Ticker

6/recent/ticker-posts

Sulhun Tankiya A Cikin Rubutattun Wakoki Da Wakokin Bakan Hausa

 Daga

DR. ABDULBASIR AHMAD ATUWO
SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA
JAMI’AR USMANU ƊANFODIYO, SAKKWATO.
Email: atuwoaa@yahoo.com
GSM NO: 07032452269

DA

DANO BALARABE BUNZA
SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA
JAMI’AR USMANU ƊANFODIYO, SAKKWATO.
Email: danobunza@yahoo.com
GSM No: 070351141980

Tsakure


Nijeriya ƙasa ce da ke da albarkar yawan al’umma, ga ƙabilu iri-iri, sannan da addinai daban-daban. Sai dai duk waɗannan abubuwa tare da albarkatun man fetur sun tattaru sun ƙara wa ƙasar ƙima da matsayi na girmama da mutantawa daga sauran ƙasashe, musamman ƙasashen Afirka. Ganin yadda Nijeriya ke batun kai shekara hamsin da uku da samun ‘yancin kai, ƙasar ta sha karo da rigingimu da nau’o’in tashin-tashina da suka kasance ba wai kawaibarazana ga zaman lafiya da tsaron dukiyar ‘yan ƙasa kawai ba har ma zuwa raba ƙasar zuwa gida biyu. Tunanin zaman lafiya da ci gaban ɗorewar Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya, amma wasu ‘yanƙasar marasa kishin ƙasar sai tunanin hanyoyin raba ƙasar suke yi. Wannan tunanin ne ke haifar da tashin-tashina a nan da can cikin Nijeriya. Marubuta waƙoƙI da mawaƙan baka na Hausa na sane da cewa idan ana zaune tare to dole ne a yi faɗa. Saboda hsks suka ga cewa ya zama wajibi ne a matsayinsu na ‘yan ƙasa kuma masu kishin haɗin kan ƙasar ya zama dole sub a da tasu gudummuwawajen tabbatar da sulhu. Wannan muƙala ta nazarci yadda mawaƙan Hausa a matsayinsu na ‘yan ƙasa masu kishin ƙasa ke gabatar da batutuwan sulhu a cikin waƙoƙinsu.

1.0 Gabatarwa


Yana daga cikin muhimman haƙƙoƙin da ke kan mawaƙa da sha’irran Hausa na su tabbatar da sun cusa saƙonnin sulhu da neman zaman lafiya tsakanin ‘yan Nijeriya. Mawaƙan baka sun rera waƙoƙI iri-iri waɗanda ke ɗauke da jigogin kwantar da rigingimu da sulhunta al’ummomin ƙasar Nijeriya. Daga cikin waɗannan mawaƙan baka akwai: Musa Ɗanƙwairo a jihar Zamfara da Sani Aliyu Ɗandawo a jihar Kebbi da Musa Ɗanba’udaga jihar Sakkwato da Adamu Ɗanmaraya Jos daga jihar Plateau da Shehu Ajilo daga jihar Kaduna. A ɓangaren rubutattun waƙoƙI kuwa, sanannun sha’irrai kamr su Ladan (1975) da Bichi (1968) duk sun wallafa ƙasidodi iri-iri kan rigingimudaban-daban da suka auku a Nijeriya musamman yaƙin basasa day a fara ranar 6 ga Yuli 1967 wanda ya ƙare a ranar 12 ga Janairu 1970. Waɗannansha’irrai sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da kira ga ‘yan Nijeriya das u guji faɗawa ga duk wani hali ko ɗabi’a da zai jawo tsimuwa da zubar mutunci a fuskar idon jama’ar ƙas ashen duniya. Haka kuma waɗannan mawallafa waƙoƙI sun jaddada wa ‘yan Nijeriya alfanun haɗin kai da zama dunƙulalliyar ƙasa ɗaya domin cigaba.

1.1 Yaƙin Basasa a Nijerya 1967-1970


Akwai tankiya biyu da suka yi illa da mummunan tasiri ga tarihin zamantakewar ‘yan Nijeriya musamman idan aka yi la’akari da irin hulɗar zama ta ‘yan Nijeriya tsakanin al’ummomi da kuma siyasance. Waɗannan rigingimu su ne yaƙin basasar Nijeriya a shekarar 1967 da kuma soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni.
Yaƙin basasan da aka fara 6 ga watan Yulin 1967 an ƙaddamar das hi ne da nufin raba ƙasar Nijeriya da ƙasar Biafara. Yaƙin dai ya ɗauki watanni uku ne kawai ana yin sa, amma daga ƙarshe an sami yin sulhun dakatar da yaƙin ranar 12 ga watan Janairun 1970 ba tare da ‘yan tawayen sun cim ma burin mafarkinsu ba.
Daidai lokacin aukuwar waɗannan rigingimu, harkokin rayuwar ‘yan Nijeriya nay au da kullum da suka shafi tattalin arziki da siyasa da sun tsaya cik a sassan Nijeriya. A gabascin ƙasar kuma inda nan ne Madugun ‘yan tawaye Odumegu Ojukwu ya yi kaka-gida can ma komai ya tsaya cik.
Tasiri da sakamakon da yaƙin basasan ya haddasa a Nijeriya babbar ill ace ga ‘yan Nijeriya. Matsalolin yaƙin da manyan bala’o’in da suka auku sun fi faɗI a yammacin Nijeriya inda a nan neal’ummomin Inyamurai da takwarorinsu suka fi yawa, musamman abin day a shafi salwantar rayuka da dukiyoyi. Waɗannan matsalolin da da ire-iren waɗannan tashin-tashina suka haddasa sun yi matuƙar tasiri ga zukatan ‘yan Nijeriya har koyaushe. A dalilin wannan tasiri nemawaƙan baka da marubuta kan waiwayi wannan tarihi mai sosa rayuwa lokaci zuwa lokaci a cikin waƙe-waƙensu da kuma rubuce-rubuce.
Yawanci wannan waiwayen da suka yi sukan yi shi ne ta fuskoki biyu, wato ko ya kasance kira ko gargaɗI sannan kuma da ƙoƙarin sulhunta ‘yan ƙasa da shirya zamantakewarsu’ Ladan (1975) a shahararriyar waƙarsa rubutacciya mai suna ‘Waƙar Haɗin Kan Afirka’ ya yi Magana a kan yaƙin basasar da wanda ya haddasa shi, wato Odumegu Ojukwu. Ladan yana cewa:
Ojukwu da ya ƙare mafarkinsa,
Day an shi kamar shi ne Pasha,
Ga-Kamba zuwan kansa,
Ga ficewa da zagayensa,
Yai imani babu kamarsa.

Duk da yake an san cewa zaman lafiya ya fi komai, amma na zagaye da girki su ne suka yi ta zuga shi yana cewa tawayen day a tsara tana kan gaskiya kuma suna tare da nasara. Wannan tunanin daga ƙarshe ya zama ƙarya. Alhaji Abubakar Ladan ya ƙara fitowa da wasu halayen da manufofin Ojukwu dangane da tawayen:
Manufarsa ya hargitsa al’umma,
Haka haddasa fitina da husuma,
Ɗan tawaye ko mai himma,
ƙarshe nasa kunya da nadama,
Haɗa kai mu yanzu muke nema.

Masu Karin Magana na cewa “Tsuntsun day a kira ruwa shi ruwa kan duka”.Domin ɓarnar yaƙin da ya auku duk a biranen matattarar ‘yan tawayen ta auku. To ammaɗangon ƙarshe na baitin day a gabata ya nuna manufar Ladan da kuma kiransa na zaman lafiya da haɗin kai domin ƙasa ta ci gaba.
Wani shahararren mawaƙin baka na Hausa, Adamu Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ‘Munafukin yaƙi’ yana cewa:
Sun ba da kuɗɗinsu,
Don a bad a man fetur,
Kuma babu man fetur,
Sai gas u sun tae.

Tushen waƙa: Munafukan yaƙi.
A wannan tushe na ɗiyan waƙar Ɗanmaraya Jos akwai muhimman saƙonnin day a kamata a lura das u. Wannan muƙala ta fahimci Ɗanmaraya ya yi amfani da Kalmar ‘Munafuki’ ne domin ya yi nuni ga abubuwa biyu a lokaci ɗaya. Su kansu al’ummomin Ibo tare das u ake tafiyar da gwamnatin Soja ta Yakubu Gowon. Kuma madugun ‘yan tawayen ma na daga cikin gwamnonin gwamnatin amma sai gas hi jikinsa da sunan yi wa gwamnatin da aka gina ta tare das hi da kuma shawarwarinsa na tawaye. Lallai wannan munafuci ne.
Sannan na biyu, ƙas ashen waje da ke ganin idan sun zuga Ibo suka yi tawaye a matsayin waɗannan ƙasashe na kanwa uwar gami ga faɗan ta hanyar shawara ko bad a makamai ko kuɗI ko sojoji saboda idan tawaye ya yi nasara za a bas u man fetur, sai gas hi ma wankin hula ya kai dare, an ma kasa wanke hular, duk sun taɓe.
Marubucin waƙa Bichi (1968) a waƙarsa mai suna ‘Baitoci dubu na waƙar tarihin rikicin Nijeriya’ wadda a cikin ta har ma da batutuwan sulhu da aka yi tsakanin gwamnatin Tarayya da ‘yan tawaye a ranar 20 ga Yuni 1970. A cikin waƙar Yusuf Bichi yana cewa:

Shawara da ta tufka nan da nan,
Suka ɗunguma duk baki ɗaya,
Gun Gawan babban Nijeriya,
Sai Gawan ya faɗa wa Ingila,
Magana ce ƙwaya ɗaya,
Shi ne ‘yan tawaye sun ce,
Duka dai tuba gaba ɗaya,
Sai ƙasarmu ta zauna lafiya.

Lokacin day aƙin basasa ya kai gaya a daidai wannan lokacin damuwa ta kai matuƙa, baa bin da ake so illa tattali yin sulhu da haɗe kai tare da watsi da aƙidar twaye. Kamar dai yadda bayani ya gabata su kansu ‘yan tawaye abubuwa sun kai musu maƙula.Sannan ita ma gwamnatin Nijeriya, jirwaye take da batun sulhu.
Tankiyar basasar ta kai ƙul a tsakanin watannin Agusta da Satumba a shekarar 1966, amma sulhun wannan tankiyar basasa ya daidaita ranar20 ga Yunin 1970. Wannan yaƙin ya laƙume rayukan mutane kimanin dubu goma zuwa dubu talatin (10,000- 30,000) kuma yawancinsu duk al’ummar Ibo ne. Bayan haka kuma, miliyoyinsu sun kasance ‘yan gudun hijira.

1.2 Sulhunta Tankiyar ƙabilanci


Al’ummomin Afirka da na duniya har ma da na Nijeriya a matsayinta na wani ɓangare na duniya duka sun fuskanci matsalolin rigingimun yaƙe-yaƙe a tsakanin ƙabilu, abin day a haddasa hasarar miliyoyin rayuka a sassan duniya daban-daban ciki hard a Nijeriya. Rigimar farko mai tasirin ƙabilanci da fara aukawa it ace ta juyin mulkin sojojin da Ibo suka fara tsarawa tare da zartarwa ƙarƙashin jagorancin wani matashi Hafsan sojaɗan ƙabilar Ibo amma haifaffen Kaduna mai suna Kaduna Nzagu Chukwuma. Daga ƙarshe shirin wannan juyin mulki ya bayyana, dukkan shuwagabannin siyasa na Arewa an kasha su.
Daga bisani kuwa, manyan Arewa suka lura da cewa ashe duk shirin an tsara shi ne domin a haɗa duk ‘yan siyasan Arewa masu faɗa a ji. Sannan aka gano cewa yawancin Hafsoshin soja da suka shirya abin duk Ibo ne. Jagoran shirin ma Ibo ne kamar yadda bayani ya gabata. Wannan abin ya hasa sabuwar wutarb ƙabilanci tsakanin al’ummar Ibo da gabascin Nijeriya da al’ummar Hausawa da ke Arewacin Nijeriya. Taken wata kalma ‘a yanka’ ta zama sanannar kalma mai ɗauke da saƙon cewa ‘A yanka ko a kasha wanda ake kusa das hi idan dai Ibo ne’. Wannan tankiyar it ace ta mamaye Arewaci da Gabascin Nijeriya jin kaɗan bayan juyin mulkin 1966 wanda ya yi sanadiyar kisan Firimiyan jihar Arewa na farko da Ahmadu Bello da Firayim Ministan Nijeriya na farko Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa. Duk waɗannan matsalolin da rigingimu suka haddasa da ɓacin rayuwar da matsalolin da suka saw a jama’a duk suna nan kwance a zukatan jama’ar da abin ya shafa.
Wata tankiya da ta taso it ace ta Zangon Kataf a shekarar 1998 a jihar Kaduna. Wannan rigima ma na da nason ƙabilanci haɗI da addini.Sai kuma tashin hankalin da aka yi tsakanin Munci da Fulanida kuma ‘yan sanda a shekarar 2000a Zakibian da ke jihar Benue. Sai tankiyar Kaduna ta 2001. Sai kuma rikicin Yelwan Shandam na 2003. Duk waɗannan rigingimu sun auku a dalilai masu nasaba da ƙabilanci ko addini, kuma sun laƙume ɗinbin rayuka tare da dukiyoyi masu yawan gaske. A waƙarsa mai suna ‘Haba ‘yan Nijeriya’, Ɗantala Jos yana ƙorafi a wurin da yake cewa:
Tushen waƙa: Haba ‘yan Nijeriya
Rassan waƙa: Ni ban gane ba,
Ni na yi gabas,
Ni na yi yamma,
Ni na yi kudu,
Ni na yi arewa,
Kullum-kullum ana ta yaƙI,
Ga yarammu su sha daga,
Su sha ƙwaya su sha giya,
Haba ai ban gane ba.

A waɗannan ɗiyan waƙa ko rassan waƙa Ɗantala na nuna damuwarsa ne ga irin halin da matasammu suka sami kansu. Ga dai rashin aikin yi, sannan ‘yan siyasa sai bas u maye suke yi suna sha suna rigingimu a tsakaninsu suna kasha kawunansu tare da ɓata dukiyoyin al’umma. Wato maimakon a mayar da yara masu alfanu ga al’umma, sai kawai a mayr das u masu yin barazana ga rayuka da dukiyoyin mutane a cikin ƙasa baki ɗaya.

1.3 Tankiyar Siyasa


Tankiyar siyasa daɗaɗɗiyar aba ce a rayuwar ‘yan Nijeriya. Ana iya waiwayar tarihin gwagwarmayar neman ‘yancin kai a Nijeriya. Waƙilan Arewacin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Sir Ahmadu Bello suka yi watsi dab uƙatar da waƙilan Kudancin Nijeriya a jagorancin Dr. Nnamdi Azikwe waɗanda su a wannan lokacin a shirye suke da a sami ‘yan saɓanin yankin arewacin Nijeriya dab a a shirye suke ba a wannan lokacin. Wannan bambanci ya ci gaba da faɗaɗa tare day aɗuwazuwa sassa daban-daban na rayuwar waɗannan al’ummu har zuwa ga ra’ayoyin siyasa da mulki da ma fannin tsaro kamar soja da ‘yan sanda. Haka kuma waɗannan ‘yan bambance-bambance na da matuƙar alaƙa da juye-juyen mulkin soja da suka yi ta aukuwa a Nijeriya.
A cikin littafinsa Uwechue (1991) mai suna ‘Africa Today’ wato ‘Afirka A Yau’ ya nuna cewa juyin mulkin farko da aka yi a Nijeriya ya faru ne a ranar 15 ga watan Yuli, 1966. Sai wanda ya biyo masa na ranar 13 ga watan Fabrairu 1976 wanda a cikinssa ne aka yi wa Janar Murtala kisa gilla. Sai wani yunƙurin juyin mulki da bai kai ga nasara ba, wanda aka ayyana tare da zartarwa a ranar 20 ga watan Disamba1986 da kuma maikam das hi da aka yi ba a cim ma nasara ba a ranar 22 ga watan Afrilun 1990. Duk waɗannan juye-juyen mulki da suka gabata ko da nasara ko babu nasarar, akwai dai kasha-kashen rayukan al’umma barkatai tare da jikkata wasu da ɓata musu dukiyoyi. Haka kuma kowane daga cikinsu na ɗauke da nason addiniko kuma ƙabilanci.
A ɓangaren yammacin Nijeriya soke zaɓen watan Yuni da aka yi a shekarar 1990 da Janar Ibrahim Badamasi Babangida , shugaban ƙasa na wannan lokaci ya yi ya janyo tsami da taɓarɓarewar kyakkyawan zamantakewa tsakanin al’ummar arewacin Nijeriya da na yammaci baki ɗaya, kuma har gobe al’ummar Yarbawan Nijeriya na raya wannan rana ta hanyar juyayin Bayarbe ya ci zaɓe shugaban ƙasa ɗan Arewa ya soke saboda bay a ra’ayin haka.
A lokacin da aka soke wannan zaɓe dukkan alamomin tankiya sun bayyana tsakanin al’ummar Arewa da ta kudancin wannan ƙasa. Shi dai M.K.O. Abiola da ake ganin shi ya lashe zaɓe tuni ya bayyana nasararsa da kuma ayyana kansa shugaban ƙasa. Haka kuma dukkan harkokin ƙasa na sufuri das aye da sayarwa da sauran harkokin tattali arzikida zamantakewar girma da arziki sun tsaya cik. A daidai wannan lokaci ne Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai abin ya dame shi har ya kai ga sai da ya yi waƙar sulhu mai taken ‘’Yan Nijeriya’, inda yake cewa:
Jagora: ‘Yan Nijeriya ‘yan uwa mu yi ƙoƙari
Mu zan haɗa kanmu mun kama hanyar gaskiya

A nan muna iya ganin yadda mawaƙin ya ƙulla turakun waƙarsa da muhimman kalmomi masu nuni da kusanci da juna da kuma ƙaunar juna. Waɗannan kalmomi kuwa su ne, ‘yan uwa da haɗa kanmu . Said a ƙaunar juna ake iya haɗa kai sannan sai an haɗa kai ake samun cigaba. Dagan an sai Ɗanba’u ya ci gaba dad a addu’a ga ‘yan Nijeriya da ita kanta Nijeriya kamar yadda yake cewa:
Jagora: Gyara min Mai sama
Allah Kai ked a mu
Ka taimaki Najeriya
Kandami babbar ƙasa
Amshi: ‘Yan Najeriya, ‘yan uwa mu yi ƙoƙari
Mu zan haɗa kanmu mun kama hanyar gaskiya.

Mawaƙa na da hanyoyi da daman a isar das aƙonninsu ga al’umma, ciki har dadabbantar da mutum ko mutane ko kuma mutumta dabba. Kamar yadda Ɗanba’u ya dabbantar da mutanen Nijeriya a nan ta hanyar alamta su da halittun ruwa kamar haka:
Jagora: Kiti da kada da kwaɗo dorina
Halittarsu daban-daban amma in mun tuna
Amshi: Dug gidansu yana ruwa.

A nan sai mu ga tamkar yadda Nijeriya ta al’ummomi daban-daban masu harsuna iri-iri da addinai kala-kala; haka ita ma teku ta ƙunshi halittu iri-iri masu ɗabi’i daban-daban amma kuma, suna zaune da junansu lafiya babu tsangwama bale tankiya. Sai kuma a gaba Ɗanba’u ya ƙara fashin baƙin karatunsaya fiton a fili ƙarara domin waɗanda aka yi dominsu su sani, sai ya ce:
Jagora: Ina Yarbawa, Nufawa, ina jama’ar Ibo?
Had da ku jama’ar Ibo
Duk ku zo mu taru gaba ɗaya mu koma ‘yan uwa.

Ɗanba’u na day aƙinin cewa zamantakewar ‘yan Nijeriya nab uƙatar kawar da tunanin ƙabilanci domin a haɗa ƙarfai da ƙarfe domin tafiyar ta yi armashi, kamar yadda yake cewa:

Jagora: Kun gani Nijeriya,
Mai yawan faɗin ƙasa,
Al’adummu daban-daban,
Addinimmu daban-daban,
Allah Mai ƙaddarowa a kowane al’amar,
Shi Ya ƙaddaro munka zauni wuri ɗaya,
Kuma ƙasarmu tana ɗaya

Amshi: ‘Yan Najeriya ‘yan uwa mu yi ƙoƙari
Mu zan haɗa kanmu mun kama hanyar gaskiya.

Ko a waɗannan ɗiyan waƙa Ɗanba’u ya kawo kalmomin hikima waɗanda tamkar ƙarfafawa ne ga zancen sulhu da haɗin kai da kuma inganta zaman tare tsakanin al’umma. Misali, inda ya ce: “Allah Mai ƙaddarowa a kowane al’amar” da “Shi Yaƙ ƙaddaro munka zauni wuri ɗaya” da kuma “ƙasarmu tana ɗaya”
A nan manuniya ce ga duk mai hankali ya san cewa duk abin da Allah Ya yi shi ne tabbatacce.Haka kuma ba mai iya kawar da abin da Allah Ya riga Yaƙaddaro sais hi da kansa.
A gaba Ɗanba’u ya nuna wani muhimmin gargaɗI ga dukkan ‘yan Nijeriya. Kamar yadda aka sani kowace ƙasa na da masoya da maƙiya kuma haka ta fi bayyana idan ƙasa na cikin yaƙin basasa da ‘yan tawayenta. Domin lokacin ne ‘yan zuga ke bayyana. Munafukai su yi ruwa su yi tsaki,wasu kuma su yi tab a ‘yan tawaye makamai da agaji na kuɗI da motoci da sauran kayan aiki, kamar dai yadda ya faru ga Nijeriya lokacin yaƙin basasa. Wasu takwarorin Nijeriya suka zamo inda munafukai sannan sai aka haɗa da wasu ‘yan baranda marasa kishin ƙasa suna ƙasa hasguɗa wutar basasar. Ɗanba’u bai manta da irin waɗannan ƙasashe da mutane ba kamar inda ya ce:
Jagora: Kar ku yarda da ‘yan baranda da ‘yan zambar ciki
Masu son su haɗa ku sauran su koma tsallake.

Idan ta rikice ba shakka buƙatarsu ta biya. Don haka wannan gargaɗI ne mai muhimmancin gaske ga ‘yan Nijeriya domin su kula da irin wannan badaƙala a ɓangaren ‘yan shigo-shigo ba zurfi.

Karanta wannan

https://www.amsoshi.com/2017/07/29/tsakanin-%c6%99-arya-da-gaskiya-nazarin-wa-d-ansu-wa-%c6%99-o-%c6%99-littafin-specimens-hausa/

1.4 Kammalawa


Bayanan da suka gabata sun tabbatar muna da cewa dukkan ƙabilun Nijeriya na iya tattaruwa su fito das aƙonnin haɗin kansu da tabbatar da sulhun rigingimu da faɗace-faɗacen da kan shigo tsakaninsu. Wannan misali da mawaƙa da marubutan waƙoƙin Hausa sun tabbatar mana. Wannan shi ya nuna cewa mawallafa da mawaƙan koyaushe a shirye suke su bad a kai bori yah au a kan za a yi sulhu da daidaita duk wata rigima idan ta taso a Cikin Nijeriya.
Sannan ƙabilun Nijeriya, wato Hausawa da Ibo da Yarbawa da Fulani da Dakarkari da Tibi duk akwai mawaƙa kuma, kowane a shirye yake ya ba da tasa gudummuwa a fagen tsara waƙa da ta shafi sulhunta duk wata tankiya da tashin-tashina cikin ƙasa Nijeriya , har ma da maƙwabtanta.

References


Atuwo, A.A (2001) “The Concept of Vocational Education as Contained in Barmani Coge’s and Karen Gusau’s Songs on Self-reliance Jovek. No 1

Atuwo, A.A; (2013) “Relevance of Folklore in Conflict Resolution” Paper presented at International Conference on Folklore and National Integration and Development, organized by Center for the Studies of Nigerian Languages , Bayero University, Kano. From 2nd – 5th, April, 2013

Adebayo, A.; (1999), Comprehending and Mastering African Coflicts: The search for
Sustainable peace and Good Governance, London, zed books.

Abdulkadir, D.; (1975) “The Role of an Oral sugar in Hausa/Hausa Fulani society” A case study of Mamman Shata Unpublished Phd. Thesis India University USA

Bichi Y.A. (1968) Baitoci dubu na waqar tarihin Rikicin Nijeriya, Zariya ,NNPC
Gusau, S.M.; (1996) Makaxa da Mawaqan Hausa, Kaduna ,FIBAS
Ladan A. (1976) “Wakar Haxa kan Al’ummar Afirika,,Ibadan , Oxford University press.
Umar M.B. (1965) Xanmaraya Jos da Waqoqinsa, Ibadan University Press
Uwechue, R . (1991) Africa today 2nd Edition, London, Africa Books
William C. (1979) How does a poem mean ? New York Hugton Mifflin
Waqar Yan Nijeriya ta Musa Xanba’u
Waqar Munafukkan yaqi ta Adamu Xanmaraya Jos
Waqar Haba ‘yan Nijeriya ta Xantala Jos
Waqar Don Zaman lafiya ta Musa Xankwairo
Waqar Yan Nijeriay ta Shehu Ajilo.

ƙuruci Dangin Hauka: Waiwayen Yarinta Cikin Harshen Sadarwa A Ma’amalar Rayuwar Yaran Hausawa Jiya Da Yau

DAGA

Sama’ila Umar
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.
07031948326 & 08022857551
E-mail: samzariya@gmail. com

Takardar Da Aka Gabatar A Taron ƙarawa Juna Ilimi Na Duniya, Kan Asalin Hausawa Da Harshensu Da Tarihinsu A Jiya Da Yau Da Kuma Gobe. Wanda Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyar Harshe, Na Jami’ar Jihar Kaduna Ta Shirya, Daga Ranar 23nd zuwa 25th Maris 2015.

TSAKURE
Ba shakka kyakkyawan tsarin zamantakewa jigo ne wajen gina ƙasa, kuma duk ƙasar da ta ke son ci gaba, ba za ta watsar da zamantakewar iyali ba. Saboda haka ya zama wajibi ga masu jagorantar al’umma na kowace ƙasa su ɗauki duk wasu mahimman matakai na inganta rayuwar iyali, don su zamo manyan ƙudurorinsu na gina ƙasa. Duk da sanin hakan sai aka sami matsaloli da suka dabaibaye iyali a yau, kuma waɗannan matsalolin su suka haifar da samuwar laifuffuka daban-daban a ƙasar nan. Haka kuma su suke haddasa sukurkucewar tsarin zamantakewa da yawan mutuwar aure da wulaƙanta yara da sace-sace da shaye-shayen kayan maye. Iyali a yau cike suke da matsalolin rayuwa, tun daga auratayya har ya zuwa yanayin zamantakewar yau da kullum. Wannan ya haddasa samun sauyi tsakanin yanayin rayuwar yarinta a ƙasar Hausa ta yau da wadda aka gabatar a da. Burin wannan muƙalar shi ne, ta gudanar da waiwaye kan tsarin rayuwar sadarwa cikin harshen ‘yan’yan Hausawa a da, da kuma yadda take gudana a yau. Shin ci gaba aka samu ko koma baya?

1.0 Gabatarwa
Iyali suna ne da ya ƙunshi dukkan mutanen da ke zaune a gida guda ƙarƙashin kulawar maigida, wanda yake shi ne jagoran tafiyar da harkokin rayuwar duk wanda yake zaune a wannan gidan. Bisa la’akari da tsarin zamantakewar rayuwar Bahaushe, iyali ba wai mata da ‘ya’ya ne kaɗai iyali ba, a’a har ma da duk wani wanda yake zaune ƙarƙashin kulawar maigida, waɗanda suka haɗa da ‘yan’uwa da ‘ya’yan ‘yan’uwa da agololi da barori da duk wanda rayuwarsa ta dogara ga maigida, ciki har da kakanni da iyayen da ƙarfinsu ya yi rauni. Sai dai abin sha’awa a fasalin rayuwar Bahaushe shi ne, kowa da matsayinsa da kuma irin rawar da yake takawa wajen ciyar da iyali gaba. Al’ummar Hausawa suna da tsarin rayuwa mai kyau, ta fuskar kula da haƙƙin rayuwa, tun kafin musulunci ya shigo ƙasar Hausa (Yakasai 2012:97). Hausawa na da matakan rayuwa na zamantakewa da suka shafi auratayya da zumunta da sauran haƙƙoƙin zaman tare da suka haɗa da maƙwabtaka da dangantaka da abokantaka da sauran abubuwan da zama tare ke haɗa wa. Da yawa daga cikin ƙa’idojin da musulunci ya zo da su ƙasar Hausa, ba su zame wa Bahaushe matsala ba, wata ƙila don ya saba da ire-iren ƙa’idojin da yake da su a tsarin rayuwarsa. Alalmisali dokokin tada da camfi da na tsafi, duk sun taimaka wajen samun sauƙi lokacin da Bahaushe ya tsinci kansa a matsayin musulmi. Bahaushe ya aminta da cewa kowane mutum tsarin rayuwarsa tana fara wa ne daga yarinta. Don haka ya yi wata karin magana mai cewa “yaro masomin babba” Kudan (2010:1). Yarinta abar sha’awa ce musamman wadda ta sami gatan kulawa. Sanin haka ya sanya wannan muƙalar take ganin ya dace da ta waiwayi wasu abubuwan da aka aiwatar a tsarin rayuwar yarinta a da, da kuma yau ta fuskar sadarwar harshe, don ganin yadda aka tsinci kai a yau. Ganin haka ya sa muƙalar ke son laɓewa don ta sabunta ko ta tunatar da mazan jiya yadda rayuwa ta gudana a yarintaka, sai ake ganin ya dace a fara da nuni cikin harshen sadarwa, domin da sadarwa ake ma’amala. Sanin mahimmancin sadarwa cikin harshe shi ya sanya masana ke ganin ita ce ginshiƙin gina iyali. In haka ne kuwa muƙalar ta yo waiwaye kan yadda sadarwa ke zama hanyar gina iyali. Daga nan sai aka waiwayi tsarin rayuwar yarinta a da, kuma aka kawo irin ta yanzu domin sanin irin ci gaban da aka samu ko kuma gano irin koma bayan da aka samu a yau. Domin samun sauƙin bincike, muƙalar ta zaɓi yankin gundumar Muchiyar Ɗan’auta da ke Sabon-garin Zariya a matsayin farfajiyarta ta gudanar da binciken.
2.0 Da Sadarwa Ake Ma’amala
Masana ilimin walwalar harshe sun yi bayanai kan sardawa da abin da ta ƙunsa. Wasu na ganin sadarwa yanayi ne na sarrafa bayanai tsakanin al’umma cikin tsarin alamomi da ishara da kuma ɗabi’a. Haka kuma wasu ke ganin sadarwa na damfare da ma’ana fiye da bayanai a tsare, ba kara-zube ba (webster 1973 a cikin Yakasai 2012). Abin nufi a nan shi ne, ma’ana cikin sadarwa ita ke haifar da ingantacciyar ma’amala a zamantakewa, irin wannan sadarwar ita ke sa yara suke iya adana mahimman abubuwan da suka gudanar a rayuwarsu ta yarinta. Ingantacciyar sadarwa na aukuwa a lokacin da ƙwaƙwalwar ɗan Adam take a matsayin wani rumbun tunani wanda ta hanyar aikace-aikacensa na yau da kullum take adana mahimman abubuwan da rayuwa ta ƙunsa, musamman abubuwan da suka auku a lokacin ƙuruciya (yarinta). ƙwaƙwalwa na adana ire-iren waɗannan tunane-tunanen ne don su yi amfani a gaba. Hasali ma ana iya cewa sadarwa ita ce ƙashin bayan kowace irin ma’amala da kan auku a tsakanin al’umma, kuma ita ke sauƙaƙa fahimtar al’amuran rayuwa gaba ɗaya. Sadarwa ba ta yin tasiri tsakanin mai ba da saƙo da mai karɓar saƙon har sai ma’amala ta dace da fahimtar da ake son samu ta hanyar sadarwa mai ma’ana. Sadarwa ita ke haifar da fahimta mai ma’ana har ƙwaƙwalwa ta sami abubuwan da za ta iya adanawa, wanda wani lokaci kan iya zama abin tunawa bayan tsawon lokaci. Irin wannan sadarwar ita ke sanya mutum ya tuna da wasu mahimman al’amura da suka faru a lokacin yarintarsa. Duk abin da ya zaunu a ƙwaƙwalwar mutum a lokacin yarintarsa ana iya samun tarsashin sa a tsarin rayuwarsa a lokacin da ya girma. Haka kuma duk irin fahimtar da aka samu a lokacin sadarwa a ma’amalance musamman ma lokacin yarinta ba a cika mantawa da shi ba. Sadarwa ba ta yiwuwa sai da ma’amala, haka kuma ma’amala ba ta inganta sai da fahimtar ma’ana a lokacin sadarwa. Don haka ma’amala ta hanyar sadarwa a lokacin yarinta ta zama kamar adanannen rubutun da ya shafi tarihin rayuwar al’umma.
3.0 Mahimmancin Sadarwa Wajen Gina Iyali
Burin kowane maigida ya ga cewa iyalinsa sun sami yanayin rayuwa mai inganci. Samun yanayi mai kyau kuwa ba ya samuwa sai da ingantacciyar sadarwa tsakanin maigida da ɗaukacin iyalinsa. Iyali kuwa su ne jama’ar da suke ƙarƙashin maigida. Waɗannan jama’ar sun haɗa da matansa da ‘ya’yansa da ‘ya’yan ‘yan’uwa da ƙanne da duk wanda yake zaune a tare da shi, kuma ya dogara rayuwarsa kacokan kan maigida. Waɗannan ƙanne da ‘ya’yan ‘yan’uwa da sauran jama’ar da suka dogara ga maigida, su ake kira da iyali. (Rufa’i 1986 in Yakasai 2012:50)
Tafiyar da jagorancin iyali ba zai taɓa yin tasiri ba, sai har an sami kyakkayawar sadarwa mai ma’ana tsakanin jagora da mabiyansa. Fahimta mai ma’ana ta sadarwa ita ke haifar da samun walwala cikin nishaɗi da iyali kan yi a lokacin da maigida ke sadar da ma’amala tsakanin sa da su. Irin wannan ma’amalar ita take taimakawa yara wajen samun tunani mai inganci, wanda zai zame masu abin tunawa kan duk abin da ya faru a rayuwarsu ta ƙuruciya. Was daga cikin abubuwa da kan sa yara su tuna da ƙuruciyarsu sun haɗa da karatunsu da wasanni da ma’amalarsu da ta shafi abokanensu da iyayensu da duk wani mutum da ya kamata su yi ma’amala da shi. Wannan mahimmacin sadarwar kan taimakawa yara wajen naɗar abubuwan da suka aiwatar a rayuwarsu ta yarinta.
Wani babban mahimmancin sadarwa wajen gina iyali shi ne sadarwa tana samuwa ne a lokacin da aka sami fahimtar juna tsakanin maigida da sauran jama’ar da yake yi wa jagoranci ta hanyar yin amfani da kyawawa lafuzzan ma’amala a tsakanin su wadda ƙaunar juna take yi wa jagoranci. Wata sadarwa da ke gina iyali ita ce ta tsakanin miji da matarsa wannan sadarwar tana buƙatar amincewa juna ta hanyar tattauna mahimman al’amuran rayuwa cikin so da ƙaunar juna da gimamawa, ba tare da tsangwama ba. Sannan kuma ƙaunar ta zamana ta koyarwa da tarbiyantarwa ga yara bisa tsarin rayuwa madaidaiciya.
Kusan duk wani ɗan Adam yana da buƙatar wani wanda zai taimaka masa kan harkokin rayuwarsa na yau da kullum. Wato wanda zai ɗauki nauyin wasu abubuwan rayuwarsa na yau da kullum. A taƙaice mutumin da za a yi ma’amala da shi ta rayuwa da ta shafi dangantaka da ma’amalar zamantakewa. Don haka Roumer (1973) ke cewa; “Rayuwa takan yi daɗi a lokacin da ma’aurata suke gudanar da rayuwa tare cikin so da ƙaunar juna”. Saboda haka wajibi ne a yi ma’amala cikin sadarwa da kyautatawa domin cikas cikin sadarwa kan haifar da matsalar zamantakewa(Yakasai 2012:97). Kenan sadarwa ita ke samar da inganci wajen gina rayuwar iyali har a sami daidaito a zamantakewa.
Wani mahimmancin na sadarwa shi ne, inda ake iya samun nasara cikin dangantakar sadarwa tsakanin iyali, ita ce ta inda duk mutumin da ya san ya kamata, kuma ya san yadda zai bayyana abin da ke cikin zuciyarsa ba tare da ruɗani ba. Wato baya ga jawo hankali da neman goyon bayan da yake yi ga iyalansa, shi kuma yana fahimtar manufar iyalin nasa da matsalolinsu. Yara kan sami nasarar walwala a lokacin da suka nuna sha’awrsu da abubuwan da iyayensu suke ƙoƙarin ɗora su a kai don samun ci gabansu na rayuwa. Haka kuma sadarwa mai ma’ana tsakanin shugabannin al’umma da mabiyansu tana taimakawa wajen samawa yara makoma ta gari, wadda yin haka ke taimakawa wajen raya ƙasa da ci gabanta. Ana gudanar da kyakkyawar ma’amala a lokacin da iyaye da yara suka fahimci junansu ba tare da ƙullatar juna ba. Sadarwa mai inganci ita ce inda iyaye suke ma’amala da yaransu ba tare da tsorata su ba, ko nuna masu ƙyama da tsangama ba. Dole ne iyaye su naƙalci iya ma’amala da yaransu cikin so da nuna ƙaunar juna cikin ma’amalarsu ta yau da kullum. Kyakkyawar sadarwa mai ma’ana ita ce hanya mafi sauƙi wajen gina iyali.
4.0 Yarinta Cikin Rayuwar Hausawa
Yarinta wani mataki ne da yake zama kamar harsashin soma tsarin rayuwa na kowane ɗan Adam. Bayan haihuwa sai yaye bayan wannan mataki na yaye kowane ɗan Adam kan tsinci kansa cikin wani yanayi na rayuwa, a wannan matakin ne mutum ke ƙoƙarin koyon wasu abubuwa da suka shafi al’amuran rayuwa. Bayan wannan mataki na yaye da uwa kan ɗauki ɗawainiyar kula da koyar da yaro ko yarinya tsarin rayuwa sai kuma matakin da sauran jama’a za su sa hannu wajen ganin yaro ko yarinyar sun sami nasara wajen gudanar da yarintarsu. Wannan mataki da ɗan Adam ya shiga shi ake kira yarinta. Don haka Kudan (2010:1) ya ce; yarinta ko ƙuruciya ita ce wata rayuwa da ke farawa daga haihuwa zuwa samartaka. Wannan rayuwa ita ake kira yarinta ko farkon rayuwa. Rayuwar ƙuruciya ba abin da ya fi ta daɗi da wuya. Daɗin wannan rayuwar shi ne, Hausawa ba suna zaune kara zube ba ne, suna da tsarin rayuwa wadda take cike da tsare-tsare da suke yi wa al’ummarsu ta hanyar jagoranci. Suna da tsari mai armashi tun kafin shigowar addinin musulunci ƙasar Hausa. Domin suna da tsarin rayuwa da aka gina ta bisa ingantacciyar hanyar sadarwa, kuma aka sama masu ƙa’idoji don su zama turakun ma’amala a harkokin yau da kullum. Hausawa suna da tsarin zamantakewa da suka shafi al’adun auratayya da na tarbiyya. A fasalin zamantakewar Hausawa suna da tsarin ma’amala tsakaninsu wadda ta shafi rukuni shekaru. Harshen Hausa na taka mahimmiyar rawa wajen bayyana yadda ake sadarwa a rukunonin jama’a ta fuskar ma’amalar yau da kullum. Bayan Bahaushe ya karɓi musulunci sai ya ƙara wasu hanyoyin na kula da rayuwar yarintar ‘ya’yansa. Wannan tsarin shi ya ƙara wa tsarin rayuwar yarintar yaran Hausawa armashi. Cikin hanyoyin akwai tsarin karatun makarantar allo. Rayuwar yarinta akwai daɗin tunawa. Ko kun iya tunawa da waɗannan al’amuran a lokacin yarintarku?
• Faɗa mini makarantar allonku da ku ka yi karatu kuna yara. Ko ka tuna irin abin da ka ke saye idan ka/kin je makaranta? Kusan kowace makarantar allo a ƙasar Hausawa tana da sunan da ake kiran ta da shi. A tsarin makarantun an fi kiran su da sunayen malamansu. Alalmisali makarantar Malam Mai toto, ko makarantar Malam Audu mai jan kunne, ko makarantar Malam Yahaya da makamantan su. A kowace makaranta ana samun wasu tsofaffi da suke kawo kayayyakin ƙwalama da yara kan saya don nishaɗi. ire-iren kayayyaki sun haɗa da; carbin malam/hajiya da kantingana da ɗantamatsitsi da alawar ƙwanƙwalati da goruba da aya da tabar malam (a sha a busa) da hallaka kwabo da ɗansililin da garin biɗiɗis da gyaɗa marau-marau da sandar ba’are da fitsarin bature da magarya da daƙuwa da ɗan tamarere da tsami-gaye da shaye-shaye da romo da alewa irin ta da. Waɗannan kayayyakin na ƙwalama kan sa yaro ya ji ba ya son fashin zuwa makaranta. A wannan zamanin iyaye ba sa ba yaransu ƙwarin guiwa ta wannan hanyar don su maida hankali kan karatunsu don haka ake samu yara da yawa masu ƙin zuwa makaranta.
• Wai kuwa yaran yanzu suna wasan daren ranar alhamis da juma’a sanda ba makarantar allo ta dare? A zamanin da kowane daren alhamis yara kan taru a dandalin unguwanninsu a yi ta wasanni iri-iri. Wasu daga cikin wasannin na nuna bajinta ne, wasu kuma na nuna basira da hikima ne. ire-iren waɗannan wasannin na nuna bajinta sun haɗa da: Turke da kulli kurciya da Allan ba ku da langa da letur da oji’ojiyo da jini ya jini danja da jangiro. Wasu daga cikin wasannin hikima da basira su ne; malam na bakin kogi da riƙe mini zobena. Yaran yanzu ba sa samun damar gudanar da ire-iren waɗannan wasannin, domin an kashe wasannin da kallon fina-finan bidiyo da sidi. Waɗannan sababbin abubuwan kallon ya raunana sadarwar da ake samu tsakanin yara da tsararrakinsu ko abokanensu, inda ƙwaƙwalwarsu take ƙara buɗewa da basira wadda ta dace da ƙasar Hausa.
• Idan na tuna lokacin da muke fita tashe da watan azumi nakan ji daɗi. Duk yaro idan watan azumi ya kama ba abin da yake son ji da gani irin a ce an yi azumin goman farko. Wannan lokacin ne yara kan yi wasannin kwaikwayo cikin nishaɗi, tare da wasu wasannin ban dariya da ban sha’awa a cikin tashe. Misalin tashen da mukan yi muna yara shi ne, maiƙiriniya: wannan tashen yaro ake ɗaurawa igiya a kwankwaso a shafa masa bula ko baƙin tukunya, idan aka shiga gida sai ya riƙa kawar da kayayyakin da aka bar su a warwatse yana jera su daki-daki, ana cewa ‘maiƙiriniya, sai ya ce iye! Wa ya saka ne sai ya ce baba, in aka sake tambayar sa sai ya ce Inna’. Haka za a yi ta tambayar sa yana ba da amsa. Yara mata kuma suna yin tashen da ake kira dare yaro mairama, wannan tashen yana koyar da yara mata halayyar zaman gidan miji ne. Domin suna kwaikwayon irin yadda mata ya kamata ta yi wa mijinta ladabi da biyayya ne.
• Ni dai ban taɓa laɓewa a banɗaki ba a lokacin da nake azumi in sha ruwa ina yaro. Kai fa? Laɓewa a banɗaki a watan azumi ga yaran Hausawa wata hanya ce da akasarin yaran kan yi amfani da ita wajen karya azumi, musamman idan ƙishi ya fara cin ƙarfin yaro. Kuma wani abin sha’awa shi ne, yara ‘yan shekara takwas zuwa goma duk suna iya ɗaukar azumi. Amma a wannan zamanin za a iya samun yaran da suka balaga ba sa iya azumi, saboda matsalar sadarwa da ake da ita tsakanin iyaye da ‘ya’yansu. A halin yanzu saboda yankewar ma’amala mai ma’ana da ake samu tsakanin iyaye da yaransu ta haifar da ƙaruwar shaye-shayen kayan maye wanda ke haddasa rashin kula da harkar rayuwa.
• Allah sarki motar karata da motar gwangwanina, ko wa ya ɗauke mini su? A tsarin rayuwar yarinta ta ‘ya’yan Hausawa a da tana tattare da wata irin baiwa da Allah ya yi masu wajen samawa kansu kayayyakin wasanni. Sannan suna nuna irin wannan basirar ne wajen ƙera wasu abubuwa da ya shafi rayuwar mutane ta zahiri don nuna hazaƙarsu ta kimiyya. Waɗannan hanyoyi na yarintar ‘ya’yan Hausawa a da, suna tattare da abubuwa masu ɗarsa zuciya har a kasa mantawa da su. Wasu abubuwan da kan zauna cikin zuciyar yarinta ga ɗan Bahaushe har da irin rayuwar da ta gudana a lokacin makarantar boko da wasu abubuwan rayuwa da zamani ya zo da su. Samun nasarar yarita ta ta’allaka ne ga irin jituwar da take tsakanin iyaye da yaransu, don haka Akpan (1980:19) yake cewa;” bayan matsayi da kimar iyaye a wurinn ‘ya’yansu, suna kuma buƙatar zalaƙa ta magana domin jawo hankali da goyon bayan yaransu”. wannan ya tabbatar mana da cewa wajibi ne yara su zama masu sha’awa ga abubuwan da mahaifa suke yi don samun nasarar iyalansu. Wannan na nuni da cewa ci gaban iyali ba ya yiwuwa sai da fahimtar juna, tsakanin iyaye da yaransu. Wannan sai ya sa nazarin ya waiwaya baya don tunato wasu mahimman abubuwa da yarintar ta ƙunsa. Ko za ku iya tunawa da waɗannan abubuwan a rayuwar jiya?
• Kun tuna sanda ake dawowa daga makarantar boko ana jin yunwa?
A zamanin da idan aka taso daga makaratar boko, ba abin da yaro yake ƙoƙarin ya ga ya yi in ban da kai wa gida. Dalilin da yake sa yaro maida hankalinsa zuwa gida abu uku ne; na farko yunwa, don haka yana hanzarin ya koma gida don ya sami abinci ya ci. Na biyu kuwa shi ne ba ya son iyayensa su shiga tunanin me ya same shi? Ya ɓata ne ko wani abu ya cutar da shi, don haka ya kasa komawa gida kamar yadda ‘yan’uwansa suka koma? Sannan kuma ya san akwai makarantar allo da yamma, ba ya son ya makara. Amma a yanzu yara na irin wannan tunanin kuwa? Da yake abin ya sauya a wannan zamanin, a da da ‘ya’yan attajirai da na talakawa duk makaranta ɗaya ake zuwa abin gwanin ban sha’awa amma a yanzu ‘ya’yan masu sukuni makarantarsu daban da ta ‘ya’yan faƙara’u, don haka wata ƙila rayuwar yarinta a makaranta ta sauya.
• Oho! Ko ka tuna wani littafin rubutunmu da muke yi wa waƙa na ɗaya fafalolo?
• Ka tuna da biron nan da ake saye, mai suna Eliganza?
• Ka tuna kyautar da Malamai ke yi wa ɗalibai a lokacin darasi, idan aka yi tambaya ka ba da amsar da ake so?
• Ka tuna da ire-iren kyaututtukan da ake bai wa waɗanda suka yi na ɗaya da na biyu da na uku a ƙarshen zangon karatu?
Duk lokacin da na tuna ire-iren waɗancan abubuwan da ake samu a lokacin rayuwar yarinta, sai tausayi ya kama ni, lokacin da na ga yaran yanzu suna fama da matsalolin rayuwarsu a makarantun boko na gwamnati. Domin sadarwa tsakanin Malamai da shugabannin ilimi da ɗalibai ba a inganta ta ba, ba a samun fahimtar juna. Hasali ma saboda mummunar ma’amala da take gudana tsakanin hukumomi da ma’aikatar ilimi da kuma malamai kullum matsla sai ƙaruwa take. Haƙƙin da ya kamata a bai wa hukumar ilimi ba a ba ta su, kuma ba a ɗaukar waɗanda suka dace su kula da haƙƙin malaman makarantun boko yadda ya kamata. An damƙa haƙƙin ga waɗanda ba su dace da matsayin ba, wato an miƙa akalar ire-iren waɗannan al’amuran a hannun ‘yan siyasa ko da kuwa ba su dace da matsayin ba. A yau malamin makarantar boko ya zama kamar bawa. To idan malami ya zama bawa ɗalibi shi kuma me ne ne matsayin sa?
Wata rayuwar ta yarinta da ta zaama abin tunawa a-kai- a-kai, ita ce rayuwar sadarwa tsakanin hukumar yaɗa labarai da jama’a. Muna yara akan kalli wasu shirye-shirye a gidajen talbijin masu ilmantarwa da nishaɗantarwa. An ya yanzu kuwa akwai irin su?
• Ka tuna sanda idan gidan T.V. za su buɗe sai su saka wani labule mai fari da baƙi?
• Ko ka tuna sanda muke kallon Indiya ranar lahadi a R.T.K?
• Ka tuna sanda ake shirin nan na R.T.K. mai suna ‘Kukan Kurciya’ da ‘ƙuliya Manta Sabo’. A wannan shirin ana ilmantar da mutane yadda za a taimaki wanda yake buƙata taimako da kuma yadda za a ba mai haƙƙi haƙƙinsa. Ana ilmantar da mutane matsalar hassada da rowa da ƙeta. Sannan a ilmantar da mutane amfani taimako da yin gaskiya da kiyaye doka da shari’a da makamantan su. Ko a duniyar yarinta ta yanzu ana ƙoƙarin ba su irin wannan gudummawar? Abin da hankali ke iya gani a duniyar yarintar yau shi ne, an fi maida hankali kan hanyoyin tara kuɗaɗen shiga komai munin su, maimakon fito da ire-iren waɗancan shirye-shiryen na ilmantar da yara.
• Allah ya jiƙan Malam Mamman da Alhaji Buguzum da ƙasimu Yero da Kasagi da Tumbuleƙe da sauransu. ‘Yan wasan kwaikwayo masu ilmantarwa da nishaɗantarwa a ko da yaushe. Yara na jin daɗi duk lokacin da suke kallon wasansu, kuma sukan fahimci saƙwannin da suke son isarwa zuwa gare su kai-tsaye, irin na a kiyaye haƙƙin juna, a guji cutawa al’umma da yadda za a gyara zamantakewar da sauran jama’a. Yara har tsokanar wanda ya yi wata halayyar da ba ta dace ba ake yi, da wani ɗan wasan.

5.0 Kammalawa
Yarinta rayuwar farko! Wannan rayuwa cike take da abubuwan tunawa masu mahimmanci da armashi. Wasu abubuwan kuma abin jin tausayi wasu kuma abin ban dariya. Wannan tsarin na rayuwar yarinta da ake kira da ƙuruciya mai cike da tarihi ga kowane ɗan Adam, ba abin da ke gina ta sai kyakkyawar sadarwa mai inganci da ma’ana. Sadarwa mai ma’ana ita ce wadda ake samun fahimtar juna tsakanin mai ba da saƙo da mai karɓar saƙo. Da zarar an fahimci juna, to an sami ingatacciyar ma’amala wadda za ta yi jagoranci ga samun ci gaban ƙasa.
Hausawa ke cewa “sarki goma zamani goma”, wannan batun abin dubawa ne, musamman idan aka yi la’akari da tsarin rayuwar yarinta ta ‘ya’yan Hausawa a zamanin da da kuma wannan zamanin na yanzu. A da yara na samun kyakkyawar kulawa ta hanyar sadarwa, kama tun daga iyaye zuwa malaman makaranta da shugabannin unguwanni da maƙwabta da abokanen iyaye, kai har ma da gwamnatoci tun daga ƙaramar hukuma har zuwa tarayya. Idan aka dubi ire-iren shirye-shiryen kafafen yaɗa labarai tun daga rediyo zuwa jaridu da gidajen talbijin duk akwai wasu lokuta da aka ƙeɓe wa yara don ilmantar da su wasu mahimman abubuwa da ya kamata su miƙe da su don su ga cewa sun kasance masu gudanar da su a lokutan rayuwarsu Allah ya jiƙan Harira Kaciya, Uwar yara ta kafar rediyo. Wasu abubuwan kuwa ana ilmantar da yara ne don su guje wa aikata ire-iren waɗannan abubuwan a rayuwarsu. Alalmisali wani shiri da ake gabatarwa a gidan rediyon da talbijin na ‘R.T.K.’ a da. Wato gidan rediyon Nijeriya Kaduna a yau, mai suna ‘yaraa manyan gobe!’ wanda in za a iya tunawa ɗaya daga cikin masu gabatar da shirin ita ce Mairiga Aliyu. Wannan shirin kowane ɗan Bahaushe da yake a Zariya da kewaye yana son lokacin gabatar da shi ya yi don ya saurara ya sami wasu abubuwan da zai ƙara masa ƙwarin guiwa don ya himmatu a makaranta. Ya yi ƙoƙari ya zama wani mahimmin mutum da zai taimaki al’umma. Domin a cikin shirin ana yi wa yara tambayoyin abin da suke son zama in sun kammala karatunsu. Haka abin yake idan ka waiwaya wajen gwamnati, a da da wuya a ce an kwashe watanni ba a yi majigi don faɗakar da al’umma ba, ko a sa wani shiri don koyar da kiyon lafiya ko hanyar inganta sana’a da sauran makamantan waɗannan ababen. Haka abin yake a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo’ akwai shafukan yara manyn gobe. Malamai kuma sukan ba yara masu hazaƙa kan darussansu da suke koyarwa kyaututtuka a cikin aji don ƙara masu ƙwarin guiwa. Shin a yau abin haka yake? Me ya hana hakan ci gaba?
Yaran wannan zamanin ruwa ya ci su! Domin ba kyakkyawar sadarwa tsakani iyaye da yara saboda matsalolin da suka dabaibaye iyaye a yau. Haka abin yake tsakanin gwamnati da sauran al’umma. Sadarwa tsakanin gwamnati da shugannin al’umma ba ta da inganci. Makarantun gwamnati sun zama matattara mashaya, saboda rashin kulawa da su. Wanda a da kowane matashi yana da abin da ya sa a gabansa ko da akwai masu mugun hali to kuwa yana jin tsoron shiga cikin makaranta ya aikata abin da bai kamata ba, saboda shakkun malaman makaranta. A da malaman makaranta suna da kima da martaba a idanu jama’a, a yau kuwa mutunci an kawar masu da shi kuma kimar ta tsere ta bar su. A yau an mai da malamin makaranta kamar karen farauta saboda saka su cikin harkokin siyasa da aka yi. Sannan wasu daga cikin malaman na firamare da sakandare ba su cancanci koyarwa ba aka ɗauke su don wani buri na siyasa. Saka siyasa a harkar ilimi koma baya ne ga rayuwar yara manyan gobe. A daidaita sahun wannan sadarwar ko a sami sauyi a gobe!

Manazarta
Akpan, E. 1980. “The Relevance of Information Theory to Human Commucation”, in Journal of Language Arts and Communication, Vol.1, No.2.
Kudan, M.S. 2010. ƙuruciya A Al’adar Bahaushe (Psychology). Kaduna: Abdulkarim Printing Press.
Rufa’i, A. 1986. “Dangantakar Harshe Da Al’umma”. Paper Presented At Hausa Week, School of Preliminary Studies, Kano.
Sheik, A.A. Da Yahya, A.B. 1999. Wannan Yaro!! Kaduna: Fisbas Media Services.
Webster, 1980. Dictionary of Contemporary Society. Hong Kong: Oxford University Press.
Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services LMD.

www.amsoshi.com

Post a Comment

5 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.