Ticker

6/recent/ticker-posts

Bamaguje Da Dan Akuya: Kauna Ko Kiyayya?

Departmental Seminar Series 2008, Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, M. B. 2346, Sokoto, Nigeria.

www.amsoshi.com

BAMAGUJE DA ƊAN AKUYA: ZARGI KO ƘIYAYYA?

Daga

Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan (Ph.D)
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
e-mail: ibrasskg@gmail.com
Tel: 0803 6153 050

GABATARWA

A rayuwa ta zahiri, son abu na sa a yawaita mu’amala da shi. Ƙiyayya kuma na iya sa rabuwa da abu kai tsaye. Misali, son da Fulani ke yi wa shanu dole kan sa a rabu. Haka kuma rashin ƙaunar da ke takanin ’yan Adam da maciji kan sa nan-da-nan ƙoƙarin kisa ya biyo baya da zarar an haɗu. Maƙasudin wannan muƙala shi ne duban irin tasirin da ke ga ɗan akuya ga Bamaguje musamman a lamurran da suka shafi matakan rayuwarsu na aure da haihuwa da mutuwa. Ganin cewa kusan duk shagalin da Bamaguje zai aiwatar sai rayukan ’yan awaki sun salwanta, shin ƙauna ce ko ƙiyayya ke takanin su?

WANE NE BAMAGUJE


Bamaguje a ta
ƙaice kuma a idon Bahaushe (Musulmi) wanda shi ya ba shi sunan yana nufin: Bahaushen asali ta gefen uwa da uba, wanda ba Musulmi ba, mai bin addini da al’adun gargajiya na Hausawa musamman waɗanda suka sa’ba wa addinin Musulunci. Kalma Bamaguje kalma ce da ke nuna jinsin namiji na kalmar Maguzawa. Mace kuma a kira ta Bamagujiya ko Bamaguza.

 
MENE NE ƊAN AKUYA

A Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano an bayar da ma’anar akuya da:

Ɗaya daga cikin dabbobin gida mai ƙaho da gajeriyar jela, ɗage a tankware, ana kuma cin namanta, ana shan nononta.”

Ɗan akuya shi ne jinsin namiji na dabbar da ake kira akuya kamar yadda ma’anar da ta gabata ta bayyana. Wasu sun fi sanin ɗan akuya da suna Bunsuru. Wannan ne ma ya sa a Ƙamusun har wa yau aka bayar da ma’ana kalmar Bunsuru ta hanyar kallon wasu siffofi ko ɗali’u nasa da cewa:

Ɗan akuya wanda ya riƙa yana wari kuma ba a dandaƙshi ba yana bin mata yana bututu.” 

WAIWAYEN MU’AMALAR BAMAGUJE DA ƊAN AKUYA A MATAKAN RAYUWA


AURE


Kusan a ce babu wani mataki na hidimar
ƙulla auren Maguzawa ko gudanar da bukin auren da ba a kawo ɗan akuya  a ciki. Misali:

-     Lokacin da saurayi ya ga budurwa yana so,
ɗan akuya  zai kama ya sayar don ya yi mata kari in tana rawa ko toshi idan ya je zance.

-     Idan bukin dangin budurwa ya taso,
ɗan akuya saurayi kan bayar a matsayin gudunmuwa.

-     Idan saurayi ya kai gayya gonar iyayen budurwar da yake so ubanta yakan ba masu gayyar
ɗan akuya a matsayin tukuici.

-     Idan budurwa ta gayyaci wanzami ya yi mata shasshawa,
ɗan akuya  saurayinta zai ba wanzami a matsayin sallama.

-     Idan za a yi wa budurwa baiko,
ɗan akuya  iyeyenta za su yanka don su tari baƙin.

-     Idan amarya na zaman lalle, duk matar da ta
ɗauki amarya sai ta yanka wa ‘yanmatan amarya ɗan akuya.

-     Idan za a
ɗaura auren Maguzawa, sai iyayen miji sun zo da ’yan awaki na tsafi ko dukiyar aure ko namaraici ko riƙon gida da sauran su (gwargwadon tanadin da al’ada ta yi).

-     Bayan
ɗaurin auren Maguzawa, akan tafi wurin tsafin da ake bauta don neman amincewa. A nan ma ɗan akuya ake yanka wa tsafin ya sha jini.

-     Idan za a yi al’adar Kai bante ga amarya, wasu
ɗan akuya ake tsafin da shi.

-     Idan za a kai garar amarya daga gidan iyayenta wasu Maguzawan sukan yanka a
ƙalla ’yan awaki ashirin (20) a soye wa amarya da ango su ta cin abin su.

-     Bayan an
ƙare buki, idan za a salami ’yanmatan amarya, ɗan akuya ake yanka musu.

-     A lokacin da mace ke zaman aure, hatsin da ta noma ’yan waki take saye ta yi sabgar dangi.

HAIHUWA


-     Idan mace ta haihu akan yanka mata
ɗan akuya  wai don ta mayar da jinin da ta rasa.

-     Idan aka zo ranar shan
ƙauri, wasu ɗan akuya  suke yankawa.

-     A wurin bukin suna wasu Maguzawan kakan jinjiri ’yan awaki yake yankwa.

-     Idan mace ta
ƙare jego ta tafi ganin gida wurin iyayenta a lokacin da za ta dawo gidan

miji akan yi mata gara har da
ɗan akuya.

-     A lokacin da aka yi wa jinjiri tsagar gado, wasu sukan sallami wanzanim da
ɗan akuya.

-     A ranar fiton
ɗan shayi, ’yan awaki ake yankawa wurin bukin, a kuma sallami  wanzami da makaɗa da ’yan waki.

MUTUWA


-     Ana birne gawar mamaci, za a yi al’adar biye gawa,
ɗan akuya ake yankawa a saman kushewar.

-     Idan za a zo gaisuwar mamaci da
ɗan akuya ake zuwa, ko dai a yanka a kan kushewar ko kuma a ajiye a yi sauran shagulgulan da su.

-     Ana kiran bukin kwana arba’in da mutuwar Bamaguje bukin ’yan awaki saboda akan yanka fiye da awaki
ɗari.

-     Idan za a sallami maka
ɗin dundufa da ya kwana yana rafsar ganga a wannan bukin ɗan akuya akan ba shi.

-     Wajen bukin fita takabar matan mamaci dole ne sai matan mamacin sun tanadi ’yan wakin da za su sake a fage maza su yi wasoso.

-     A bukin cika shekara na mutuwar Bamaguje ba a cin tsafaffen tuwon noma ba tare da an kawo gasasshen
ɗan akuya ba.

 
KAMMALAWA


Ganin yadda dangantakar Bamaguje da
ɗan akuya ta zama kamar ta tsoka ta jini, wane dalili za a ce ya kawo haka?

-    
Ɗan akuya ƙaramar dabba ce. A al’adance ya fi daɗi da rashin sauri guna.

-     Abu ne mai sau
ƙi a ce a nemo ɗan akuya kasancewar sa dabbar gida ba kamar biri ko kura ko gada ba.

-     Kowane gida ana iya kiwon
ɗan akuya saboda sauƙin  lamari. Ba sai an turke ba.

-     Yanayin muhalin Maguawa ya tanadi irin abincin da ’yan awaki ke so da kuma yanayin da ya dace da rayuwarsu.

-     Karkata ga
ɗan akuya (bunsuru) ba akuya ba bai rasa nasaba da fifikon jinsin namiji a kan mace a al’adance.

Wa
ɗannan dalilai su suka sa a iya cewa, yanka ɗan akuya  ga Bamaguje ba ƙiyayya ba ce sai don sauƙin biyan bukata kawai. Wani abin jawo hankali dangane da amfani da ɗan akuya wurin bukukuwa da tsafe-tsafe na gargajiya musamman a nahiyar Afrika abu ne da ya zama ruwan dare. Wannan ya sa na ɗauki alwashin zurfafa bincike domin tabbatar da haka. Hausawa na cewa, “ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba.

MANAZARTA


Abdullahi I. S. S. (2008) “Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye A Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa

Na Aure da Haihuwa da Mutuwa” Kundin Digiri na uku (PhD) Jami’ar Usmanu 
Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Abu Mainasara, (1985) “Al’adun Aure da Canje-canjensu a Katsina,” Kundin Digirin farko (B.A. Hausa),  Jami’ar Sakkwato.

Adamu, M.  (1976), “The Spread of Hausa Culture in West Africa 1700 – 1900” Savanna No 5 Vol. 1, A  Journal of the Environmental and Social Sciences.  Published at  Ahmadu Bello University, Zaria.

Adamu,  M.  (1980) “The Hausa and The Other People f Northern Nigeria, 1200-1600 A. D.” Chapter 11 in UNESCO’s History of Africa, Vol. IV.

Akodu, A. (2001), Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications. Gaskiya Corporation Limited. Zariya – Nigeria.

Alhassan, H. da Sauransu (1982), Zaman  Hausawa (Babu Ma
ɗaba’a).

Bunza, A. M. (2006) Gadon Fe
ɗe Al’ada  Tiwal Nig. Ltd Lagos.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeria Jami’ar Bayero, Kano (2006) 
Ƙamusun Hausa,  Ahmadu Bello University Press Zaria.

Elias, T. O. (1957) “Hausa Marriage” In Nigeria , A Quarterly Magazine  of General  Interest No 53 published by the  Federal Government of Nigeria, Exhibition Centre, Marina, Lagos.

Ferguson, J. (1970) The Yorubas of Nigeria. The Open University Press, London.

Fletcher, D. C. (1929) “The Kai-na-Fara.” Extract from Re-assessment  Report on ’Yan
ɗaka District, Katsina Emirate, Zaria Province. M. P. No K. 8833 National Archives and Monuments, Kaduna.

Furniss, G. (1999), Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, Edinburgh University Press, London.

Gennep, A. V. (1960) The Rites of Passage The University of Chicago Press, USA.

Greenberg,  J. (1946) The Influence of Islam on a Sudanese Religion: Monographs of the American Ethnological Society. J. J. Augustin Publisher, New York.

Gwarjo, Y. T. da  wasu  (2005)  Aure a Jihar Katsina Hukumar BincikenTarihi Da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina,

Ibrahim, M.S. (1985), Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci, Cyclostyled Edition – Hausa Publications Centre – Zaria.

Ibrahim, M.S. (1982), “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero, Kano.

Kado, A.A. (1987), “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

Krusius, P. (1915), “Maguzawa” in: Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.

Lawal, A.T. (1986), “Al’adun Hausawa Jiya da Yau”, Kundin Digirin farko (B.A. Hausa) Jami’ar Sakkwato.

Madauci  I. da  wasu (1968) Hausa  customs Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

Mainasara, S. (2001), “Bautar Magiro A
Ƙasar Zamfara”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Mairukubta, H. (1999) “Jego da Reno a
Ƙasar Hausa: Tsokaci Kan Hausawan Kabi” Kundin digiri na  biyu (M. A.  Hausa),  Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Malumfashi, A. A. (1987) “Hausa Language Speech  Usage Norms: A Case Study of Maguzawa Society in Malumfashi Area” (B. A. Hausa Project), Bayero University, Kano.

Morel, E.D. (1968), Nigeria Its Peoples and Problems, Frank Cass and Company Limited London.

Mashi, B.U. (2001), “Maguzanci Da Zamananci: Nazari A Kan Al’adun Maguzawan Bula A Gundumar Mashi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Nyamwaya, D. and Parkin, D. (1987) Transformation of African Marriage. Manchester University Press, United Kingdom.

Ottenberg, P. and Simon (Ed.) (1960), Cultures and Ethics of Africa, H. Wolff Book Mfg.Co., Inc. U.S.A.

Safana, Y.B. (2001), “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Sallau, B. A. S. (2000) “Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a
Ƙasar Hausa.” Kundin digiri na biyu (M.A. Hausa) Jami’ar Bayero, Kano.

Saulawa, I.A. (1986), “Yanayi da Tsarin Al’adun Aure A
Ƙasar Katsina”. Kundin Digirin farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

Sufi, A. H. (2001) “Hanyar Kiran Maguzawa Zuwa Ga Addinin Musulunci.” Ma
ƙalar  da aka gabatar  a  taron Kwamitin Yaɗa Addinin Musulunci na Jihar  Kano.

Tambuwal, M.S. (2001), “Mutuwa A Idon Bahaushe: Nazari Daga Wasu Rubutattun
Ƙagaggun Labaran Hausa”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Travitt, L.  (1973) “Attitudes And Customs In Childbirth Amongst Hausa Women In Zaria  City,”  Savanna No 2 Vol. 2, A  Journal of the Environmental and Social Sciences Published at  Ahmadu Bello University, Zaria.

Tremearne, A. J.  N. (1913) Hausa Superstitions And Customs.  John Bale, Sons and Danielsson,  LTD Oxford.

Umar, M.B. (1980), Al’adun Haihuwa A
Ƙasar Hausa. Hausa Publications Centre Zaria.

Yahaya, I. Y.  da wasu editoci  (1982),  Studies  in Hausa Language, Literature and Culture: Procedings of the Second  International Conference, Centre for  the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Yusuf, A.B. (1986), “Wasannin Maguzawan Ƙasar Katsina”, Kundin Digirin farko, Jami’ar Sakkwato.

Post a Comment

3 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.