Ticker

6/recent/ticker-posts

Tauhidi A Bakin Makaɗan Baka Na Hausa

Daga

Umar Aliyu Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
07063532532, 07014529336, 08095750999
aliyubunzaumar@yahoo.com

Yuni, 2014

1.0 Gabatarwa

Tauhidi shi ne kaɗaita Allah Ta’ala da bauta tare da amincewa da dukkanin abin da ya jingina wa kansa na sunaye da siffofi da ayyuka. Tauhidi ne abu na farko da ke tabbatar da kasancewar mutum Musulmi. Kaɗaita Allah (tauhidi) shi ne ginshiƙi na farko mai ƙarfi da addinin Musulunci yake kansa. Don a kaɗaita shi (Allah) ne ya aiko Annabawa da manzanni masu yawa daga zamanin Annabi Adamu (AS) zuwa Annabi Muhammadu (S A W). Bayan tauhidi sai sauran ayyukan ibada kamar Sallah da Azumi da Zakkah da Hajji da sauran al’amurran zamantakewa.
Al’ummar Hausawa mutane ne da suka kasance Musulmi, kuma masu riƙo da tauhidi cikin kowane lamari nasu. Wannan ya sa kowane abu ya faru mai kyau ko maras kyau, Bahaushe kan danganta kasancewar abin daga Allah (S W T). Mawaƙan baka wani rukuni ne cikin Hausawa da ke da cikakken tasirin Musulunci cikin rayuwarsu. Wannan tasirin ya kasance wani muhimmin abu har cikin waƙoƙinsu. Kasancewar tauhidi ginshiƙi babba cikin rayuwar Musulmi, ya sa mawaƙan bakan suke tsarma tauhidi cikin waƙoƙin. Suna yin haka ne saboda wani lokaci su yi wa al’umma wa’azi da faɗakarwa. Wani lokaci kuma suna yi saboda tasirin Musulunci da kuma ƙarfin imaninsu ga kasancewar Allah mai iko kan komai da kowa, kuma mai aikata abin da ya so, da kuma kasancewar Allah abin dogara da neman biyan buƙata da kuma kariya.
Manufata a wannan maƙala ita ce nazarin tauhidi da ke ƙunshe cikin wasu ɗiyan waƙoƙin mawaƙan baka na Hausa. Duk da yake daga cikin waƙoƙi ne zan duba tauhidi, na kauce wa kawo ma’anar waƙa da tarihinta domin wasu masana da manazarta (Ɗangambo, 1981 da 2007 daYahya, 1997 da Gusau, 1993 da 1996 da Ibrahim, 1983 da Isma’ila, 1998 da Lere, 1987 da Gumel, 1992 da sauransu) sun riga sun yi rubuce-rubuce kan wannan. Don haka wannan maƙalar ta fara da duba tauhidi.

2.1 Ma’anar Tauhidi


Sanin ma’anar tauhidi abu ne mai muhimmmanci ga kowane Musulmi. Idan Musulmi suka san tauhidi, suka kuma kiyaye shi, zai zama mataki na farko na kiyaye tanade-tanaden Ubangijinsu da kuma bauta masa bisa haƙiƙa. Wannan ya sa wasu masana lamurran Musulunci suka dubi matsayin tauhidi a Musulunci da kuma ƙunshiyarsa suka fito da ma’anoni daban-daban gwargwadon fahimtarsu. Ga kaɗan daga cikinsu. A cewar Wazirin Kano (1980: 8):

“Tauhidi shi ne tabbatar da samuwar zati, ƙadiri, mai siffofin kamala, tsarkakakke daga kowace irin tawaya da kowace irin naƙasa wanda bai yi kama da komi ba, kuma babu wani abu da ya yi kama da shi ta kowace fuska da kowane hali”

A taƙaice, idan aka yi la’akari da wannan ma’ana ana iya cewa tauhidi shi ne tabbatar da samuwar Allah Maɗaukakin Sarki mai kowa mai komai tare da bauta masa shi kaɗai ba tare da tarayya da komai ba a cikin kowane nau’i na bauta masa ba da kuma sakankancewa ga samun sakamako ga yi masa bauta da kuma azaba ga yi masa tarayya a bauta.

3.1 Rabe-Raben Tauhidi A Musulunci


Tauhidi ya mamaye dukkan rayuwar Musulmi wanda hasali ma shi ne ƙofar da ake shiga addinin Musulunci daga gare ta. Wasu malaman Musulunci kamar Asimina (1980) ya karkasa tauhidi zuwa gida uku kamar haka:
i) Tauhidur-Rububiyyat (kaɗaita Allah da ayyuka) wanda shi ne tauhidin kaɗaita Allah da ayyuka misalin halitta, da azirtawa, da rayuwa, da kashewa, da juyar da al’amurra, da kawar da cuta, da makamancin waɗannan. Wannan nau’in haƙiƙa kafirai sun yi iƙirarinsa tun bisa lokacin manzon Allah (SAW) amma bai shigar da su cikin Musulunci ba.
ii) Tauhidul-uluhiyyat (kaɗaita Allah da bauta) shi ne na kaɗaita Allah da bauta misalin, addu’a, da yanka, da alwashi, da neman taimako, da neman tsari da wanin waɗannan. Wannan nau’i na tauhidi shi ne wannan da kafirai suka yi musun shi, kuma jayayya ta kasance a cikin shi take tsakanin mazanni da al’ummunsu tun daga Nuhu amincin Allah ya tabbata gare shi har zuwa ga Annabibimmu Muhammadu sallalahu alaihi wasallam.
iii) Tauhidul-Asma’u was-siffat. (kaɗaita Allah da sunaye da siffofi) wannan na nufin miƙa wuya (imani) ga dukkan abin da ya tisgo (ya zo) a cikin Alƙur’ani mai girma da hadisai ingantattu na daga sunayen Allah da siffofinsa waɗannan da ya siffanta kansa da su, ko manzonsa ya siffanta shi da su a kan haƙiƙan (tabbaci). Waɗannan su ne muhimman kashe-kashen tauhidi da malaman Musulunci suka yake kansu.

4.1 Tauhidi A Bakin Makaɗan Bakan Hausa


Tauhidi abu ne da ya zama ruwan dare cikin waƙoƙin makaɗan Hausa saboda tasirin Musulunci a zukatansu. An yi ƙoƙarin kawo misalan tauhidi ta hanyar bijirowa da ɗan waƙa da ake ganin akwai tauhidin a ciki tare da bayanin sa domin haƙa ta cim ma ruwa. Ga misali, Alhaji Musa Ɗanƙwairo yakan sanya tauhidi a cikin waƙoƙinsa a wurare da dama. A waƙarsa ta Ado Bayero wadda ake yi wa amshi da ‘Barkak ku da taurin gaba, na yarda da Sarki Ado’ akwai tauhidi kamar haka:
‘Gaskiya na nan ga wurinta,
Mutane mu yarda da Allah,
Wanda duk yay yarda da Allah,
Ka san wannan bai taɓewa’

Al’amarin yarda da Allah, tauhidi ne da ya game duk kashe-kashen tauhidi. Wannan ɗan waƙan ya game yarda da samuwar Allah, da kaɗaita shi da bauta, da ayyuka da duk wani abin da ya ƙunshi miƙa wuya ga Allah. Haka kuma, makaɗin ya bayyana sakamakon duk wanda ya tsai da ƙafa ga yarda da Allah a ɗango na ƙarshe na rashin taɓewa koyaushe.
A waƙarsa ta ‘Mai dubun nasara garnaƙaƙi Sardauna’ nan ma Ɗanƙwairo ya shigo da tauhidi inda yake cewa:
‘Tun da Allah shi ya hukunci bawa nai,
Shi ka ba shi komai,
Kuma shi ka hana mai,
‘Yan uwa ku riƙa,
Ba ƙarfi nai na ba,
ƙarfin Allah ne’

Wannan ɗan waƙa ya ƙunshi tauhidi na kaɗaita Allah da ayyuka. Hukunta kowane lamari ya wanzu, ya tabbata abu ne da ya kaɗaita ga Allah kawai. A nan mawaƙin ya bayyana Allah a matsayin mai hukunta komai ta hanyar bai wa bawansa komai, ko hana mashi. Haka kuma ya nuna ko da mutum na da wani abu ya san ba ƙarfinsa ya ba shi ba, sai dai ƙarfin Allah wanda imani da haka tauhidi ne tsayayye, kuma ingantacce.
Bayan Ɗanƙwairto, shi ma Narambaɗa sanannen makaɗi ne da ke amfani da salon wa’azi da faɗakarwa a cikin waƙoƙinsa. Wannan ya sa al’amarin tauhidi ya zama abu mai sauƙin gani da yawanci ake tsinta cikin wasu waƙoƙinsa. Ga misali, a waƙarsa ta Sarkin Ɓurmin Moriki Muhammad, Narambaɗa ya sanya al’amarin tauhidi a inda yake cewa:
‘Jahilci rashin sanin Allah,
Abu dai in ya taho,
Ga Allah aka mai sai’

Wannan ɗan waƙa babu shakka ya bayyana al’amarin tauhidin kaɗaita Allah da bauta ne. Mai da dukkan abin da ya zo ga Allah al’amari ne na kaɗaita Allah da bauta ta hanyar imani da ƙaddara mai kyau, ko maras kyau duka abu ne daga Allah.
A waƙar Gamda’are Sarkin Kudu Ali, nan ma Narambaɗa cewa ya yi:
‘Batun Allah mu shi muka biya,
In Allah ya zaɓi abin da kash shukka,
Ka san shina hita.’
A cikin wannan ɗan waƙa an samu tauhidin kaɗaita Allah da ayyuka ta inda makaɗin ya bayyana Allah a matsayin mai zaɓen abu da kuma tabbatar (fitar) da shi. Bayan wannan ma akwai kuma tauhidin nan na kaɗaita Allah da siffofinsa. Hakan zai inganta ganin yadda makaɗin ya bayyanar da bin maganar Allah wanda magana na cikin siffofin Allah Maɗaukaki.
Shi ma Aliyu Ɗandawo fitaccen makaɗin fada ne da ke ƙoƙarin fito da tasirin addininsa na Musulunci a cikin waƙoƙinsa da dama. Saboda haka, ba zai zama abin mamaki ba a ga lamarin tauhidi ya fito a cikin waƙoƙinsa. A waƙarsa ta Tukur Sarkin Yauri Aliyu Ɗandawo ya kawo lamarin tauhidi yana cewa:

‘Tukur ka yi don Allah,
Shi ka bari don Allah,
Halinka ba ɗai da halin na yau ba tun can hwarko,
Abin da duy yas same shi bai cewa wani yay yi mai,
Ga Allah shi ka dogara,
Shi ko tuban mai,
Abin da duy yas samu shi tabbata,
Allah yan nuhwai shi tun farko.’
Ilimin tauhidi ne ya mamaye wannan ɗan waƙa kuma ya ƙunshi tauhidi na kaɗaita Allah da bauta ne. Tun farko, ana iya fahimtar tauhidin ta inda mawaƙin ya bayyana duk abin da ya samu ba maganar wani ya yi sai dai ya mai da lamarin ga Allah. Ya kuma nuna cewa, Allah ne ya nufa tun farko hakan ya kasance. Haka lamarin tauhidin kaɗaita Allah da bauta yake. Bawa ya san Allah yake hukunta masa komai, ba wani halitta daban ba.
A wani ɗa na wannan waƙar ga yadda Aliyu Ɗandawo ya sake fito da tauhidi a inda yake cewa:
“Ka ga komi tsananin hwari,
kana ishe tohwahiya da kunnuwa na ɗanya,
Cikin sarautar Allah ta rayu ba da ruwa ba,
Allah bai yi sarautad da za a koyo nai ba.”

Rayawa da kashewa abu ne da ke hannun Allah Maɗaukakin Sarki. Allah yakan raya abin da ya ga dama koda kuwa a muhallin da ba a al’adanci rayuwar abin ba. Yakan kuma kashe abin da ya ga dama duk da irin tanade-tanaden da aka yi masa na ɗorewar rayuwarsa. Yarda da haka ga mutum, tauhidi ne na kaɗaita Allah da ayyukansa. Ke nan wannan ɗan waƙa ya taro sha’anin tauhidin kaɗaita Allah ne da ayyuka. Hakan ya tabbata ne bisa ga la’akari da yadda ya ƙunshi al’amarin ikon Allah na raya wani tsiro ba tare da ruwa ba wanda ko shakka babu yana daga cikin ayyukan da Allah ya kaɗaita a kansu. Idan fari ya tsananta, kowane tsiro na mutuwa, amma ita tunfafiya koyaushe tana ɗanyar ta kamar babu fari. Wannan ƙarfin iko na Allah ne kawai kamar dai yadda ya halicci Annabi Adamu (AS) ba uwa ba uba, ya kuma halicci Annabi Isah (AS) da uwa kawai ba uba.
Mamman Shata shi kuma makaɗin jama’a ne da ya yi fice sosai a waƙar Hausa. Mamman Shata yakan sanya tauhidi a cikin waƙoƙinsa a wajen ƙoƙarin warware jigon waƙarsa. Ga misali, a waƙarsa ta Ado Bayero wadda ake yi wa amshi da ‘Ado na Kano Ɗan Abdu’ Yana cewa:
‘Ka ji birnin Kano har daji,
Allahu wanda ya yi ta,
Ado na Kano yab baiwa.’

A wanna wuri, ana iya fito da tauhidin nan na kaɗaita Allah da ayyuka inda mawaƙin ya yi bayanin cewa, Allah ne Mahaliccin da ya halitta Kano, kuma shi ne mamallakin mulki mai ba da mulki da ya ba da sarautar Kanon ga Ado Bayero.
Wani makaɗin jama’a da ake samun tauhidi cikin waƙoƙinsa shi ne Sani Ɗan-Indo. A waƙarsa ta ‘Mai mai da tasha sabuwa’ Ɗan-Indo cewa ya yi:
‘Sani nay yi tunani na sani,
Mai tunani na sani,
Shin wa ka baje ma wuri,
Allah ɗai ka baje ma wuri.’

Tauhidin da yake ƙunshe cikin wannan ɗan waƙa shi ne tauhidin kaɗaita Allah da ayyuka. Tauhidin zai tabbata ta kallon yadda makaɗin ya bayyana Allah ne kaɗai ke iya wa mutum wuri, ya ba shi dama ya yi abin da yake so. Yarda da wannan tauhidi ne tsayayye a addinin Musulunci. A wata waƙar tashi ta Garba Abu kuwa cewa ya yi:
‘Na ji abin mamaki a’a Garba Abu,
Ka ji abin tarihi a’a Garba Abu,
Wasu ‘ya ‘ya sun ce da Aljani nika aikin ga,
Wasu ‘ya ‘ya sun ce da malamai nika aikin ga,
Wasu ‘ya ‘ya sun ce da ilimi nika aikina,
Wasu ‘ya’ya sun ce da boka nika aikina,
Su san da komi Allah ya ce,
A yi shi don ya zan ba illa.’

Babu shakka, za a iya hango tauhidin nan na kaɗaita Allah da ayyukansa a cikin wannan ɗan waƙa. Al’amarin tauhidin zai iya tabbata ganin yadda mawaƙin ya miƙa lamarin fasaharsa ta w aƙa ga hukuncin Allah. Yarda da cewa, duk abin da Allah ya ce shi ke tabbata da kore kowane abu kan haka, tauhidi ne tabbatacce a Musulunci.
Bello Ɗan Sha-biyu na cikin makaɗin Hausa da ke sanya lamarin tauhidi a waƙoƙinsa. Ga misali, a waƙarsa ta motar siyasa cewa ya yi:

‘To Allah shi ka canza mutum,
A in bai canza mutum ba,
Na san kowa ba ya canza shi.’

Lamarin canza mutum abu ne wanda ya taƙaita ga ikon Allah kawai. Yarda da haka abu ne da ke kyautata imanin Musulmi da kuma inganta tauhidinsa. Ke nan wannan ɗan waƙa yana ɗauke ne da tauhidin kaɗaita Allah da ayyuka, inda makaɗin ya tabbatar da Allah ne kaɗai mai canza mutum. Allah ya kaɗaita ga wannan domin shi ne muƙallabil ƙulub kuma mudabbirul amri. Haka kuma duk wanda Allah bai canza ba, haƙiƙa ba wani wanda zai iya canza shi.
Shi kuma Ɗan’anace sanannen makaɗin maza ne da ya yi fice sosai a ƙasar Hausa musamman a waƙoƙinsa na dambe. Ɗan’anace mawaƙi ne da ke shigowa da tauhidi a cikin waƙoƙinsa musamman saboda tauhidi shi ne ginshiƙin addininsa na Musulunci. Ga misalan tauhidi a cikin wasu waƙoƙinsa.
‘Bismillahi Alhamdu,
Mun gode ma Allah
Kyawon ɗan Musulmi
Ya san Allah guda na.’

Sanin Allah ɗaya ne da sakakancewa kan haka shi ne ƙololuwar tauhidi. Wannan ɗan waƙa Ɗan’anace ya kawo tauhidin kaɗaita Allah da sunayensa da siffofinsa ta inda ya bayyana ingantacciyar siffar nan ta Allah Guda (Ahad) wanda ba ya da abokin tarayya ta kowane gefe. Ɗan’anace har kuma ya bayyana cewa, yin imani da kasancewar Allah shi kaɗai shi ne daidai ga ɗan Musulmi. A wani ɗan kuma Ɗan’anace na cewa:
‘To Allah shi ad da mutane,
Allah shi ad da iyawa,
Kuma Allah shi yay yi sarki,
Yay yi talakka,
Yay yi makafi, yay yi guragu,
Yay yi talakawa, yay yi matsaci.’

Babu shakka, wannan ɗan waƙa ya ginu ne a kan tauhidin kaɗaita Allah da ayyukansa ta la’akari da yadda makaɗin ya bayyana Allah a matsayin Mahalicci, kuma mai cikakken ikon halitta abubuwan halitta daban-daban. Da ikonsa ya halitta mutane aji daban daban kamar sarakai da makafi da guragu da talakwa da sauransu.
Shi ma makaɗa Muhammadu Gambo makaɗin maza ne da ya yi fice musamman a waƙar ɓarayi. Ko da ya ke makaɗin ɓarayi ne, akan sami tauhidi a cikin waƙoƙinsa wanda zai tabbatar muna da cewa, komai munin waƙa in dai daga bakin Musulmin Bahaushe ta fito, to ba za a rasa tsarmin lamarin tauhidi ba a cikin ta. Tasirin Musulunci a rayuwar Gambo ya sa wani lokaci yakan yi amfani da salon wa’azi da faɗakarwa a waƙoƙinsa. Ga misali, a waƙarsa ta Inuwa Ɗan Maɗaci, Gambo cewa ya yi:
‘Wanga ba wada Allah bai iya ba,
Ko mis same ka a filin duniyag ga,
Kak ka kuka da kowa wanga dangana,
Haliƙu Allah ke matsama.’

A nan Gambo ya fito ne da tauhidin kaɗaita Allah da ayyuka ta inda ya bayyana Allah a matsayin mai ikon aikata komai. Haka kuma ya bayyana cewa,ba wani a faɗin duniya da zai iya sa wani abu ya sami mutum face Allah kawai. Saboda haka, duk wani abin da ya sami mutum, ya dangana ya bar wa Allah kawai. Samuwar irin wannan tunani a zucci na tabbatar da kaɗaita Allah da yarda da ƙaddarorinsa. A wani baitin da ke cikin waƙar Jibirin Mugun Tsoho a gunduwoyin ƙarshe da ke ɗauke da mai da jawabin wata mata ga ɓarawon da ke yi mata barazanar kashi, Gambo ya kawo tauhidi inda yake cewa,
……………………………….
‘In ya yi tunani sai ya dangana,
Don ba wani kuka za shi yi ba,
Ya ce haka Allah yah hukunta,
Kowa ajali nai na tahowa.’

A nan ma Gambo ya sake bayyana tauhidin kaɗaita Allah da ayyukansa ne ta hanyar bayyana dangana da abin da Allah ya hukunta. Miƙa wuya da ga abin da Allah ya ƙaddara ga bawa, tauhidi ne da ke kan kaɗaita Allah da ayyukansa.
Shi kuma Amali Sububu makaɗin sana’a ne da ya yi fice a waƙoƙin noma kuma wanda a cikin waƙoƙin yake sakaɗa lamarin tauhidi. Ba wani abin mamaki ba ne ganin Amali Sububu na sanya tauhidi a waƙoƙinsa saboda akwai tasirin Musulunci tare da shi. Ga abin da ya ce a waƙarsa ta Isah Mai Kware mai amshi kamar haka:
‘Allah Ubangijinmu hiyayye mai sama,
Jabbaru Mai dare Mai rana Haliƙu,
Na gode mashi,
Da yai man lafiya,
Da hura ta yah haɗa,
Sutura ta mai sama,
Kuɗɗina Haliƙu,
Mui ta zaman duniya,
Kahin lahira ta ce musu,
Ta amshe musu,
Jatau duniya,
Ba komi ba ce.’

Idan aka yi la’akari da abin da ke cikin wannan ɗan waƙa, za a iya ciro nau’in tauhidi biyu a cikinsa. Na farko shi ne tauhidin nan na kaɗaita Allah da sunayensa da siffofinsa inda makaɗin ya jera siffofin Allah a ɗangaye uku na farko. Daga nan kuma sai makaɗin ya juya akalarsa zuwa ga fito da tauhidin nan na kaɗaita Allah da ayyukansa inda makaɗin ya bayyana Allah a matsayin mai baiwa ga kowane abu kamar ba da lafiya da abinci da arziki da sutura da sauransu. Ya kuma tabbatar wa Allah siffarsa mai halitta (haliƙi).
Haruna Uji shi kuma fitaccen makaɗi ne a fagen sha’awa. Kasancewar sa Musulmi ya sa ake samun tauhidi a waƙoƙinsa. Ga misalin tauhidin a waƙarsa ta Baƙar Rama inda ya ce:
‘Komi da ka duba,
Sha’anin Allah ne,
Arziki da karatu,
Wannan nufin Allah ne,
Da dukiya da haƙuri.’

Idan aka yi nazarin abin da yake ƙunshe a wannan ɗan waƙa za a ga cewa Haruna Uji ya yi kawo tauhidin kaɗaita Allah da ayyuka ne ta inda ya bayyana duk abin da mutum ya duba ya gani, ya san sha’anin Allah ne. Yarda da kasancewar komai cikin yarda da ƙudurar Allah abu ne da ke tabbata tauhidin Musulmi. Allah cikin ƙudurarsa ya halitta komai. Ba wani abu zai kasance idan ba da ƙudurar Allah ba. Wannan kuwa ya haɗa da dukiya, da karatu, da arziki da haƙuri da ma sauran abubuwan da bai kawo ba.
Da yake a nan ne aka cimma ƙarshen misalan tauhidia cikin wasu waƙoƙin makaɗan Hausa, ana iya cewa, misalan tauhidi da aka samu a rukunan waɗannan makaɗan sun yi ƙoƙarin fito da nau’o’in tauhidi wanda idan aka yi nazari za a ga ba tauhidi ne manufar, ko saƙon waƙoƙin ba, sai dai don kasancewar sa tauhidi abu ne wanda tun farko muka nuna yana tafiya da rayuwa gaba ɗaya ya sa suka shigo das hi cikin waƙoƙin nasu. Wato abu ne mai wuya Musulmin mawaƙi Bahaushe ya buɗe baki ya yi waƙa har ya ƙare bai ambaci wani nau’i na tauhidi ba.

5.1 Kammalawa


Idan aka yi la’akari da misalai da bayanai da maƙala ta zo da su, za a ga cewa, lamarin tauhidi abu ne babba, kuma mai tasirin gaske cikin rayuwar Hausawa. Wannan ya kasance ne ganin cewa, ko da yake ana kallon waƙoƙin bakan Hausa matsayin sharholiya, kuma na raha, amma kuma sai ga shi ana tsintar batutuwan tauhidi masu yawa cikin waƙoƙin. Haka na ƙara tabbatar da cewa, lamarin tauhidi ta kowace fuska aka dube shi, abu ne da ya yi kaka-gida cikin rayuwar mawaƙan bakan Hausa. Irin wannan kaka-gidan ta sa ko da ba don Musulunci kai tsaye suke shirya waƙoƙinsu ba, amma kuma tauhidi na shiga da fice da kuma giittawa cikin wasu ɗiyan waƙoƙin nasu.

Manazarta


Altine, H. (1983), Aliyu Ɗandawo Da Waƙoƙinsa. Kundin Digiri na Farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

Asimina, S. M. S (1989), Attauhidu Walfƙhu Wat-tajwid lil- Faslir Rabi’u Al- Ibtida’iyyat. Mahfulzatil-Wizaratil Ma’arif. Saudi Arabiya.

Bunza, U. A. (2001), Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu: Tauhidi A Bakin Makaɗan Bakan Hausa. Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Bunza, U. A. (2013) Wa’azi A Bakin Gambo Dogo Mai Kalangu. Cikin Mujallar Makaɗi A Mahangar Manazarta. Jerin takardun da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan tubar Muhammadu Gambo Mai Kalangu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto. ISBN. No: 978-8082-02-5

Gumel, M. A. (1992), Tarbiyya Da Dangoginta A Waƙoƙin Makaɗan baka Na Hausa. Kundin digiri na farko, Jami’ar Bayero, Kano..

Gusau, S. M. (1993), Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Fisbas Media Services, Kaduna.

Gusau, S. M. (1996), Makaɗa Da Mawaƙa Na Hausa. Fisbas Media Services, Kaduna.

Gusau, S. M. (2014), Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Song). BUK Inaugural Lecture Series No 14. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kono.

Ibrahim, M. S. (1983), Kowa Ya Sha Kiɗa 1. Longman Nigeria Limited, Kaduna

Isma’ila, S. S. (1998), Shahararrun Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali (1875-1960). Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Lere, N. D. (1987), Wasu Jigogin Waƙar Baka. Kundin digiri na farko, Jami’ar Bayero, Kano.

Mahe, A. (1984), Ɗan’anace Da Waƙoƙinsa. Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Muhammad. A. W. (2000), Littafin Tauhidi. Ma’aikatar Kula da Harkokin Addinin Musulunci da Waƙafai da Wa’azi daShiryarwa daga Aljihun Cibiyar Ibrahim ibn Abdul Aziz al-Ibrahim ta Taimakon Al’umma, Saudi Arabiya.

Tsoho, M. Y. (2013), Tsabar Rashin Tausayi Da Ɓurɓushin Tauhidi A Waƙoƙin Ɓarayi Na Gambo Mijin Kulu. Cikin Mujallar Makaɗi A Mahangar Manazarta. Jerin takardun da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan tubar Muhammadu Gambo Mai Kalangu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto. ISBN. No: 978-8082-02-5

Wazirin Kano. A. A. (1980), Tauhidi Mai Dalilai. NNPC, Zariya.

Yahya, A. B. (1997), Jigon Nazariin Waƙa. Fisbas Media Services, Kaduna.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.