Ticker

6/recent/ticker-posts

Matakan Gudanar Da Bincike Na Ilimi 2


Na
Mannir Shehu


Gabatarwa


A ilimance, bincike na nufin aiwatar da nazari a kan wani al’amari ko abu domin fito da wani sabon abu ko inganta wani abu, ko kuma warware wata matsala domin cimma wani buri ko biyan wata buƘata. Bincike dai wani muhimmin al’amari ne musamman a fagen ilimi wanda aka fara aiwatar da shi a wajen Ƙarni na shekarar miladiya (500 BC), a matsayin wani muhimmanci lokaci na tarihi domin kuwa ko ba a wannan lokaci ne aka fara gudanar da bincike ba, to a daidai wannan lokaci ne aka sami gaggarumin ci gaba a harkar ilimin a duniya, wanda kuma bai samu ba sai ta dalilin mawuyacin bincike da masana Girkawa suka riƘa gudanar a wannan lokaci.

Ma’anar Bincike


Masana da dama sun bayar da ma’anar bincike. Bello, (2010: 1-2), cewa ya yi: “Bincike ba Ƙaramar rawa yake takawa ba a fagen ilimi ďungurugun da bincike tsararren tafarki da ake amfani da shi domin shawo kan matsalar ilimantarwa.”
Wani masanin bincike mai suna Odediran, (2007) ya ce: “Bincike ilimantarwa ce da ake amfani da ita don a gano wasu bayanai na Ƃoye a kan wata matsala ko batu.”
Onyene da Anunmu, (2006) sun ce bincike ba wani abu ba ne illa dabara ce da ake amfani da ita don a sami damar magance wata matsala.
Bincike kamar yadda kalmar ta nuna matsayin muhimmin abu ne a fannin ilimi, wanda ke nuni a kan yadda za a gudanar da nazarin wata matsala ko batu da ya shige wa wani mai binciken duhu ta yadda za a fito da shi fili a warware mk.atsalar ko a yi bayani ko zayyano shi ko kintace shi a yi hasashen abin da zai biyo bayan binciken.
Abubuwan da Ake BuƘata Ga Mai Gudanar da Bincike Ya Yi La’akari da Su
Wajibi ne ga mai bincike ya buƘaci wa ďannan matakan a wajen gudanar da bincike. Idan mai bincike ya ďauki batun da yake son ya yi bincike a kai, to ya zama
a. Batu f. Amfanin Bincike
b. Dalilin Bincike g. Amfanin Bincike
c. Hasashen Bincike h. Bitar Ayyukan Da Suka Gabata
d. Gudummuwar Bincike i. Hanyoyin Tattara Bayanai
e. Farfajiyar Bincike ko Iyakar Bincike j. Ma’anar BaƘin Kalmomi
Bari a ďauke su ďaya bayan ďaya domin a yi tsokaci a kan kmowane daga cikinsu.
Dalilin Bincike: Ana buƘatar mai bincike ya san dalilin da ya sa yake yin wannan bincike. Don haka a nan ana sa ran mai bincike zai fito da dalilan da suka sa shi ko yake son gudanar da bincike a kansu. Akan so a tafi kai tsaye a rubuta bincike, ba da tsawaita magana.
Amfanin Bincike: Dole ne mai bincike ya kasance ya san amfanin abin da yake bincike a kansa. A nan ana nufin a yi bincike wanda zai ilimantar don haka wajibi ne mai bincike ya fito da amfanin da ke tattare da binciken.
Manufar Bincike: Abin nufi a nan, mai bincike zai fito da manufar bincike da yadda za a nuna Ƃaro-Ƃaro ga inda aka sa gaba, kuma manufarsa ita ce ta ƘirƘiro wani abu sabo, ko yin gyara ko Ƙari a kan batun da ake bincike a kai da dai sauransu.
Gudummuwar Bincike: Ana buƘatar ga mai gudanar da bincike ya yi la’akari da cewa shin wane irin gudummawa ce bincike zai bayar, ko amfani da ilimin zai bayar a yayin da aka kammala gudanar da shi? Wannan ita ce tambayar da ta dace mai bincike ya amsa a nan.
Matsalolin Bincike: A nan ana Nufin ire-iren matsalolin da suka asasa gudanar da wannan bincike ko suka haifar da yin binciken. Wato wasu matsaloli ne da mai bincike ya hango dangane da batun da ake bincike a kai, kuma ake son a warware, don haka ana sa ran mai bincike zai lissafo matsalolin da suka haifar da shi binciken.
Batu: Shi ne mai bincike ya yi tunanin wata tambaya wada yake da tabaci in har ya ƘirƘiro ta to zai iya samar da amsarta gwargwadon tambayar tare da rakiyar hujjoji da dalilai ko madogara da za ta gamsar da shi kansa mai bincike, da wa ďanda za su karanta binciken ta yadda za a yaba.

Kammalawa


A wannan aiki an taƂo ma’anar bincike a taƘaice. Bayan haka, aikin ya lissafo abubuwan da dole mai bincike ya yi la’akari da su. Daga Ƙarshe aikin ya yi tsokaci a kan wa ďannan abubuwa da za a yi la’akari da su a yayin bincike.

Manazarta


Akinboye, J. O. (1999). Simple Research Methods. Ibadan: L. R. Publishers.
Bichi, M. Y. (1997). Students’ Guide to Research Methods: Kano: Debis-Co Press Publishing Company Limited.
Daramola, S. O. (1992). Research Methods and Statistical Analysis in Education for Students and Research in Tertiary Institutions. Ado-Ekiti: Petoa Educational Publishers.
www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments