu babu aikin yi, babu jarin sana’a. An kashe wa yara da iyayensu rahowar ɗaka ba a gina musu ta waje ba. An hana wa yaro koyon noma da aikin ƙarfi, an shagwaɓa shi, an hana masa more karatun da ya yi. Wannan shi ne musabbabin samun fanɗararrun yara kangararru, ‘yan shaye-shaye, ‘yan bangar siyasa ga su nan dai. Hausawa sun ce, kowa ya faɗi kansa yake yi wa nishi. Me zai hana mu yi tunanin:

1. Ƙirƙiro wasu hanyoyin da yaranmu za su samu abin sa wa bakin salati maimakon tsayi jiran aikin da ba ya da ranar samuwa?

2.     Mu taimaka ga sama wa yara uku (a ƙalla) kowace shekara da kyauta ta musamman a kan hazaƙar da suka yi a karatunsu da jari babban wanda zai ba saura sha’awar zama zakara a shekarunsu.

3. A yi tsaye ganin matasa masu ilmi sun more wa duk wata kafa da hukuma ta buɗa domin wanda ke kusa ga wuta shi ya kamata ya fi kowa jin zafinta.

4. A zaɓe manyan ‘yan boko na Zauro kowanensu a yi masa kalangu da matasan da suka kammala karatunsu lafiya lau a ƙalla guda uku, ya tabbata ya sama musu aikin yi a hukuma. Idan kowa ya ce daga ɗansa sai ƙanen matarsa, marayu da marasa galihu fa?

5. Zaluncin da muke yi na saka ‘ya’yanmu da matanmu cikin bococin albashin gwamnati ana biyansu kuɗin iska shi ya haifar da matsalolin rashin tsaro da muke ciki a yau. Wanda ba ya da, ba ya da dabara, kuma a wurinsa komai lauje ya kama haki ne.

Zama Lafiya Ya fi Zama ‘Dan Sarki


Amfanin ilminmu na addini da boko shi ne, ya ba mu haɗin kai na fahimtar juna, da ciyar da garinmu gaba. Bambance-bambancenmu na Mazhabobi da ‘Dariƙoƙi da Ƙungiyoyi da Fahimtoci ka da mu mayar da su wani asusu da muke laɓewa gare shi na tsutsar jinin muridanmu da sunan addini. Ka da mu yi amfani da su wajen nisantar da masu imani da junansu domin biyan buƙatocinmu. Mu daina amfani da su a fagen siyasa cikin rigar addini domin cika muƙamuƙƙanmu da gyaran cefanenmu. Mu nisanci buɗe wa maƙiyanmu kafa ta yi muna kan mai uwa da wabi da sunan ta’addancin da aka ƙirƙiro muna. Ya zama dole, mu sa wa masu wa’azinmu takunkumi na cin zarafin juna, da gina ƙiyayye a zukatan mabiya, da jefan juna da ƙazaffan da kan iya bai wa maƙiyanmu damar shigowa cikinmu su yi muna fitsari a kaburan kakanninmu da masalatanmu.

A halin da ƙasarmu take ciki yau (2013/2014) idan ba mu yi amfani da ilminmu muka ƙwato ‘yancinmu ba, ilminmu bai amfane mu ba. Don me abokanmu na ƙasa a kowane salo na siyasa addininsu ne fatinsu, mu ko fatinmu na addininmu? Me ya sa sai ana cikin fafitikar siyasa kumallon bambance-bambancen aƙidojinmu ke zaburowa? Wace musibar yunwar abin duniya ke damunmu mu sayar da ‘yancinmu da addininmu da ‘yankinmu don tsarin da ba a taɓa samun yardar Allah ta hanyarsa ba? Me ya sa addininmu bai taɓa samun gata a ƙarƙashin kujerinmu? Me ya sa muka fi kowa tsoron hasarar kujera da bushewar aljihu da faɗuwa zaɓe? Me ya sa rayuwarmu ta fi ta kowa arha? Jininmu ya fi na kowa sauƙin zubarwa? Sunanmu ya fi na kowa ɓaci ga abin da aka yi taron dangi a kansa? Na tabbata kun fi ni hankalin gano abin da nake nufi don haka ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Idan muka yi zaune, muka sake baki da sunan wata jam’iyya, aka ci wa addininmu mutunci, mu saurari gyaran maƙeri daga mai addinin. Ai sakamakon ne aka ɗan sunsuna muna aka mayar da mu baƙin haure cikin ƙasarmu ta gado.

Naɗewa


Bisa ga albarkar ilmi da Allah Ya albarkaci magabatanmu da shi, suka ɗebe wa kansu takaici da wulaƙanci ga mulkin Nasara. Mu muka fara kafa tsarin da ya gagari rusawa har ya zuwa yau. Dubarun yaƙin kakaninmu ya rinjayi na Nasara, karo uku suna kwasan kashinsu ga hannun zuwa barikokinsu. Mai musun haka, ya waiwayi kundin tarihin Satiru da Ningi da Haɗeja da Bussa da Yawuri da Kuryar Dabo, magabatanmu ba su sa ido aka yi musu yadda ake yi muna a yanzu ba. Tilas, kowane ɗan boko ya yi amfnai da kujerarsa wajen kare muna addininmu da al’adunmu da ‘yancinmu. ‘yan kasuwanmu su ƙwato muna haƙƙinmu a fagen kasuwanci. Malamanmu da matasanmu da ma’aikatan tsaronmu ga saƙon malaman Satiru ga Turawan mulkin mallaka, 1906:

Marafa ya daɗe bai zaka ba,

Waziri ya daɗe bai zaka ba,

Balle Nasara mai ɗan wando,

Babban mutum da wandon yara,

Ku sa kiɗi mazaizai mu gani

Ko can gida faɗa mun ka sani,

Ba mui san gudu ba sai dai a mutu!

Ko an kashe mu babu hasara,

In mun kashe su sun yi hasara,

Ko yanzu mun kashe Hillere.

Post a Comment

0 Comments