Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Hada-Hadar Kudi A Tattalin Arzikin Hausawa: Duba Ga Wasu Littattafan Kagaggun Labaran Hausa

Na

Umar Aliyu Bunza

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07063532532
Ƙibďau: aliyubunzaumar@yahoo.com


Money is one of the most important things that have direct and indirect impact on the life of people. It is with money that people buy, sale as well as paying taďes etc. In Hausa society, money plays important role in changing the minds of many people. Many Hausa people change their decision for the purpose of money. It is in Ƃiew of the above, that the paper aimed at studying the role of money in some Hausa novels which include Ruwan Bagaja, Tura ta Kai Bango, Fitsarin FaƘo Mallakin Zuciyata, ‘Yartsana etc. The method used for this study, is the reading and analysing of some portions of the noƂels in which the role of money is found.

1.0 Gabatarwa


Dukkan lamurran tafiyar da rayuwar ďan Adam a yau sai tare da kuďi suke tafiya yadda ya kamata. Da kuďi ake hada-hadar kasuwanci mafi sauƘi. Da kuďi ake nuna isa da neman girma da alfarma da sauransu. Ganin irin matsayin kuďi a al’amurran duniya ya sa wasu mutane suke neman kuďi ido rufe. Mutum kan sauya tunaninsa don ya ga kuďi, ko don a ba shi, ko kuma don an ba shi. Wannan ya zama ruwan dare har cikin adabin Hausa.
Ƙagaggen labari nau’i ne na rubutaccen adabin Hausa, kuma wata taska ce ta musamman da ake iya tsintar kowane irin abu da ya shafi rayuwar ďan Adam. La’akari da kusancin rayuwar mutum da kuďi ya sa wasu marubuta labaran suke sakaďa yadda kuďi ke sauya tunanin mutane cikin wasu sassan labaransu. Manufar wannan maƘala ita ce, nazarin hada-hadar kuďi a tattalin arzikin Hausawa daga wasu littattafan Ƙagaggun labaran Hausa.

2.1 Dangantakar 'Dan Adam Da Kuďi


Tun da Allah (SAW) ya halicci mutum ya Ƙawata masa son wasu abubuwa guda 7 cikin zuciyarsa. Kuďi na ďaya daga cikin waďannan abubuwa. Allah ya ce:
An Ƙawata wa mutane son sha’awoyi daga mata da ďiya da dukiyoyi abubuwan tarawa daga zinariya da azurfa, da dawaki kiwatattu da dabbobin ci da hatsi. Wannan shi ne daďin rayuwar duniya. Kuma Allah a wurinSa kyakkyawar makoma take (Surah ta 3: 14).
Kuďi sun kasance abokan rayuwar mutum ta yadda kowane irin abu na rayuwa da su ake yi. Neman biyan buƘatar rayuwa ya sa wasu mutane ke neman kuďi ta kowace hanya. Wasu mutane kan rasa rayukansu wajen neman kuďi. Wasu kuma sukan halaka wasu don su sami kuďi. Wasu kuma sukan bi kowace irin hanya ta gaskiya ko rashin gaskiya don kuďi kawai. Lamarin kuďi ya sa tunanin mutane da yawa yakan sauya daga fari zuwa baƘi, ko daga baƘi zuwa fari. A yau mutane da yawa ba su da tsayayyen tunani, ba su da tsayayyar magana ko zaƂin rai saboda kuďi kawai.

3.1 Kuďi A Adabin Bakan Hausa


Adabin bakan Hausa (adabin gargajiya) shi ne adabin da Hausawa suka gada daga kaka da kakanni. Wato adabin da yake asalinsa, in ma daga wani wuri ya zo, to, yana da nisa (Ɗangambo, 1984: 9). Shi wannan adabi fage ne mai faďi da ya Ƙunshi lamarin rayuwar mutane ta kowane gefe. Cikin adabin bakan Hausa akan sami abin da ya shafi zamantakewa, tsarin mulki, addini, da sauran abubuwan da mutane suke so, ko kuma suke Ƙi. Lamarin kuďi na ďaya daga cikin abubuwan da ake hangowa cikin adabin. Wannnan ya Ƙunshi tasirin kuďi cikin rayuwar mutane ta hanyar fa’ida da illa. Da yake adabin baka na da rassa daban-daban zan dubi karin magana da waƘoƘi da labarai don ganin tasirin kuďi a rayuwar mutane.

3.1.1 Karin Magana

Karin magana na ďaya daga cikin muhimman rassan adabin bakan Hausa da ke Ƙunshe da lamarin rayuwar Hausawa. Shi dai karin magana wata ‘yar gajeruwar jimla ce ta hikima wadda ta Ƙunshi ma’ana mai yawa in za a tsaya a yi bayaninta (Muhammad, 2005: 59). Karin magana fili ne babba da ke Ƙunshe da darussa masu yawa da suka shafi rayuwar mutane. Ƙimar kuďi a rayuwar mutum na cikin darussan da ake iya gani cikin karin magana. Ga misali:

Kuďi abin zaman duniya
Kuďi ba ku son Ƙazamar buƘata
Kuďi na gwamna masu gida rana
Kuďi tushen jin daďi
Yaro nemi kuďi tun abin saye bai zo ba
Kuďi maganin wata magana
Yaro da kuďi abokin tafiyar manya
Yaro ba kuďi abin tausayi

Nazarin waďannan karuruwan magana ya nuna cewa, Hausawa na kallon kuďi da wani matsayin na musamman a lamurran rayuwarsu ta duniya. Wannan ya Ƙunshi yadda kuďi ke mai da yaro babba da wurin neman kuďi da yadda kuďi ke iya kashe kowace irin magana da yadda mutum ke zama abin tausayi don rashin kuďi da sauransu. Daga waďannan karuruwan magana ana iya ganin hoton yadda kuďi suka zan komai da ruwanka cikin rayuwar mutane.

3.1.2 WaƘoƘi

WaƘa magana ce mai Ƙunshe da saƘo da ta shafi zaƂen kalmomi da tsara su cikin tsarin da ba lalle sai ya dace da maganar yau da kullum ba (Yahya, 1997). A cikin waƘoƘin bakan Hausa, mawaƘa kan sanya abubuwa masu yawa don ilmantar da al’umma da nishaƘantar da su, ko yin zambo da sauransu ko da kuwa ba kan wannan jigon suka shirya waƘa ba. Da yawa akan sami lamarin da ya shafi amfanin ilimi, kiyon lafiya, sana’a, tarbiyyar yara, kula da addini, da sarrafa kuďi ta kashe su inda ya dace da kuma nuna haďarin kuďi a wasu lokuta. Fitacciyar waƘar Hausa da tafi nuna matsayin kuďi a rayuwar mutane ita ce ta Abdu Wazirin Ɗan Duna mai gindin waƘa kamar haka:
Uban waƘa: Tsakanin ďan Adam da kuďi
A cikin wannan waƘa Abdu ya faďi abubuwa da yawa da kuďi ke sa mutum ya aikata kamar sawa da hanawa, shiga kunya da fita kunya, kowace irin hulďa, ďebo rigima, zare ido, lumshe ido da sauransu. Ga kaďan daga cikin ďiyan waƘar:
Yanzu ba wata haraka sai kana da kuďi
Saboda ba ka sawa sai kana da kuďi
Kuma ba ka hanawa sai kana da kuďi
Zamani ya zo sai kana da kuďi
Ba ka komi sai kana da kuďi
Ba a yi maka komi sai kana da kuďi
Kuma kakan gaza komi in kana da kuďi
Kana iya komai don saboda kuďi
Akan shiga kunya ma saboda kuďi
Akan fita kunya ma saboda kuďi
Ana shanye huďďa saboda kuďi
Ana ďebo rigima saboda kuďi
Ana yajin aiki saboda kuďi
Ƙaramin yaro saboda kuďi
Ka ga anai masa ban girma saboda kuďi
Ana son mummuna saboda kuďi
Ka ga ana Ƙin kyakkyawa saboda kuďi

Idan aka yi la’akari da waďannan baituka za a ga cewa, mawaƘin ya nuna rayuwar mutune a yau ta kasance ta kuďi inda kuďi ke sa mutum ya aikata kowane abu ko mai kyau, ko maras kyau.

3.1.3 Labarai

Labari wani zance ne da akan shirya shi a gargajiyance na hikima da yake zuwa kai tsaye a kan wani abu da ya taƂa faruwa ko ma wanda ba a taƂa yin sa ba a sakamakon hulďa da jama’a (Gusau, 1984). Labari adabin baka ne da ya taskace lamarin rayuwar mutane na abubuwa da yawa. Da yawa akan sami labarin mutuwa, haihuwa, aure, kasuwanci, kishi da sauransu. Ba wani labari da ba ya ďauke da wani abu na rayuwar mutane da aka shirya don wani darasi da nishaďantarwa. Akan ci karo da wasu labaran baka da ke nuna lamarin hada-hadar kuďi da tasirin kuďi a cikin rayuwar mutum. Ga misali, labarin Matafiya Biyu yana Ƙunshe ne da irin yadda hada-hadar kuďi ke sauya tunanin mutum. Wasu matafiya ne su biyu Abdu da Ali suna cikin tafiya za su wani gari sai suka hangi Ƙunshi a gefen hanya. Ali ya ďauka ya buďa sai ya ga kuďi ne. Abdu ya ce ‘Kai, mun taki sa’a’ Ali ya ce’A’a! Mun taki sa’a, ko dai na taki sa’a?’ Abdu ya ce ‘To Allah ya ba mu lafiya’
Suka ci gaba da tafiya. Sun yi nisa cikin wani baƘin daji sai ‘yan fashi suka Ƃullo musu. Suka ruga da gudu, ‘yan fashi suka bi su. Can Ali saboda nauyin kayansa sai ya kasa gudu, ya ce, ‘Wayyo! Yau za mu yi hasara’ Shi kuma Abdu da yake can gaba sai ya ce, ‘A’a. Za mu yi hasara, ko dai kai zaka yi hasara’ (Sudan Interior Mission, 1938: 10-11).
Wannan labari ya nuna yadda mutum ke yin butulci ga abokinsa saboda kuďi. Ali wanda yake tare da abokin tafiyarsa Abdu komai bai shiga tsakaninsu ba, sai da ya sami kuďin tsintuwa sannan ya san kansa kaďai. A wannan wuri an nuna son kan Ali ya fito fili saboda dalilin kuďi.
Shi kuma labari Mai take Maci Amana Yana Tare Da Kunya labari ne na wasu aminai biyu; Ali da Tanko. Wata rana Ali zai yi tafiya sai ya sa kuďinsa cikin wani bango ya ďura zuma ya liƘe. Ya je ya kai wa Tanko don ya aje masa har ya dawo. Bayan shekara biyu, sai Tanko ya buďe don ya ga ko zumar ba ta lalace ba. Ko da ya zubo sai ga kuďi. Nan da nan ya kwashe, ya nemi wata zuma ya liƘe, ya aje. Ana nan Ali ya dawo ya tambayi Tanko ajiya. Tanko ya kawo ya ba shi. Ko da Ali ya buďe bango ba kuďi. Nan suka ta yin rikici har suka isa kotu. AlƘali ya sa aka kirawo dillalan zuma ya tambaye su ko tsohuwar zuma ce wannan. Suka ce a’a. Nan AlƘali ya sa Tanko ya biya kuďin Ali, aka kuma yi masa hukuncin zamba cikin aminci. (Sudan Interior Mission, 1938: 28).
Wannan labari ya nuna kuďi ne suka sauya tunanin Tanko daga aminci zuwa zamba. Tanko ya yaudari abokinsa ta yadda ya musanya masa ajiyarsa da abin da ba ita ba bayan ya kwashe masa kuďi.
Yanayin kowane ďaya daga cikin waďannan rassan adabin baka ya nuna tasirin kuďi wajen sauya tunanin wani mutum. An ga yadda kuďi suka Ƃata zaman aminci da kuma tafiya tare.

4.1 Hada-Hadar Kuďi a Tattalin Arzikin Hausawa a Wasu Littattafan Ƙagaggun Labarai


Ƙagaggun labaran Hausa wasu littattafai ne waďanda wasu mutane da Allah ya yi wa baiwar hikimar tsara tunani da shirya shi don isar da wani saƘo da suka rubuta. Su waďannan littattafai an fara samar da su ne daga shekarar 1933 lokacin da Hukumar Talifi ta shirya gasar Ƙaga labari. Tun daga wannan lokaci zuwa yau, an samar da littattafai masu yawa da ba a tantance adadinsu ba. Malumfashi (2010) ya nuna a wajajen shekarar 2010 akwai littattafai sama da 3,500. An shirya littattafan kan jigogin ilmantarwa, soyayya, zaman aure, da sauransu.
Tasirin kuďi wajen sauya tunanin mutum ya kasance ďaya daga cikin muhimman Ƙananan jigogin da suke taimakawa wajen warware manyan jigogin wasu littattafai. Wannan kuwa ya shafi yadda kuďi ke sa wani ko wasu su aikata wani aiki kamar na kisan kai, ko sata, ko fashi, tona asiri ko rufa shi, fyaďe, zina ko sauya akalar shari’a. Ga misali a littafin Ruwan Bagaja na Alhaji Abubakar Imam (1934) an kawo yadda kuďi suka sa wani AlƘali ya sauya akalar shari’a. Ga yadda aka kawo batun a shafi na 12:
‘Na ce, ‘Malam Ɗalhatu da ďan’uwansa sun shaida. Malam Sule da ďan Ƙanensa malam Hashimu sun shaida. Bari ta su ma, har autansu Malam Muhtari yana nan aka yi. Waďansu mutane ma kamar ďari masu zuwa da tsakad dare duk za su shaida!’
Ko da malam ya ji haka sai ya fahimta da maganata. Malam Ɗalhatu da ďan’uwansa dala biyu ke nan. Malam Sule da Malam Hashimu kuwa sule da sisi ke nan. Malam Muhtari kuwa taro ke nan, mutane ďari ke nan masu zuwa da tsakad dare kuwa sule ďari ke nan.
Watau da tsakad dare zan kawo masa sule ďari da shida ba taro idan ya ba ni gaskiya. To, yanzu zamani ne dai na wanda ba mai gaskiya sai mai sule. Nan da nan mai bakin cin rashawa ya birkita maganar, ya ba ni gaskiya. Aka ďaure baƘauye wata uku don ya sa mini sata. Da dare na kawo wa AlƘali waďannan, na koma na shiga shagali da sauran.’

Idan aka dubi yadda aka kawo wannan batu ya nuna yadda kuďi ke sauya tunanin mutane. Alhaji Imam ba ya da gaskiya a shari’ar, shi kuma baƘauye ba ya da kuďi. Lokaci guda Alhaji Imam ya gabatar wa AlƘali zancen kuďi sai aka ba shi gaskiya. Ba don kuďin da ya gabatar da zancensu ba, da AlƘali ya tabbatar wa baƘauye gaskiyarsa.

A littafin Tura Ta Kai Bango marubucin ya kawo yadda kuďi suka sauya tunanin wasu mutane suka aikata wani abu da ake son su aikata ba tare da nazarin sakamakon abin ba. A shafi na 45 an nuna yadda aka yi amfani da kuďi aka haďa wata mata fitina da ďanta. Wani mai suna Alhaji Kaukai ya je wajen matar tare da wani yaronsa mai suna Karen Ɓuki inda bayan sun gaisa da ita suka gabatar da buƘatarsu, daga nan Alhaji ya kawo kuďi ya ba ta. Ga yadda aka kawo batun:
‘Alhaji ya ce, ‘To kin ji dai abin da muka gaya miki. Muna fatan ki sami shawo kansa. Ga kuma wannan ki sayi nono’ Ya kawo naira ashirin ya ba ta. Ita kuma ta yi ta sa musu albarka har suka fita. Na farko dai tana ganin ga shi sun zo sun faďa mata gaskiya game da ďanta. Na biyu kuma ga naira ashirin ta samu haka tun da sassafe. Abin da rabon da ta sami masu yawansu tun wata shekarar da sulu ya yi tsada.’
Idan aka yi la’akari da wannan batu za a ga cewa, samun wannan kuďi ya sa matar ta sa wa Alhajin albarka, kuma ta gaskata abin da ya gaya mata tun kafin ta bincika. Wannan ya faru saboda ta daďe ba ta sami kuďi masu yawan waďanda ya ba ta ba. Haka kuma abin da ya nemi ta yi na jan kunnen ďanta Hassan, haka ta yi lokacin da ya dawo gida. Ga yadda aka kawo abin da ya biyo baya a shafi na 49:
Zuwa can ta nisa ta ce, ‘Yanzu ďan nan irin sakamakon da za ka yi wa mahaifinka ke nan? Yana kwance Ƙasa maimakon ka dinga yi masa addu’a sai ka je ka shiga cikin kahurai?...’
Wannan ya nuna tunanin matar ya sauya domin tsawon zaman ta da Hassan ba ta taƂa jin irin wannan zance ba sai wannan karo. Haka kuma wannan karo ne na farko da ta yi sa-in-sa da shi. Shi ma shafi na 69 an kawo yadda kuďi suka sauya tunanin wata yarinya har aka ci kanta, aka biya buƘatar da ake so kanta. Ga yadda aka kawo batun:
Ruga ya ďan ja ta waje guda suka gaisa. Bayan da za su rabu sai ya kawo naira ďari ya ba ta, ‘yan Murtaloli guda biyar. Shi ma Taiki ya yi wa tasa yarinyar kyauta, kana suka yi ban kwana da su da cewa za su dawo kwanan nan..
Ashe kuwa wannan kyauta ta Naira ďari, ta rikitar da ita, ta kuma ba ta mamaki. Ita da za ta dawo hutu daga gida bai fi a ba ta Naira ashirin ba, sai ga naira ďari, Murtala ko canzawa ba a yi ba. Ta kwana tana mamaki da murna. Don haka yau da aka ce ta zo, da rawar jiki ta zo, ta gaishe da su cikin harshe na girmamawa. Kuma da aka ce su je su shirya za a ďan je yawo da su, ba ta tsaya wata-wata ba, ta je ta shiryo.’

Idan aka yi la’akari da wannan wuri za a ga cewa, kyautar kuďi da aka ba wannan yarinya ya yi tasiri Ƙwarai wajen sauya tunaninta har aka yi nasara kanta. Kuďin suka rikita ta, ta yi ďa’a da girmama wannan mutum da ba ta san shi ba, kuma karo na farko ta gan shi ke nan. Daga Ƙarshe ya ďauke ta ya je ya biya buƘatarsa kanta. Irin haka yake faruwa kan wasu mata da yawa.
Shi ma marubuci littafin Fitsarin FaƘo ya kawo irin wannan tasiri na kuďi da sauya tunani da suke yi na mutane. Wani mai suna Tahir Hassan ne ya yi amfani da kuďi don binciko wasu bayanai, kuma ya yi nasara. Ya yi amfani da kuďi a wani Hotel inda ya sami bayanai na farko daga wani ma’aikacin Hotel duk da hana fitar da bayanan da Hotel ya yi. Bayan kashe Faruku wani abokinsa ya je Hotel na Daula da can ne aka ce ya sauka. Da yake Hotel ďin na da tsaurin mataki kan karƂar cin hanci, kuma yana son bayani kan wani ďaki da ya leƘa cikin dare, sai ya yi amfani da kuďi ta wata dabara ga ďaya daga cikin ma’aikatan wurin ya sami bayani. Ga yadda abin ya wakana.

‘Na dubi saurayin nan, muka haďa ido, na yi murmushi. Na ce, ‘Da za ka yarda, da mun ďan zanta da kai. ....na sa aka kawo mana lemun kwalba, muka sami wuri muka zauna. Na sa hannu a aljihu na zaro ‘yar Murtala sabuwa fil na aje a ƘarƘashin kwalbar lemuna. Idanunsa suka shiga karakaina tsakanin Naira ashirin ďin da fuskarsa. Duk ya Ƙosa ya ji abin da zan ce....Amma kuma saboda yabawa da kirkin da ka yi mini, nake so in ba ka wannan ka sayi goro. Take na ga ya saki jikinsa. Na miƘa masa Naira ashirin ďin nan, ya karƂa, ya riƘe ya Ƙi sa ta a aljihu. Ya ce wane tsegumi kake so in yi maka?’ (shafi na 24).
La’akari da yadda wannan bayani yake, ya nuna ma’akacin ya amince ya bayyana sirrin ne bayan da ya karƂi kuďi. Ba don da ya karƂi naira ashirin ba, da bai amince ya ba da bayanan ba. Shi Tahir ma yana sane da yadda kuďin za su iya sauya masa tunanin ma’akacin, wannan ne ya sa ya fitar da su.
Tahir Hussaini a ci gabansa na binciko lamarin mutuwar Faruk ya haďu da Madam Ƃera a gidan Yashi Kulob inda ya yi amfani da kuďi don samun biyan buƘatarsa. Lokacin da ya tattauna da ita bai sami kanta ba sai da ya haďa da kuďi. Ga yadda aka kawo batun a shafi na 59-61:
...ta yi ‘yar dariyar jin daďi, ta ce, ‘wace ni?’
Na yi dariya na ce, ‘Ashe kin ji Hausa kamar jakin Kano.’
Ta ce, ‘A’a kaďan dai’
Na fitar da kuďin da ke aljihuna na ďan yar da su. Na lura Madam Ƃera ta Ƙyalla ido ta gan su. Na mayar cikin aljihu. Na ce, ‘ban sani ba, ko zai yiwu ki ba ni ďan lokaci mu tattauna...’
‘Ka san ni ne da ma?’
Na ce mata ‘Ina jin na san ki, sai dai ba zai yiwu mu ci gaba da magana a nan ba. In dai kin yarda to mu keƂe kaďan’ Na sake fito da kuďin na ware Naira dari biyu na ajiye bisa tebur. Sai fuskarta ta canza....’
Ta ce, ‘Shi ke nan, za mu iya zuwa ďaya daga cikin ďakunan manyan baƘi da ke sama..’
Biya na aka yi in sa ido a kan Faruk, ko da zan same shi da wasu takardu da aka aiko daga Afrika ta Kudu in kai rahoto.’

A nan Tahir ya sauya tunanin Madam Ƃera ne da kuďi. Ya yi amfani da dabarar da ya yi amfani da ita a Hotel, ya fitar da kuďi ya sami kanta, ta saurare shi har ta sanar da shi abin da ya faru kan abokinsa Faruk. Ba don tasirin kuďin da ta Ƙyalla ido ta gani suka sauya tunaninta ba, da wata Ƙila ba ta saurari Tahir ba.
Shi ma Sulaiman Ibrahim Katsina a litafinsa na Mallakin Zuciyata ya kawo yadda aka yi amfani da kuďi aka sauya tunanin mahaifiyar wata yarinya kan maganar aure. Ga yadda ya kawo labarin a shafi na 118-119:

‘Alhaji ya sake ďaukan naira ďari ya ba wa yaronsa. Can hantsi na yi ya je ya iske uwar yarinya ya gaya mata abin da ya kawo shi. Ya kuma kawo naira hamsin ya ce, Alhaji ya ce a kawo mata. Ta amshi kuďi, ta ce a gaya ma Alhaji in dai wajenta ne ba damuwa. Sai dai wajen yarinya da ubanta...
Da Sakina ta dawo daga cikin gari, kuďin suka sa uwar ta gaya mata cewa, ‘Zo nan zauna kusa, yau abin arzikƘi ya same ki. In kin yarda kin dace ainun..’
Uwar ta ce, ‘Yau ga zancen banza. Alhaji ne mummuna? Je ki ki ga matansa mana. Ga shi kuma da arziƘi.’

Abin da ya faru a wannan wuri tsakanin Alhaji Garanhotsami da mahaifiyar Sakina ya nuna kuďin da ya aika mata ne suka sa ta bijere wa yaron da ta san yana tare da ďiyarta tun da daďewa. Da wannan ta sauya tunaninta, ta shiga jan hankalin Sakina ta hanyar nuna mata matsayin Alhaji don ta amince ta so shi.
Shi ma Ibrahim Sheme a littafinsa na ‘Yartsana ya kawo tasirin kuďi da yadda suke sauya tunanin wasu mutane su aikata wani abu. Ga yadda ya kawo yadda wani mai suna Alhaji Maidogonsoro ya yi amfani da kyauta ya sauya tunanin wata tauraruwa mai suna Zainab da kakarta Kandala:
‘Nan fa ya dinga ba Zainab kyaututtukan kuďi da kayayyaki, ya na kuma ba Kandala. Da fari Zainab na jin tsoro, ganin cewa akwai igiyar aure a wuyanta, kuma ga shi Alhaji sa’an tsohon ta ne ...To amma Kandala ta Ƙarfafa mata gwiwa, ta ce ta riƘa karƂar duk abin da ya ba ta. Ba a jima ba ta riƘa karƂar duk abin da ya ba ta. Ba a jima ba ya riƘa ďaukar Zainab ya na kai ta wani gidan sa na shaƘatawa a bayan gari...’ (shafi na 91).
La’akari da wannan wuri, ya nuna kuďi ne kan gaba wajen sauya tunanin mutane domin a nan kuďi ne aka kawo kan gaba ga kyautar da Alhajin ke ba Zainab. Da wannan kyauta Kandala ta Ƙarfafa wa Zainab Ƙafa, ta ci gaba da hulďa da Alhaji har ita ma ta saba, ta cire tsoro. Wannan ya nuna irin tasirin kuďi wajen sauya tunanin mutane a yau.
A littafin Turmin Danya akwai yadda wani mai kuďi mai suna Alhaji Gabatari ya je neman wata kwangila a wajen wani shugaban ma’aikata. A Ƙa’idar wurin ba a barin masu son yin aikin su san sirrin tsare-tsaren aikin. Shi Alhajin ya yi amfani da kuďi inda kai tsaye aka karya Ƙa’idar. Shi Alhaji Bagatari bayan ya je wajen cayaman sun gaisa ya gaya masa ya sami labarin sun fitar da kwangila. Ya ba cayaman kuďi don ya sami haske kan tsarin aikin. Ga yadda aka kawo batun yadda suka yi da shi:
Alhaji ya ce, ‘To’ Sa’an nan ya sa hannu aljihu ya ďauko kuďi Nera dubu ya ba shugaba. Ya ce, ‘Ga wannan a saya ma yara cakuleti’
Kai har da ďawainiya. Ka bari man....’
Cayaman ya karƂa ya ce, ‘Na gode Ƙwarai. Sai ka biya wajen Sakatare ya baka istimet ďin kwangilar ka gani.’

Da ya isa ofishin Sakatare suka tattauna, sai sakatare ya ba shi tsarin kwangilar abin da kuma ba a haka a Ƙa’idarsu ba. Ga yadda suka yi:
...Ya kulle kabod ďin sa’an nan ya zo ya miƘa ma Alhaji wannan takarda. Ya mayar da makullan cikin aljihun teburinsa, ya ja kujerarsa, ya zauna.’
Ya ce ma Alhaji, ‘Ka duba ko? Ofisoshi uku ne za’a gina. Guda mai ciki biyu, wato kamar ofisoshi huďu ke nan. Kuma za a yi su ne kan Nera dubu ďari. Ina jin yau zaka rubuto ko? (shafi na 36-38).

Da aka taru wurin bitar takardun masu neman kwangila, kwamitin ya amince da takardun Alhaji Bagatari ba don cancanta ba, sai dai don kuďin da ya ba su. Ga abin da marubucin ya nuna:
‘Da faďin haka su sauran sun fahimce shi sun kuma gane wanda ya kamata a baiwa, sun kuma amince. Domin kuwa ban da Cayaman da Sakatare, babu wanda Alhaji bai kaima Nera ďari biyu a gidansa ba, ko kuma ya aika masa’ (shafi na 44).

Wannan dogon bayani ya nuna kuďi ne suka sa waďannan mutane masu alhakin kula da kwangilar suka saƂa Ƙa’idarta. Ciyaman da ya karƂi kuďin Alhaji, sai ya ba shi dama ya je ya ga Sakatare. Shi kuma Sakatare da ya ji ta kan Ciyaman Alhaji ya biyo, shi ma sai ya miƘa wuya, ya nuna wa Alhaji takardun asirin kwangilar har da yi masa bita. Nan shi ma ya karƂi nashi rabon. ‘Yan kwamitin ba da kwangilar su ma da yake kowanensu ya karƂa, dole suka amince a ba shi. Wannan duk ya faru ne saboda tasirin kuďaďen da suka karƂa, tunaninsu na kiyaye Ƙa’ida ya sauya, suka aikata wani abu daban.
A wani wurin a wannan littafi an nuna yadda lamarin kuďi ya sa Alhajin bai yarda da kowa ba. An nuna mahaifiyarsa ma ba ta tsira ba domin koyaushe lamarin kuďi ya shiga tsakaninsu sai ya zarge ta. Ga yadda aka kawo batun:
‘Akwai ma labarin da ya bazu cikin Karaini, musamman ma wurin na kusa da shi Alhajin, game da uwarsa da shi, game da kuďi. In har ya bata don a yi wani abu, to sai yayi ta zarginta ko ta saci wani abu daga ciki. Duk wanda zai yi tu’ammali da kuďinsa, gani yake sata yake yi masa. Sanin yadda ma yake ma uwarsa yasa mutane basu faye damuwa da halinsa ba.’
Bansuwai ne kuwa yaji shi wata rana yana cema uwar, wai ya bata kuďi game da haihuwa duk ta kashe, bata yi abin da ya ce ayi da kuďin ba. In ba kashewa tayi ba, ya ya za’a ce har waďannan kuďi sun Ƙare. Shi in tana haka bai Ƙara sa kuďin duk da za’a yi wata hidima hannunta, sai ya sa hannun amarya’ (shafi na 47-48).

Lamarin kuďi abu ne da ya kai gaya ga wasu mutane. Alhaji irin mutanen nan ne da kuďi kan mantar da su komai. A bayanin da ke sama ya nuna kuďi kan sa Alhaji ya fita hayyacinsa, ya ci zarafin kowa. Bai aminta da kowa ba cikin sha’anin kuďi. Mahaifiyarsa ma wadda aƘalla ta ci a ce ta tsira, ba ta tsira ba. Zargin da yake yi mata ya tabbatar da cewa, kuďi suka sauya tunaninsa gaba ďaya, ya manta da girma ko matsayin kowa. Haka wannan rayuwa take ga wasu mutane da yawa. Kuďi kan sauya tunaninsu, su manta komai, su kuma aikata komai ido rufe komai muninsa.
Shi ma littafin Tsumangiyar Kan Hanya marubucinsa ya kawo yadda kuďi ke sauya tunanin wasu mutane. Wani mutum ne mai suna Malam Sambo wanda daga farko shi talaka ne Ƙwarai. Ana nan ya sami hanyar samun kuďi abin da ya sauya tunaninsa ya fara neman mata. Da kuďin suka Ƙaru sai ya sake sauya tunaninsa gaba ďaya. Ga yadda aka kawo sauyin tunanin nasa:
‘Ganin kuďi na shiga na fita a hannun Sambo sai ya sake wani sabon salo na neman mata, ya kuma yi mirsisi da magan-ganun jama’a, suna da ďaurin aure, da jana’iza duk ya Ƙaurace musu. Kyauta ga karuwai, da ‘yan daudu ya Ƙaru, yaran ‘yan daudu kuma suka sami dokinsu mai daďin hawa, da zaran sun hango shi tafe kafin ya Ƙaraso gidan matan sai sukan yi rige-rigen buďe masa motar da gaisuwa don neman shiga domin sukan washe, sukan kuma ci kaji da Ƙwai da soyayyar doya da ‘yan daudu ke yi a Ƙofar gida. ...Sambo bai tsaya kurum ga bai wa karuwai kuďi ba har kayan ďaki yakan yi musu, ya kuma biya musu kuďin haya, ya ďauki ďawainiyar su, san nan ya kawo na taba da giya ya ba su..’ (shafi na 40).
Idan aka yi nazarin wannan wuri za a ga cewa, lallai kuďi suka sauya tunanin Malam Sambo. Da can shi talaka ne wanda sai da Ƙyar yake samun abinci. Wannan yanayin rayuwa ya sa bai damu da kowace mace ba sai matarsa ďaya. Da ya fara samun kuďi, sai ya shiga neman mata. Da kuďin suka Ƙaru, sai ya manta da al’amurran abokan zamansa, ya tsira inganta rayuwar karuwai da ‘yan daudu. Wannan sauyin tunani na Sambo ya wakana ne saboda tasirin kuďi a kansa. Haka ake samun irin wannan sauyin tunani a rayuwar wasu mutane da yawa.
A littafin Ado Ahmad Gidan Dabino na In Da So Da Ƙauna an kawo wata tsohuwa wadda kuďi suka sauya mata tunani. Ita wannan tsohuwa an nuna ba ta san komai a sha’aninta ba sai kuďi, kuma don kuďi tana bin kowace irin hanya. Ga yadda aka nuna halayenta game da kuďi:
‘Da AbdulƘadir ya ga Sumayya ba ta ba shi haďin kai ba, sai ya nemi a rake shi gidan kakannin Sumayya. Haka aka yi, Aminu da AbdulƘadir suka je gidan kakannin Sumayya. Wata tsohuwa ta fito. Ita wannan tsohuwa kowa ya san ta wajen son kuďi, in dai ba aka da kuďi, to ba ka da mutunci a wurinta. Sannan ba ta sa Allah a cikin al’amuranta sai dai kuďi. In dai ta san za ta bi hanya ta samu kuďi, ko da wannan hanya ta saƂawa shari’a ce za ta bi... Bayan sun gama gaisawa, Aminu ya gaya mata abin da ke tafe da su. Yayin da kakar Sumayya ta ji haka, sai ta ce, ‘Ai wannan abu ne mai sauƘi. Ba mu muka haifi iyayenta ba, ta isa ta Ƙi bin umurninmu? Iyayenta ma mun juya su ballantana ita.... AbdulƘadir da Aminu suka ji daďin wannan bayani da ta yi musu, nan take AbdulƘadir ya ciro naira dari biyar ya bai wa kakar Sumayya. Nan da nan ta karƂa tana tsima.’ (36).

Wannan tsohuwa da aka kawo bayaninta a sama ta ďauki kuďi da Ƙima sosai. Kuďi sun sauya tunaninta ta yadda ba wani abu da take kallo idan dai ba kuďi ba. Ba wani abu da take ba muhimmanci komai dacewarsa idan ba da kuďi a ciki ba. Wannan ya sa AbdulƘadir ya yi nasara kanta ga lamarin soyayyarsa da jikanyarta Sumayya. Ita Sumayya ba AbdulƘadir take so ba, wani mai suna Ahmed take so, amma shi Ahmed ba ya da kuďi. Wannan yanayi ya sa kakar ta goya wa AbdulƘadir baya, ta tursasa mahaifan Sumayya kan aurar da ita ga AbdulƘadir.
Littafin Kitse Rogo ya Ƙunso wani bayani da yake nuna tasirin kuďi wajen sauya tunanin mutane a yau. A cikin littafin an kawo yadda wani ďan sanda kuďi suka hana shi kama mai laifi. Ga yadda ya kawo batun.
‘...In ka fahimci zancena, yallaƂai wallahi ba shi da nakasa, illa gaskiya, a bisa kanta, mai ďacin taunawa. Ado yana maganar yana saka hannayensa a aljihu. Ko ba ka ji abin da Shata ya ce bane? Ya sasanta ya sami abin sayen dussa..’ (shafi na 11)
‘Ai wannan ba sasantawa ba ce. Laifin Ɗan kunama ya cika muni, Kofur ďin ya faďa da murya mai saukowa.’
..To, na ji maganarku. Ni dama ba wai an bi rahoto ba ne. Na ďauke ku kamar Ƙannena saboda haka dole in kwaƂe ku, in gargaďe ku..’
Kofur Tanko ya zazzare musu idanu ya ce, ‘Na gaya muku ku bar wurin nan, in wani ya kama ku ba ruwana.’ Ya juya ya kaďa Ƙafa ya fita.’ (shafi na 11-12).

Musa ya yi kisan kai ne. Ana nemansa don gurfanar da shi gaban AlƘali abin da ya sa har aka buga hotonsa a jarida. Tsawon lokaci ba a sami wani jami’in tsaro da ya gan shi ba. A wannan wuri ne kofur Tanko ya gan shi, kuma ya cancanta ya kama shi don a caje shi. Sanin yadda kuďi ke sauya tunanin ‘yan sanda su Ƙi yin abin da ya dace, ya sa Ado abokin Musa ya sa hannunsa aljihu. Ko da yake ba a nuna Ƙarara kuďi ya ba da ba, amma sanin kowa ne idan aka sa hannu aljihu kuďi ake fitarwa yawanci. Aljihu ma’ajiyar kuďi ne a jikin mutum. Kuďin sun sauya tunanin kofur Tanko har suka sa ya sauke muryarsa Ƙasa. Batun kama Musa ďan kunama Tanko ya bar shi. A maimakon haka sai ya gargaďe su su bar nan wurin. Wannan ya nuna yadda kuďi ke sauya tunanin mutanen da aikin tsaron Ƙasa.
Shi ma tauraron littafin ZaƂi Naka mai suna Kyauta samun kuďi ya sauya tunaninsa inda yake ganin ya fi Ƙarfin zuwa daji. Ga yadda aka kawo labarin:
‘Maigidana dai bai yi haƘuri ba sai da ya ga ya saman mani aiki na wani ďan lokaci a wata ma’aikatar ruwa, ana biyana Naira sittin a wata. Ganin na kama aiki, sai kankanba. Ga ma’aikacin Gwamnati. Ran nan sai damana ta faďi. Dama Mallam Tausayi riƘaƘƘe manomi ne, saboda haka, ranan ya yo shirin gona sai ya ce mani in ta so mu tafi in ďan taimaka masa aiki. Sai na ji kamar ya zage ni saboda ni ina ganin na fi Ƙarfin noma tunda na kama aiki. To, don kada in tozarta shi sai na ce masa ya ci gaba ina nan zuwa.’ (shafi na24)
Kyauta da aka kawo labarin yadda kuďi suka sauya tunaninsa, maraye ne shi. Wannan mutum malam Tausayi shi ne ya ďauke shi ya riƘa. Shi ya yi masa komai har da lalurorin karatunsa. Ya nema masa aikin da yake samun albashi. Albashin na naira sittin a wata ya sauya tunaninsa har ya yi wa wannan mutum butulci. Kafin wannan albashi, Kyauta ba ya tsallake maganar malam Tausayi domin ba ya da kowa sai shi. Samun kuďin sai ya kangare masa ya bar taya shi noma Ƙarshe ma ya bar gidansa. Irin wannan na cikin sauyin tunani da kuďi ke haddasawa a rayuwar mutane da yawa.
Shi ma Musa da ke cikin littafin Tuwon Ƙaya kuďi sun sauya tunaninsa. Musa na cikin matsin talauci ta kowane hali. Ana haka sai matarsan Hassana ta sami kyautar naira miliyan ďaya daga yayanta Mustafa. Samun wannan kuďi sai Musa ya yi tunanin tsayawa takarar kansila a unguwarsu. Ga yadda aka kawo shi:
‘Bayan samuwar wannan kuďi da wata Musa ya Ƙi sanya hannu a kan duk wata shawara ta yadda za’a yi da wannan kuďi da Hassana ke kawowa, sai wata rana ne ya zo ya shaida mata shawarar da ya yanke na tsayawa ďan takarar kansila a unguwarsu. Inda ya nemi alfarmar rance wannan kuďin don yaƘin neman zaƂe. da fari dai Hassanan ta tirjewa wannan ďumbin kuďi mai tsautsayi ba, kuma ba wai don nata ba ne a’a’ ta ce ko na Musa ne ma ba za ta bari ya yi wannan kasada ba. (shafi na 30)

Idan aka yi nazarin wannan labari za a ga cewa, Musa bai nuna sha’awarsa ba ga tsayawa takarar kujerar siyasa ba sai da ya ga waďannan kuďaďen. Da can Musa abin da zai ci ne yake fafutukar biďa domin bai ga alamun kuďi ba. Wannan ya nuna tasirin kuďin ne ya sauya tunaninsa daga yadda yake a can farko na mai neman yadda zai ci abinci zuwa ďan takarar kujerar kansila.
A littafin Kowa Ya bar Gida an nuna yadda kuďi suka yi tasiri wajen sauya tunanin wasu iyaye suka yarje wa wani tsoho auren ďiyarsu tare da ba ta son sa, tana da saurayi daidai ita da take so. Ga yadda aka kawo wannan batu:
‘...A yadda ta ce mini, wai ita Bakanuwa ce kuma wannan Alhajin ya tura wa iyayenta kuďi masu yawan gaske domin ya aure ta, amma ita ba ta son shi. Saboda haka sai iyayenta suka riƘa hana ta fita wajen wani saurayin da take mutuwar so, suka kuma ce masa kada ya sake taka musu Ƙofar gida da sunan ya zo wurin ‘yarsu. Suka kuma ce tilas Alhajin za ta aura domin gidansa gidan hutawa ne. Shi kuma wancan saurayin nata da ya ga haka sai ya haƘura, daga baya kuma sai ta sami labarin cewa ya yi aurensa..’ (shafi na 39).

Wannan bayani ya nuna tasirin kuďi ta yadda suka sauya tunanin iyayen Zinaru. Suna sane da akwai wanda ďiyarsu ke so, amma da yake Alhaji ya ba su kuďinsa, sai tunaninsu ya sauya zuwa gare shi.
Bisa ga waďannan misalai da suka gabata ana iya tabbatar da cewa, kuďi na taka rawa Ƙwarai wajen sauya tunanin mutane su aikata abin da ba shi ya cancanta su aikata ba.

5.1 KAMMALAWA


Kuďi a rayuwar mutum abu ne mai muhimmancin gaske. Kowane mutum yana son ya sami kuďi. Son samun kuďi abu ne wajibi saboda kasancewar kuďi komai da ruwanka. Ba wani abu a duniyar nan da ke tafiya daidai ba tare da kuďi. Abinci, lafiya, kariyar mutunci da sauransu duk masu kuďi suka fi samun su a yau. Irin wannan yanayi ya sa kuďi suke sauya tunanin mutane.
Wani abin lura shi ne, a duk lokacin da kuďi suka sauya tunanin mutum ya aikata wani abu, Ƙarshe sakamako zai zama akasin abin da ake so. Da yawa daga cikin misalan da aka gabatar, mutanen da kuďi suka sauya tunaninsu, Ƙarshe sun ci karo da abin da ba su so. Da mutane za su lura su zan masu tsayayyen ra’ayi, su hana kuďi gurƂata tunaninsu da lamurransu za su tafi daidai, Ƙarshe kuma ya yi kyau.
Daga Ƙarshe dai muna iya cewa, ba shakka rayuwar yau ba ta yi sai da kuďi, kuma da kuďi ake sauya tunanin mutane ko dai saboda matsin talauci da ke tare da su ko kuma saboda Ƙarancin wadatar zucci. Da mutane za su nemi kuďi su kashe su inda ya dace da lamurran duniya sun tafi daidai. Shi kuma tunani da ra’ayi su tsaya inda suke, su kasance suna juya mutane, abin da ya kamata a yi shi, wanda bai kamata ba a bar shi. Yin haka zai gyara tsare-tsaren rayuwar mutane, duniya ta zauna lafiya.

6.1 Manazarta


Abdullahi, A. B. 2008. Kasuwanci A Ma’aunin Karin Magana. Kundin digiri na farko, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Abdul-Majid, A. 2004. Tuwon Ƙaya. Kano: Gidan Dabino Publishers
Adamu, Y. M. 2013. Ruwan Saman Marubuta A Ƙasar Hausa: Daga Damunar 1980 Zuwa Yau. MaƘalar da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani na farko da Cibiyar Nazarin Hausa, Kano: Jami’ar Bayare ta shirya daga ranar 14-16 ga watan janairu- 2013.

AƘur’ani Mai Girma Da Kuma Fassarar Ma’anoninsa Zuwa Ga Harshen Hausa.
Bambale, M. B. 2010. Kowa Ya Bar Gida. Zaria: NNPC
Bello, M. M. 1982. Tsumangiyar Kan Hanya. Zaria: NNPC
Bunza, A. M. 2013. Death In Hausa Folkloric PerspectiƂe. MaƘalar da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani kan Adabin Bakan Hausa don karrama Farfesa Ɗandatti AbdulƘadir, Kano: Jami’ar bayero a ranakun 2-5 ga Afrilu, 2013.
Ɗangambo, A. 1978. Kitsen Rogo. Zaria: NNPC
Ɗangambo, A. A. 1984. Rabe-Raben Adabin Hausa Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa. Kano: Kamfanin Triumph, Gidan Sa’adu Zungur
Garba, M. T. 2007. Fitsarin FaƘo. Zaria: NNPC
Gidan Dabino, A. A. 1990 In Da So Da Ƙauna. Kano: Nuraddeen Publication
Gusau, S. M. 1984. Adabin Hausa Na Gargajiya: Ma’anarsa Da Yanaye-Yanayensa. MaƘalar da aka gabatar a taron raya harshen Hausa wanda Ƙungiyar Hausa ta Makarantar Tarbiyyar Malamai Mata Ta Arbiyya (W. A. T. C), Maru ta shirya ranar 17-7-1984.

Imam, A. A. 1970. Ruwan Bagaja. Zaria: NNPC

Katsina, M. M. 1982. ZaƂi Naka. Zaria: Gaskiya Corporation Ltd

Katsina, S. I. 1980. Mallakin Zuciyata Zaria: NNPC

Katsina, S. I. 1982. Turmin Danya. Zaria: Gaskiya Corporation Ltd

Katsina, S. I. 2010. Tura Ta Kai Bango Zaria: NNPC
Ƙamusun Hausa 2006. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero

Malumfashi, A. I. 2010. Hausa Literature At 50: The Interface Of Tradition, Arab and Colonial Heritages, Takardar da aka gabatar a taron cikar Nijeriya shekaru 50. Jami’ar Port Hacourt, Nijeriya.

Muhammad, Ya. M. 2005. Adabin Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press, Samaru

Mukhtar, I. 2004. Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai. Kano: Adamu Joji Publishers

Sheme, I. 2007. ‘Yartsana. Kaduna: Informart Publishers
SIM, 1938. Ka Ƙara Karatu. Jos: Sim Bookshop
Yahya, A. B. 1997. Jigon Nazarin WaƘa. Kaduna: Fisbas Media Services

Yahaya, Y. I. 1988. Hausa A Rubuce : Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC

 www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments