Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa na Farko Kan ‘Al’ummar Hausawa, Harshe Da Tarihi: Jiya, Yau Da Kuma Gobe’ da ƙungiyar Malamai Manazarta Hausa Kaduna 2014 ta shirya wanda za a yi a Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya da Ilimin Harsunan, Jami’ar Jihar Kaduna, Kaduna a ranakun 22-25 ga watan Mayu, 2015.
Na
Umar Aliyu Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07063532532, 07014529336
ƙibɗau: aliyubunzaumar@yahoo.com
Da
Abdulbasir Ahmad Atuwo
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07032492269, 08084298903
ƙibɗau: atuwoaa@yahoo.com
Tsakure
Adabi fage ne babba da ake iya hango kowane abu da ya shafi rayuwar Bahaushe.
Wayon Bahaushe na cikin muhimman batutuwan da suka zama ruwan–dare cikin wasu
sassan littattafan adabin Hausa, musamman littattafan adabin Abubakar Imam.
Wannan wayo ya ƙunshi ko dai dabara don fitar da kai, ko ceton wani ko wasu
jama’a, ko cutar wani, ko wani hali na girma don birgewa da samun karɓuwa ga
wasu mutane. Dukkan waɗannan nau’o’i ko matakan wayo ana amfani da su domin a
tantance Bahaushen asali a muhallin zamantakewa da wasu ƙabilu. Manufar wannan
maƙala ita ce duba cikin adabin Abubakar Imam don sharhin yadda Bahaushe ya
nuna kansa ta hanyar wayo ga wasu ƙabilu da suka yi tarayya ta wani lamari.
1.0
Gabatarwa
Wayo hikima ce da mutum yake amfani da ita don ya fitar da kansa daga wata
matsala ko ya sami wani abu na amfani ko kuma wani lokaci ya yi zamba ga wani.
Bahaushe mutum ne da Allah ya yi wa arzikin wayo cikin rayuwarsa. Duk inda
Bahaushe ya sami kansa a zamantakewa, wayo na kasancewa kan gaba da ake iya
gane shi kai tsaye. Wannan ya sa wani lokaci har wayon nasa kan zamar masa
wauta, ya jefa kansa cikin matsala da sai ya sake shiri, ya kintsa wani wayo,
sannan ya samu wata mafita. Da yawa a sassan adabin Hausawa akan ci karo da
yadda suke kallon wayo cikin hikimarsu. Marigayi Abubakar Imam fitaccen
marubuci adabin Hausa ne da masana da manazarta suka yi rubuce-rubuce masu yawa
kansa. Alhaji Imam marubuci ne da yake sakaɗa lamurran wayo cikin adabinsa.
Hasali ma, wayo kan kasance ruhi ko ƙashin bayan warware jigogin wasu labaran
nasa. Yana amfani da hikimar wayon Hausawa ga wani tauraronsa domin ya nuna
yadda Bahaushe ya kai gaya ga hikima fiye da sauran ƙabilun da yake hulɗa da su
na kusa ko nesa. A wannan maƙalar muna son duba yadda wayon Bahaushe ya fito
cikin adabin nasa.
2.0
Ma’anar Wayo
Kalmar wayo na ɗaukar ma’anoni daban-daban gwargwadon yadda aka sarrafa ta
cikin zance. Akwai masana da manazarta da suka bayar da ma’anar wayo ta fuskoki
da dama.
Skinner (1999) ya fassara kalmar wayo da:
‘Hankali, ko kangado, ko fahimta, ko basira.’
A cikin ƙamusun Hausa (2006), wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero Kano, an kawo ma’anar wayo da cewa:
‘kyakkyawan shiri, ko hikima, tsari.’
Hornby, (2006), shi kuma sai ya bayar da ma’anar kalmar da cewa:
‘Gane, ko fahimta, ko hasashe, da tunani a kan wasu abubuwa, ana danganta wannan
ga mutum ko dabba.’
Mish da Promila (2010), su kuma su kuma cewa suka yi:
‘Fita, ko kuɓuta, ko iya warware matsaloli da aka shiga, ta hanyar yin amfani
da ilmin yau da kullum, ko kuma goguwa da harkar rayuwa’.
Shi kuma Mu’azu (2014), ya kawo ma’anar wayo da cewa:
Wayo na nufin dabara, ko basira, ko sanin makamar al’amurra, ko samar wa kai
mafita (kuɓuta) idan an shiga wani baƙon yanayi
Ta la’akari da waɗannan ma’anoni, ana iya fahimtar cewa, wayo yanayi ne na
rayuwar Bahaushe da ke zo masa kai tsaye cikin sauri don tattara hankalinsa da
tunaninsa wuri ɗaya, ya cimma wata manufa da ya sa a gabansa cikin sauƙi. Da
wannan yake ceton kai ko yaudara ko kuma neman matsayi. Kishiyar wayo ita ce
wauta. Ba wani wuri da za a nuna wayo face sai an sami wauta ta bayyana. Sau da
yawa Bahaushe kan nuna wayo don ya fito da wautar wani a fili. Bari mu dubi
ma’anar wauta don daidaita wannan nazari.
3.0
Ma’anar Wauta
Wauta kalma ce da Bahaushe ke ƙyamar a danganta masa. Kalma ce da ke nufin
shashanci ko rashin hankali ko rashin natsuwa (CHCN, 2006). Bunza (2014), ya
nuna wauta a matsayin kalmar da ba ta daidaitu ɗaram ga sikelin hankali ba,
kuma ba ta hau buzun hauka sosai ba. ƙa rashin girma ko rashin kyautatawa.
Wauta ta ƙunshi dukkan wani hali na rashin kirki da rashin girma ko rashin
kyautatawa.
Hausawa mutane ne da ke kallon kowace ƙabila da wani abu na wauta. Wannan ya sa
kusan kowace ƙabila akan ci karo da wani abu na adabin Hausa da ke nuna
wautarta a fili ko da kuwa tana riya wayewar kai a duniya. Akwai ƙabilun da
Bahaushe ya haɗa zamantakewa da su, kuma ya nuna wautarsu cikin wasu labaransa.
ƙabilu kamar Fulani da Buzaye da Nufawa da Yarbawa da sauransu duka akwai wasu
labaru daban-daban da ke nuna wautarsu. Kowace ƙabila akwai wani abu da
Bahaushe ke kiyayewa game da ɗabi’arta wanda ta kansa yake fitar da wautarta.
Idan aka yi la’akari da wannan, yana nuni yadda Bahaushe yake kallon wasu
al’ummu wawaye. Wannan ya sa yake ƙoƙarin nuna kowace al’umma yana da basirar
da zai iya yi mata wayo don ɗayan abu uku: ko ceton kai, ko zamba, ko kuma ya
sami wani matsayi.
4.0
Wayon Bahaushe A Mahangar Adabin Abubakar Imam
Abubakar Imam marubuci ne da yake sakaɗa halayyar Hausawa da yawa cikin
rubuce-rubucensa. Wayon Bahaushe na cikin muhimman abubawa da yake amfani da su
domin warware wasu jigogin labaransa. A wannan wuri muka duba irin matakan
wayon Hausawa da ya yi amfani da su domin cimma wata manufa ta warware jigon labarinsa.
Waɗannan su ne ceton kai ta cikin dabara, da cuta ta hanyar zamba cikin aminci
da kuma neman matsayi ta hanyar halin girma.
4.1
Dabarun ceton Kai
Wayo ne da Bahaushe yake yi ya ceci kansa ko wani daga cikin wani hali na
matsuwa da ya shiga. Ta wannan ceton ne akan yi amfani da wasu dabaru da masu
ban mamaki da kuma nuna wayon Bahaushen asali.
4.1.1 Iya Ruwa Fid Da Kai
Wannan wata dabara ce da Bahaushe ke amfani da ita ya ceci kansa daga cikin
wata matsala. Ta wannan wayo ne mutum kan yi amfani da hikima don ya taimakin
kansa, ya fitar da kansa ko wani daga wani hali na ƙaƙa-ni-ka-yi da ya shiga. A
wannan hali mutum kan yi amfani da dabara ko hikima ko fasaha cikin ruwan
sanyi. Wannan dabarar na iya kasancewa ta magana ko wani aiki da za a iya gani
ko jin samatarsa. Bahaushe mutum ne da Allah ya yi wa dabarar da yake sarrafa
tunaninsa, ya samar da wata mafita a wani halin matsuwa da ya shiga. Wannan ya
sa yake ganin mutumin da ba ya da dabara bai cika mutum na haƙiƙa ba. Dabarar
Bahaushe ta iya ruwa fid da kai ta kasance wani muhimmin ado ga adabin Abubakar
Imam. Ga misali, a cikin littafin Ruwan Bagaja, akwai wurare da dama da
Bahaushe ya yi amfani da dabara ya ceci kansa kamar a shafi na 13 inda Alhaji
Imam ya shiga hali mawuyaci wanda sai da dabara zai iya ceton kansa da abokin
tafiyarsa. Mahaukacin raƙumi ya bi su suka haye ice, ba ruwa, ga rana, ba kowa
da zai taimake su. Ga yadda aka kawo batun:
...Muna cikin tafiya a daji, sai wani mahaukacin raƙumi, amale, ya biyo mu baki
buɗe. Muka sheƙa wurin wata itaciya muka hau. Shi kuwa raƙumin ya tsaya nan
gindin itaciyar yana jira wai sai mun sauko, ya tasam mana. Muka rasa yadda za
mu yi tun safe har azahar, ga shi kuwa cikunammu suna ta kiran ciroma. Can zuwa
la’asar sai na ga waɗansu Filani za su yawon sharo. Da dai na hange su kan
hanya, sai na ce, ‘Kai masu tafiya, uwaku.’
Ka san Bafillace kan baƙin rai, daga can kuwa sai suka nufo mu da gudu, wai su
ji dalilin da ya sa na zage su. Da dai raƙumin nan ya ƙyalla ido ya gan su, bai
sake komawa ta kammu ba, sai ya ce da ku aka gama mu. Kowanne ya ranta, suka yi
dawa! Mu kuwa muka sauko, muka yi tamu hanya..’
Raƙumi dabba ce abin tsoro bale ma mahaukaci. Ba yadda za su yi da shi, dole
suka haye ice. A can saman ice suka ɗauki lokaci ba wanda ya biyo ta wurin bale
ya taimake su. A irin wannan hali suka ga Fulani. Fulani mutane ne da Hausawa
ke dangantawa da rashin wayo da zafin rai, ga kuma saurin fushi. Sanin wannan
hali nasu ya sa ya yi amfani da basirarsa ya zage su. Idan ya nemi ceto Fulanin
za su zo ne cikin natsuwa. Wannan zai sa su lura da mahaukacin raƙumi su yi ta
kansu. Wayon da ke nan shi ne ya husata su, su zo ido rufe, shi kuma raƙumi ya
bi su. Wannan ya nuna dabarar Bahaushe ta kira wa wani ruwa, shi kuma ya bi ta
kai ya gudu.
4.1.2 Ba A San Maci Tuwo Ba...
Wani nau’in wayo ne da Bahaushe ke amfani da shi domin fito da hikimarsa a
fili. A irin wannan wuri ne ake samun wata gaggaƙa tsakanin mutum biyu kan wani
abu ɗaya wanda dole mutum ɗaya zai tsira da shi, ko kansa. Bahaushe na son
shiga irin wannan gaggaƙa domin ya nuna basirarsa, ya tsira ta hanyar da ba a
zaton kuɓuta daga gare ta. A cikin Littafin Ruwan Bagaja, a shafi na 16-17
Abubakar Imam ya kawo irin wannan gasar, ya kuma yi amfani da zurfin wayon
Bahaushe ya yi wa tauraronsa mafita, ya ceci kansa daga wani taliki mai suna
Zadoro ɗan Zotori. Alhaji Imam ya haɗu da wannan taliki ne a wani gari mai suna
Baku kusa ga teku. Zandoro ɗan Zantori wani mutum ne ɗan ƙabilar Iwaja ɗan Unƙa
wanda ya yi zamani da Annabi Nuhu (AS). Yana da tsawon zira’i saba’in. Wannan
mutum ne Alhaji Imam ya yanka sansa da alkawarin zai taɓa kansa, ya kuma san
hakan ba ta yiyuwa sai da wani wayo dole. Ga yadda batun yake:
...Can an yi kwana biyar sai wata dabara ta faɗo mini. Rana ta bakwai tun da
jijjifi, sai ga shi zalam-zalam, na dube shi na ce, ‘Wai Zurmi!’
Mutane sun dafo shi don su ga yadda zai canye ni. Da ya zo, ya ce, ‘To, fito,
alkawari ya cika.!’
Sai na ce masa, ‘Dakata kaɗan, in gama lallabce bangon ɗakin nan da ya tsage da
damina.’
Ya ce, ‘Kai, yaya ake ɗinkin bango?’
Na ce, ‘Ai ba wuya a garinmu, leƙo ka gani.’ Sai ya cuso kai don ya gani.
Sai na yi farat na taɓa kansa, na ce, ‘Ah, na taɓa!’ Mutane suka ce, ‘I, ya taɓa!
I, ya taɓa!’
Idan aka dubi yadda lamarin yake za a ga cewa, Alhaji Imam ya sha ta fi
cikinsa. Ba wani abu da ya rage masa sai tunanin dabara. Da ma Bahaushe na
cewa, dabara ƙafa. Wannan ya sa ya shigo da dabarar lallabce bango. Ɗinkin
bangon ɗaki abu ne da ba a san shi ba duk da yake an yarda bango na tsagewa
kamar yadda ƙwarya take tsagewa. Abin lura a cikin zancen shi ne, Alhaji Imam
ya danganta aikin ɗinkin bango da garinsu kaɗai domin kada wani ya yi musun yin
haka domin duniya faɗi ke gare ta. Abin da yake a nan, sau da yawa ba shi yake
can ba. Shi kuma Zandori jin ɗinkin bango ya sa shi mamaki har ya manta da taɓa
kansa, ya nemi ya ga yadda ake yi. Shi kuma Alhaji Imam ya san ba a gani sai
tare da sunkaya kai domin idanu a ɓangaren kai suke. Wannan ya sa Alhaji Imam
ya nemi Zandori ya sa kansa cikin ɗaki don ya gani. Idan aka yi la’akari da
wannan wuri za a ga cewa, wayon da ya nuna a nan shi ne na ƙirƙira abin da ya
saɓa wa hankali don ya ceci kansa. Wannan ya sa Zandori ya yi hasarar sansa,
shi kuma Imam ya ci banza.
4.3
Shigo-Shigo Ba Zurfi
Wayo ne da Bahaushe yake amfani da shi domin cimma wata manufa da ya sa a
gabansa. A wannan wayo Bahaushe kan yi maraba da wani da ke nufin cuta masa ta
yin amfani da daɗin baki da shimfiɗar fuska. A shafi na 28 an nuna irin wannan
wayo inda Alhaji Imam ya ceci kansa daga ɓarawo. Ya sauka a wani gari Miska a
gidan wani malamin addini. Wata rana da dare ɓarawo ya shigo ɗakinsa. Ganin ɓarawon
ya sa ya yi tunanin dabara, ya kuma ceci kansa da ita:
Da ya matso kusa da ni sai na tashi, na ce, ‘Maraba, maraba. Ga tabarma nan ka
zauna. Ashe za ka zo ka ƙi gaya mini tun da rana da muka gamu kasuwa?’ Na yi ta
yi masa magana kamar na san shi.
Da ya ga haka, sai ya zauna yana tuna inda ya san ni. Ya juya wajena ya ce,
‘Ina ka san ni?’
Na ce, ‘A! Ai tun tuni na san ka, bari ta kai ma duk danginka na san su, duk
kuwa ma sun san ni. Na sha gamuwa da ‘yanuwanka ƙwarai har sun tambaye ni
labarinka, ina cewa ban sani ba. Yau da dare Allah ya nufa sai mun sadu.’
Ya sake dubana daga ƙasa har bisa, ya ce, ‘Kai in ka san ni ina sunana?’ Sai na
ɗaga kai sama. Na yi ihu ƙwarai na ce, ‘Ai sunanka ɓarawo!’
A nan Alhaji Imam ya lura da haɗarin da ke gabansa. ƙato, kuma ɓarawo da bai
san wane shiri yake da shi ba ya shigo masa ɗaki. Wannan ya sa ya ƙi kowace
irin kiza-kiza ko barazana. A maimakon haka sai ya bi ta dabara cikin ruwan
sanyi ya kori ɓarawon. Bahaushe ya san daɗin baki abu ne da ke sa jikin kowane
mutum sanyi. Wannan ya sa ɓarowan da kansa ya buɗa wa Alhaji Imam kafa ta yin
kuwa da sunan faɗar sunansa. Da wannan ana iya tantance wani wayon Bahaushe na
daɗin baki don yi wa kai mafita da ceto a yanayi mawuyaci.
4.2
Dabarun Sata
Sata wani wayo ne ko wata dabara ce ta raba mai abu da abinsa ko dasaninsa ko
ba da saninsa ba, amma ba da son ransa ba bale yardarsa (Bunza, 2014). Bahaushe
mutum ne da ke amfani da dabaru don yin sata idan ya sami damar yin haka. Akwai
Hausawa da yawa da suka ɗauki sata wata ƙawa ko sana’a. Wannan ya sa wasu ƙabilu
masu yawa suke tsoron sake jiki da Hausawa da kuma ba su amana. Akwai dabaru da
Bahaushe ke amfani da su domin ya yi sata ga wani ko wasu. Dabarun sun haɗa da
shigar burtu da wayon wayo da sauransu.Waɗannan dabaru ana samun su wurare da
dama cikin adabin Abubakar Imam.
4.2.1 Shigar Burtu
Wata dabara ce da ake amfani da ita domin a yi sata. A irin wannan shigar ce
Bahaushe ke sanya sutura irin ta wasu mutane da aka sani da wani hali ko
yanayi. Akan yi wannan shigar ce domin a amince masa, aɗauke shi cewa shi ma ɗaya
ne cikin waɗancan mutane masu wannan shigar. Wannan zai sa a karɓe shi, a sakar
masa jiki kamar waɗancan mutane, sai daga ƙarshe ya yi sata, ya gudu. A cikin
littafin Ruwan Bagaja, a shafi na 7an kawo irin wannan dabara inda aka ce:
Bayan na yi kwana saba’in ina tafiya, sai na isa Tamtubu. Na yi shiri irin na
fatake, na isa gun Sarki, na ce ni falke ne, kayana suna baya, za su zo bayan
kwana uku...Kullun da yamma sai in sami taro, in sayo miya, in bi ƙofar gidan
da na sauka, in warwatsa ko’ina. Abin da ya sa nake haka, don ina da wani aboki
ne attajiri’
Alhaji Imam ya isa Tambutu ba ya da komai, kuma bai bar komai a baya da yake
zuwa ba. Isarsa wurin Sarki, maganarsa ta farko ya saka cuta (ƙarya). Sarki
Haka kuma kai tsaye ya shirya wa abokinsa zamba cikin aminci. A nan ma ƙarya ya
shirya, ya yi wa wanda ya amince da shi wayo, ya karɓi dukiyarsa. Abin da ya sa
ya sami wannan amincewa shi ne, shigar fatake da ya yi, ya kuma yi iƙirarin shi
falke ne. Ganin wannan shiri nasa ya sa Sarki da attajirinn suka ba shi amana.
A hankali ya kwashi kuɗin attajiri da sunan jiran shanunsa a matsayin shi falke
ne. Wannan na nuna Bahaushe mutum ne da ya naƙalci wayon shigar burtu, ya
shirya yaudara da cuta bayan an amince masa cikin zamantakewa, kuma idan aka ba
shi amana zai yi amfani da wayonsa na zamba cikin aminci ya yi cuta cikin
amanar.
4.2.2 Wayon Wayo
Wata hanyar sata ce da Bahaushe ke amfani da ita ya yi wa wani mai jin wayo
cuta. A duk lokacin da aka sami wani mutum da ke jin wata baiwa ta wayo, to
akan sami Bahaushe ya bi ta wannan wayo nasa, ya yi masa wani wayo cikin ruwan
sanyi. Ta wannan wayon wayo ne Bahaushe kan rungumi aradu, ya kutsa kansa cikin
wata kasada, daga ƙarshe ya yi sata cikin wannan hali. A shafi na 32 an kawo
irin wannan wayo inda ya ce,
Dare na yi, sai na sayi wata sharɓeɓiyar wuƙa na shiga gari yawon sata, sai na
kawo ga wani babban zaure, na tarar da waɗansu samari sun kunna fitila suna ƙirgar
dukiya, don gobe Salla, sun kuwa rufe ƙofar gidansu. Ko da na ga haka, sai na ƙwanƙwasa
ƙofar, wani daga cikinsu ya ce, ‘Wane ne nan?
Sai na ce, ɓarawa ne.’
Suka ce, ɓarawo?’
Na ce, ‘I’
Suka ce, ‘To, da wacce ka zo?’
Na ce, ‘Na zo ne don in yi muku sata.’
Sai wani daga cikinsu ya ce, ‘To, zo saci!’
Ni kuma na ce, ‘Ku buɗe ƙofar zaure mana ku gani in ban sata ba.’
Sai babbansu ya tashi da fushi, ya buɗe zauren. Ni kuwa da ganin ya buɗe sai na
faɗa ciki fagagam, na kashe fitilar, na dubi bangon na karta da wuƙa, na koma
gefe guda na faɗi ris, na ce, ‘Wayyo Allah, ya kashe ni. Ko da suka ji haka,
sai suka yi tsammanin wani ɗan’uwansu ne na soka. Sai na ga duk sun yi cikin
gida da gudu. Na tashi na naɗe kayansu sarai, na bar garin.’
Idan aka dubi wannan jawabin, Alhaji Imam ya yi amfani da wayon wayo ne ya
yaudari samarin, ya yi musu sata. Asali an yi masa sata ne, kuma samarin nan ba
su da labari. Ɗaukar fansa a kansu ba daidai ba ne. Wayon su samarin shi ne
yawansu da suke ganin za su rinjayi ɓarawon da ƙarfi. Wayon da shi kuma Alhaji
Imam ya yi na gaggauta kashe fitila da karta yuƙa ga bangon ɗaki da faɗar wayyo
ya kashe ni ya sa samarin suka tsorata, suka bar kuɗinsu, shi kuma ya kwashe.
Yana sane cewa, kowane mutum yana tsoron mutuwa. Ya san da ya bari samarin suka
gan shi, ko kuma ya tsaya kokawa da su da bai kai ga buƙatar da ya je da ita ta
yaudarar samarin, ya yi musu sata ba. Falsafar da ke nan tana nuna Bahaushe
mutum ne mai fasahar gaske da yake sarrafa ta ya yi nasara ko da cikin taron
jama’a ne.
4.3
Wayon A Ci
Wayon a ci wani nau’in wayon Bahaushe ne da yake amfani da shi domin ya yi wa
kansa wata kafa ta samun abinci da wani matsayi cikin mutane. Domin nasarar
wannan wayo, Bahaushe yakan yi amfani da dabaru irin na halin girma da kum ci
da addini.
4.3.1 Halin Girma
Halin girma na nufin karimci ko kyauta ko shimfiɗar fuska ko kuma duk wani abu
na sadaukar da kai don amfanar da wani ko wasu. Halin girma wayo ne da ke sa a
amince da mutum a ja shi ga jiki, a ba shi amana da yarda. Duk lokacin da mutum
ya yi wani abu na halin girma za a kyautata masa zaton zama zarumi, kuma abin
yarda. Irin wannan wayo abu ne sananne cikin rayuwar Hausawa.
Hausawa mutane ne da ke nuna halin girma cikin zamantakewarsu da kowa. Bahaushe
na ba abu baya ko da yana son sa don tsammanin ya sami wanda ya fi shi a can
gaba. Wannan ya sa har karin maganar Hausa ke cewa, ‘Aje alheri bayanka, ka
tsince shi gabanka.’ Abubakar Imam ya yi amfani da irin wannan wayo don cimma
nasarar warware zaren labarinsa a wurare da dama. Ya yi amfani da halin ga
tauraronsa Alhaji Imam da ke cikin littafin Ruwan Bagaja a shafi na 10 inda ya
kawo cewa:
Ina tafiya sai ga wani yaro yana gudu za shi wurin biki. Na kira shi na ce,
‘Kai samari, yau garin lafiya?’
Yaron ya ce, Ɗan’mori? Sarki aka kawo wa mata yau.
Na ce, ‘Daga ina?’
Yaron ya ce, ‘’Yar Sarkin ƙaryatun Ni’am ce aka gama su.’ Ko da na shiga garin,
ban ko zauna ba sai ƙofar fada wajen da ake biki. Na shiga biki, na yi ruwa, na
yi tsaki, kamar ƙanena aka sa a lalle. Nan da nan duk na shahara ga maroƙa,
suka tambayi sunana. Na ce, ‘Alhaji Imam.’ Ana biki da dala dala. Amma ni da
fam guda guda, nake yi.
Wannan shagali da na yi ya sa Sarki ya yi maraba da ni. Muka yi abota da ɗan
Sarki, dare kaɗai ya ke raba mu.
Gaisuwa ko ina daga gidajen fadawa, da attajirai, da malamai da sauran manyan
gari. Da haka fa duk na azzama cikin ƙasar. Saboda haka wurina masu laifi ke
kamun ƙafa. Masu son sarauta gare ni suke nemanta.’
Idan aka yi la’akari da abin da Alhaji Imam ya aikata sai a ga wani nau’in
wayon Bahaushe ya nuna ƙarara. Yana cikin wayon Bahaushe ya yada abu don ya
tsince shi gaba. Alhaji Imam ya kau da kai ga kuɗinsa, ya yi bikin da ba a
gayyace shi ba, bai kuma san kowa ba ciki. Ya watsar da kuɗinsa ga maroƙa. A
maimakon ma ya yi yadda kowa yake yi, sai ya yi abin da ya fi na kowa don a san
da shi. Wannan wayon ya sa ya sami farin jini da karɓuwa ga sarki da ɗansa har
ya shiga cikin manyan fada da ake kamun ƙafa da neman alfarma wurinsu. Haka ne
da ma gurinsa.
4.3.2 Ci Da Addini
Wani wayo ne da wasu Hausawa suke amfani da shi su nemi abinci. A irin wannan
wayo ne wani ke sake kamannunsa da halayensa, ya ɗauki na wani mai addini.
Yawanci masu irin wannan dabara idan suka sauka wani wuri, suka kuma lura
mutanen wurin sun damu da addini, sai ya tattara kansa, ya koma kamar wani
salihin bawa ko da kuwa shi ja’iri ne. Kintsa kai da zama kamili mai addini
wani nau’in wayo ne na Bahaushe idan yana son ya sami matsayi ga wani ko wasu.
Bahaushe mutum ne mai fasahar sauya kamanninsa ya yi irin na wasu mutane don
cimma manufa. Hausawa da yawa sukan yi irin wannan sauya kama, su yi shiga irin
ta mutanen Allah domin su sami karɓuwa da amincewa ga wani da sunan su mutanen
Allah ne. Wannan ke sa a amince da su, su nemi abinci da wannan hali. Da irin
wannan kamar sai mutanen wurin su girmama shi, su riƙa neman fatawa kan
lamurran da suka shafi addininsu. Idan aka ci karo da su masu ƙarancin sani ne,
sai ya zan duk abin da ya gaya musu, da shi za su dogara. Abubakar Imam ya kawo
irin wannan wayo lokacin da Alhaji Imam ya sauka garin Nasarawa ya shiga rigar
malamai waliyya kamar haka:
..Na tafi wurin Sarki na sauka, na biɗi wani masallaci na kame, ba ni kome sai
jan tasbaha. Duk garin aka yi ta kawo mini sadakar abinci iri-iri, sai na taɓa
ko loma biyu in ƙi ci. Da ma na yiwo guzurin ƙaton buhu cike da nakiya da
gurasa, shi nake ci kullun. Abin da ya sa ba ni cin abinci da ‘yan garin suka
kawo mini sadaka, so nake su mai dani Waliyyi ne, su riƙa girmama ni. Bayan
kwana kaɗan kuwa suka soma tsammanin haka nan. Kowa ya kawo abincinsa sai ya ce
in sa masa ko loma don ya sami tabarrukin hannuna.
Haka na yi zamana garin nan abin girmamawa.Idan za a yi wani abu na addini
kamar su salla, sai su ce in shige gaba. Ni kuwa ka san inda jahili duk ya kai
na kai, saboda haka ko sun yi juyin duniyan nan sai in ƙi. Kowane malami kuwa
aka sa, sai ya riƙa nonnoƙewa, don yana tsoron kada ya yi ɗan ɓata, ga kuwa
masu abin watau ni’ (shafi na 30-31).
Alhaji Imam a wannan wuri ya yi kama ce irin ta masu tsoron Allah. Ya tare
Masallaci ga tasbaha yana ja koyaushe. Irin wannan siffa ce ta mutanen da ke da
gudun duniya (zuhdu) da neman kusanci kawai da Allah. Da wannan wayo ake
amincewa da su, aja su jiki, daga ƙarshe su yi yaudara, wato abin da aka fi
sani 419. A nan da wannan wayo ya sami kan mutanen garin har suka ɗauke shi
wani mutumin Allah, suka riƙa kawo masa sadakar abinci don neman albarka. Don
ya tabbatar da wayonsa ya sa ba ya cin abinci mai yawa don ya ƙara tabbatar da
waliyantakarsa. Wannan nau’in wayo na ci da addini sananniyar ɗabi’a ce ga
Hausawa masu yawa.
4.4
Kafin Ka Ga Biri...
Wani wayo ne na sanin dabarar mai dabara. A irin wannan wayo ne wani mutum ke
shirya wata dabara ko don ya cuci wani, ko kuma ya kama shi, shi kuma wanda aka
shirya wa dabarar ya san dabarar, ya kuma naƙalce ta. Bahaushe mutum ne da yake
da hikimar hangen nesa da ɗaukar hannu a duk lokacin da ya sami wani mutum ya
shirya dabararsa. Da wannan wayo ne yake kintsa kansa, ya aje hankalinsa, ya yi
wa wani lamari dogon nazari kafin ya auka masa.
A shafi na 10, Abubakar Imam ya kawo tauraronsa, Alhaji Imam ya yi nasarar kuɓuta
daga tarkon ƙwara. ƙwara (farar fata) mutum ne da ke jin yana da wayo. Duk
wayon ƙwara Bahaushe na iya yi masa wayo cikin ruwan sanyi don ya yi wa kansa
mafita, ko kuma ya yi yaudara. Ga yadda aka kawo wayon Alhaji Imam ga ƙwara;
A kwana a tashi, sai na yi gaba zuwa Sasa. Da shiga garin sai Allah ya yi mini
gamo da katar, na sauka gidan wani ƙwara mai sule. Na kama kaina sai ka ce wani
mummini. Da ƙwara ya ga halina, sai ya fara jana a jika. Bayan ‘yan kwanaki kaɗan
ya mai da ni yaronsa, ya sakan mini al’amuransa duka, na shiga cikin dukiyar
ina bundum bundum, ba ni aikin fari balle na baƙi, sai dai ko da yaushe in
wanke goma in tsoma biyar!’
..... Da ƙwara ya ji haka, sai ya fara ƙoƙarin da zai kama ni, ya sa a ɗaure,
ya haƙa mini wannan tarko nan in kuɓce nan, ya haƙa nan in kuɓce nan. Da ya ga
haka, ran nan sai ya aiko a gaya mini ya mutu. Aka zo aka gaya mini, aka
rarrashe ni in je in gani, don ba shi da ɗa ba shi da jika sai ni. Ni kuwa na
san halin ƙwara da wayo. Ban dai ƙi ta mutane ba, sai na tafi. Aka ce ga ɗakin
can, ko rufe shi ba a yi ba, sai na zo don ni ne ɗansa. Na leƙa ta taga, sai na
gan shi kwance baki buɗe. Shi kuwa abin da yake so in shiga ɗakin ne ya kama
ni.’
Ko da na dube shi da kyau sai na yi sai na yi sansanar mutuwarsa, sai na ce,
‘Allah Sarki! Amma ban yi tsammani ya mutu ba.’
Wanda ya kira ni ya ce, ‘Subhana lillahi! Don me?
Na ce, ‘Don na ji an ce ƙwara ba su mutuwa da baki buɗe sai a rufe. To, ga
wannan ƙwara nasa a buɗe.!’
Da ƙwara ya ji jawabina, sai ya rufe baki wai don in yarda ya mutu; sai ka ce
ni gaula ne. ‘Ashe, wanda ya mutu ya taɓa motsi, balle har ya rufe baki?’ Ko da
na ga haka, sai na yi waje.’
Idan aka dubi labarin za a ga cewa, Alhaji Imam ya riga ya cuci ƙwara, kuma ba
shakka ya san idan aka kama shi zai fuskanci hukunci. ƙwara ya shirya masa
tarko iri-iri yana tsallakewa. Wannan ya sa ya riƙa nisa da duk inda zai haɗu
da ƙwara. Yana cikin haka sai aka gaya masa mutuwar ƙwara wanda shi ne maƙurar
wayon ƙwara na kama Alhaji Imam. Tilas ta sa ya yi dogon tunani. Ya karɓa kira,
ya kuma amince ya je ya gani, amma a cikin shakku. Wannan ya sa ya ƙi shiga ɗakin
da mamacin yake kwance sai dai kawai ya kula da yanayin da ya sami mamacin. A
tunanin ƙwara, Alhaji Imam ba zai tsallake wannan tarko ba. Shi kuma Alhaji
Imam ganin bakin ƙwara buɗe sai ya kawo zancen ƙwara ba ya mutuwa baki buɗe.
Idan aka dubi wannan zance sai a ga cewa, Imam ba cewa ya yi ba a mutuwa baki
buɗe ba, cewa ya yi ‘ƙwara ba ya mutuwa baki buɗe’. Abin lura a nan shi ne,
ambaton ƙwara ba ya mutuwa baki buɗe wata dabara ce ta koɗawa ya yi amfani da
ita wadda ya san za ta iya yi masa mafita. Shi ƙwara ya ɗauki batun kamar wani
ban girma, sai ya rufe bakinsa. Rufe bakin sai ya bayyana wautarsa a fili,
domin ya ƙaryata kansa, shi kuma Imam ya gudu. Wannan ya nuna hikimar Bahaushe
ta kowane abu yana yi masa duba cikin tsanaki, sannan ya yi amfani da hikimarsa
don nuna wayonsa da yi wa kansa mafita.
Ita ma wata yarinya mai suna Jamilatu da irin wannan wayo ne Alhaji Imam ya yi
nasarar auren ta. Ya shiga neman ta ne tare da wasu samari biyu, suka zama su
uku. Yarinyar ta rasa wanda za ta zaɓa, saboda haka ta shirya mutuwar ƙarya don
ta tantance mai son ta na haƙiƙa. Mahaifinta ya je ya gaya wa sauran samarin
biyu cewa Jamila ta mutu, suka nuna rashin damuwarsu har suka ce ‘Gwai’ Shi
kuma Alhaji Imam da aka same shi sai ya nuna baƙin cikinsa. Ga yadda aka kawo
wannan batun;
Tsoho ya sa kai ya fita, ya nufi gidana. Ko da na ji wannan jawabi, sai na yi
shakkar mutuwan nan, ko da ya ke na san ikon Allah ya fi da haka. Nan da nan
sai na ɓarke da kukan ƙarya. Na ruga na sawo tufafi, na nufi gidan, ina
matse-matsen ƙarya. Da na isa gidan, na tarad da ita a kwance. Sai na rungume
ta, ina salati. Da ta ji haka sai ta buɗe ido, ta ce a ɗaura mana aure ta yi
miji!Nan da nan aka ɗaura mana aure da ita. Aka sa ranar biki, aka yi shagali
aka gama’ (shafi na 14).
Abin lura a nan shi ne, dabarar Jamilatu ita ce ta sami mai son ta da gaske.
Wannan ya sa ta shirya mutuwa wadda ba kasafai ake ƙaryar ta ba. Shi kuma
Alhaji Imam zamansa Bahaushe ya san kowace mace namiji ɗaya yake auren ta a ƙa’ida.
Ya san dole a nemi yadda za a sami mutum ɗaya da zai doke sauran mabiɗanta, ya
aure ta. Wannan ya sa da aka gaya masa mutuwarta ya ɓoye hankalinsa da
shakkunsa, ya shirya kukan ƙarya.
Kukan ƙarya wani wayo ne da Bahaushe yake amfani da shi don cimma wata buƙata.
Kukan mutuwa wani hali ne na Bahaushe. Yana kuka don nuna tausayi da kuma jin
ciyo na rashin da aka yi. Idan mutuwa ba ta zan kusa sosai ga Bahaushe ba, yana
shirya kukan ƙarya don a zaci shi ma ya ji ciyo kan wannan rashi. Wannan wayo
na sa dangin mamaci su yarda da mai kukan a matsayin mai ƙaunarsu. A nan Alhaji
Imam ya shirya kukan ƙarya har da rungumar gawar don ya nuna tsananin jin ciyo
ga mutuwar Jamilar. Wannan wayo ya sa dabarar Jamilatu da mahaifinta ta tashi,
da ita da danginta suka amince shi ne kaɗai mai ƙaunarta cikin masu biɗanta.
Don haka aka aurar masa da ita shi baƙo, aka bar ‘yan gari. Wannan yana nuna
wayon Bahaushe na sanin dabarun rayuwa da zamantakewa.
5.0
Kammalawa
Idan aka yi la’akari da yadda wayo ya game littafin Ruwan Bagaja sai a ga cewa,
shi ne ya zan ƙashin bayan jan zaren labarin. Idan aka auna yadda zaren wayon
yake da rayuwar Hausawa, sai a ga cewa, wayo da aka yi amfani da shi cikin
adabin, wani abu ne da yake da ainihin sila da rayuwar Hausawa ta zahiri. Wayon
ceton kai da dabarun sata da wayon neman abinci abubuwa ne da Bahaushe ya yi
suna da ƙwarewa kansu. Kasancewar Alhaji Abubakar Imam Bahaushe, ya sa ya yi wa
adabin nasa zobe da wayo don ya nuna Bahaushe ne na haƙiƙa. Ya fito da yadda
Bahaushe ke shigar burtu ya sauya kama da daɗin baki da halin girma da kasada
da ba wani abu baya don ya kai ga buƙatarsa ta ceton kai ko cuta, ko wani
matsayi da yake dubi. Wannan ya sa marubucin bai yarda ya kawo wani mutum daga
wata al’umma da ya yi wa Bahaushe wayo ba komai kururuta wayewar kan wannan
al’umma.
Manazarta
Abdullahi A. M. (1988), Abubakar Imam: Nazarin Tubali Da Giniwar Ayyukansa na
Adabi. Kundin digiri na biyu, Jami’ar Bayero, Kano.
Abraham, R. C. (1947) Dictionary of the Hausa Language. Hodder & Stoughton
London.
Abubakar, A. I. (1988), Nazari Kan Littafin Ruwan Bagaja Da Jiki Magayi. Kundin
digiri na farko, Jami’ar Bayero, Kano.
Adamu, M. T. (1997), Asalin Hausawa Da Harshensu. Ɗan Sarkin Kura Publishers,
Kano.
Bargery, G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa ɓocabulary
Buhari, I. (1988), Nazarin Jigon Wasu Littattafan ƙagaggun Labarai Na Hausa.
Kundin digiri na biyu, Jami’ar Bayero, Kano.
Bunza, A. M. (1991) Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja, maƙalar da aka
gabatar a taron Makon Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bunza, A. M. da Noofal, M. A. (2013), Humanities In The Sub-Saharan World Ruwan
Bagaja in Perspectiɓes Eight Decades of a Hausa Masterpiece in Prose (1933-
2013). Institute of African Research and Studies, Department of African
Langugaes, Cairo University, Egypt in Collaboration with Department of Nigerian
Languages, Umar Musa Yar’adua University, Katsina, Nigeria.
Bunza, A. M. (2014), Wauta A Tunanin Bahaushe. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara
wa juna sani na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua
Katsina-Nijeriya a Tsangayar Fasaha ranar Larba, 18l6l2014.
Bunza, A. M. (2014), In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka (Muryar Nazari Cikin
Tafashen Gambo) Elkods Printing House, Cairo.
Bunza, A. M. (2006), Hoton Buzu A Adabin Bahaushe. Maƙalar da aka gabatar a
taro na ƙasashen kan Adabi da Harshe da Ilmin Harsuna, ƙarƙashin jagorancin
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato da Jami’ar Abdou Moumini Yamai, Nijar daga
ranar Larba 31 ga Mayu, zuwa 2 gatan Yuni, 2006. A Sashen Koyar Da Harsunan
Turai na Zamani, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
CNHN (2006) ƙamusun Hausa. Jami’ar Bayero, Kano.
Iliyasu, M. (1995), Gaskiya Da Raha A Cikin Littafin Ruwan Bagaja: Sharhi Ciki
DaWaje. Kundin digiri na farko, Jami’ar Bayero, Kano
Ilyas B. I. (1986) Arabic-English Dictionary. Darul Fikr Lebanon Beirut.
Imam, A. A. (1989) Ruwan Bagaja, NNPC, Zariya.
Malumfashi, I. (2009), Adabin Abubakar Imam. Garkuwa Media Services, Sokoto.
Malumfashi, I. A. M. (2005), Kama Da Wane Ba Wane Ba Ne! Kakkaɓo
Littafin Ruwan Bagaja Daga Cikin Taskar Tarihin Adabi. Cikin Mujallar Ɗunɗaye Vol. 1,
No. 2, December 2005. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Mukhtar, I. (2004) Jagoran Nazarin ƙagaggun Labarai. Benchmark Ltd, Kano.
Press Zaria.
Skinner N. (1999) ƙamus na Turanci da Hausa. Northern Nigerian Publication.
Yahaya, Y. I. (1988), Hausa A Rubuce : Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC,
Zaria.
Yunusa, M. M. (1985), ‘Kasancewar Tatsuniyar Ruwan Bagaja Tushen Littafin Ruwan
Bagaja na Abubakar Imam. Kundin digiri na farko, Jami’ar Bayero,Kano.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.