Ticker

6/recent/ticker-posts

Rahama Abdulmajid: Jarumar Jarumai Mata Marubuta

Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa na Biyu Kan Heroes And Heroines of Hausaland da Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya da Ilimin Kimiyyar Harsunan, Jamiar Jihar Kaduna ya shirya, a ranakun 3-5 ga watan Yuni, 2016.

Daga

Dr. Umar Aliyu Bunza
Sashen koyar Da Harsunan Nijeriya,
Tsangayar Fasaha Da Nazarin Musulunci,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07063532532
Ƙibďau: aliyubunzaumar@yahoo.com

Tsakure


Ciwon mace na mace ne! Mata jinsi ne da ke fama da matsaloli a zamantakewar al’umma. Wannan ya sa wasu marubuta mata suke faɗi-tashi da fitar da rubuce-rubuce domin yayata matsalolin da ke tarnaƙi ga rayuwar mata. Rahma Abdulmajid wata jaruma ce da ta yi fice ga wallafa ƙagaggun labarai da ke ƙunso matsalolin mata iri-iri. Ta rubuta littattafai masu yawa waɗanda wasu cikinsu suke nuna matsaloli iri-iri na jinsin mata. Manufar wannan maƙala ita ce shiga cikin wasu littattafan Rahma domin sharhin wasu matsalolin mata da ta yi wa fiɗa.

1.0 Gabatarwa


Mace mutum ce da Allah ya halitta domin namiji ya haɗu da ita ga ci gaban rayuwarsu. Allah ya yi ta mai rauni don haka ya sa namiji ya zan jagora gare ta, ya kuma taimaka mata zuwa ga kowane irin nasara. Wannan ya sa mace ta kasance amanar Allah babba ga hannun namiji ta hanyar kawo mata abinci, samar da muhalli da bayar da kariya da sauransu.
Duk da kasancewar mace ƙarƙashin kulawar namiji, mata da yawa sukan tsinci kansu cikin matsaloli da ke hana su sauke nauyin bautar da take ƙashin bayan da Allah ya halitta su dominta. Matsalolin mata, wani lokaci, sukan ginu daga yadda maza suka yi riƙon sakainar-kashi da haƙƙin da Allah ya ɗora musu, wani lokaci kuma matsalolin sukan taso daga gefen mata ta yadda suke jan ƙafa ga kiyaye iyakokin da Allah ya gindaya musu. Ta dalilin matsaloli daban-daban, mata da yawa sun rasa rayukansu, wasu suka haukace, wasu kuma suka faɗa fitintinun rayuwa masu yawa.
Adabi kafa ce da ake iya hangen kowane abu na al’umma ta kowane gefe. Matsalolin mata wani abu ne da ake ganinsa a cikin rassan adabin Hausa masu yawa kamar tatsuniya da karin magana da waƙa da sauransu. A shekarar 1933 aka fara samun rubutaccen ƙagaggen labarin Hausa wanda shi ma ya kasance wata taska da ake hangen kowane abu da ya shafi rayuwar al’umma. A shekarar 1978 mata suka fara shiga ƙaga rubutaccen labarin Hausa lokacin da Hafsat Abdulwahid ta yi nasarar gasar Kamfanin Buga Littafai Na Nijeriya Ta Arewa (NNPC) Zariya, da littafinta mai suna So Aljannar Duniya. Tun daga wannan lokaci sai mata suka sami wata kafa ta bayyana matsalolinsu domin a ji muryoyinsu cikin waɗannan mata har da Rahma Abdulmajid.
An haifi Rahma Abdulmajid a shekarar 1980. A shekarar 1996 Rahma ta fara rubuta ƙagaggen labari da wani littafi mai suna ‘Wa Ya Fi Kishi.’ Ciwon mace na mace ne! Rubuce-rubucen Rahma wata kafa ce muhimmiya ta haska matsalolin mata da kuma hanyoyin warware su. Idan aka yi nazarin adabin Rahma, sai a ga cewa, ta fi damuwa da mace da matsalolinta kama daga soyayya har zuwa aure. A gefe ɗaya, sai kuma takan damu da kawo hanyoyin da mace za ta ceci kanta, ta inganta rayuwarta ta kowane hali. Manufar wannan maƙala ita ce nazarin adabin Rahma da zimmar nuna ta a matsayin jarumar jarumai mata marubuta. Za a yi haka ne ta duba yadda ta kalli matsalolin mata cikin adabin nata, abin da ya sa adabinta ya yi fice, musamman ga mata. An fara da duba tarihinta a taƙaice, sannan aka juya akala zuwa duba matsalolin mata cikin adabin nata.

2.1 Taƙaitaccen Tarihin Rahma Abdulmajid


An haifi Rahma Abdulmajid a ranar 15 ga watan Afrilu na shekarar 1980. Sunan mahaifinta Abdulmajid ɗan asalin ƙasar Sudan. Ya shigo Nijeriya, ya zauna a Unguwar Agege cikin birnin Lagos a gida mai lamba 21 Isa S.T.F. Abdulmajid ya rasu a shekarar 1986, lokacin Rahma na ƙaramar yariya mai shekaru 6 a duniya. Kafin rasuwarsa ya haifi ‘ya’ya 22. A cikinsu akwai maza guda 11 da mata 11. Rahma ce auta a cikin ‘ya’yan nasa duka.
Rahma ta fara karatun Alƙur’ani mai tsarki a makarantar mahaifinta (gidansu) har zuwa shekarar 1989 lokacin da mahaifinta ya rasu. Wannan ya sa ta ci gaba da karatu a wata makaranta da ake kira Nibrasil Huda. A wannan makaranta ce Rahma ta faɗaɗa karatunta a fannonin ilmin Musulunci kamar Hadisi da Nahawu da Fiƙihu da sauransu.
Ta fannin ilmin boko, Rahma ta fara karatun boko tana ‘yar shekara goma sha ɗaya, wato shekarar 1991 a makarantar Keke Primary da ke unguwarsu. Haka kuma ta sami wata malama mai suna Latifa wadda suka yi shekara biyu tana ƙara koya mata karatu. Da ta kammala sai ta sami takardar shiga makarantar gaba da firamare mai suna Diary Farm. Daga baya aka yi mata sauyin karatu zuwa wata makarantar Arabiyya da boko mai suna Rahmatu Islamic School da ke Ikeja inda nan Rahma ta karɓi shaidar karatu na matakin farko. Daga nan ne ta zarce da karatun Larabci zalla a makarantar Ulmil Islamiyya.
A shekarar 2000 Rahma ta sami wani sauyi karatu zuwa Zariya inda a can ta kammala karatunta na shekara ɗaya a Kwalejin Jama’atu Nasrul Islam. Da ta kammala sai ta yi difiloma a ɓangaren shari’ar Musulunci har zuwa 2002 lokacin da ta kammala difiloma.
A wannan shekara (2002), Rahma ta sami gurbin ƙara karatu a Jami’ar Al’azhar da ke birnin Alƙahira na ƙasar Masar inda ta haɗa digirinta a fannin tarihi da al’adun duniya a shekarar 2007.
Aure yaƙin matai Rahma AbdulMajid ta yi aure a ranar Asabar sha ɗaya ga watan Nuwamba shekara ta dubu biyu da shida (11-11- 2006) da masoyinta mai suna Auwal Sa’ad. A daidai wannan lokaci, (2016), Rahma na da ‘ya’ya biyu mata: Maryam da Fatima. Malam Auwal Sa’ad mijin Rahma sojan Nijeriya ya rasu a ranar 10-11-2015 a can yankin Sambisa a ƙoƙarin sojojin Nijeriya da aka tara a jihar Borno domin yaƙar ƙungiyar Boko Haram wadda ta hana yankin zaman lafiya. Ya rasu a daidai lokacin da washegari zai cika shekara tara (9) da aurensa da Rahma AbdulMajid. Allah ya jiƙan sa, ya yi masa rahama, amin.
Rahma ta fara rubuta adabinta na Hausa a shekarar 1996 wato tana daf da cika shekara goma sha shidda (16). Littafin da ta fara rubutawa shi ne mai suna Wa Ya Fi Kishi wanda yake cikin juzu’i uku (1-3), aka kuma buga shi a shekarar 1996 daga maɗaba’ar Sauƙi Bookshop, Kano. Daga wannan lokaci zuwa yau, Rahma ta rubuta littattafan ƙagaggun labaran Hausa da ba su kasa 30 ba kan jigogin soyayya, faɗakarwa, tarihi, fafutukar ‘yancin mata da sauransu. Fitacce daga cikinsu wanda kuma aka fi jin sunan Rahma da shi, shi ne mai suna ‘Mace Mutum’ wanda ta wallafa a shekarar 2012, aka kuma buga shi a maɗaba’ar Iya Ruwa Publishers Kano.
Idan aka yi la’akari da littattafan Rahma, za a ga cewa, yawancinsu sun ƙunshi matsalolin rayuwar da mata suke faɗawa cikinsu. A lokaci ɗaya Rahma kan shirya wa wata mace gagarumar matsala wadda za ta jima cikin tarnaƙinta, sannan bayan wani lokaci sai ta ɓullo mata da mafita. Wannan na nuna, Rahma jaruma ce da ke yi wa mata hannunka-mai-sanda domin koda sun sami kansu cikin wata matsalar rayuwa, ya zan suna iya fitar da kansu cikin ruwan sanyi ba sai sun dogara ga namiji ba. Wani abu kuma shi ne, Rahma ta cika sanya namiji ya zan sila na matsala ga mace cikin adabinta. Haka kuma, wajen samar da mafita ga matsala, ta fi amfani da hikimar mata, a maimakon amfani da namiji a matsayin tsanin mafita ga mace.



3.1 Matsalolin Mata A Adabin Rahma


Matsala wani yanayi ne maras daɗi da mutum ke shiga a dalilin wani abu da ya aikata, ko aka aikata masa. Sau da yawa mata kan shiga matsaloli saboda wani dalili. Matsalolin mata da ke ƙunshe cikin adabin Rahma sun haɗa da kishi, soyayya, da aure da maraici, da jahilci da sauransu. Dukkan matsalolin kan haifar wa mata tarnaƙi da shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi da wani lokaci har yake sa wata mace rasa ranta.

3.1.1 Kishi


Kishi kumallon mata! Kishi wata sifa ce da mutum kan nuna ta hanyar harzuƙa da bayyana ɓacin ransa, saboda wani da yake so ko soyayya da shi, ya nuna sha’awarsa ga wani ko kuma wani ya nuna sha’awa gare shi. Tsananin son da mace ke yi wa mijinta ko neman keɓancewa zuwa ga mijinta ko wanda take son ta aura, da take nuna ƙauna, da kyakkyawar fata gare shi, tare kuma da nuna ƙiyayyarta ga duk wata da take son sa da aure ko kuma shi yake son ta da aure Bakura (2014: 5-6).
Kishi ga mace, shi ne jin haushi da ƙin jinin kusanci na so, ko mallaka ko tarayyar wata mace ga wani abu da take so, ko take tarayya da shi. Kishi sau da yawa ya kasance matsala ga wata mace har ya kai ta ga rasa sukuninta da ‘yancin walwalarta.
Rahma ta ɗauki kishi a matsayin wata babbar matsala, kuma barazana da ke dagula lamurran mata na yau da kullum. Wannan ya sa a wasu littattafanta ta kawo wasu mata da suka rungumi kishi, ya dabaibaye su da matsaloli masu yawa. Ga misali, littafin Wa Ya Fi Kishi wanda a ciki ta kawo labarin wata mata Binta da kishi ya yi sanadiyyar ciwon hanta gare ta. A cikin littafi na 2, Rahma ta kawo yadda Bintar ta bayyana kishi a matsayin silar shigarta matsalolin rayuwa inda take cewa:
Binta ta juyo suka fuskanci juna, haba ɗahir baka da godiyar Allah so kake na haɗiye ka? Wace irin ƙauna ce ban nuna maka ba? Duk abin da nake yi maka ina yi ne abu biyu, ƙauna da kishi gudun kada ka hango wata bayan, kada kai min munafinci kana tare da Nafisa tun ina tarairayarka, me ye dalilin juya maka baya da nai? Haba dai ɗahir ka cuce ni, ta ƙara fashewa da kuka, ɗahir ina cikin shagwaɓaka ka kawo min zancan ƙarin aure wanda har yanzu ban daina jin haushi ba amma na daure don maganar da kai min na cewa in ba na kyauta maka sona zai yi maka rauni ina cikin lallaɓawa, ashe kai cuta ta kake kada ka ɗauki alhakin wani ka ce shi ne ya gaya min, na je makaranta a nai mana gargaɗi amma hankalina na wurinka, na je wurin aikinka aka ce ka tafi gida, raina bai so na sauya shawaran zuwa J. S, in siyo abinci dan kada ya kasance kana gida kana jin yunwa, kuma zai ɗau lokaci ban ƙare abinci ba, duk da gajiya ta na tafi dan hidimarka, amma ɗahir dan cin amana na same ka a can da ido na ganka kuna riƙe da hannun juna kai da Nafisa, wannan shi ne abin da ya jawo min baƙin ciki, ƙunar hanta, taɓuwar hankali da kuma zuwan ‘yata ba rai wacce na ɗora rayuwata akanta, haba wace irin cuta ce ba ka yi min ba?’ Ta daɗa fashewa da kuka da gyaɗa kai. Wa Ya Fi Kishi 2? (shafi na 35-36).
Ashe kafin shigar kishi cikin zuciyar Binta, tana zaune lafiya, cikin ƙoshin lafiya da mijinta. Tana kowace irin kyautatawa gare shi. Daga lokacin da Binta ta sa kishi a zuciyarta, sai lamurranta suka sauya. Yau lafiya, gobe ciwo, musamman daga ranar da ta ga mijin nata da wata mai suna Nafisa wanda shi ne babban abin da ya hura wutar kishin zuciyarta. Nafisa wata ce da ke son ɗahir, amma shi ba ya kula ta. A wannan ranar da Binta ke maganar ganin su, ba riƙon hannun juna ne suka yi ba, ita Nafisar ce ta riƙo shi bayan ya gaya mata ba daɗi, ya juya zai tafi. Ba ta tsaye binciken komai ba, sai ta sa ciwon kishin cikin ranta. A hankali rashin lafiya ya ci ƙarfinta, aka kwantar da ita asibiti. Abu ya tsananta, amma ba a san mene ne dalili ba. Ranar da ɗadir ya gaya mata tsakaninsa da Nafisa, sai ta yi da-na-sani, ta ba shi haƙuri bisa zargin da ta yi masa masa cikin rashin sani, sannan zamansu ya koma daidai. Irin haka wasu mata da yawa suke faɗawa fitina saboda kishi maras dalili.
Shi ma littafin Ni Ma ‘Yata Ce 2, akwai matsalar kishi a cikinsa wanda wasu mata biyu suka nuna. Rahina mata ce ga Ma’amun, kuma ita ce mahaifiyar Rashida. Bayan mutuwar aurenta sai Ma’amun ya auri wata mai suna Amina. Ya ɗauki Rashida ya ba ta domin kula da karatunta da sauransu. Ita kuma Rahina ta auri wani mijin. Wata rana Rahina ta zo ganin Rashida, ta ji ‘yar ta kira Amina da kalmar momi. Wannan ya sa kishi ya motsa a zuciyarta. Ga yadda Rahma ta kawo bayanin:
Rahina ta amshi baƙuncin wasu yanayi da ba ta san da zuwansu ba, wanda a yayin da ƙwaƙwalwarta ta kasa kunne wajen jin ‘yarta na kiran wata mata Momi ba ita ba, sai ta fahimci baƙin cikin na so ya nuna gazawarta, da sauri ta shirya yaƙar yanayin ta hanyar dawo da ilahirin walwalarta ga Ma’amun da ke ba ta kujera (shafi na 27).
A wannan wuri, kishin Rahina shi ne damuwarta ga ‘yarta ta kira wata mata momi. Ba shakka, mace na kishin wata ta auri mijinta koda bayan rabuwar aurensu, haka kuma tana ƙin jinin zaman ‘yarta a hannun wata da tsohon mijinta ya aura. Irin haka ne ya sa kishin Rahina ya motsa jin yadda ‘yarta ta kira wata momi ba ita ba.
Ita kuma Amina matsalar kishi ya motsa mata ne lokacin da ta fito ta sami mijinta Ma’amun da tsohuwar matarsa cikin fara’a. Ga yadda marubuciyar ta kawo batun:
Amina wadda ta sanya dogon hijabi mai ruwan toka ta yi hakan ne da zaton Rahina ta zo da mijinta, amma da ta gan ta ita kaɗai da kuma kwalliyar da ta sha ita da kyawunta, sai ta ji dama ita ba hijabi ta sanya ba kwalliyarta ta caɓo, ba ta tsaya a nan ba, sai ta ji wutar kishi ta lulluɓe ta a yayin da ta ga mijinta da tsohuwar matarsa na rayuwa cikin fara’a (Shafi na 28).
Amina mace ce kyakkyawa, mai natsuwa, da ladabi ga mijinta Ma’amun. Ba ta zarginsa da komai a zamanzu, amma kishi ya motsa mata a lokaci guda da ta gan shi da tsohuwar matarsa Rahina. Yadda Ma’amun ya tarbi Rahina ba abin zargi ba ne, domin shi ta sama a falo, kuma ta shigo cikin yanayi na lumana bayan da ta yi sallama.
Idan aka dubi halin kishi da kowace mace ta nuna, ana fahimtar cewa, shi kishi wata matsala ce babba a rayuwar matan Hausawa wadda a lokuta da dama takan sanya su shiga damuwa da ba wani dalili ƙwaƙƙwara.

3.1.2 Aure


Aure yaƙin mata! Aure halartacciyar zamantakewa ce tsakanin namiji da mace. Aure shi ne wata yarjejeniya c eta zama tare tsakanin namiji da mace bisa wani tsari na addini ko al’ada (Adamu, 1998: 4). A al’ummar Hausawa, aure ya kasance wani muhimmin mataki na cikar kamala ga kowane mutum, namiji ko mace. Idan mutum ya yi aure, akan dube shi a matsayin wanda ya dace da mutuntawa, wani lokaci har ma abokin shawara. Wannan kan sa kowa, namiji da mace na son yin aure idan suka kai balaga, kuma suka sami abokin aure da hankali ya natsu da shi.
A lokuta da dama akan sami gittawar matsaloli cikin auren wasu mutane. Matsalolin aure na kasancewa na rashin samun haihuwa, ko haihuwar ‘ya’ya mata, ko zargi ko kuma rashin jituwa da ke tasowa tsakanin ma’aurata.
Idan aka sami matsala cikin aure, yawanci mata ne suka fi shan wuyarta. Mata kan tsinci kansu a halin ƙaƙa-ni-ka-yi tsakanin gidan miji zuwa gidan iyayensu. Miji kan tilasta mace barin gidansa. Idan ta ƙi, sai ya ci gaba da azabtar da ita ba yadda za ta yi. A irin wannan hali ne ake samun mace na fama da rama da rashin lafiya nau’i-nau’i ba tare da an san mafari ba. Yawanci a irin wannan hali, mata ba su buɗa baki su faɗi, shi kuma miji sai ya dage ba wani abu mai illa da ya sani.
A gidan iyaye, mace da ta sami matsalar aure kan fuskanci tsarguwa da tsana daga mutanen gidan har ya kai ba ta sha’awar zama gidan. Wani lokaci wasu iyaye kan sanya mata dokar leƙa koda ƙofar gida, musamman idan ya zan an yi zama da mijin, kuma rashin gaskiyar ya ƙare kanta.
Rahma ta dubi matsalar aure a matsayin wani muhimmin abu da ta kawo shi cikin wasu littattafanta. Ga misali, littafin Baya Na Suka 1-2.
Baya Na Suka labari ne da wata yarinya mai suna Zainab ta fito a cikinsa. Ta yi ilmin addini har ta hardace Alƙur’ani. Ta auri wani saurayi Al’amin. Kafin aure, Zainab mace ce da ba ta da kowace irin gurɓatar tarbiyya. Kowa yana yaba kirki da halayenta. Bayan aurenta da Al’amin sai ta shiga shan giya a dalilin magani da mahaifiyar wata yarinya da ta so shi ta yi mata. Lokacin da Al’amin ya fahimci shan giyar Zainab sai ya nemi ya ji ta yaya ta fara shan giya, sai ta amsa masa da cewa:
Komai bai ishe ni rago tunaninka ba hatta karatuna, a yayin da ina buƙatar hakan domin samar da cikar burin abin da ya nisanta ni da kai, kwatsam sai barasa ta ɗauke mini wannan nauyi. Ana gobe zan zana jarrabawata ta ƙarshe a shekara ta biyu da daddare ka bugo mini waya da misalin ƙarfe ɗaya ka bayyana mini irin halin kaɗaici, takurawa da azabtuwar da kake ciki a domin rashina. A wannan rana ban yi barci ba, kuka nake da tunani, da zan samu duk wata hanya da za ta isar da ni gare ka a wannan lokaci da na yi ko da zan bar jarrabawata. Ko da haka ba ta samu ba, ya yi tasiri a jarrabawata inda sai da na maimaita wannan takarda a shekarar gaba da ita. Ba na son hakan ya sake faruwa don haka na shiga neman duk abin da zai sassauta mini. Baya Na Suka 2, Shafi na 9-10.
Idan aka yi nazarin wannan bayani sosai, sai a fahimci cewa, matsalar rayuwar aure ce ta sa Zainab ta faɗa a halin shan barasa. Halin tunanin mijinta shi ne abu na farko da ya buɗa kafar fara shan giya gare ta. Tunani kan miji, musamman a lokacin da aka yi nisa da shi, wani abu ne da ke jefa mata cikin ƙuncin rayuwa. Mace da ta auri namijin da take so, kuma ya zan yana ba ta kowace irin kyakkyawar kulawa na sa ta sami sukuni a rayuwarta, ta manta da komai. Wannan zai ba ta damar samun kowace irin walwala da ‘yancin rayuwa da fita daga kowane irin baƙin ciki. A irin wannan hali, idan mace ta yi nisa da miji, takan kasance cikin damuwa da tunaninsa, musamman idan ya zan wasu al’amurra da ya ɗauke mata sun koma kanta. Haka idan irin wannan miji ya sanar da matarsa halin kaɗaici da kewarta da yake ciki, abin zai dame ta. A irin wannan yanayi, mace na iya aukawa a kowace irin hanya ido rufe domin sassauci ga halin da take ciki. Irin haka ne Zainab take ciki, kwatsam sai wata mai suna Salamatu ta gabatar mata da giya a matsayin wani abu da zai sassauta damuwarta. A hankali ta mai da giya wani sashe na wartsake damuwar rayuwarta.
A cikin littafin Za Ta Iya 1-3, nan ma wata mata ce mai suna Hajiya Rabi ta faɗa matsalar zaman aure. Tana zaune da mijinta tsawon lokaci ba su haihu ba. Ana nan matar da ya aura ta biyu mai suna Zuwaira ta haihu. Bayan wannan lokaci ne sai Hajiya Rabi ta sami ciki, ta haifi tagwaye. Haihuwar Hajiya Rabi ya sa Hajiya Zuwaira ta shirya yadda Alhaji Zakanya zai tsani uwar gidarsa da ‘ya’yanta. Hajiya Zuwaira ta fara da shirya ƙaryar cewa, direban Alhajin mai suna Lauwali ne ya yi wa Hajiya Rabi ciki. Ga yadda batun ya gudana:
Jiya Allah ne ya kiyaye da ƙyar na ƙwaci kaina wajan direban ka Lawali….
Jiya ne da ya kai ni makaranta wajen taron iyayen yara, muna dawowa, sai ya biyo ni ɗaki, na ce akan me? Wai zai gaya mini cewa, nan gaba in ban tayar ba yaya za ta ƙwace gida, domin wai ba ka haihuwa, ga shi wai na kawo Sadik ka karɓa, dan haka ita ma yanzu za ta shiga kawo maka ‘ya’ya, wai shi ne take nemansa, yanzu wai har ya yi mata ciki, kuma a haka za ta yi ta haihuwa, to wai ni ma in zo mu ƙara wai ba mai sani. Za Ta Iya 1, Shafi na 34.

Shi kuma Alhaji Zakanya bai tsaya bincike ba, sai ya wuce asibiti. Koda ya isa ɗakin nata, sai ya sami wata wasiƙa da aka bari a ƙarƙashin filon Hajiya Rabi, kuma wasiƙar na da sunan Lauwali. Bayan da ya karanta, sai ya tayar da ita cikin fushi, ya tambaya te game da wasiƙar. Ta nuna ba ta san komai ba. Da bai amince ba ne, sai ta ce:
Na fahimci inda batun ya dosa Alhaji, babu kuma abin da ake nufi da ni, ban da a yi mini sharri, a raba ka da ni da ‘ya’yan da muka samu, amma ni ba ni da wata kariya, ban da shaidar Allah da taka, dan haka ka shaide ni Alhaji, ban da wata alaƙa da wani namiji kafin –da-bayan na aure….Ya haɗe hannayenta zuwa wuyanta da shaƙa. Za Ta Iya 1, Shafi na 36-37
Matsalar da Hajiya Rabi ta shiga, matsala ce babba. ƙiren ƙarya a jingina ga mace, musamman game da wani namiji, matsala ce da take shafuwar matan aure da yawa. Matsala ce da take kawo rashin zaman lafiya, wani lokaci har da mutuwar aure. Ita kan ta Hajiya Rabi, wannan ƙiren ƙarya ya haifar mata matsala da mijinta, ya yi watsi da ita da ‘ya’yanta duka. Mahaifinta shi ma ya hana ta zuwa gidansa. Don haka sai kakarta ce ta zauna da ita a wani ƙauye. Wannan ya sa yaranta; Ahmad da Nafisa suka taso da rayuwarsu a ƙauye. A zamantakewar rayuwa, irin wannan hali da Hajiya Rabi ta shiga ana samun sa ga wasu matan aure masu yawa.
Ita ma Hassana da ke cikin littafin Tuwon ƙaya matsalar aure ta kai ta ga rasa gata, da shiga halin ƙunci da rasa rayuwarta. Ita ɗiya ce ga wani attajiri mai suna Alhaji Idris. Ta wayi gari cikin mutuwar son wani saurayi Musa. Babbar matsalarta ita ce iyayenta sun ƙi amincewa da Musa saboda sun san ɗan bangar siyasa ne da ba shi da kykkyawar madafa. A haka dai Hassana ta dage ita shi take so, kuma za ta aure shi. Alhaji Idris ya yi yarjejeniya da ita kan aurenta, ta ce duka ta ɗauka. Aka ɗaura auren. Bayan lokaci da auren sai iyayenta suka rasu a haɗarin jirgin sama. Aka bar ta da yayanta mai suna Mujitaba.
Ana nan siyasa ta tashi, jam’iyyar adawa ta tsayar da Mujitaba takara. Ita kuma jam’iyya mai mulki ta su Musa ta tsayar da maigidan Musa. Musa ya sa Hassana ta riƙa sukan yayanta har aka yi zaɓe ya faɗi. Cin zaɓen ya ba Musa damar ya je hajji ya sayi gida da mota. Ita kuma Hassana a maimakon ta sami sassauci, sai ƙara lalacewar lamurra. Ta kwanta rashin lafiya, Musa ya fita batunta, ya koma yana neman mata abinsa. Sabon gidansa ya gyara shi, ya ce na amarya ne. Rashin lafiya ya ci ƙarfin Hassana, a maimakon ya kai ta asibiti sai ya tura ta wajen wani boka da ya gallaza mata azaba. Ta tsero, Musa ya sake tura ta Kamaru inda a can ta rasu cikin ƙasƙanci. Kafin rasuwarta, wata rana ta taɓa bayyana masa damuwar da take ciki na aurensa. Ta ce:
Musa dubi rayuwata a sunan wai ka samu aiki. Ban buƙaci ƙaryar arziƙi ba, amma a ƙalla don ka canja mini ɗaki ko ka sai mini rasho dan in samu sauƙin ciwo na Musa ba ka faɗi ba. Kuɗin rashona fa bai kai kuɗin ko turaren da kake fesawa ba, amma kake ƙyashi, kullum kai ne canja kaya, canja abinci yawon kashe kuɗi wa har matan waje. Amma ni da ‘ya’yana ne ba mu kai mu huta ba don da kuɗin makarantarsu da na abincinmu da shi za ka sai gidan da har yau ko labarin tubali ban taɓa ji ka ajiye ba. Shafi na 45.
Kalaman Hassana na bayyana irin matsala da ƙuncin rayuwa da take ciki. Dukkan buƙatocinta masu sauƙin aiwatarwa ne ga irin Musa, amma sai ya yi watsi da su. Kafin aurensa kuwa, Hassana tana cikin kowane irin jin daɗi. Ba ta cikin kowace irin matsalar rayuwa. Irin wannan matsala da Hassana ta shiga musamman rashin abinci da kula da neman matan waje ga mijinta na cikin manyan matsalolin aure da wasu mata suke faɗawa a hannun maza har su rasa rayukansu. Ita kuma Indo matsalar aure nesa ya sa ta shiga wasu matsaloli. Ga yadda nata matsalolin suka kasance:
Ku bari ya sake ni ko a mai da ni inda ya ɗauko ni, na gaji. Baƙin ciki da wuya za su kashe ni a gidan nan. Ban taɓa ganin iyayena ba tun da na aure shi, ai ko bauya sai haka! Jikina da zuciyata ba su taɓa hutawa daga bauta da baƙin cikin da ake cusa mini ba. Na haihu, ‘ya’ya sun mutu, babu tausayi. Waɗanda suka saura an raba ni da su. In na haɗa gumina na tara dukiya don ‘ya’yana ko don na gan su sai a kwashe a yi aure. Wayyo ni Allah na! Mace Mutum shafi na 49
Aure a wani gari mai nisa matsala ce ga mata wadda ke sa wasu su ɗauki lokaci mai tsawo ba su je garin iyayensu ba. Indo wannan matsalar ce ta daɗe cikin zuciyarta har lokacin da ta sami damar faɗarta. Tun da ta auri Malam babba ta baro garinsu ba ta sake ganin iyayenta ba har ta haifi ‘ya’ya da ba su kasa huɗu ba. Matsala ta biyu ita ce, yadda mijin nata ke amsar kuɗaɗenta da sunan kai wa ɗiyanta da ke raye a wasu garuruwa da ya tura su karatu, amma sai ya je ya yi aure abinsa. Wannan matsala ce da ke sa mace ba za ta mallaki komai nata ba. Irin wannan na cikin matsalolin aure da wasu mata suke fuskanta a ƙarƙashin mazajensu.

3.1.3 Soyayya


Soyayya gamon jini! Soyayya na nufin nuna ƙauna daga ɓangarori biyu na masu ƙaunar juna, musamman mace da namiji (CNHN, 2006). Shi kuma ɗakingari (…., 22-23), cewa ya yi, soyayya ita ce ƙawa-zuci ko tsananin ƙauna da buƙatar kusantuwa ga wani mutum, ko wani abu daban. A taƙaice Soyayya ita ce wata irin shaƙuwa da amincewa da ke shiga tsakanin wasu mutane kan wani dalili na musamman. Yawanci, an fi lura da soyayya tsakanin namiji da mace wadda a hankali wani lokaci take kai ga aure.
A sha’anin soyayya, yawanci mata sun fi fuskantar matsala. Mace kan faɗa matsalar soyayya ne saboda takan yi saurin miƙa wuya da rungumar wanda take so ba tare da la’akari, ko bincike game da tarbiyyarsa ba. Da yawa mata kan faɗa tarnaƙin soyayya saboda yadda suke ruɗuwa da abin duniya ko kwalliya da matsayin da namiji ya jingina wa kansa, ya kuma gabatar gare su. Wannan yakan sa wata mace ta zurfafa ga son wani namiji, ta ƙaƙaba shi a cikin zuciyarta ta yadda lokaci guda sai ta faɗa haɗarinsa.
Yawancin matsalolin soyayya da mata suke faɗawa sun fi alaƙa da gurɓata rayuwarsu da tozarta matsayinsu. Matsalolin sun haɗa da cikin shege, guje wa iyaye, haukacewa, barin gari, shiga karuwanci da sauransu.
Rahma Abdulmajid ta saka matsalolin soyayya a matsayin wani abin dubawa da kuma yin tsokaci cikin wasu littattafanta. Ga misali, a cikin littafin Za Ta Iya, Rahma ta kawo yadda tarnaƙin soyayya ya sa wani saurayi ya ci zarafin wata mai suna Nafisa. Nafisa tana soyayya ne da wani saurayi mai suna Sadiƙ. Mahaifiyar Sadiƙ ba ta son alaƙar ɗanta da Nafisa. Wannan ya sa ta shiga hanyoyi masu yawa don yadda za ta tozarta ƙimar Nafisa a zuciyar Sadiƙ. Irin wannan sharri ne saurayin ya zo wa Nafisa da shi lokacin da take tafiya tare da Sadiƙ. Ga yadda Rahma ta kawo bayanin:
Nafisa a gefensa ita ma da doguwar riga ta rungume litattafai a ƙirjinta, suna takawa a hankali a harabar makarantar dan fitowa daga ciki. Kwatsam sai ga wani saurayi mai shigar rashin natsuwa ya shawo gabanta yana ƙoƙarin jawo hannunta. ….wai kina nufin ki ce ba ki san ni ba ne dan kin gan ki da sabon saurayi?....Au ai da kin gaya mini cewa kin nunawa wani cewa ke ‘yar mutunci ce, sai na tufa miki asiri tun da na san ba ni kaɗai ne namijin da ke tare da ke ba, amma tun da abin na wulaƙanci ne, zan tona miki asiri yau… Oga ka ɗauki ragowarmu sai maneji, ba ta da kowa ba ta da komai, mu ne ke ɗauke da nauyinta, mu kuwa ba dan Allah muka ɗauki nauyinta ba, sai dan mu ma ba mu da kamarta wajan biya mana buƙata. Ka gane mana, dan haka in kana so in gaya maka siffanta ne sai in gaya maka kai ma yau ka je ka gwada ta ka gani ko.’ Za Ta Iya 2, Shafi na 3
Sharrin da wannan saurayin ya yi wa Nafisa abu ne da ake samunsa a tsakanin masoya, musamman idan ya zan ba a son dangantakar tasu. ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke zubar da mutuncin mace shi ne danganta ta da fasiƙanci da wani namiji. Yawanci, masu neman aure ba su amincewa da alaƙar budurwarsu da wani daban. Don haka, abin da saurayin ya yi, ya yi ne domin ya sa Sadiƙ ya tsani Nafisa, soyayyarsu ta lalace. Bayan wannan sharri bai ci ba, sai aka sake ƙulla mata wani na daban. A wannan karo an yi amfani da wani saurayi ne aka tura shi domin ya yi zance da ita. Shi kuma saurayin mai suna Ahmad, yana ganin ta sai ya gane ita ce ƙanwarsa da ta ɓata tana yarinya. Bayan ɗan tattaunawarsu, sai suka rungume junansu. A wannan lokaci an riga an zo da Sadiƙ yana laɓe domin a ƙara tabbatar masa yarinyar da yake so fasiƙa ce. Ganin abin da ya faru ya sa Sadiƙ ya suƙe, ya kuma yarda da labaran da aka yi ba shi game da Nafisa. Nan take ya shirya halaka ta wanda dole ta bar gari tare da mamarta. Da suka shirya barin gari sai ta rubuta masa cewa;
Na bar garin nan, amma a domin ka Abubakar. Ban san lokacin haɗuwa ba, amma ina fatan ya zamo ka huce a lokacin don mu iya samun hafimtar juna….Ina ci gaba da sonka Sadik a kowane hali muke kuma a ko’ina. Domin ka dace da zuciyata…Nafisarka. Za Ta Iya 2, shafi na 73.
Shi ma littafin Hadari Sa Gabanka 1, yarinyar da take cikinsa mai suna Nadiya ta faɗa matsalar soyayya. Nadiyya yarinya ce mai natsuwa, amma sai ta faɗa soyayya da wani saurayi mai suna Faruƙ. Ga yadda Rahma ta kawo wani ɓangare na soyayyar Nadiya da Faruƙ:
….Tun da take ba ta taɓa haɗuwa da zanen zuciyarta a samarin da ke zabarin son ta ba sai da ta ci karo da soyayyar Faruƙ a shekarar bara, kamar wasa yake cewa ita dama gidansa ke jira a dalilin ta ce masa ‘Gidanka na da kyau’ A wata ziyara da ta taɓa raka Mudi gidan Faruƙ. Mudi da Faruƙ ba su ɓata lokaci ba suka sami shawo Nadiya har ta faɗa matsanancin son Faruƙ kamar za ta haɗiye shi. Shafi na 13.
Faruƙ wani ɗan ta’adda ne da sana’arsa ita ce satar dukiyar mutane ta hanyar yanar gizo. Koda Nadiya ta fara soyayya da Faruƙ yana tunanin hanyar da zai washe dukiyar mahaifinta. Wannan ya sa da ya sami karɓuwa ga Nadiya sai ya ga cewa ya sami hanya mafi sauƙi da zai kai ga manufarsa. Rahma ta kawo bayanin Faruƙ a cikin littafin nan na Hadari Sa Gabanka 1 kamar haka:
A idon jama’a dai sana’arsa ita ce haɗa tashar yana gizo da tauraron ɗan Adam amma a kan aikinsa da ya sani shi da yaransa shi ne raba me kuɗi ko wani babban asusu da haƙƙinsa. Ya yi kuɗi yadda ba a zato, yana da gidan da ba kowane irin wane ne zai iya zama ya dace da shi, kamar yadda yake hawa kowace mota sabuwar yayi matar da zai sa gidan nasa ne bai ga wadda ta dace ba sai da ya haɗu da kyakkyawar Nadiya ‘yar hamshaƙin me kuɗin asali wato Alh. Sagir sai dai kash! Tun kafin haɗuwa da ita ubanta ya shigo layin waɗanda yake mafarkin yi wa yasa don cika aninin da ya rage masa a fadar kuɗi. Sai dai baƙuntar zuciyarsa da ta yi bai sauya komai ba, sai ma ganin da yake aurenta a matsayin babbar ɗiyar Alhaji kuma wadda take wakiltarsa a komai bayan Mudi zai iya kai shi ga mallake ilahirin dukiyar wannan bawan Allah….. Shafi na 11-12.
Ga ‘ya mace mai mutunci irin Nadiya, soyayya da irin Faruƙ matsala ce babba gare ta. Shi Faruƙ ba Nadiyar ce a zuciyarsa ba, amma ya riƙe soyayyarta a zahiri domin cimma burinsa na sace dukiyar mahaifinta cikin sauƙi. Daga ƙarshe, a ƙarƙashin soyayyarsa ta yaudara ya tarwatsa iyayenta. Ya kashe ƙanin mahaifinta Mudi, ya kashe mahaifinta Alhaji Sagir, da ƙaninsa kanal….. ya kuma ƙona ofishinta. Ita ma ranta ya tsira ne daga sharrinsa dalilin wani saurayi mai suna fatihu. Wannan ya nuna matsalar son Faruk ga Nadiya wani tarnaƙi ne babba wanda da yawa wasu mata sukan tsinci kansu cikin makamancinsa, su rasa gaba ko baya, wasu ma har su halaka.
Shi ma littafin Ba Ita Ba Ce 1-2 wasu mata tagwaye ne suka faɗa tarnaƙin soyayya. Salma da Salima sun faɗa son wani saurayi guda mai suna Mus’ab. Mus’ab ya fara gabatar da soyayyarsa ce ga Salma. A wannan ranar da suka rabu ne Salma ta sami haɗarin mota abin da ya kai sai da aka kai ta asibiti a ƙasar Afrika ta Kudu. A yanayin jinyarta son Mus’ab ya ci gaba da bunƙasa cikin zuciyarta alhali ba ta da wata hanya ta haɗuwa da shi.
Ita kuma Salima ta haɗu da Mus’ab a gidan wata ƙawarta da ta auri abokinsa mai suna Yusha’u. A nan gidan ne Mus’ab na ganin Salima sai ya zaci ita ce Salma saboda kama da suka yi. A nan ya nuna mata sani, ita kuma ta nuna ba ta san shi. Ya gabatar da buƙatarsa ta soyayya, ta kuma yarda. Salima ta ci gaba da soyayya da Mus’ab har lokacin da ta koma wajen jinyar Salma. A can ne ta gabatar wa Salma labarin tsananin son da take yi wa saurayinta da ta yi wa suna Bawan Allah. Ga yadda ta ce mata:
Haba ke dai bari Sal Sulaiman, ban taɓa zaton a rayuwata zan faɗa soyayyar wani namiji kamar yadda na faɗa son Bawan Allah. Kin san wani abu ne, masoyin ya haɗe ne, yana da karatu, kyau, aji, da hankali. Kuma dai…. Kai gaskiya Salma ba abin da zance miki, sai ina matuƙar son Bawan Allah na oh! Irin son mutuwa tare rayuwa tare ɗin nan. Sal dan ina jin rayuwa ba shi za ta yi mini wuya. Ba Ita Ba Ce 1, shafi na 28.
Ita kuma Salma, a nan a karo na farko ta faɗa wa Salima abin da ya daɗe a zuciyarta kamar haka:
Sali na faɗa soyayyar wani saurayi da ya gan ni ya yi tayin soyayya tsakanina da shi. Bai wuce awoyi da shigarsa kacokan cikin tunanina ba, na sami wannan matsala. A halin yanzu ya yi kowane irin siye tunanina, ya kutsa kowane loko na zuciyata da raina. Ina jin duk inda kike ji a soyayyarki da Bawan Allah, ko in ce fiye da haka, amma fatana yanzu shi ne in cire shi daga zuciyata sai dai ya gagare ni. Shafi na 29.
Matsala mafi girma da ke cikin soyayyar waɗannan tagwaye ita ce, sanya tsananin son wani da haƙiƙance ba a iya rayuwa idan aka rasa shi. Wannan abu ne kuma ya ci gaba da bunƙasa cikin zuciyar kowacensu, ba tare da sun san saurayi guda ne suke tarayyar so su biyu ba. Bayan da aka sallamo Salma daga asibiti ne sai Salima ta gayyaci Mus’ab gidansu. Zuwansa Salma ta haɗa ido da shi. Wannan ya haifar mata ciwon zuciya. Ita ma Salima a nan ta fara rashin lafiya mai tsanani. Su biyu suka kwanta ciwo asibiti dalilin Mus’ab. Kowace na tsananin son sa. Irin wannan makauniyar soyayya, matsala ce da ake samu ga wasu mata da ke sa son wani abu cikin ransu, idan suka rasa shi sai ya zama sanadiyyar shigarsu wani mawuyacin hali.
Shi ma littafin Da Hannun Maza 1, wata yarinya ce ta shiga matsalar soyayya da wani saurayi mai suna Ibrahim. Salamatu ta fara haɗuwa da Ibrahim ne a lokacin da ya taimake ta, ya ƙwato mata jakar hannu da wani ya fizge a hannunta. Tun a wannan ranar Salamatu ta shiga tarkon son Ibrahim.
Wata rana tana ƙofar gida sai Ibrahim ya biyo. Suka gaisa inda a nan ta nuna buƙatar ya riƙa biyowa gida su gaisa. Sannu-sannu son Ibrahim ya nuna cikin zuciyarta. Salamatu ta kasance mai yi wa Ibrahim hidima; ta ba shi kuɗi da abinci, ta kuma yi masa wankin tufafi. Takan je ɗakinsa taya shi hira. A haka ya yi mata ciki. Da ciki ya bayyana, sai Ibrahim ya gudu, ya bar ta. Wannan hali ya sa Salamatu sambatu da furta kalaman da-na-sani da ke nuna ta faɗa tarnaƙin soyayya. Ga kalaman da ta furta:
Ibrahim me na yi maka ka yi mini wannan sakayyar? Ibrahim ban taɓa tunanin guje maka ba, duk rintsi duk tsanani. Na ci da kai, na sha da kai, na siturta ka. Ni ce har wankinka Ibrahim, na ba ka ruhina da jikina, ashe sakayya ta ita ce ka yi mini ciki ka sanya ni a uƙuba ka gudu ka bar ni! Allah Sarki! Wayyo Ibrahim. Shafi na 53.
La’akari da wannan kalami na Salamatu na nuna matsala ce ta faɗa cikinta. Kafin shiga soyayyarta da Ibrahim, Salamatu yarinya ce natsattsiya da ba ta kula maza balle shiga ɗakin kowane saurayi. Son da take yi wa Ibrahim ya sa ta manta matsayinta, ta ba shi amana, shi kuma ya yaudare ta, ya yi mata ciki. A al’ummar Hausawa, bayyanar ciki ga mace ba tare da aure ba na cikin mafi munin abin kunya da ƙyama da ke nuna gurɓatar tarbiyyarta. Sanin haka ne ya sa Salamatu kuka da shiga mawuyacin hali.
Ita ma wata mai suna A’isha da ke cikin littafin Mace Mutum sakamakon soyayyarta da wani saurayi da ya fito da sunan aurenta, ta yi ciki, ya kuma yi watsi da ita.
….. Baba na ji ya sauko daga benensa, cikin fushi ya dinga taka ni, yana rafka mini duk abin da ya samu, ana riƙe shi wai sai ya kashe ni. Daga baya bayan na yi laga-laga sai ya sanya cewa sai na faɗi wanda ya yi mini. Ban san abin da zai kai ni ga yin ciki ba, amma da na yi na san wanda ya yi, kuma na faɗa. Baba ya ɗauki hularsa ya tafi gidan. Nan aka bar ni tsakanin masu la’anata, tir, da tofin Allah tsine. Wasu na alhaki ne ya cika da ni, wasu na gadon uwata na yi. A haka muke har baba ya dawo yana ture-turen ashar ya sake rufe ni da duka da ƙyar aka ƙwace ni, ‘shegiya, ‘yar shegiya…. Ba ni kika yi wa ba, kanki kika yi wa, gashi can shi da ubansa sun kafe kai da fata cewa ba shi ya yi ba, sai ki kama hanya ki bar gidan nan, ki je ki nemi wanda ya yi miki ciki…. Shafi na 369.
Idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa, A’isha ta yi ciki ne a daidai lokacin da ba ta san ciki ba. Ta yi ciki ne tana da shekaru goma sha biyar. Ke nan tana sabuwar balaga idan har ma ta balagan. Wanda ya yi cikin zumunta ne da ya fito da sunan son ya aure ta. Mahaifinta ya amince da shi, ya kuma yarje masa zuwa zance. A wurin zancen, yana keɓewa da ita wuri mai ɗan nisa ga idanun mutane. Ba a ankara da abin da saurayin ke yi ba, sai da ciki ya bayyana. Bayyanar cikin ya kawo wa A’isha matsaloli da suka jefa ta cikin rikicin rayuwa. Bayan duka na fitar arziki da mahaifinta ya yi mata, ya yi iƙirarin ta bar masa gidansa. Da aka lallaɓe shi, sai ya bar ta, amma ba ta huta da tsarguwa da tsangwama ba. Da ta haihu sai kuma aka kashe yaron alhali tana son abinta. Waɗannan matsaloli ne da mata ke faɗawa ciki da sunan soyayya da wani, sai a yaudare su, a bar su a igiyar ruwa.

3.1.4 Maraici


Maraici shi ne mutuwar iyaye, musamman ga ƙaramin yaro. Maraici hali ne na rasuwar mahaifi, da ke kula da lamurran ‘ya’yansa. Maraici abu ne da ke kawo talauci ga yara da yawa. Maraici na cikin manyan matsalolin da ke jefa ‘ya’ya mata halin ƙuncin rayuwa a koyaushe.
Babban abu na farko da maraici yake haddasa wa ga mace shi ne talauci. A cewar CNHN (2006), Talauci shi ne rashin wadata. Talauci yanayi ne na rashin abin masarufi da zai ishi mutum tafiyar da al’amurran rayuwarsa na yau da kullum. Talauci abu ne da kowane mutum ba ya son sa. Manzon Allah (S A W) ya roƙi Allah kariya daga abubuwa uku ciki har da talauci inda ya ce:
‘Ya Allah ina neman tsarinka daga talauci da ƙaranci da ƙasƙanci, ina kuma neman tsarinka daga in yi zalunci ko a zalunce ni. Tirmizi da Abi Zarri suka ruwaito hadisin.
Talauci kan sa wasu mutane su rasa ‘yancinsu, su yi watsi da damarsu, su faɗa cikin halin ƙunci da matsuwa. Mutane da dama sun shiga kunya da aikata miyagun ayyukan ta’addanci domin ƙoƙarin fita daga cikin talauci.
A halin zamantakewar jama’a, jinsin mata ne talauci ya fi yi wa illa babba. Mace ta kasance mai raunin ƙarfin jiki da za ta iya fafutuka da ƙarfinta da kai-kawo domin kawar da talauci gare ta. Rashin ƙarfi na sa duk lokacin da talauci ya shafi mata, sai wasu su shiga sayar da mutuncinsu, daga ƙarshe sai rayuwarsu ta gurɓata, kuma ƙarshe a yi watsi da su.
Wani abu da halin talauci ke shigar da mata shi ne sayar da ‘yancinsu. Kowace mace na son ta huta gwargwado, ta sami walwala, ilmi da shiga cikin tsara a dama da ita. Mata da ke cikin talauci kan bar damarsu da ‘yancinsu, su kama ayyukan cikin gidajen masu hali. Yawancin ayyukan cikin gida da matan suke yi sun haɗa da shara, wanki, wanke-wanken kayan abinci, dafuwar abinci, gyaran ɗaki da sauransu. Dukkan waɗannan ayyuka ne na yau da kullum da ba za su bar mace ta sami damar neman ilmi da sauransu ba. Irin wannan na sa har mace ta ƙare rayuwarta ba ta sami ‘yancin sanin Ubangiji ba, bale ta bauta masa.
Wata illar kuma ita ce talla. Talla wata babbar hanya ce da ke kai mace ga gurɓatar rayuwa. Hanya ce ta ɗaukar wani abin masarufi, ana zagayawa da shi domin masu buƙata su gani, su saya. A rayuwar mace talla aibi ce babba da ke kai ta ga kowace irin hasara.
Idan mace musamman budurwa ta fara talla, wannan zai kasance wata kafa ga ashararun maza na fara neman hanyar hulɗa da ita. Shaiɗanun maza kan fara shiga hulɗa kai tsaye da yarinyar da ke talla ta hanyar sayen abin da take tallatawa. Daga saye yau da gobe, sai su shiga neman zance da ita, a hankali sai kyauta da sauransu. Wannan sai ya ba su damar gabatar da buƙatarsu gare ta . Idan ta bijire, sai su shiga ci mata mutunci da neman ta biya su har abin da ba su ba ta ba. Idan magabatanta suka yi yunƙurin ba ta kariya, sai cin mutunci ya haɗa da su domin su suka saya mata.
Abu na biyu mai aibi da talla ke haifarwa ga mace shi ne zubar da mutunci. Mace mutum ce mai mutuncin gaske ga kowane namiji nagari. Maza kan mutunta mace, su ba ta kariya a yanayi mai yawa, matuƙar ba ta yi wani abu na zubar da mutuncinta ba a addini ko al’ada. Talla hanya ce da ke yada mutuncin mace kai tsaye ga kowane namiji. Idan mace ta shiga hanyar talla, ana kallon ta a matsayin yasasshiya, wadda ta rasa kulawa tagari. Ana dubanta a matsayin ‘yar iska koda ba haka take ba. Wannan na sanya a yawancin lokuta ko da an gan ta a halin buƙata ba a ba ta gudunmmuwar da ta dace. Wannan kan haifar da matsaloli masu yawa ga mata.
Rahma Abdulmajid ta sanya maraici matsayin ɗaya daga cikin manyan matsalolin mata cikin adabinta. A littafinta na Za Ta Iya, ta nuna yadda halin maraici ya sa wata yarinya mai suna Nafisa ayyukan cikin gida ga wasu gidajen masu hali guda biyu. Gida na farko shi ne gidan mahaifinta wanda ya kore su tare da mahaifiyarsu tun suna jarirai A gidan ta yi ayyukan wanke-wanke da gyaran ɗakin wani saurayi mai suna Sadiƙ. Sadiƙ ya faɗa tarkon son Nafisa, amma ita ta yi ƙoƙarin nisantar da kanta domin tsoron matsayinsa. Ga yadda Rahma ta kawo yadda Nafisa ta bayyana ƙorafinta cikin littafin Za Ta Iya 1:
Da ni ‘yar iska ce, to sai in ce za ka iya nemana, domin kowane lokaci ɗan iska kan kai kansa inda Allah bai kai shi ba, amma ta’adata ba ita ce iskanci ba, dan haka a aure kam ka fi ƙarfina, dan ba zan kai kaina inda Allah bai kai ni ba. Shafi na 49.
A wani wuri cikin wannan littafi ta ci gaba da nuna fargabarta take cewa,
Na lura in har zanci gaba da zama a ƙarƙashinka ma’ana ina yi maka aiki, to ba za ka haƙure mini ‘yancina ba dan haka ka yi haƙuri, zan bar aikin a yau ba a gobe ba. Shafi na 49.
Bayanan Nafisa na nuna fargaba da ƙin jinin da take yi ga soyayyar Sadiƙ. Ta lura ci gaba da aikinta a ƙarƙashin Sadiƙ zai haifar mata rashin ‘yancin da take ji tana da shi a gidan. ‘Yancinta a wannan hali shi ne rashin sa mata ido da mahaifiyar Sadiƙ Hajiya Zuwaira da duk masu aikin gidan ke tsoro ba ta yi ba wadda tana iya yi mata komai idan ta ji irinta marashiya gata tana soyayya da ɗanta. Tsoron abin da zai iya faruwa ya sa Nafisa ta yanke barin aikinta kai tsaye, babu ɓata lokaci.
Gida na biyu da Nafisa ta koma aiki shi ne gidan wata mata mai suna Ester inda a can yayanta Ahmad ya taras da ita. Ga yadda Rahma ta kawo batun a cikin lttafin Za Ta Iya 2:
A ƙofar gidan suka haɗu. ‘Ahmad wana’ Nafisata’ suka rungume juna. Tuni mutanen ginin suka soma taruwa. ‘Waye wannan? Wata mata ce ta tambayi Nafisa, …..Nafisa ta juyo, ‘Madam yayana ne.’ Matar ta juyo Ahmad gare ta tana murmushi, ‘Ko shi ne Ahmad da kike faɗi?’ ya juyo gare ta, ‘Wace ce wannan Nafisa?’ ‘Ita nake yi wa aiki Ahmad. Shafi na 7.
Idan aka dubi rayuwar Nafisa kacokam, sai a ga cewa halin maraici ne ya saka ta cikin talaucin da ya sa ta shiga ayyuka a gidajen waɗannan mutane. Irin wannan yanayi matsala ce babba a rayuwar mata masu yawa cikin al’umma. Wasu mata ta irin wannan hali suke rasa ‘yancinsu da damar da suke da ita, wasu ma a irin haka har su rasa rayukansu.
A cikin littafi Mace Mutum akwai wata yarinya mai suna Amina wadda matsalar maraici ya jefa ta cikin yanayin rayuwa mai wuya. ɗaya daga cikin yanayin shi ne na tallar ruwan sanyi ba da son rayuwarta. Ga yadda Rahma ta kawo batun tallar Amina:
…Amina dai ba ta son wannan sana’a, amma ta tuna ba ta da zaɓi. Ba za ta ma iya cewa ba za ta yi ba. Sai dai ta kasa rabuwa da tunanin makaranta. Yanzu an kusa jarrabawar ƙarshe. An kusa yin jarrabawar gasar shiga sakandire wato. An wuce ta a komai, ɗalibai sun yi nisa sun bar ta. Da abin ya dame ta sai ta yi wa Mama Bilki magana, wadda ta yi mata alƙawarin yi mata sauyin makaranta da za ta shigar da ita sahun wannan jarrabawa. Amma da sharaɗin sai ta sayar da ruwa na wata ta tara kuɗi. Haka za ka ga Amina tsakanin cunkoson motoci da ruwan ƙwandaloli tana ratsawa tana tallar ruwa mai sanyi…. shafi 289-28
Amina ɗiya ce ga wani mai suna Alhaji Garba Ciroma wanda ya ƙi karɓarta a matsayin ɗiya lokacin da aka haife ta. Ciroma ya zargi mahaifiyar Amina mai suna Fatima Goɗiya da samu ciki da wani, amma ba shi ba. Dalilin Ciroma shi ne malaminsa ya gaya masa namiji zai haifa matuƙar dai shi ya yi ciki. Matakin da Ciroma ya ɗauka ya tilasta Fatima Goɗiya barin Sakkwato ta koma Lagos. A can Lagos ne Fatima ta rasu, ita kuma Amina ta ci gaba da rayuwa a hannun mutane daban-daban. A hannun wata Bayarba mai suna Mama Balki wadda ta kuɓutar da ita daga rikicin ƙabilar Yarbawa ta fara talla kan dole. A ra’ayin Amina karatu take so ta yi, amma dole ta karɓi tallar ruwan sanyi domin shi ne sharaɗi na ƙarshe na ba ta damar karatunta. Wannan ya nuna ba don maraicin uba da ya ƙi karɓar ta a matsayin ɗiya, da mutuwar mahaifiya ba da Amina ba ta tsinci kanta da tallar ruwan da ya kusa kawar da matancinta ga wani ba. Irin wannan matsala ce ke sa a yau ake samun yara na yawon gararamba, ba karatun addini, ba na boko. Wasu cikin yaran da za su sami damar ilimi, da sun zama masu ɗimbin amfani ga al’umma kamar yadda Amina ta kasance bayan da ta sami ilmi.

4.1 Kammalawa


Adabin Rahma Abdulmajid taska ce da ta tattara al’amurran da suka shafi rayuwar mata. A zamantakewar al’umma, mata na fuskantar matsaloli masu yawa waɗanda su ne suke dagula ci gabansu. Wannan ya sa ake ta yekuwar taimaka musu ta hanyoyi masu yawa. Matsalolin mata da Rahma ta kawo cikin littattafanta waɗanda a wannan maƙalar aka yi nazarin wasu kaɗan cikinsu, na nuna Rahma ta nuna damuwa da jarunta sosai wajen yin fashin baƙin matsalolin a cikin fasalin ƙaga labarin hira.
Wani abu kuma shi ne, la’akari da aka yi da zamanin fara rubuta adabinta zuwa yau, ta rubuta littattafai da suka kai 30. Rubuta irin wannan adadi cikin shekaru 20, abu ne wanda sai namijin tsaye, mai yalwar lokaci zai iya. Rahma tare da kasancewarta matar aure, mai hidimomin miji da ‘ya’ya ba su hana ta amfani da ɗan lokacin da take da shi ba ta yi wannan gagarumar gudummuwa ga adabin Hausa ba.
Wani abu da maƙalar ta gano na jaruntar Rahma shi ne, kasancewarta ta farko da ta rubuta littafin ƙagaggen labarin Hausa mafi yawan shafuka da yawan kalmomi. Littafinta mai suna Mace Mutum ya ƙunshi shafuka …. da yawan kalmomi miliyan sha ɗaya da dubu sittin da bakwai da ɗari bakwai da saba’in da biyar (11, 67775).
Daga ƙarshe, akwai buƙatar ci gaba da nazarin littattafan Rahma saboda akwai amfani mai yawa da za a samu cikinsu. Ba lamarin rayuwar mata kawai ba, akwai darussan da suka shafi kyautata tarbiyya, da dabarun sasanta husuma, da faɗakar da al’umma da sauransu. Ta hanyar nazari kaɗai za a iya fito da waɗannan muhimman abubuwan ci gaba a sarari ga ɗalibai da alumma baki ɗaya.

Manazarta


Abdulmajid, R. (1996), Wa Ya Fi Kishi? 1-3. Kano: Sauƙi Bookshop
Abdul-Majid, A. (2004), Tuwon ƙaya. Kano: Gidan Dabino Publishers.
Abdulmajid, R. (2004), Ba Ita Ba Ce 1-2. Kano: Jakara City Bookshop.
Abdulmajid, R. (2005), Hadari Sa Gabanka 1-2. Kano: Gidan Dabino Publishers
Abdulmajid, R. (2005), Baya Na Suka 1-2. Kano: Gidan Dabino Publishers
Abdulmajid, R. (2006), Ni Ma ‘Yata Ce 1-2. Babu Maɗaba’a
Abdulmajid, R. (2012), Mace Mutum. Kano: Iyaruwa Publishers
Abdulmajid, R. (BS), Za Ta Iya 1-3. Kano: Jakara City Bookshop
Abdulmajid, R. (BS), Da Hannun Maza 1-2. Kano: De Couple Publishers
Adamu, M. T. (1998), Aure Da Biki A ƙasar Hausa. Kano: ɗan Sarki Publishers Ltd.
Aliyu Rila, M. R. (1990), Tafsiri Manar, Juzu’i na 4. Misra: Hai’atil Misriyyatil Amati Lil Kutubi.
Bakura, A. R. (2014), Kishi A ƙasar Hausa. Kaduna: Garkuwa Media Services.
CNHN, (2006), ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

ɗakingari, J. B. (2011), Alƙalami A Hannun Mata: Nazari A Kan Ayyukan Sadiya Garba Yakasai. Kundin digiri na farko, Sakkwato: Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo.

ƙahɗani, S. A. (2008), Addu’a’u Minal Kitabi was Sunnati wa Yalihi Al-Ilaju bir-Ruƙa Min Alkitabi was-Sunnati. ƙahira: Darul Ibrahimiyyati.

Malumfashi, I. A. M. (2006), Ginuwar ƙagaggun Labaran Hausa: ƙarin Haske. Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, ɓol. 1 No. 1. Kano: Jami’ar Bayero.

Malumfashi, I. A. M. (2011), Ta’aziyyar Adabin Kasuwar Kano. Cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture The Si
xth Hausa International Conference, Centre for the Study of Nigerian Languages, Kano: Bayero University.

Mukhtar, I. (2004), Jagoran Nazarin ƙagaggun Labarai. Kano. Adamu Joji Publishers.

Usman, A. K. (2007), Aure Yaƙin Mata: Balkisu Salisu Ahmad Funtuwa Da Rubuce-Rubucenta. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa kan Nazarin Hausa wanda Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato ta shirya daga ranar 7-9 ga watan Febrairu, 2007.

Yahaya, Y. I. (1988), Hausa A Rubuce : Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.