1. A haifi ďa da arziki, ya fi a mutu a bar masa gado
2 Ya aka yi aka haihu marata
3. A haihu ina miji?
4. An yi gaba ďaya haihuwa da hanji
5. Ana raba ka da kiwon awaki, kana Ƙyalla ta haihu
6. Ana son wawa haihuwarsa ce ba a so
7. Ba a yi kome ba, mace ta haifi mace
8. Bari, Ƙetar haihuwa
9. Baya ta haihu
10. Duk mai haihuwa ana yi masa mutuwa.
11. Ganganci haihuwa ga damina.
12. Haihuwa mai rana.
13. Haihuwar guzuma, ďa kwance uwa kwance
14. Haihuwar tsakar dare munafukai na barci
15. In ka haifi yaro ba ka haifi halinsa ba.
16. In ka haifi yaro, ba ka haifi halinsa ba
17. Katane ciwon masu haihuwa
18. Na gaji da haihuwar ďiya rana na kashewa
19. Ƙulya ba ta haifa ďa mai ido
20. Ranar haihuwa ake guďa
21. Takaici zalla haihuwa da maƘiyi
22. Wuta ke haihuwar habďi

 

Karanta kacici-kacici

https://www.amsoshi.com/2017/07/01/kacici-kacici-da-amsoshinsu-cikin-hotuna-5/